Chapter 12 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 26

33K to 36K   out of 76.5K words

fahimci abinda ke faruwa ba, duk maganganun da Hajjaju keyi ita sam ba ganewa tayiba, hankalinta a tashe yake, domin suna hada ido da mommy se hararar, daddy kam yamaki bari suhada idon. Burinta kawai su isa gida taji meke faruwa.


Bayan sun sauka kai tsaye falon gidan suka nufa, Hajjaju, daddy da mommy suka zauna kan kujera,.
Munnir ya zauna gefen daddy a kasan carpet, Siddika da Sofiyya suka xauna gefe guda a kasan carpet suma.


Ikram dake jikin daddy tana gyangyadi, daddy yace

"Mamana jeki kwanta ko"

Kai tsaye tanufi stairs tashiga dakinsu tacire kaya ta kwanta.



Cikin ladabi daddy ya kalli Hajjaju yace "hajiya meyake faruwa ne haka,? "


Hajjaju na huci tace "katanan 'yarka zaka tambaya, tun yaushe take yawon lalata bamu saniba"



Gaban Sofiyya ne yafadi, me matar nan take nufi?

Ran mommy ya sosu jin irin furucin da Hajjaju tayi, sunkuyar dakai kawai tayi domin koma meya faru Sofiyya ce tajawo.


Daddy ma beji dadin kalaman Hajjaju ba, dukda cewa besan takamaiman abinda yafaru ba.
Daurewa yayi yace

"Hajiya kiyi hakuri zanfi gasgatawa idan kece kikayimin bayani"



Yatsine fuska tayi sannan tace "yoni ina nasan cikakken bayani? Manniru zaka tambaya, kuma duk abinda yafada gaskiya ne, tundadai agabanmu wannan yaron yasauketa a mota tareda tarin tulin kaya a katuwar leda"



Daddyne ya kalli munnir yace, "meya faru dan hajiya, kagayamin gaskiya"


dama abinda yake jira kenan don haka yagyara zama yace "daddy wannan wanda yasauketa a mota tunba yau ba nake ganin yana sauketa a mota a can saman layi, don ranar ma har kusan dukana yayi, sannan yau kuma dana gansu tare nayi mata magana shine yakama mata hannu yajata suka shiga mota suka tafi"


Shiru yayi sannan yakara dacewa "kuma wlh ba mutumin kirki bane, don nayi bincike a kanshi sosai, fasiki ne"


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun" kalmar da Sofiyya keta maimaitawa kenan cikin ziyartar ta, tanabin munnir da kallon mamaki.


Siddika kuwa banda hararar munnir babu abinda takeyi.


Daddy da mommy kam duk shiru sukayi suna nazari.


Hajjaju ta mike tace "nikam Allah ya isana wlh bazan yafemiki ba safiya, kin cuceni kin lalatamin zuri'a, wlh ko gaban Allah se anmana shari'a da DaDa data aurawa dana matar da bata iya tarbiyya ba" ta kare da share hawayen munafurci.



Mommy kam in ranta yayi dubu ya6aci, abin yawuce kanta har kan mahaifiyarta? "Hmmm dan kuka mejawa uwa zaki kenan" tafada a zuciyar ta.



Hakuri daddy yahau bawa Hajjaju don shikanshi maganganun ta basuyi masa dadiba, soyake ya lalla6ata tatafi inyaso seyaji da gidansa kuma.


Mommy tace "yayi kyau Sofiyya kinga dai abinda kika jawomin yamiki kyau"


Rasa mezata ce tayi hakan yasa tafashe da kuka tana "wlh mommy ba...... "



Bata kai karshe baHajjaju takatseta da cewa "kafin kibamu bayani maza jeki dauko abinda yabaki mugani tukunna, bakar munafuka"


Sum sum Sofiyya ta mike tayo waje tana share hawayenta, tsanar munnir na ninkuwa cikin zuciyar ta.

...................


Tunda Abdul ya figesu Bashir keta salati yana addu'o'i don harga Allah ya tsorata ba kadanba.



Seda sukaxo get din gidansu Sofiyya sannan yayi parking
Ajiyar zuciya Bashir yasauke yana furta "Alhamdulillah Allah mungode daka kawomu lafiya lou"



Batareda Abdul yace mishi komai ba yabude motar yafita yanufi kofat gidan yahau bugawa.



Megadine yazo yabude yana karewa Abdul kallo,


Bashir ne yafito gazo yamikawa megadin hannu suka fara gaisawa, shikuma Abdul yayi anfani da wannan damar yashige cikin gidan kai tsaye kamar dama yasan kan cikin gidan.


Megadinne ya bishi da kallon mamaki yana cewa "malam lafiya? Wakake nema ne? "


Hakuri Bashir yabashi, sannan yace "gun megidan mukazo"


Hanya megadin yabashi yawuce, shikuma yazauna yana mamakin kodai Abdul kurmane?.



Sofiyya tabude mota tadau ledan da Abdul yabata tarufe zata koma, juyowar dazatayi tayi tozali da sanyin idaniyarta, wani sanyin dadine ya ziyarci zuciyar ta, sannan fargaba tabiyo baya.



Dasaurinta ta taho gurinshi tana karemai kallo, duk ya sauya, babu annuri a tare dashi ko kadan, bata ta6a ganin fuskarsa hakaba.


.......................


Koda suka isa gida umma kasa zama tayi duk takasa nutsuwa.
Anty zee tanada tausarta da kwantar mata da hankali amma kamar ma bata fahimtarta.


Hakan yasa anty zee cewa "to mugwada kiranshi a waya mana muji ko lafiya"



Duk kwakwalwarsu bata kawo musu hakan ba seyanzu.

Anty zee taciro waya, umma taciro Raliya taciro usman ma yaciro, kowa kokarin kira yake.



Abin seya bawa zuly mamaki yadda kowa yadamu da Abdul

"Kai family akwai dadi" tafada cikin ranta kamar zatayi kuka.


Duk kira suke wayar nata ringing ba'a dauka, shiko yabar waya a mota bama ta waya yakeba.



Cike da damuwa mommy tanemi guri tazauna tana "kodai har sunyi accident ne? "



Girgiza kai Raliya keyi tana "basuyiba Umma, bazama suyiba insha Allah zedawo lafiya"


Anty zee tayi tagumi tana "oh Allah kome yake faruwa dashi? "


Zuly tayi gyaran murya tace "nasan abinda yafaru Anty "


Duk juyowa sukayi suna zuba mata idanu.



"Akan Sofiyya ne, akwai alkawarin da sukayi da wani dan uwanta akan shine ze aureta dazaran tagama karatun secondary, toshi dan uwan nata gaskiya bashida kudi yanadai da rufin asiri, toshine bayan tahadu da yaaya taga yanada kudi shine tace shi dan uwan nata ya hakura don dama ita wai ba sa'ar aurensa bace, ita diyar me kudice kuma don haka dole mekudi zata aura"



Tayi shiru, umma ta numfasa tace "sekuma akayi yaya"


Zuly dako kunyar yin karya batayi tacigaba "Shine shi dan uwan nata daya fahimci cewa Yaaya ne me nemanta yasaka mata ido, daga karshe kuma yau suka hadu har sukayi fada yace wlh indai yaaya befita hanyarta ba to tabbas seya nakasa shi"





"Innalillahi wannan wace irin masiface" inji anty zee.


Umma tace "kinga irinta ko? Ni wlh banason rikici, yadawo kawai yakyale yarinyar nan Allah yahadashi da wata"






Anty zee tace "aikuwa kam bata kyauta ba gaskiya, amma shi Abdul seya hakura ga matanan dayawa a gari, nise in nema masa wata ma dakaina in yanaso"




Zuly da ranta yayi fesss tasake cewa "wlh anty naga ran Yaaya ya6aci sosai dazu"



Raliya itadai tunda akafara labarin bata wani yarda ba tace "ke a ina kikaji wannan labarin? "




Nan zuly tafara kame kame tace "aishi dan uwan nata malamin mune na Islamiyya kuma zancen duniya ai baya 6uya"



Umma tace "nidai Allah yadawo dashi lafiya, yafita a harkar yarinyar tunda Allah ma yasa abun beyi nisa ba"



"Uhmmm Allah yakyauta" inji Raliya tamike tayi dakinta.


.......................


adan tsorace tace "Yaaya lafiya kuwa?"


Kallon idonta yayi tabbas tayi kuka, ranshi yakara sosuwa yajuya kai daga barin kallonta yace "kaini ciki"



Zaro ido tayi tace "ciki ina?"


Hanyar dayake tunanin nanne falo yanufa kai tsaye.
Bin bayanshi tayi tana "yaaya wait don Allah katsaya"



Ko juyowa ma beyiba balle yasake kallonta.



Bashir ma kuma mara musu baya yayi suka nufi cikin falon dukansu.




Sallama yayi ciki-ciki wanda babu wanda yajishi, kai tsaye kuma yanufi kusada munnir yazauna yana fadin "ina yinin ku"



Cikinsu babu wanda ya shaidashi se Siddika da munnir, wanda mamaki ya cikasu.



Kafin kowa yayi magana Sofiyya tashigo sum sum kanta a kasa tawuce gaban Hajjaju ta ajiye ledar hannunta sannan tawuce mazaunin ta tazauna tana duke kai a kasa.



Bashir ma kai tsaye yataho kusa da Abdul yazauna yana gaidasu.

Daddy ne kawai ya amsa, mommy da Hajjaju kuma jira suke suji waye wannan din.



Munnir ne yamike tsaye a fusace yana "how dare you come to my house?"


"Will you calm down munnir, kabarshi yayi mana bayani" inji daddy


Nuna Abdul dayatsa yayi yace "daddy shinefa dan iskan da yake daukar Sofiyya sufita yawo"



"Nace kakoma kazauna ko" inji daddy


Zama yakoma yayi yana kwafa

"Oh wai dama kaine don bakada mutunci kuma kazo mana har gida, wato abinda kukaje kukayi be isheku ba kenan"



Wani daci ne yakeji a ransa amma dai yadaure bece komai ba.

Sofiyya kam tuni hawaye yagama wanke mata fuska, Siddika na shafa mata baya alamun rarrashi.



Daddy ya numfasa yace "kiyi hakuri hajiya"


Sannan ya kalli Abdul yace "to bawan Allah mekazo yi gidannan"



Hadiye wani daci yayi sannan yace "sunana Abdullahi kuma nazo neman auren Sofiyya ne"



Zaro ido Bashir da Sofiyya sukayi don duk basuyi tsammanin jin furuci irim wannan yafito daga bakinsa ba.


Daddy da mommy kuwa mamakin karfin hali irin nashi sukeyi.


Siddika kuwa har cikin ranta taji dadi don haka taita murmusawa.



Hajjaju da masifa kecinta ta bude baki zatayi magana Munnir yarigata da fadin " what nonesense, bayan kagama lalatata sannan kazo kace zaka aureta? Angaya maka mahaukata ne mu dazamu hada jini da lalatacce irinka,. Ai koda........... "




A tsawace daddy ya katseshi da "munnir fita kabamu guri shashashan yaro kawai"



Mikewa yayi yafice yana gunguni.
Daddy yamaida kallonsa kan Abdul yace "naji abinda yakawoka, tashi kuje zan nemeku in bukatar hakan tataso"




Beso jin hakaba, yaso ace a yanzun nan anbashi auren *Cutie* Koda ba'a daura auren ba, atleast amusu alkawari.
Amma bakomai zejira,

Mikewa sukayi shida Bashir suna fadin "mungode" suka nufi waje



Daddy yamaida kallonsa kan Sofiyya yace "tashi kuje kuma"



Harsun mike Hajjaju tayi saurin dawo dasu ta hanyar fadin "zonan kibude ledar nan da hannunki"



Dawowa tayi tabude ledar Siddika naciro abubuwan dake ciki.

Frames ne kala kala har guda 5
Daya anrubuta I LOVE YOU CUTIE
Daya anyi definition din SOFIYYA according to mr Abdul
Daya anrubuta Sofiyya +Abdul =Sofdul
Daya anyi definition din SOFDUL according to mr Abdul
Na karshe kuwa addu'o'i ne da aka tsarawa Sofiyya da iyayenta.


Se sauran abubuwan dasuka hada da turaruka, sabulai, jeweries, bangles dasu 'yan kunnaye sekuma wani silver ring me sheki da bala'in kyau.



Banda wow wow wow ba abinda Siddika ke furtawa.


"Tarkacen banza kawai, sekace mehada kayan lefe" Hajjaju ta furta.




Mikewa Sofiyya tayi tahaura sama Siddika ta tattara kayan tadauka tabita dashi.


Daddy yace "ni yanzu bansan yazanyi da wannan al'amarin ba ga munnir gakuma wannan yaron"



Mommy tace "kamarya ga Munnir?"


Se sannan yake basu labarin tattaunawar dasukayi da baban Munnir kan hadasu aure



"Tabdijam awani gidan za'ayi wannan kwamacalar? To wlh badai Munnir jikana tilo na miji za'ayiwa mugunta a hadashi da sauran wani ba, gara kusake shawara". Hajjaju tafurta tanayin waje da kwala kiran Munnir kan yazo yamaidata gida.




Bayan fitarsu Abdul munnir yataho yasha gabansu yana karemusu kallo sannan yace "idan baka fita jarkar Sofiyya ba don Allah, to tabbas zaka fita don azaba, last warning". Yakarasa yana karkada masa dan yatsa.


Ko kyakyawan kallo Abdul bemasa ba suka wuceshi.




Mommy dajin zancen hadinnan yakara 6atamata rai mikewa tayi batareda tace uffan ba tayi dakinta.



Shigarsu mota keda wuya wani kiran na katsewa daga wayar Abdul, dauka yayi domin duba kowaye, ganin missed call 40 yasashi jin wani dummm anya lafiya, yafurta hakan a zuciyarsa.


Wannan karon Bashir ne ke tukin shikuma Abdul na kokarin kiran Raliya....................
'?


https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?=?O?=?O?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*

By

*Maryam-Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Don Allah Mata zallah=?O? kuma inkinsan bazaki dingayin sharhi/comment me ma'ana ba kada kishigo=?L? ba sticker da godiya nakeso ba' addu'a da sharhi/comments masu ma'ana nakeso'


_*TALLA*_
kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway karshen wata ga wacce tasiya yakai sau biyar, koda 500mb take siya=?L? tanada kyatar 1GB, wadda tasiya sau hudu kuma tana ds kyautar 500MB.
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Muna saida kowani network if needed=?L?
Call/WhatsApp 07946767662
Chat on Facebook =?G?
Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 29

Daddy ne kewaya da Alhaji salis, "kanajina ko yaaya, wata guda kenan da faruwar wannan abin dakaji na fada maka, tun sannan kuma gaba daya babu jituwa tsakanin yarannan wlh"


Alhaji salis yace "karka damu wata kila hadin babu alkhairy a cikine shiyasa Allah ya wargaza tsakanin su, bawata matsala ai Adam mudai mucigaba da addu'a kawai Allahu ya za6a mana abinda yafi alkhairy"


Amin ya Allah " injj daddy
Dahaka kuma sukayi sallama.

........

Daddy ne kezaune tareda baba megadi sunadan ta6a hira, dayake yamma ce 5:30pm.


Kwankwaso kofar gidan akayi hakan yasa baba megadi yayi hanzarin mikewa domin jin ko waye.



Wani dattijo yagani cike da shiga ta alfarma da kamala, daganinsa kasan nera tazauna mishi, bakowa bane illa Alhaji Mu'az Gallafi.




"Barka dai baba" inji Abba

"Alhaji barka kadai sannu sannu dazuwa" baba megadi yafada


"Yawwa sannu baba, don Allah kome gidan nanan?"



Baba megadi yace "eh yananan wlh, bari inyi maka magana dashi"



Komawa yayi yasanar da daddy, ba'a jimaba daddy yafito, ganin bakon nashi babban mutum ne yasashi mika mishi hannu suka gaisa, sannan yace

"Bangane fuskar ba"


Abba yayi murmushi yace "sunana Mu'az Gallafi mahaifin Abdullahi wato manemin 'yar wajenka"



Daddy yayi mamakin jin cewa shine Mu'az Gallafi, domin sunan sananne ne a Nigeria, amma fuskar ba sananniya bace, hakan yasa besanshi a fuska kamar yadda yasan sunanshi ba.

Gashi kuma wai baban Abdul ne, ikon Allah kenan.


Hakan yasa daddy cewa "a, a Alhaji bismillah ai bazaka tsaya a wajeba, mushiga ciki ko"


Abba yace "ai dole in nemi izini tukunna"


Jagora Daddy yayi masa har falon saukar baki, sannan yanufi cikin gidan domin yasanar da mommy akawo masa abin ta6awa.



Momy ma tayi mamakin jin wai baban Abdul shine Mu'az Gallafi, sanya Sofiyya tayi tahada komai a trey sannan takira 'yar aikinsu tadauka takai musu.



Sofiyya dake taya mommy shirya drawer din kayanta taji duk abinda daddy yafada, hakan yasa duk tafara jin kunya, takasa cigaba da surutun da takeyi, sannan taki yarda suhada ido da mommyn.


Tsab mommy tana sane da abinda takeyi amma tayi kamar bata ganta ba.

Can dai dataga kamar mommy bata ganeba se tace "mommy zanje indan watsa ruwa ne"
Takarasa tana sake sunkuyar dakai.



Mommy tayi murmushi tace "zakije dai ki 6uya, oya go"



Wata kunyar ce takara baibayeta, aikuwa dasauri harda dan gudgudu tafice.


Tana shiga daki takulle kofa harda saka key,

Kan gadonta tahau tana fadin "Alhandulillah" dasauri kuma tarufe idanu da tafin hannunta, don ita kanta taji kunya,.


Farinciki takeyi marar misaltuwa, tarasa meya kamata tayi, fuskarta cike da murmushi tadau wayarta tana, "lets enjoy da happiness together yaaya". Tafada tana dialing number din Abdul.


..............


Abdul dake tuki yaga kiran *Cutie* be dauka ba, seda yaje gefen titi ya faka motar sa sannan yakirata, tana dauka tace mishi.

"Albishirinka"


Yace "tooo! Meya faru? "

Tace kaidai Albishirinka"


Yace "to goro"

Seda tazo fadan maganar kuma tarasa ta inama zata fara, sekuma tayi shiru tana tunani.


Jin tayi shiru yasa Abdul cewa "Cutie are you there? "


Tace "uhm dama Abbanku ne yazo gidabmu yanzu"

Tana fada takashe wayar.



Wani farinciki yaji ya mamayeshi, beta6a tsammanin za'a saurari zancen cikin sauki haka ba, segashi abu da wirwuri haka!


Kiranta yayi amma sam taki dauka, yagane me take nufi, "wai kunya" yafada yana murmushi.


Whatsapp yakunna data ya leka cikin dace kuwa yaga tana on itama.

"Meyasa kikaki daukan kirana? " yatambayeta true chat.


"Uhm uhm" tamishi reply hade da emoji irin najin kunyar nan.


"Uhm uhm me? Malama kawai kidaga min waya, yanzu zan kira"


Bamusu ta kashe datar, yana kira kuwa tadauka.

Tuntana nokewa seda yasa tasake sukasha hirarsu kamar yadda suka saba.


Sebayan da suka gama wayar tayo tsalle kan gadonta tace "finally nakusa insake sakaka cikin idanuna, after one good month da aka hanani fita saboda wancan tsinannen" tafada tana cije baki, irin zasu hadun nan.


Zama tayi tadau wayar tana kiran siddika domin tashafa mata wannan daddadan labarin.


............


Tattaunawar su daddy ta kammala, inda daddy yanemi da Abba yabashi sati guda yayi nazari da shawarwari tukunna.


Koda yashigo gidan ya taradda mommy ita kadai a falo, yace "bari muyi sallah sannan mu tattauna kan batun yarannan"


Mommy tace "to shikenan Allah yakaimu"


..............

Zuly fa abun nema yasamu, don yanzu kullum tana gidan anty zee, se faman shishige mata takeyi, kullum burinta ace Abdul yazo gidan tadan gashi kotaji dadi amna shiru.


So takema tadingajin labarin abinda ke faruwa akan maganar su Abdul amma shiru haryanzu bataji komai ba, koda maganar tafara yiwa anty zee sedai tace Allah yakyauta kawai.



Zuly da munnir sun sake kullawa, domin cinma burinsu suna bukatar hadin kan juna, hakan yasa kullum suna tare cikin waya ko chat, suna gudanar da shawarwari kan yadda zasu raba tsakanin Abdul da Sofiyya.


Yanzu ma zaune suke a wani restaurant an ajiye musu abinci da abinsha,.

Zuly takai loma, bakinta cike da abinci tace "munnir yakamata fa kadage"


Wani haushi tabashi, don me bazata bari tacinye abincin tukunna tayi magana ba, yatsani yaga ana cin abinci ana magana kamar dole, don haka yace

"Dalla kibari ki hadiye abincin bakinki tukunna mana, kanar wata mayya wai munnir yakamata fa ka dage" yakarasa yana kwaikwayon yadda tayi maganar.


Tun sannan bata sake cewa komai ba, seda suka gama cin abincin duka sannan yace "to inajinki, wacce shawara ce dake"


Tace "ni inagani wannan

12 / 26