Chapter 23 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 26

66K to 69K   out of 76.5K words

yanada abinda zefada miki" juyawa yayi ya kalli Abba yace "Alhj bismillah"

Gyaran murya Abba yayi sannan yafara sanar da ita dalilin dayasashi kin dawowa gareta dakuma nemanta daya dungayi har izuwa relationship din Sofiyya da Abdul, da haduwarshi da zuly nafarko da haduwarshi da mommy dakuma abubuwan dasuka faru bayan nan har zuwa yau duk a takaice yayi bayani sannan yamike yanufi inda take ya durkusa gwiwowinsa a kasa yace "ina rokonki zulaikha don girman Allah, don darajar manzon Allah s.a.w kuma albarkacin dota kiyi hakuri da abinda yafaru kiyafemin"

Sosai take ganin girmansa duk kuwa da abinda ya aikata mata, ganin tayi shirune yasa zuly tasowa itama tazo ta durkusa kusada Abba tace "mama nasan abinda Abba yayi sam bekyauta ba amma don Allah kiyafemishi" takarasa tana kuka, itama mama har lokacin jawayen take tace "nayafe maka Allah yayafe mana duka"

Mikewa yayi da murmushi a fuskarsa yakoma mazaunin sa yazauna, a 6angaren Abdul da usman kam bakaramin haushin durkusawan shi sukaji ba, amma koma menene shine yajawa kansa.

Mommy aka bawa damar magana, itama labarin halin da DaDa suka shiga tabayar a takaice, kuka kam sun shashi kamar ba gobe, a karshe dai Abba yazo da bukatar auren mama, kallon tsantsar mamaki su Abdul da usman suke binsa dashi amma basuda damar yin magana don haka sukayi shiru, shikuwa mijin aunty zee beyi mamaki ba don dama yasan za'ayi hakan. mama kuwa cewa tayi "wallahi tallahi billahillazi la'ilaha illahuwa koda babu namiji a duniyarnan seka kadai bazan aureka ba ma'azu so mubar wannan maganar anan na rokeka" takarasa da hade hannunta guri daya alamar roko.

Shiru yayi don be tsammaci jin hakan daga gareta ba sam.

Mommy kam ta6e baki tayi don dama bata goyon bayan wannan shashancin.

Mijin aunty zee dasu Abdul kuwa murna sosai sukayi dajin amsar da mama tabayar, gyaran murya mijin aunty zee yayi yace "a matsayina na uba ga Abdullah ina nema masa alfarma tunda komai yafaru yakare abashi dama ya auri Sofiyya domin dama basuda laifin komai cikin wannan lamarin"

Daddy yayi murmushi yace "ai dama bawai anfasa bane, lokcin da aka saka ma ba canzawa za'ayi ba insha Allah, za'a hada harda na yar uwarta ayi duka"

Kara sunne kai Sofiyya tayi don kar aga murmushin datakeyi, Abdul kam kare fuskarshi yayi da wayar hannunshi gudun kar aga yadda yake murmushin da yakasa control, sarai usman yaje lura daduk wani motsinsu.

Mommy da mama kuwa mamakin jin abinda daddy yace suke, to ina zesamowa zuly mijin dawuri haka? "What ever bazadai ayiwa dota auren dole ba" mommy tafada a hankali .

Abba ne yakara requesting abashi zuly sutafi tare takoma gidanshi dazama, daddy yace "banki tataka ba, amma kadanyi hakuri gobe nakeson muje suleja idan Allah yasa mundawo setazo gidan naka don kaga yakamata mutafi tare da ita"

Addu'a sukayi sannan daddy yatasa kan yaransa gaba suka wuce, Aunty zee da mijinta ma suntafi, mommy daddy, mama dasu sofiyya ne suka rage a gurin.


Atake daddy yakira Dan uwnsa baban munnir yasanar dashi duk abubuwan dasuka faru, tsabar murna Alhj salis bejira se gobeba atake yayi kiran munnir yace yaje yashirya zasu jos, dukda cewar yamma tayi haka suka bi flight suka taho.

Mommy CE ta requesting mama da zuly subiyota da kayansu su kwana a gidan ta inyaso dasafen sesu wuce suleja daga can.

Hakan kuwa akayi, sun tattara yan kayayyakinsu driver yajasu zuwa gidan.

Da magriba su munnir suka iso, daddy yaje yadaukosu ya wuce dasu gidan hajjaju.
Hajjaju dake tsaka da alwala tajiyo sallamarsu bata amsa ba suka karaso tana wanke kafa tamike tana kare musu kallo tace "badai hijira ce takamaku ba don banida inda zan ijiyeku anan atoh haka kawai kudiromin gida katin katin daku babu sanarwa, kadai Aminu kaji tsoron Allah duk wani tuggu kaine kake shiryawa" takarasa tana wucewa parlonta, bin bayanta sukayi don abinda tayi ba abin mamaki bane agurinsu.

Zama sukayi a kan kujera dukansu suna gaidata, ko kallon inda suke batayi ba ta shimfida sallayarta tafara sallah, haka suka zauna jugum suna jiranta don insuka sake sukayi magana tana sallah tabbas idan ta idar zasuji maganganu.

Bayan ta sallame tayi addu'a ne tajuyo tana kallonsu, washe baki tayi tana kallon munnir tace "yo aise kucemin tare kuke dashi Allah sarki manniru kaje kaga yadda nafi uwarka sonka ko shine kadawo, ainasan za'ayi haka dama wannan lutiyar uwar taka meta iya inbanda tusa kaidai nasan kayi hakuri da kumburin ciki wlh"
Mikewa tayi tanufi kutchen tana cewa "bara injika muku tazargade ubanka yaci albarkacinka don da'ace shikadai ne ma bazan bashi ba, tunda aishi dakanshi yadauko jibgegiya bodara me tusa inda ace yayi hakuri ya auri zulai Aida lafiya lau" tafada tana jika tazargaden sannan tafito dashi a Kofi tana juyawa tace "kasan itama zulai Aida laifinta wlh dayanzu itace uwarka ba waccer me tusar ba, aikuwA daka more uwa manniru amma kasan ni banason rashin tarbiyya ne iron na DaDa sam matarnan kaga dai kawatace amma batada tarbiyya wlh" tafada tana zama kan kuje, duk cikinsu kuwa babu Wanda ya kulata seda tagama surutunta sannan kuma tace "to Aminu da salisu ina yininku tunda kunga kunfini tsayi ai kunga dole nice zan gaidaku ko?" Dasauri suka sauko kasa suna gaidata, amsawa tayi da murmushi kamar ba itace me maganar ba.

Bayan duk sunyi sallahr isha ne suna zaune a parlon daddy yafara yimata bayanin duk abubuwan dasuka faru, seda yakare sannan tace "todama yaya barewa zatayi gudu danta kuma yayi rarrafe, wannan yaron Audu yagado ubansa wlh, itakuma 'yarka seta gado kanwar uwar," kuka tafarayi tana cewa "nidai DaDa ta cuceni ta gur6atamin ahalina Allah ya isana wlh"

Sosai munnir yayi mamakin jin duk abubuwan dasuka faru kuma sarai yagane cewa zuly friend dinsa itace dai zulyn su Sofiyya a yanzu.

Dakyar hajjaju tayarda suje suleja amma tace tare da ita za'aje kuma babu yadda suka iya dole haka suka amince mata.


Bayan sun nutsu ne mama tacewa mommy "Aunty yakamata ayi kiran yaya asanar dashi, tunda kinga shi DaDa tadaurawa laifi semuje muduka munemi gafararta duk dacewa wlh yaya bashida laifi ko daya" mommy tace "eh kam gaskiya bari inkirashi" tafada tana lalubo numbern shi, bugu biyu yadauka, nan takoro masa bayanin abubuwan dasuka faru sosai yayi farinciki a daren shima yabiyo flight yataho jos, a hotel ya kwana, da sassafe kuma yashirya yataho gidan mommy basu wani samu damar yin doguwar hira ba a gurguje duk sungama shiryawa sun hadu a gidan daddy, hajjaju se hura hanci take taki amsa gaisuwar kowa a gidan, sungama saka kaya a mota kenab segasu Abba da Abdul suma sunbukaci aje tare dasu, mota biyu sukayi zuwa suleja.

Sunayin parking a suleja hajjaju tafito dasauri harda gudunta tayi cikin gidansu DaDa tana fadin "DaDa aminiya ta kifito yau gani nazo miki zulanki wlh"

DaDa dake lazimi tafito a wargaje don ko a mafarki bazata manta muryan hajjaju ba, kuma rabon da akirata da DaDa tun kafin 6atan zulai.

"Hajjaju kece ina zulan?" DaDa tafada bayan sunyi ido biyu da hajjaju, kafin hajjaju tayi magana su mommy sunyi sallama.

Mommy CE agaba, se Sofiyya tareda zuly, sannan mama, tunda DaDa tayi tozali da zulanta tayanke jiki tafadi agurin a sume "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun" duk suka fada sannan sukayi kanta suka cicci6eta zuwa dakinta, aka kwantar da ita kan sallayya anayimata fiffita, mama duk hankalinta yatashi se kuka takeyi zuly nabata hakuri.

hajjaju CE tadibo ruwa cikin Kofi batare da kowa ya lura ba kawai ta kwarama DaDa a fuska, farfadowa tayi hadida shidewa tana salati, a hankali tafara bude idonta tana karewa yan dakin kallo, Abba, Abdul, Salisu, Munnir, Aminu, Alhjin kano, Mardiyya, Zulaikha, Sofiyya, Zuly dakuma hajjaju maida iron tayi ta kulle sannan a hankali tace "kuje kuyi kiran ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?su Siddika"

Sofiyya CE tamike tanufi sashensu, babu zato suka ganta, baban siddikan ma yananan bayajin dadi don haka befita ba, sanar dasu tayi duk suzo inji DaDa, don haka babu wani 6ata lokaci duk suka taho, koda suka shigo sukaga bakin fuska sundauka rasuwa akayi amma se sukaga kowa da kowa agurin, Aunty hafsat dai binsu da kallo takeyi daya bayan a hankali idonta yasauka akan mama, dasauri tamike taje kusa da ita tana fadin "Aunty ashe da rabon zansake sakaki cikin idona" itadai mama kallonta takeyi amma takasa gane ko wacece ..................
'

07046767662 Maryam-Ashner CE
[9/10, 8:45 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*

_*Ina maraba da kowa, ammal duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_


_*TALLA*_
Kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway duk karshen wata ga wacce tasiya yakai sau bakwai koda 500mb take siya tanada kyautar 1gb, wadda ta siya sau 5 kuma tanada kyautar 500mb.
MTN AIRTEL
500MB 150 200
1GB 300 350
2GB 600 700
3GB 900 1000
4GB 1200 1350
5GB 1500 1700

Cal/whatsapp 07046767662 facebook Maryam-Ashner Isma'l Usman.


_*TALLA*_
Turaruka kamar humra me dadin kamshi da kama jiki, dakuma saukin farashi, akwai hadin amarya, turaren wuta, set na musk, turaren kaya, turaren mopping, body spray d.s muna maraba damasu siyan daya ko sari, dakuma masu online business gameson sari kuma batada jari, zata iya tara kudinta a gurina, 07046767662 domin karin bayani.

_*TALLA*_
Lace, shadda, atampa, yadi, voil, abaya, lafaya, material, takalmi, jaka, akwati dakuma kayan kitchen kome kikeso zaki samu da yardar Allah, cikin saukin farashi 07046767662 domin karin bayani.

Episode 48


aunty hafsa ta fahimci kamar kallon rashin sani mama keyi mata don haka Kafin mama tayi magana tayi saurin cewa "baki ganeni bako? Hafsat CE little hafsynki ta yola" zaro idanuwa mama tayi cike da mamaki, tabbas tunda sukayi ido hudu take tunanin tasan fuskar amma da dadewa, kulle idanunta tayi cike da tausayawa don ko makaho yashafa hafsat seyasan batajin dadin rayuwarta, duk ta rame, tayi baki tawani kyamushe ba kyan gani, hafsat din datasani nada haske, kyakykyawa me tsabta kuma yar gayu, bude idanunta tayi tana kare mata kallo tace "yaya akayi little me yakawoki gidanmu"

Hawaye aunty hafsa tagoge sannan tace "is a long story aunty lets wait for a chance zan Baki labari"
Hajjaju datasake baki tanabin hafsat da kallo dasauran matan gida tamike zunbur taje kusada mama tafashe da kuka tana fadin "zulai ashe rai kanga rai, oh duniya, kullum senayi mafarkinki nayi sadaka addu'ata ta kar6u kenan"

DaDa ce tatashi tazauna tana hararar hajjaju tace "Allah wadaran makaryacin daya kasa canza hali" Alhajin kano yaga zasu fara abinda suka saba, dukda tsawon shekarun dasuka diba basa tare bazesa su mutunta juna ba don haka yayi gyaran murya yafara magana bayan sallama da salatin annabi sannan ya daura da "batare da 6ata lokaci ba, na wakilta Aminu yayimana bayanin bakin fuskar damuke gani dakuma abubuwan dasuka faru a takaice"

A nutse daddy yayi bayanin komai da komai, sannan mama tadaura da bada labarin yadda sukayi rayuwa itada zuly da dadi daba dadi har izuwa yau, masu saurin kuka tuni sunfara kuka, masu jimamami sunayi, Abba kuwa yakasa hada ido dakowa a gurin se sunkuyar dakai yakeyi, bayan komai ya lafane Abba yasake neman yafiyarsu duk suka yafemishi.

Har yamma duk sunanan, mazan sunanan sashin su DaDa a dakin marigayi BaBa, matan kuma suntare a sashin su siddika, duk sunso tafiya amma aka hanasu dole suka hakura zuwa gobe dasafe.

Bayan anyi isha'i zuly, siddika da Sofiyya suna zaune a dakinsu siddika sunacin abinchi suna yar hirarsu wayar Sofiyya tafara haske, lekawa tayi taga handsome kekira ai ba 6ata lokaci ta ajiye spoon din hannunta tadau wayar tana fadin "nidai nayi fushi tunda seyanzu ake nemana"

Siddika tarike ha6a tana kallon zuly tace "sis kinga rashin kunya ko, nima bari inkira nawa mijin" tafada tana dauko wayarta, murmushi zuly tayi tace "Allah yabar kauna" tana rufe baki itama wayarta tafara ringing, dubawan dazatayi taga sunan MUNNIR ya bayyana, dadan mamaki kan fuskarta tadauka tare dayin sallama, amsawa yayi sannan yace "inbabu damuwa inason ganinki, a harabar gidan gurin bishiyoyin nan don Allah kizo" yakarasa yana marairaicewa

To tace tana mikewa tazari hijabin siddika dasukayi sallah dashi, tazo fita Sofiyya dake waya ta kalleta tace "sis to where?" Zuly tace "banisa zanyi ba, munnir keson magana dani a waje"

Sofiyya tazaro mayafi tana yafawa tace "muje inrakaki aiba sanin kan gidan kikayi ba" Siddika tafasa wayar dazatayi tadau mayafi itama tace "I cant stay here a lone"

Fjtowa sujayi su ukun, Siddika da zuly suna yar firarsu yayinda Sofiyya ke wayarta da handsome.

Bayan sun hango munnir ne suka dakata sukabar zuly takarasa itakadai, Abdul dake kallonsu yana zaune bakin wata bishiyar dake nesa kadan datasu munnir yabukaci Sofiyya takarasa can, ba kunya tacewa siddika "since you were not invited kika biyomu, u can stay alone here and wait for us don nima ga mijina can yana jirana, if you can't then go back" takarasa tana mata gwalo da dariya tayi gaba, Cizon yatsa siddika tayi tana fadin "illar yin saurayi awani garin kenan, nima dayanzu nace yazo muzanta ai" tajuya takoma cikin gidan cike da takaici dakuma kudirin kulle kofa kosun dawo bazata bude ba.


Adakin Baraka duk suka baje, mommy da mama, itama aunty hafsat albarkacinsu yasa tazauna suna hira, can dai mama ta kagu taji abinda yafaru tace "little tell me about it now, I can't wait any longer" mommy tace "gulma nacinki ai bakya iya jiraba, hafsat dauketa kuje can kuyi hira bcos I'm tired you guys shouldn't disturb me" mikewa sukayi suka fice itakuma mommy tamike kafafunta akan kujera.

Bayan sunje dakin hafsat sun zauna aunty hafsat tace "kinsan mu familynmu ba'a auren bare, tunkafin kitafi nakeson yaya (baban siddika) araina amma ban bari kowa yasani ba, nayita rikewa har Allah yasa shida kanshi yafurta min yana sona, tun a lokacin daya furta Alhjn kano ya tsawatat masa kuma yasanar dashi baza'a bashi aurena bcos yasan komai na familynmu amma yaya bejiba ya dunga bibiyata to dama nima inasonshi din don haka nabashi har number muka fara Soyayya tun munayi a 6oye har yafara fitowa, lokacin da muka zana waec ne akaso ayimana aure nida yar uwata amma nabijire nace niduk dangi babu Wanda yamin se yaya, kinsan meya faru aunty? Kasancewata marainiya a hannun yayan babana nake dama haka suka kwacemin waya suka kulleni, nasha wahala sosai kuma na kafe duk wuyar danasha besa na canza ra'ayina ba, daga karshe suka bani za6i, indai nayarda na auri yaya yataho dani garinnan to natafi kenan babuni babusu, kokuma inhakura su auramin wanda sukeso inyi zamana tareda yan uwana. A lokacin idanuwana duk a rufe suke don haka nadauki za6in farko akayi auren aka kawoni nan, a satin danazo nafara danasani, mijina dagaske yake kaunata babu irin kaunar dabaya nunamin, amma uwar mijina ko hada ido dani batason yi, balle kuma kishiya ta datadau tsanar duniya tadauramin, aunty duniya tamin kunci, dana tambayi yaya ina kike seyake bani labarin tsautsayin daya sameki, kullum nakai goshina kasa senayimiki addu'ar Allah ya bayyanar dake aunty, tun da iyayena suka rasu bansan menene maraiciba sebayan aurena, yaxama banida mutumin dazan kira nawa, balle har insanar dashi damuwata insamu sauki, ahaka nasamu ciki da dadi daba dadi har lokacin haihuwata yazo amma sanadin kishiyata wlh narasa babyn, nayi kukan rashinsa domin tun yana ciki yazamemun abokin hira" nan dai aunty hafsat tabata labarin dukkab abubuwan dasuka faru daga haihuwarta zuwa yau data ganta.

Dukansu kuka sukeyi sosai suna rungume juna mama tace "share hawayenki yanzu nadawo gidannan rayuwar kunci takare a gunki insha Allah" murmushi tayi tace "Aunty aiba zama zakiyimana anan ba, nan dadan lokaci kadan kema zamu aurar dake insha Allah" nan dai suka cigaba da hirarsu, sosai mama taji tausayin hafsat har cikin ruhinta.


Hajjaju kam nacan tare da aminiyarta ayi fada ashirya,.
Cikin hirar tasuce hajjaju kecewa "nifa haryanzu bason hadin auren zulai da salisu najeba atoh, garama kar asoma don abinda yawuce yariga yawuce, mucigaba da amintarmu kawai"
Kallonta kawai DaDa take da mamaki tace "to idankuma yaran suka nuna sunason junansu fa?"

Mikewa hajjaju tayi tana karewa DaDa kallo tace "ba wannan maganar wlh, duk na gano sokike ahadasu aure kuma billahillazi sedai sumutu koke kimutu amma baza'ayi wannan hadinba"

Itama DaDa mikewa tayi tace "sedai ke kimutu hajja, insha Allahu sekin mutu" da kuka hajjaju tabar dakin tafita tana neman su daddy, tana tafe tana surutu "Aminu kuzo mutafi yanzu kafin DaDa ta kasheni, indai namutu wlh DaDa ta kasheni" sambatun datake famanyi kenan tana tafiya, gurin bishiyoyin nan tafito don anan ne take tsammanin ganinsu,.

Tundaga nesa munnir kejiyo surutunta a fili yace "anan dinma setayi haukar kaiii" zuly tayi dariya tace "nagafa kamar kuka takeyi kozamuje muji menene" mikewa sukayi suka nufi inda take.

Abdul da Sofiyya ma sunjiyo surutun nata, tsaki sofiyya

23 / 26