Chapter 20 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 26

57K to 60K   out of 76.5K words

a kasan carpet kuma harzuwa lokacin kukan take bata daina ba.
dakyar daddy yasamu ya lallasheta tayi shiru sannan yace "niduk ban fahimci abinda kikayi ba mardiyya"

numfashi tasauke sannan tace "katuna da zulai 'yar uwata? wannan mutumin shine sanadin rabuwarmu da ita har abada, wannan mutumin shine sanadin kunchin da mahaifiyata take ciki sama da shekara gomq sha kuma shine sanadin rasa mahaifinmu da mukayi har abada" ta share hawayen daya zubo mata sannan tacigaba "nasan kasan komai amma Sofiyya batasan komai ba domin abin be shafeta ba, amma yanzu kam yashafeta don haka zan bata labarinmu tun yarinta" gyara zaman ta tayi sannan tafara.



*******************



Mu hudu iyayenmu suka haifa, biyu maza biyu mata, yayan kano shine babba sannan ni da 'yar uwata Zulaikha sekuma auta baban siddiqa, muntaso cikin rufin asiri don muba masu kudi bane sedai munada rufin asiri, muna zaune a garin suleja inda mukeda makwabtan damuka shaku sosai wato gidan Hajjaju, a wancan lokacin mahaifiyar mu muna kiranta da DaDa kuma sunan yasamo asaline daga bakin zulaikha itace take kiranta da hakan har yabita.

DaDa batada aminiya kamar hajjaju, domin halinsu yazo daya, a lokacin hajjaju yaranta biyu duk maza wato daddynku dakuma baban munnir hakan yasa takeson yara mata amma Allah bebata ba, don haka setadau son duniya ta daaura mana, tana matukar kaunarmu muma kuma muna sonta sosai, kullum muna gidanta barchi ke maida mu gida.

sukuma su daddynku suna gidanmu tare dasu yaya, a haka muka tashi cike da shakuwa harma ake tsokanarmu cewa za'ayi mana hadin gida tunda nice babba se ahadani da daddynku itakuma zulaikha ahada ta da baban munnir.

wasa wasa abu yafara neman zama gaske muna jss three Yayanmu yasamu aiki a kano, bayan tafiyarsa kuma dawowar dazeyi yadawo da zancen aure, munsha biki ya tattara yakoma kano dazama, a lokacin dazamu shiga ss one soyayya tayi nisa a tsakaninmu nida daddynku zulaikha da baban munnir, fortunately se yaya yasamawa baban munnir aiki a kano don haka seya tattara yatafi.

shikuma daddynku Allah yataimakeshi yasamu aiki acikin garin abuja so sh yananan tare damu,

tunda salis (baban munnir) yakoma kano shikenan yafara mantawa da zulaikha, ko hutu yazo baya bari suhadu, idanma sunhadu seya nemo uzurin dazesa surabu, itakuma tadau son duniya tadaura mishi.
abin yana bawa kowa mamaki don salisu mutumin kirki ne kuma kowa ya shaida irin tsananin kaunar dayake yiwa zulaikha amma daga komawarshi kano abin yasauya ya canza sosai.

hajjaju macece keson yaranta dakuma 6oye laifinsu kda zulaikha takai karar salisu se cewa tayi "yo dacan ninasashi balle in dawwamar dashi? kawai ki hakura dashi ALLAH yabamu alheri"

tun sannan zulaikha tarasa nutsuwa muna ss2 tabukqci komawa kano wurin yayanmu, bayan tasanar da DaDa ba musu tace "dama naji shiru matar tasa da alama juyace gara kije kidubomin insan abinyi" babanmu kuwa da tasanar dashi kin amincewa yayi don yasan abinda zekaitq kanon bewuce salisu ba ,ammq DaDa takqfa ta tsare harseda ya amince tatafi.

bayan tajene ta fahimci cewa salisu soyayya yakeyi dawata harma ansanshi a gidansu sannan tuni yabar aiki karkashin yayanmu yakoma aiki karkashin baban yarinyar dasuke soyayya, tabbas zulaikha ta kadu sosai dasanin haka, tundaga wannan lokacin kuma tafara kokarin cire salisu cikin ranta.

Rayuwa tacigaba da tafiya dadi da rashin dadin duka, yau da gobe har su muka kai matakin ss3 mukayi jarrabawar neco da waec, dawowar zulaikha hutu da kwana biyu salisu yazo hutu, tabbas har izuwa wannan lokacin zulaikha bata mance dashi ba, don lokaci zuwa lokaci takan yimin zancensa yananan makale a zuciyarta har tausayi takebani.

Wannan karon salisu yazo da abin mamaki matuka domin da matarsa yazo harda ciki a jikinta, Daddynku, ni, DaDa, babanmu, yayanmu, baban Siddika uwa uba zulaikha duk mun razana dajin cewa salisu yayi aure amma hajjaju kam ko ajikinta domin da saninta yayi auren.

A wannan ranar ne zulaikha ta dada tabbatarwa kanta cewar salisu yadena sonta don haka itama zata cireshi cikin ranta.

A ranar takoma kano duk dacewa bata kare hutun nata ba.

Ansamomin admission a federal college dake cikin garin Abuja, Alhamdulillah nacike komai nafara karatu, itama 'yar uwata tasamu admission a BUK muna karatunmu hankali kwance.

Bayan watanni matar salisu ta haifo yaronta wanda aka sakawa suna MUNNIR. murna gurin hajjaju ba'a magana, ba kunya taje gurin DaDa take cewa "yo inbanda ikon Allah waya isa yakai salisu kano, todai alkhairy ne tunda gashi an haifomin jika namiji"

Haka dai rayuwa tacigaba da tafiya.

Bayan shekara uku na kammala karatuna itakuma zulaikha saura mata shekara daya ta kammala.

Bayan wata uku aka tsaida ranar aurena wanda za'a hada bikin dana baban siddika.

Anyi biki lpy lou zulaikha ta halarci bikin wanda a hanyarta na komawa kanone ta hadu da wancen azzalumin MA'AZU.

Yanuna mata soyayya sosai musamman dayaji labarin yaudararta da salisu yayi.

A lokacin da salisu yasamu labarin sabon saurayin da zulaikha tayi hankalinsa ya matukar tashi, yadawo gurinta yana magiya da bata hakuri akan tadawo sucigaba da soyayyarsu.

Amma zulaikha taki amincewa a karshe ma tahadashi da ma'azu domin yaja masa kunne yadena bibiyarta.

Bayan zulaikha takare karatunta suka taho tare da ma'azu har suleja a gaidasu DaDa sannan takawoshi har abuja muka gaisa dashi, anan gidanmu yayi kwana har biyu kafin yatafi akan zeturo magabatan sa ayi maganar aurensu.


'Yar uwata tacigaba dazama tare dani musamman dayake inata laulayi lokacin inada cikinki wata hudu.

Wata daya yashude ma'azu bekawo wakilanshi ba, idan tayi masa magana seyayita kame kame, wata biyu wata uku......

Zulaikha tashiga damuwa sosai ganin yadda ma'azu kemata wasa da hankali wanda har hakan yasa tafara zazza6i, abun yakici yaki cinyewa hakan yasa na roki daddynku akan mukaita asibity Adubata.

Mun shiga matsanancin tashin hankali bayan likita ya tabbatar mana cewar zulaikha nada juna biyu tsawon wata uku da kwanaki.

Tunda muka dawo gida bansake kulata ba nafita a hanyarta gaba daya bana shiga sabgarta.
Daddynku yazaunar dani yacemin "irin wannan hukunci baze gyara komai ba sedai yadada 6atawa, kikirata kijawota a jiki ki binciketa waye yayimata cikin"

Hakan nayi, nakirata na tambayeta cikin kuka tacemin "ma'azu ne" banyi mamaki ba don nasan babu wanda take kulawa seshi don haka nace mata "yanzu duk tarbiyyar damuka taso dashi kin zubar cikin karamin lokaci zulaikha? Meya rudeki dashi haka?"

Cikin kuka tace "wallahi bada amincewata hakan yafaru ba, satin dazamu tahone naje yin siyayyar kayan tsaraba yayi kirana a waya yanason zuwa zance, nace mishi bana gida ina wajen shopping aikuwa segashi yazo, harma yabiya kudin siyayyar danayi, yadaukoni a motar zedawo dani gida sekuma yacemin zan dan rakashi gidan abokinsa don matar tadameshi akan yakawoni mugaisa, munje wani katon gida muka zauna a parlon dayaji kayan alatu babu kowa parlon se tv da lemuka akan tebur, agabana yabude lemo yazubamin a cup yabani wai kafin matar gidan tafito, bayan nagama shan lemun bansan abunda yafaru ba se farkawa nayi naganni a tsakiyar gado bako kaya a jikina, azabar danakeji ne ya tabbatar min dacewa fyade yayimin, nayi kuka dayimishi Allah ya isa yafi a kirga, haka dai yayita lallashina da lalla6ani dayimin alkawarin aure, nasamu nagyara jikina yadaukoni yadawo dani gida, koda matar yaya taganni ba'a yadda nafita ba taso ta bincikeni amma nayi saurin cewa kaina keciwo nayi shigewata daki, kwana nayi ina kuka har gari ya waye, bayan kwana biyu jikina yayi sauki sosai nafara shirin tahowa, ma'azu yadage lallai sedai mutaho tare don dagaske aurena zeyi, nasake bashi dama ganin kamar dagaske yakeyi na yarda muka taho" takare tare da fashewa dawani sabon kukan meban tausayi.

Ni narasa abin cewa kawai nima sena fara kukan, daddynku se lallashi yakeyi daga karshe ya amshi numbern ma'azu yakirashi yasanar dashi halin daya jefa zulaikha, bakadan ba shima hankalinsa yatashi hakan yasa yakira zulaikha yake shaida mata indai tanason ya aureta seta yarda anzubar da cikin tukunna amma zulaikha tace sam bazata zubar da cikin ba.

Tundaga ranar ba'a samun wayar ma'azu gaba daya, daddynku yasa anyi masa iya bincike amma ba'a samu labarin ma'azu ba,.

Bayan sati biyu nidakaina na bukaci zulaikha tatashi muje asibity a zubar da cikin amma kememe taki yarda, babu irin lallamin daban yimta ba amma taki amincewa a karshe tabani haushi nace ta tattara shirginta takoma gida, ba musu ta tattara kayanta ta dawo suleja.

Koda iyayenmu suka fahimci halin da take ciki nan take DaDa ta suma, shikuwa babanmu dama yanada ciwon zuciya atake ciwon nashi yatashi dasauri aka daukeshi akayi asibity dashi wanda kafin azo adubashi har rai yayi halinsa.

Mun shiga matsanancin tashin hankali dasamu labarin rasuwar babanmu amma babu yadda zamuyi se hakuri.

Bayan wata uku nahaifeki, kinada wata biyu a duniya aka haifi siddika, itakuma tanada wata daya zulaikha ta haihu.

Ranar suna zulaikha ta radawa yarta suna ZULAIKHA, a wannan lokacin salisu yazo suleja yakuma bukaci auren zulaikha tareda rike 'yartata, amma hajjaju tayi tsalle tadire kan cewa bazata sake hada zuri'a damuba, nimadai a rashin sanine tabar daddynku ya aureni amma baza'a kuma ba. Da salisu ya matsa akan auren zulaikha hajjaju cewa tayi zata tsine mishi kawai don haka yatattara yakoma kano ya hakura da zancen auren.

Bayan zulaikha tayi arba'in DaDa ta bukaci lallai sedai akayi jaririyar nan gidan marayu don wlh bazata rike shegiya ba, babu irin hakurin da bamu bawa DaDa ba amma sam taki sauraronmu ganin bazata hakura ba yasa zulaikha tattara kayan sawarta dana yarinyarta cikin dare tadau yarta suka gudu, setabar letter a dakinta cewa "kuyi hakuri da 6ata muku suna danayi, amma bazan iya rabuwa da 'yata ba don haka natafi ba lallai kusake ganina ba DaDa kiyafemin"

Bayan karanta wasikar haukane kadai DaDa batayi ba, don duk cikinmu babu wadda take matukar so da kauna irin zulaikha, tundaga wannan ranar DaDa ta cire yayanmu cikin 'ya'yan ta domin acewarta kome yafaru shine sanadi, don da'ace yasamata idanu dakyau da bazatayi cikin shege ba, DaDa tahanamu zuwa inda yake kwata kwata ko wayama sedai muyi a 6oye bata sani ba.

Bayan tafiyar zulaikha da shekara daddynku yasamu transper awajen aiki zuwa jos muka tattaro muka dawo jos dazama.

DaDa tadena amsa sunan DaDa ne saboda aduk lokacin da aka ambaci sunan seta tuno da zulaikha kuma tayi kuka, shine kawai yasa aka kashe wannan sunan.

Mundawo jos da shekaru biyar hajjaju ta matsa lallai seda aka nema mata gida tadawo jos din itama, sannan da karfin rigimarta tasa aka bata munnir yadawo gurinta dazama.

Yau shekara 18 kenan babu zulaikha babu labarinta anyi neman anyi addu'ar daga karshe munzubawa sarautar Allah ido, kotana raye kota mutu babu wanda yasan halin datake ciki.

**********************

Goge hawayen daya zubo mata tayi sannan tace
"Kiyiwa kanki adalci Sofiyya, shin idan nace ki auri dan ma'azu zaki amince?"

Itama sofiyya hawayen nata ta goge sannan tace cikin raunanniyar murya "mommy nifa ba Abbansu Abdul zan aura ba, Abdul zan aura kuma......"

Kafin takai aya mommy ta buga mata wata razananniyar tsawa "ki rufemin baki nonesense kawai wadda batasan ciwon kanta ba, tashi ki6ace min anan kafin inci ubanki"

Dagudu Sofiyya tatashi tayi dakinta, daddy kuma yace "nagode" sannan yatashi yayi wucewarsa shima..................
'


07046767662 Maryam-Ashner

[9/3, 10:21 AM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 43

A parlo duk suka baje, duk wanda ka kalli fuskarsa zakaga tsantsar damuwa a cikinta, duk sun kagu suji bayani daba bakin Abba, bama kamar Abdul wanda gaba daya yagama rasa nutsuwarsa, sekuma umma da zuciyarta keta bugu, Raliya da usman kam jira suke su Abba yace karya mommy takeyi shi besan komaj ba.

Umma ce taja numfashi sannan tace "muna jinka Alhaji kayi mana bayani akan abinda matar nan take nufi"

Abba gaba daya yarasa courage dukda cewa yasan dazuwan wannan ranar kuma kullum gani yake a shirye yake amma kash a yanzu kam jiyake be shirya ba sam, addu'o'i yadingayi a zuciyarsa sannan daga bisani yafara dacewa "dafarko dai zan baku hakuri akan abinda zan sanar daku yanzu, don babu komai cikin abinda zakuji se 6acin rai, amma ance ranar wanka ba'a 6oye cibi saboda haka kuyi hakuri, tabbas nayi kuskure, kuskuren da a yau yake neman ruguje farin cikin gidana, shekaru goma sha takwas zuwa sha tara dasuka wuce, a wancen lokacin muna zaune a kano ina karkashin ogana Alhaji sunusi dala, nahadu da zulaikha, wato kanwar mahaifiyar Sofiyya, tunda naganta naji inasonta da aure, hakan yasa kai tsaye na tunkareta kuma nasamu kar6uwa a gurinta, ahaka har muka saba nakanje gidansu duk lokacin dana gadama muyi fira, bayan wani dab lokaci data kara amincewa dani, tabani labarin yadda saurayinta ya yaudareta harma da yadda akayi tadawo kano dazama domin iyayenta da 'yan uwanta duk suna suleja ne, na tausaya mata sosai tare da yimata alkawarin bazan yaudareta ba, tafiya tayi tafiya, lokacin kunyi tafiya zuwa niger nakasa rike kaina har shedan yayi galaba akaina nayi anfani da maganin gusar da tunani nayiwa zulaikha fyade" yakarasa yana fashewa da matsanancin kuka, Raliya da Usman na tayashi, umma ma kukan takeyi Abdul kam tashin hankalin daya shiga yahanashi yin kukan, idanunsa sunyi jawur zuciyarsa na tafarfasa yarasa meke yimasa dadi.

Tsagaita kukan nashi yayi yacigaba "a lokacin dahakan tafaru nayi nadama kuma nayiwa kaina alkawarin auren Zulaikha no matter how, hakan yasa na lallasheta harma tayarda nayimata rakiya zuwa suleja nagaisa da 'yan uwanta da danginta duka, hakan yakara tabbatar mata cewar dgske zan aureta, bayan nadawo kano da yab kwanaki kuka dawo a lokacin Alhj Sunusi yana jinyar jikinsa, same time daya mallakamin dukkan dukiyarsa kasancewar bashida da bare jika, bayan rasuwarsa seya zamana nine a matsayinsa gidan tv radio jarida duk zancena akeyi, alokacin ba'a haifi usman ba akwai dai cikinsa, a lokaci daya nazama sanannen attajiri fiye da shi marigayi Alhj sunusi, duk dahaka bandena tunanin auren zulaikha ba, kwatsam sega kiran mijin yayarta yake shaidamin cewa zulaikha nada juna biyu kuma nawane, hankalina yayi matujar tashi dajin hakan kai tsaye na kirata nace mata azubar da cikinnan semuyi aure amma sam taki amincewa, danaga dai kamar bazata yarda ba sena fita hanyarta, karshema na karya sim din damuke waya, nayi hakane gudun 6acin suna, domin a wannan lokaci idanun yan jarida a kaina yake, duk wani motsina suna biye dashi. Nacigaba da rayuwata amma deeo down da zulaikha nake kwana cikin raina, bayan kamar shekara da faruwar hakan abin yafara damuna don haka nashirya naje suleja domin mu daidaita amma sena samu labarin cewar zulaikha ta haifi yarinya ta mace anbukaci takaita gidan marayu don haka ta dau yarta suka gudu, tunda nadawo ranar nashiga matsananciyar damuwa kuma nadukufa da addu'ar Allah ya bayyanamin su, duk lokacin da kukaganni cikin damuwa to nayi mafarkin zulaikha ne kokuma na tuno ta, kwanaki can nahadu da ita a kano amma kafin in ankare ta 6acemin, wannan ciwon na karshe ma danayi sanadin ganin 'yata kuma 'yar zulaikha ne, domin inada yakinin yarinyar dana gani jinina ce, saboda shock yasa nayi collaps, don Allah kuyafemin yayana, matata kema kiyafemin naci amanarku ban kyauta muku ba" kuka sosai sukeyi dukansu, umma kam tashi tayi tanufi dakinta ta kulle, Abdul ma tashi yayi yafice abinsa, Raliya da Usman kuwa kusa da Abba sukaje suka rungumeshi suna kukan atare.


Tunda yafita yake tafiya a kafa shikanshi besan inda zashi ba, harga Allah Abba ya cuceshi, yasan a yanzu Sofiyya tasamu labarin wanene mahaifinsa kuma yasan duk tarin kaunar datake masa yanzu tsanarsa zatayi, gaskiya mommy tafada babu wanda zeso yahada zuri'a dasu, ji yayi anjashi an wurgashi gefe, ashe motace taso bi takanshi shi bema sani ba, mutumin daya jashi gefe yace "haba malam kadinga kula mana"

Bekulashi ba yacigaba da tafiyarsa, a ransa yace "aidama kabari ya bugeni namutu nahuta, don ko hauka nakeyi yanzu nasan narasa Sofiyya har abada,

20 / 26