CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 26

15K to 18K   out of 76.5K words

dawuri sukahau Shirin tafiya suleja, Sofiyya Baki harkunne Dan murna.
Tundaga wannan rana Sofiyya da Abdullah kullum sesunyi waya, bashida takamaimai lokacin kiranta, duk sanda zuciyarsa tatuno Masa da ita kiranta yakeyi, abin har mamaki yake bashi ganin kusan tunaninta yafi yawa yanzu a rayuwarsa. Ko agida umma kasa shiru tayi rannan tace mishi "kwana biyu naga nishadi kakeji, kodai kudinkane yazo" Abba kuwa is like ya harbo jirgin, dan har wani littafi yabashi yace yakaranta it will help him in that situation, shikam ko ajinkinsa yakarba ko duba sunan beyiba yaje ya aje yacigaba da hakkokinsa hankali kwance.
A 6angaren Sofiyya madai abin ba sauki, dan 'yan suleja babu Wanda besan labarin Abdul ba, kodan yawan kiranta dayakeyi ya Isa yasa asanshi, balle kuma abun yahadu da parrot Baki ba hutu, duk inda tayada zango zatace Mr handsome kaza da kaza but sincerely speaking ita batasan cewa soyayya takeba sam tadauka kawai kamar irin friends suke, maganar number din Usman kuwa harta gaji da magiya yahanata, haka tahakura ta kyaleshi badan tasoba.

Bayan kwanaki, zulyce zaune kan kujera tazuba uban tagumi, tayi zurfi cikin tunaninta, mama da shigowarta dakin kenan tazuba Mata idanu cike da tausayi tace "zulaikha" dasauri tashare guntun hawayen daya zubo Mata, tace "mama harkin dawo?" Mama tace "zulaikha bansan yazanyi da wannan taurin Kan nakiba, nace kidena yawan tunani Amma kullum Abu secigaba yake" numfashi zuly taja sannan takamo hannun mama tace "mama kiyi hakuri kiyitamin addu'a, Nima ba'ason Raina bane, tunda naganshi nakasa samun sukuni, Kuma Gashi bansan inda zansake ganinshi ba" lallashinta mama tahauyi, Dan tasan Koda taganshi aure baze yiwu a tsakaninsu ba.

Suleja
Sofiyya ce zaune kan irin fararen kujerannan, acan bayan gidan Inna tana Danna waya Kiran Mr handsome yashigo, Dan murmushi tayi batareda tadau wayanba harya katse, wani kiranne yasake shigowa, seda yakusa katsewa sannan tadauka tana sakeyin murmushi,
A office, Abdul ne kishingide Kan kujerarsa jin tadau wayan yasa yayi gyaran murya yace "nagode" yar dariya tayi tace "you are welcome" yataso daga kishingidar da yayi yace "Wai yaushe za'a denamin yanga ne" tayi fari da idanu kamar Yana ganinta tace "wakemaka yanga?" Yace "dawa nake waya" tace "dawata bafullatana" yace "tonidai afadamin yaushe zankira sau daya adagamin Kira?" Tayi murmushi tace "I don't know fa" yace "ok towaima meyasa senayi Kira uku kofin haka Kika picking?" Tace "au hakama zakace? Yanzufa Kira na biyu nayi picking, but tunda haka kakeso done" yace "yauma dai nayi sa'a ne ai ka'idarki ce se mutum yakira fin sau uku" tayi murmushi sannan ta kautar da zancen da fadin "ya office" yace "kalau, when will you return" tace "well garinne bawani dadima wlh, not like before, inaga two weeks to my graduation party zandawo" yace "meya hana garin dadi this time around" kafin tabashi amsa, siddiqa takaraso wurin taja kujera tazauna tana kya6e baki, kallonta Sofiyya tayi tace "kekuma fa" hararata tayi sannan tace "done with your man malama" itama Sofiyya hararatan tayi tace "kyaji dashi jarababbiya" sannan tamaida hankalinta kan waya tace "can you call me later?" Duk abinda take fadama siddiqa yaji, but wannan ai yazama rainin hankali, tayaya suna waya zata tsaya hira, after that kuma tacemishi Wai can he call her later? What nonesense, inama laifin tace mishi I will call later? Kin kulata yayi, tasan sarai yajita hakan yasa tace "kajifa menace" kit yakashe wayar batareda ya amsa mataba. Kallo tabi wayar dashi cikeda mamaki, what rubbish, "Wai meyake damun wannan guy dinne?" Tafada a fili, siddiqa ta kwashe da dariya tace "better Kinga madan huta before kudawo daidai" hararata tayi tace "munafuka ashe idonkine kekan waya, kunnuwanki nikaina" tabe Baki Siddiqa tayi, batadaice komaiba, Sofiyya tamatso da kujerarta kusada ta Sofiyya tace "ke bani insha, naga kinzo kina zunbura baki" siddiqa tayi Dan gajeran tsaki tace "waye inba waccar tsohuwar ba, Wai mutum be Isa yadanyi dariya taganiba setahau hawaye, kalan taja yanzu a zageni inma ba'a hadamin da dukaba" kyalkyalewa da dariya Sofiyya tayi harda Dan guntun hawayenta, seda tayi me isarta sannan tadago tace "siddiqa ta Inna, Inna ta siddiqa, shiyasa wlh Sam garin bemin dadiba wannan zuwan, duk gidan kamar gidan makoki" siddiqa tace "sekace me ciwon aljanu haka take wlh, daga tayi mafarki shikenan setabo ta dagamana hankali" Sofiyya tace "waini mafarkin me takeyine haka? Ni banta6a ganin hakaba wlh" siddiqa tace "waifa akwai wata 'yarta data 6ata naji ana fada, shinefa intayi mafarkinta sekiji tafarka tana zulai zulai" duk su biyun dariya sukayi, Dan yadda siddiqa tayi maganar kamar inna, Sofiyya tace "wlh yarinyar nan bakida mutunci" tasake cewa "itakam Inna tana yara dayawa gsky, tab runduna" siddiqa tace "wani irin yara, kwata kwata su nawane? Daga Alhajin kano, se ummanki se ita wadda akace ta6ata, se antyn yara ta garinku se Abbana, su biyarfa kenan" Sofiyya tace "eh hakane fa bawani yawa, uncle din kanon nema banfiye ganinsa ba" siddiqa tace "yo ai kamarfa ancireshi a dangi, Dan yadda naji labari Wai can gidanshi ita zulai din ta6ata, shine Inna tace kada wadda yake zuwa wurinsa, tofa shine kikaga bame zuwa sedai shi yazo, kuma duk sanda yazo nan baya tafiya da farinciki Dan Inna agaba take sakashi taita kuka Wai yanemo mata 'yarta" Sofiyya ta girgiza Kai tace "Allah sarki, Allah ya bayyanata" siddiqa tace "watakila fa tamutu, tunfa kafin a haifeni, ancedai ke anhaifeki Amma ko sunanki ba'ayiba" Sofiyya tace "kaiiii Ashe abin yadade" hakadai sukayita hirarsu har yamma sannan suka shiga gida.

Abdullah kuwa ranshi duk a 6ace yatattara yanufi gida, Koda yaje gidan ma haka yashiga kamar saniya, sa6anin da dayake shiga fuska a sake, dukda dai bawai murmushi yakeba but fuskar asake take, Amma yaukam, halin dane yadawo, daga furta inayini wa umma yashige dakinsa, ya ajiye jakarsa ya zauna kan kujera, zuciyarsa zafi take masa, jiyake kamar yadau waya ya kirata but baze biyewa zuciyarsa ba, Dan seta jawo masa raini, daukan remote yayi ya kunna tv, rabonshi da kunna tvn dakinsa harya manta, idonshi akan tvn but zuciyarsa na suleja, a fili yace "can't call me an apologize?" Girgiza Kai yayi irin zakisani dinnan, a tvn ya hango budurwa da saurayi se shouting sukewa junansu, nutsuwa yayi yana sauraron abinda suke cewa, it's like laifi budurwar tamasa tana Kuma bashi hakuri but yaki sauraronta hakan yasa itama ta tunzura tafara yimishi shouting itama, ganin yakiyin shiru yasa tayi wucewarta, Zama a wurin yayi, can sega wani yazo da alamu abokinsa, ya tambayeshi meyakeyi Nan shikadai, yabashi labarin abinda yafaru, amaimakon yayi masa jaje se tintsirewa da dariya yayi sannan yace masa "you are in love man" zabura yayi yace "what!" Abokin yace "yes because.........." Tsab yakaranto abinda Abdullah yakeji kan Sofiyya kamar dashi yakeyi, shima zaburan yayi yamike tsaye, hannunsa narawa yadau remote yakara volume, seda yagama ji tsab Kuma babu maraba cikin abubuwan da yakeji kan Sofiyya, gumine yajikashi sharkaf, zarya yafarayi daga farkon falon zuwa tsakiya zuwa karshe, "what love! No no I'm not ready wlh," haka yayita maimaita wa cikin ranshi, Jin ana Kiran sallahn magrib yasa yanufi toilet yadauro alwala yafito yanufi masallaci.

Koda dare kasa runtsawa yayi, ga sanin tabbas cewa he's in love, gakuma rashin Jin muryar masoyiyar, Yana cikin tunanin mafita yatuno da book din da Abba yabashi rannan, mikewa yadauko, se sannan yaduba sunan 'YOU ARE IN LOVE' murmushi yayi yace "so Abba yasani tunkan insani, much ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????love abi" Zama yayi yahau Karantawa, aciki yaga solutions na many problems akan soyayya, seda yafarajin barchi sannan yazo rufe littafinyaga wani topic Wai 'how to express' rufewa yayi yace "sekuma gobe " addu'a yayi yakwanta, ba'adau lokaciba kuwa barchi yayi gaba dashi.

Suleja
Hankalin Sofiyya duk baya tareda ita, gaba daya tarasa nutsuwarta ganin har tazo kwanciya bataga Kiran Mr handsome ba, dukta damu takuma rasa dalili, barchi ya kauracewa idanunta har kusan 11pm Bata rintsaba, se juye juye take, setadau wayan zata kirashi sekuma tafasa, ranar dai barchi barawone yadauki Sofiyya....................
............
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Episode 14
Koda gari ya waye Sofiyya tashi tayi da kunci a ranta, duba wayarta tayi kozataga missed call din Mr handsome, but wayam bata ganiba, hakan yakara 6ata mata rai, kashe wayar tayi gaba daya, yinin ranar dai yinshi tayi kamar marar lafiya, ko a gidanma se cewa tayi ciwon Kai ke damunta saboda yadda akayita tambayar ta ganin tazama so silent.

A 6angaren Abdullah ma hakan take, Abu biyu sunhadu sundameshi he admitted that he's in love wannan ba karamar damuwace a gareshiba and Gashi yahadu da stubborn girl zata dinga samishi headache, Koda yayi Shirin office harya fita yatuno da book dinnan, hakan yasa yadawo yadauka sannan yatafi.
A office babu wani aikin da yayi, yasaka littafin a gaba yana Karantawa, topic din dayafi bawa muhimmanci kuwa shin 'how to express' tabbas yakaru sosai Kuma ya fahimci abubuwa dayawa but wani abun seyakega kamar baze ta6a iyawa ba, zuciyarsa nata zugashi akan yakira Sofiyya amma yahana kanshi kiranta acewarsa ita zumace seda wuta tukunna,.
Dadare kasa hakuri Sofiyya tayi, duk yadda taso ta daure takasa abin hardasu hawaye, tun magrib ta kunna wayarta expecting his call but yanzu almost 10pm ko flashing dinsa bata ganiba, zuciyarta tagama raunata jitake inbatayi waya dashiba kamar mutuwa zatayi, gashi batasan halinda yake cikiba hakan yasa tilas tadau waya tayi dialing numbern shi, but unfortunately wannan matar tace mata is kindly switched off, wurgi tayi da wayar ta rushe da kuka, harseda siddiqa tafarka tahau tambayar ta, cikin kuka take cewa "yazanyi inwani abu yasameshi? I'm the course of everything wlh" dukda cewa siddiqa batawani fahimceta ba Amma haka tahau lallashinta har tasamu tayi shiru sannan tace "Kinga tunda kinyi shiru ni bari inyi kwanciyata, kekuma inkika Gama tunanin kyayi barchi, Amma Dan Allah kada kisake irin wannan kuka, idanma yazama dole sekinyi to kifita waje kokuma kirufe Baki kiyita hawaye Dan kada kitasheni, inyaso dasafe kyabani labarin abinda yasaki kukan" tana gama fadin haka taja bargo tacigaba da barchinta hankali kwance. girgiza Kai Sofiyya tayi cikeda takaici, watoma she don't care koma meya sameta "hmmm zan ramane" tafada sannan tamike tanufi bandaki tadauro alwala tahau yin sallah.
Abdullah tunda yadawo office yakasa hakuri seda ya dialing numbern ta, but Jin wayar switched off yasashi jin tsananin takaici, watoma kashemasa waya tayi, hakan yasa shima yakashe wayar tashi, "yarinyar nan dole Sena koyamata hankali tukun zamu zauna lafiya" yafada a fili sannan ya ajiye wayar, dakyar yasamu yadanne zuciyarsa yayi barchi.
Dasafe duk zuciyoyinsu Babu Dadi, kowa da abinda yake tunani, itadai Sofiyya tunda garin Allah yawaye take kokarin kiranshi but amsar Bata canza ba, shikuma gogan yaki kunna waya se kunci yakeyi.
Bayan azahar PA dinsa tazo takawo masa waya Abba nason magana dashi, cemata yayi taje ze kirashi, bayan fitarta ya kunna waya yakira Abba, sungama waya ko cire waya a kunnensa beyiba Kiran Sofiyya yashigo, dubawa yayi ganin number dinta yasashi kara ware idanu Yana sake tabbatarwa, murmushi yayi yace "where's the stubbornness baby?" Bedauka ba harta katse, ko seconds ba'ayiba wani Kiran yasake shigowa, girgiza kafa yake sannan yace "now is my turn" daga wayan yayi yakara a kunne batareda yayi magana ba.
Sofiyya da tunda tayi sallah take zaune kan darduma taketa faman Abu daya wato kiranshi a waya, kuma take samun amsa daya wato switched off, hawayene yahau zarya kan kumatunta, Bata gajiba tacigaba luckily taji yashiga, da murnarta tasaka handsfree but abin takaicin harta katse ba'a picking ba, sake kira tayi, tayita ringing harta fidda tsammani sekuma taji andauka.
Kuka tafashe dashi Wanda dama kiris take jira, hankalin Abdullah yatashin Jin sautin kukanta, a rikice yahau tambayar ta "cutie menene? Meya faru please" kasa yimishi magana tayi se kuka take, shiko dukya rikice se jeramata tambayoyi yake, dayaga batada niyyar amsa mishi seya hau lallashi, dakyar yasamu tayi shiru se sauke ajiyar zuciya take, bayan 'yan mintuna yace mata "now can you tell me what really happened" cuno Baki tayi kamar Yana ganinta tace "meyasa ka kashe waya tun jiya? Inata Kira akashe I thought something bad happened to you" wani dadi yaji na musamman, har yakasa rufe bakinshi tsabar murna, gimtsewa yayi sannan yace "you caused it cutie" cikeda shagwa6a tace "I caused what?" Yace "you never call me sedai ni inkiraki, kuma innakira ma ba lallai kidagamin ba that's why I decided to stop calling everyday" dasauri tace "no please don't stop calling me, kaji nadena" cikeda farinciki yace "promise?" Tace "promise" dahaka suka cigaba da hirarsu wadda a zahiri hirar masoyace, duksu biyun sunyi missing din juna, sosai kowannensu yayi farinciki, sundade suna wayar harseda suka farajin kiraye kirayen sallahn la'asar sannan sukayi sallama, kowa na farinciki.

Dadare wurin dinner a gidan Abba, kowa nazaune Amma Abba shiru begitoba, Abdullah yakalli umma yace "umma Abba fa" umma tace "uhm bayajin Dadi" Usman yace "umma badai wancan ciwon nashi ba ko?* Abdul ya harareshi yace "who told you ciwone ke damunshi?" Umma tace "uhm to ai abin yazama kamar ciwo Abdullah, tunda dazaran yayi mafarki shikenan sekuma ya canza" Abdullah yace "to umma mafarkin me yakeyine Dan Allah" umma ta ware hannu alamar i don't know sannan tace "shekaru kusan 17 kenan Yana fama dawannan matsalar Amma haryau beta6a fadamin mafarkin me yakeyiba" Usman yace "to umma muje asibity Mana please aduba manashi" umma tace "eat your food and be quite" shiru yayi Dan yau Sam beji dadiba, kasancewar babu Abba a gurin, dama shikadai keyimasa hira, to yaukam sedai yayi gum Dan bame kulashi.

A kd baban munnir ne da amminsa sunacin abinci, Alhaji salisu yace "kinsan danki aure yakeso" Ammi ta ajiye spoon tace "Wai munnir kowa?" Yace "eh shifa, zuwanda yayi kwanaki bananan ai abinda yakawoshi kenan" Ammi tace "tofah, sudan hajiya angirma" Alhaji salisu yayi murmushi yace "naso zuwa can gidan hajiyan but lokacinne aka turani ibadan dinnan that's why bansamu najeba, se faman damuna yake da waya, shiyasa nace Miki this week zanje insha Allah" ammi tace "tofa, yarinyar acan take kenan?" Alhaji yace "eh ai 'yarkice Sofiyya 'yar wajen Yaya Adamu" murmushi sosai Ammi tayi da farinciki a fuskarta tace "alhmdulillah aikuwa ya iya za6e wlh Masha Allah" shima Alhaji murmushin yakeyi yace "aikuwa dai, but kinsan akwai alkawarin auren 'yar wajen zulaikha akanshi, shiyasa nakeson inje muhadu dashi tukunna kafin inma Yaya magana" gum ammi ta kimtse fuska ta hade rai tace "to kasandai hajiya bazata amince ba, Kuma Nima mahaifiyar munnir ban amince ba, aitun farko nafada maka bazan yarda da wannan hadinba" Alhaji ya marairaice fuska yace "haba sarauniya, abinda yafaru aiya wuce, kiyi hakuri kibani hadinkai incika alkawarin Dana dauka" tsuke fuska takumayi tace "gsky alhaji nidai banaso, kumama wayasan inda suke yanzu? Watakilama yarinyar tayi aure, aita girma sa'ar Sofiyya ce inban mantaba" Alhaji yace "nasan zeyi wuya idan tayi aure, don zulaikha nason yarinyar tayi karatu sosai, kuma inda suke bazeyi wuyar samuba, Zansa a bincikamin a hankali" mikewa ammi tayi tace "to wlh badai danaba, tabdijam yarinyar dabata da uba shegiya Kuma gantalalliya wadda ba'asanma inda takeba, wlh garama ka janye" tana gama fadin haka tawuce tashiga dakinta takwanta cikeda takaici,. Shiko Alhaji cigaba dazama a wurin yayi, tabbas yasan akwai yaki a gabanshi, Amma ashirye yake............................
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?
By
*Maryam Ashner*

Adinga comment adinga sharhi please
https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn
Join my watsapp group
Mata zallah please =?O?=?O?=?O?

Episode 16
A ranar dai Alhaji salisu besamu sunyi magana da daddy ba, kasancewar gajiya daya kwaso ta tafiya, hakan yasa daddy cewa
"Yakamata dai yau kasamu kahuta, gobe in Allah yakaimu anan Zan wuni, semu tattauna"
Sosai Alhaji salisu yaji dadin maganar, dankuwa sosai yake bukatar hutu.
Dahaka sukayi sallama yawuce gidansa.
Ran munnir inyayi dubu ya 6aci, danshi yaso ace anyi komai angama yau yau, Amma bakomai yau da gobe aiduk dayane.

Abdullah fushi yake sosai, dan bakaramin 6acin rai Bashir yasashi ba, especially ma idan yahau Kiran beautiful jiyake kamar yashakeshi yahuta, haka yatattara yanufi gida rai babu Dadi.
Koda dare yayi lokacin da suka sabayin waya da cutienshi kin kiranta yayi, domin har itama yau haushinta yakeji,
"don me zata barima Bashir yaganta harma ya rada Mata suna Wai beautiful,"
abinda zuciyarsa tadinga fada Masa kenan, Kuma hakan yayi tasirin daya hanashi kiranta, yayi duk wani abunda yasabayi kafin barchi, sannan yayi kwanciyarsa.

Sofiyya ma duk tagama Shirin kwanciya, taduba wayarta taga har 9:30pm Amma babu Kiran Mr handsome, daukan wayan tayi ta kunna data tahau watsapp, waiko zata ganshi, but Nan dinma shiru baya online.
Sauka tayi takashe datan tazuba uban tagumi,.
Inna dayanzu tadan Fara warwarewa tashigo dubasu, taga Sofiyya zaune ga uban tagumi datayi, karasowa tayi tazauna gefen gadon tadafata tace
"Kyakykyawar kishiyata, meya faru da tagumi haka?"
Murmushi ta kakalo tana girgiza Kai tace
"Inna bakomai fa, barchinne bezoba kawai"

Siddiqa dake waya a sununnuke cikin bargo ta leko tace
"Inna wannan mijin nakine bekirata bafa, shine takasa barchi"
Mamaki yakama Sofiyya, lallai siddiqa ta iya munafunci, wato Ashe ba barchi takeba.
Inna tace "haba haba, yo indai mazane kyadena barchi har yaumul kiyama, maza Mike kiyi kwanciyarki"

Murmushi Sofiyya ta kuka kakalowa sannan taja bargo tayi kwanciyar ta.

Bayan Inna tafitane Sofiyya ta dakawa siddiqa duka tana fadin

"Kedai anyi munafuka wlh, jinake barchi kikeyi, amma Ashe ba barchi kikeba kina zaman munafurci,"

Tsaki siddiqa tayi tace

"Kyadaiji dashi, mutum be iya abu saffa-saffa ba, to Bari kiji soyayya ba'a Mata haka wlh"

Harara Sofiyya keyi, dukda ma ba kallon juna sukeba tace

"Soyayya kamar wata ke, kece Kika hada kanki da wannan, hypocrisies everywhere"

Tana gama fadin haka, taja bargonta ta lalubo wayarta, ganin har 10pm yasa ta yanke hukuncin kiranshi.
Dialing numbern tayi, yafara ringing.

Abdullah da kunci ya isheshi se juye-juye yake ya gagara yin barchi, yaga wayarsa tadau haske, janyowa yayi yaga numbern cutie ne, kamar baze daukaba, Amma yasan shima yanada bukatar

6 / 26