Chapter 15 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 26

42K to 45K   out of 76.5K words

daddy yadawo yau bayan sunyi dinner yamikawa Sofiyya wayarsa yace "samin numbern yaronnan Abdul"


Bamusu ta karfa wayar tasaka mishi.

Tabbas yayi mamakin yadda kai tsaye tasaka mishi numbern batare da ta bukaci yabata wayar ta ba.
Wato harma ta iya haddace numbern yaronnan, anya kuwa munnir zeyi nasara akan ta? Ya tambayi zuciyar sa.


Bayan ya kar6a wayar ne yakira numbern kai tsaye.

Da ladabi suka gaisa sannan daddy ya gabatar da kansa, har sunkuyar dakai Abdul yayi jin da wanda yake waya dashi.


"Inaso katuromin numbern Abbanka yanzu" daddy ya bukaci haka.


Suna gama wayar kuwa ya turo mishi numbern, kiran numbern yayi Abba dake zaune tare dasu usman da umma a parlor haji ringing wayarsa.


Shiko Abdul dqya Riga yawuce daki fitowa yayi domin jin me daddy zecewa Abba.


"A alhaji kaine? "Allah sarki"

"To to bakomai, aiba damuwa da yau da gobe duk dayane a gurin Allah, Allah yakaimu bakomai " abinda Abba kefada cikin wayar kenan.



Bayan sun gama wayar ne ya kalli umma yace "dama ranar juma'a ne zankoma gidan su yarinyar nan Sofiyya to mahaifin yarinyar ne yakirani yanzu ya bukaci a kara mishi sati daya, ma'ana kar inje se juma'a tasama"



Wata zufa Abdul yaji ta fara tsatstsafo masa, sum sum yajuya Yakima dakinsa ya kwanta rub da ciki kan gadon sa.


"Ya Allah na rokeka ka bamu ikon cinye duk wata jarrabawa da zamu fuskan ta, Allah ka sassauta zuciyoyin mu" addu'ar dayayi kenan jin yadda zuciyar shi ke tafarfasa.




A gaban Sofiyya daddy yayi waya da Abba so taji duk abinda suka tattauna batasan lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, mikewa tayi ta haura dakinta, ta kwanta ta hau rera sabon kuka.



Mommy ce ta kalli daddy tace "amma meyasa kayi haka? Wannan fa kamar karanta ne"



Beko kalleta ba balle ma ya kulata, shikuma daddy yayi hakan ne don Munnir yasamu isashshen lokacin da zeyi nasara akan Sofiyya, so idan Abban su yadawo se kawai yace mishi yarinya bata son Abdul.





Sofiyya da Abdul kwana sukayi suna addu'ar samun mafita, itakam tanayi tana kuka, shimadin dauriya kawai yafita dase yayi kukan.



Dasafe mommy tawuce kitchen domin shirya musu breakfast daddy ya dau waya yayi kiran munnir.


"Kana jina, kayi duk wani kokarin ka nan da sati daya ka tabbatar Sofiyya ta amincewa aurenka, karka bani kunya "



Karaf a kunnen mommy data dawo hada mishi ruwan wanka, fasa shiga dakin tayi takoma kitchen ranta a 6ace "wato duk wannan abun akab munnir akeyinsa? Hmmmm inkunsan wata ai bakusan wata ba" mommy tafada tana murmushi.



Yauma dai har seda daddy yafita a gidan kafin Sofiyya tafito, don dai kar mommy tamata fada ne wlh dabazata zoyin breakfast dinba don sam batajin wata yunwa kuma.



Tunda tafito mommy ke kallonta cike da tausayi dakuma mamakin yadda ta daurawa kamta son Abdul irin haka.



Tun kafin takarasa gurin dinning mommy tace "zonan kizauna".

Bamusu ta taho tazauna kasan carpet

"Sofiyya har yaushe kika bari som yaronnan yayi miki yawa haka? Bakya tunanin zuwan kaddara ta rabaku? Bakya tunanin mutuwa ta rabaku? Bakya tunanin halin maza nan gaba? Inaso kiyiwa kanki fada kikoyawa kanki hakuri dakomai idan kin rasa ko kuma baki samu ba"



Kuka takeyi silently tabbas mommy tayi gsky wannan son datake ma Abdul yayi yawa to amma yazatayi itama batasan lokacin da soyayyar sa tacika mata zuciya hakaba.



Mommy taci gaba da fadin "duk wannan abinda kikaga daddyn ki nayi shirin Munnir ne, so inaso duk rintsi duk wiya kada kibari munnir yayi nasara akanki, da nayi niyyar siya miki waya karama kudinga wayar ku da Abdul but yanzu kam nafasa becouse yakamata ki koyi hakuri da juriya akan komai, idan har naga kin saki ranki kamar da i will be helping you but inkika cigaba da wannan koke-koken da tunane-tunane tabbas zan barki da daddy "




Tabbas munnir yacika azzalumi, munafiki, macuci kuma maha'inci wlh ko sama da kasa zata hadu bazata ta6a amincewa auren munnir ba, kuma ko mazan duniya sun kare bazata yarda ta aureshiba.


Goge hawayen fuskarta tayi tace "mommy insha Allah zancire damuwar komai a raina, komai yafaru dasanin Allah kuma shine ze taimakemu, amma mommy kenan daddy yafison munnir akaina ko"



"Kul karna sakeji, duk abinda yakeyi yanayine domin baban Munnir din, shi mutumin kirki ne wlh shiyasa wani lokacin nake rangwan tawa munnir din, kitashi kije kiyi breakfast lastly karkiyi wasa da addu'a koda yaushe kinji ko" mommy tafada



Mikewa Sofiyya tayi tana "to mommy insha Allah zanyi kokari"


Dinning tawuce kai tsaye tayi breakfast dinta as usual don dai kar mommy tafasa siya mata wayane amma sam batajin wata yunwa..........
'?




Gameson shiga group dina yayi min magana ta 07046767662
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*


By


*Maryam-Ashner*


_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks*=?L?_


_*TALLA*_
kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway karshen wata ga wacce tasiya yakai sau biyar, koda 500mb take siya=?L? tanada kyatar 1GB, wadda tasiya sau hudu kuma tana da kyautar 500MB.
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook =?G?Maryam-Ashner Isma'l Usman

Episode 34

Yinin ranar Abdul yayi shine cikin kunci, aikin ma bewani maida hankali yayishi yadda yakamata ba, haka ya tattaro yabaro office din.



Har yayi hanyar gida ya tuno da anty zainab, juya akalar tukin yayi zuwa can gidanta.



Dazuwansa yatarar da anty zainab tana yiwa zuly kitso don a yanzu zuly tamaida gidan tamkar gidan tsohonta, kullum data gama aikace-aikacen da takewa mama zatayi mata sallama tanufi gidan anty zainab, duk wannan abun tanayinshi ne don tadinga samun update akan su Abdul amma shiru, don kuwa ko ita anty zainab din batasan komai ba so far.



Komawa yayi dasauri don yayi garajen shiga gidan batare da neman izini ba.



Zuly kuwa rai se farinciki, dasauri ta kwace kanta daga hannun anty zainab ta daura dankwali tana ta fara'a tace "anty yaronki nefa yazo bari inje inshigo dashi"



Girgiza mata kai kawai anty zainab tayi tana murmushi don wannan rawar kan datakeyi akanshi ba lallai ne tasamu ganin hakoransa bama.




Lekowa zauren tayi tace "yaaya bismillah kashigo"


Tabbas seyanzu ya tuno da labarin karyar data bayar akan munnir waccen ranar, nan yaji wani haushin ta yacika mishi zuciya, batare da yasake kallonta ba yawuce yashige cikin gidan.



dasauri tabi bayanshi tayi kitchen ta dibo masa ruwa takawo masa, nan ma dai ko kallonta beyiba baikuma da niyyar shan ruwan.



Anty zainab tace "yanaga ka rame ne yaro, kayi rashin lpy ne? "



Sosa kai yadanyi yace "a, a anty aikine kawai"


Zuly dai na gefe tace "sannu da zuwa yaaya ina yini? "


Badon da anty zainab a gurin ba to dababu abinda zesashi amsawa amma bayason anty zainab taita mishi mita don haka yace "lpy"



Anty zainab batace komai ba, don daganin shi tasan akwai matsala a tattare dashi sedai babu yadda za'ayi yayi magana a gaban zuly tasani sarai don haka tace "zulaika kozakije gida idan yatafi na aika akiraki mu karasa kitson ko"



Ba haka tasoba, taso ace a gabanta yafadi komai don dama abinda take jira kenan, amma bakomai zatasan yaddda zatayi ta bugi cikin anty har tafada mata komai.



Sallama tayi musu sannan tafita, koda tafita bata tafi gida kai tsaye ba, seda tatsaya tayi kiran munnir domin jin abinda ke faruwa don kwana biyunnan tayita kiranshi amma baya amsa wayar ta.



Bugu uku yadau wayar yana "kedai idan mayyace kika kama mutum yashiga uku wlh"


Maganar sa sam bata wani dameta ba, don inda sabo aita saba don haka tace "ya ake cikine maganar su Sofiyya? Yanzu naga guy din yazo unguwar mu"



Munnir dake tare da sabit yace "to ina ruwana, niyanzu nariga naci nasara domin saura kiris kiga invitation card na yawo a gari"



Wani iri taji a zuciyar ta, bakinciki da kuma farinciki, katse kiran tayi don jin wasu irin hawaye na kokarin zubo mata.



Durkusawa tayi a gurin tahau kuka, can kuma tahau goge hawayen ta tana cewa "to kukan mekuma nakeyi, akan me ma zanyi kuka, ai abinda nakeso kenan kuma yafaru, yanzu kokari zanyi insamu gurbi a zuciyar guy dinnan kawai"



Mikewa tayi tana goge sauran hawayen ta tanufi gidan su.



Abdul kuwa be 6oyewa anty zainab komai ba cikin abubuwan dasuke faruwa, bayan tagama sauraron shi tace "kaga babban kuskuren da kayi ko yaro? Sam babu kyau cin amanar iyaye a rayuwa, kaine kasaka Sofiyya taci amanar iyayenta ta hanyar amsa kiranka da kuma gayyotoka, sannan harda binka zuwa inda kukaje duk batare da sanin iyayen ta ba, wannan seya zama darasi a gareku duka, don da'a ce baku hadu a wancen ranar ba toda duk abin bekai hakaba"



Mekaratu yakamata kasan cewa
_*base mace nada aure ne ya wajaba akanta ta tambayi izinin zuwa ko ina kafin taje ba, idan da ladabi da biyayya yanada kyau duk inda 'ya zataje tafara sanar da iyayenta tukun domin zuwa cikin aminci da dawowa cikin aminci =?L? hakika iyayen dasuka dage da sanya idanu kan tarbiyyar 'ya'yansu basu cancanci karya da cin amana daga wurin 'ya'yayensu ba*_ Allah yasa mugyara




Haka dai anty zainab tayita yimasa fada daga karshe kuma tayi masa nasiha takuma bashi hakuri sannan ta tunatar dashi addu'a a komai dakuma ko'ina.




Godiya yayi mata sannan sukayi sallama ya wuce, tuki yake yana tunanin maganganu anty zainab, tabbas yayi kuskure amma insha Allah baze sake ba.

Kuma yadan samu sassauci kan bakin cikin dayakeji dazu.



................... Dadare gurin dinner yau tare da munnir daddy yashigo gidan, kuma tare suka hallara gurin yin dinner.



Sofiyya da gangarowarta kenan taja kujera tazauna ta kalli munnir tayi murmushi sannan tace "yaaya munnir barka da dare"



A bazata yaji maganar tata, mommy da daddy kam mamaki ne ya lullu6esu, daddy na farinciki mommy kuwa na akasin haka.




Washe baki yayi yana "barka dai sister, yakike"


Tana murmushi tace "lpy kalou kaifa? "


Yace "kalau nima, yau kinga tare zamuyi dinner "



Suna cin abinci suna hira tamkar babu abinda yata6a faruwa, da munnir zetafi har rakiya tayi masa, a jikin motar sa tatsaya tana kallonshi tace "yaaya Munnir don Allah kayi hakuri kan abubuwan dasuka ta faruwa, wlh sharrin shaidan ne, amma insha Allah hakan baze sake faruwa ba i promise" takarasa tana hade hannunta waje guda alamun ban hakuri.




Yau munnir mezeyi inba farinciki ba, ai babu wani 6ata lokaci yace "haba Sofiyya wlh bakomai ai ninema yadace inbaki hakuri nikam ai bakimin komai ba"



Sallama sukayi ta shige gida, shikuwa yana shiga motar yasake dj yana girgiza kai, yau ina ze tsoma kanshi don dadi?



Kiran wayar sabit yayi ya shaida masa abinda yafaru, tunda sabit yaji labarin ya girgiza kai yace "akwai lauje cikin nadi malam kama dena wani farinciki kawai kazo gobe muyi magana"



Katse kiran kawai yayi don bayason jin komai idan ba fatan alkhairi za'ayi masa ba,



Mommy kwana tayi tana yiwa 'yarta addu'ar za6in Allah don abinda Sofiyya tayi yabata tsoro harma tafara tunanin kodai munnir ya tsafe mata 'yane?




Daddy kam kwanciyar sa yayi rai fesss da farinciki don bakaramin dadin yadda Sofiyya tayi ma munnir yaji ba har addu'a yake Allah ya tabbatar da alkhairi.




Itakam Sofiyya ita kadai tasan dalilinta nayin hakan.



Tundaga wannan ranar Sofiyya ta sakewa munnir kullum gidan yake breakfast dakuma dinner, sannan susha hirarsu kafin yatafi, shikam yama manta dawani sabit don tunda yafara cemishi akwa lauje cikin nadi yayi watsi daahi, ko kiranshi yayi baya dauka.


Zuly ma data matsa da kiranshi zageta yayi tsab sannan ya danna numbern ta a blacklist.



Abdul kuwa duk ya rame bayajin dadin rayuwarsa kwata-kwata amma haka yake daurewa yake zuwa aiki kullum ba fashi, babu irin tambayar da umma da Abbanshi basuyi masa ba amma yaki fada musu gskyr abinda ke faruwa kawai dai yace sutayashi da addu'a.




Sofiyya ma tadanyi rama amma idan kaganta bazaka ce tanada matsala ba.



Mommy dai sam hankalinta be kwanta da abinda ke faruwa ba, amma dai batace komai ba se addu???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?'a datake binta dashi.




Yau sati kenan da faruwar duk wannan abun, yakama saura 3dys kwanankin da aka dibarwa Abban su Abdul yacika.




Abdul yau kam yakasa karasa zaman office din don haka tunda yafito sallahr la'asar yarufe office din yatashi kenan.



Yau yanason jin nishadi don haka kai tsaye ya wuce wani garden dake da karancin mutane kuma akwai lambu da tsuntsaye, yanayin gurin kam babu hayaniya sam, yawanci masoya ke ziyartar gurin domin nishadan tuwa.



Dazuwansa ya shimfida darduma yazauna, yafito da wayarsa yana kallon hotunan Sofiyya yana murmushi.



"Inama tare mukazo dake *Cutie Naa* da gurin seyafi haka samar da nutsuwa da kwanciyar hankali" yafurta a hankali.




Tana idar da sallahr la'asar tahau shiryawa, doguwar riga tasaka blue da stones pink ajiki tayi rolling kamta da pink veil tasaka takalmi flat shima pink sannan tadau purse dinta blue tafito se kamshi takeyi.




A parlo suka hadu da munnir yasakar mata murmushi itama ta mayar masa sannan tace "bari inje inyima mommy sallama"



"Okay" munnir yace



Tunda tashigo mommy kebjnta da kallo tana mamaki tace "mommy yaaya munnir yazo zamu tafi"



Mommy tace "to Sofiyya nidai ina dada jaddada miki kirike mutuncin ki kinji"



Murmushi tayi tace "insha Allah mommy "


Mommy "tose kundawo ko"



Fita tayi suka dau hanya, itadai batasan inda munnir ze kaita ba, don tun kwana biyu dasuka wuce yake rokarta data shirya zata rakashi anguwa amma sam taki seyau ta amince, kuma tayi tayi yafada mata inda zasuje amma yaki sanar da ita don haka tazuba ido kawai...........
'?

Gameson shiga group dina seya tuntu6eni ta 07046767662.

[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutei Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*


_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks=?L?*_



_*TALLA*_
Akwai turaren humra me kamshin kwantar da hankali dakuma kama jiki. Muna maraba da masu siyan daya daya ko sari. Dakuma masu talla ta online abasu a farashin sari sukuma sukara nasu akai, in ansamu me siya sucire ribarsu=?L?
Mace seda kamshi, game bukata yayi magana ta 07046767662 kokuma chat ta Facebook =?G?Maryam-Ashner Isma'l Usman


Episode 35


Tunda suka dau hanya zuciyar ta ke bugawa tarasa dalilin bugun nata, se maimaita "hasbunallahu wani'imal wakeel" take a zuciyar ta,.



Munnir kam se surutu yake zuba mata, wani ta amsa mishi wani kuma tayi mishi shiru a haka dai sukayita tafiya har suka samu isowa wani park.



....... Abdul dai nazaune a gurin jin bugun zuciyar sa na karuwa yasashi daga kai ya kalli gabansa "wow" yafurta ganin yadda aka kayata wani gefe dake gabanshi kadan sa furanni dakuma baloons masu kyau, anyi docorating gurin sosai sannan aka rubuta SOFIYYA da manyan baki da colours daban-daban.



Gurin ya tsaru iya tsaruwa don haka Abdul yatsaya kallon abun yana murmushin da ya kwana biyu beyi irinsa ba.


Daga wayarsa yayi yafara daukar wurin a photo yana fadin "i will keep this duk randa aka dawo da wayar ki kokuma muka hadu zan nuna miki, nasan u will like it *Cutie Naa*"

Yakarasa yana murmushi sannan ya cigaba da daukar photon.



.......... Bayan munnir yayi parking yace "sweetheart is a surprise so muna fara shiga zaki rufe ido harse munje kin zauna tukunna"



"Okay" tafada tana kokarin fita daga motar, harga Allah daurewa kawai takeyi don gaba daya nutsuwarta tabar jikinta tarasa dalili.



Saukowa tayi munnir yayi gaba itakuma tana binshi a baya, suna shiga park din yace "close your eyes"

Babu musu ta rufe idon yafara yimata jagora tana biye dashi.



........... Abdul daya maida hankali wurin daukar photo yaji zuciyar sa na azalzalarsa daya juya, tun yana basarwa har yakasa basarwa don jiyake inhar be juya ya kalli bayansa ba kamar zeyi asara babba don haka ya juyo da kansa a hankali.



Munnir yafara gani wanda tun a kallon farko suka hada ido, farinciki sosai munnir yayi da ganin Abdul a gurin don haka yasake bada himma wirin fadin "sweetheart tanan zaki biyo"




Abdul bedamu da ganin munnir a gurinba sedai zuciyar sa dake matukar son ganin dawa munnir din ke tare, dan gefe munnir yayi hakan yabawa Abdul damar yin tozali da *Cutie*.



Hankalinshi begama tashi ba seda Sofiyya tazo wucewa tagabanshi, fuskarta dauke da murmushi, idanunta a rufe yayin da munnir keyi mata jagora da kiranta dasunaye irin na masoya "sweetheart darling sister" sune sunayen da munnir ke ambato kuma da karfi.



"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun" kalmar data fito daga bakin Abdul kenan yayin da idanuwansa ke cigaba da kallon Sofiyya zuciyar sa kuma take

15 / 26