Chapter 18 Reading CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc Arewa Novels

CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 26

51K to 54K   out of 76.5K words

rasashi" yana kaiwa nan yayi musu sallama yayi ficewarsa.

Mommy kam mamaki tayi sosai kuma tayi kudirin cewa sedai duk abinda zefaru yafaru, wanda yamutu kwanansa ne yakare amma baza'a kashe 'yarta don a raya Munnir ba.

Hankalin daddy yatashi sosai tunanin abinyi yafarayi, shidai bayason matsawa Sofiyya kan auren munnir amma tunda wannan abun yafaru babu yadda zeyi dolene tayi hakuri ta ceci ran dan uwanta.

Hajjaju kan hankalinta yakai kololuwa gurin tashi, cikin kuka tace "Adamu me manniru keso kakasa yimasa, so kake yamutu koyaya, duk cikin jikokina babu namiji seshi kuma shinafi so, kodai bakin ciki kakeyi ne adamu? Yo inba bakinciki ba tayaya bazaka sai masa mota kota dubu nawa bace? To wlh indai akan motane ka tabbatar dazaran ya farfado duk kalar motar dayace yanaso se ansiya masa koda duka kudinka bazasu isaba sekaci bashi billahillazi se ansai masa mota"

Hakuri daddy yayita bawa Hajjaju yana tausar ta don bayama son tasan akan me Munnir yashiga wannan halin, don haka bazema bari munnir ya farka a gabanta ba.



......... Ganin yadda Abdul yafito yayi breakfast sannan yatafi office cike da walwala yasanya umma da Abba fahimtar abinda ke damunsa kwana biyun can, bakaramin mamaki hakan yabawa umma ba, "tabdijam lallai Sofiyya taci gari" umma tafada tana murmushi.

Abba yace "banfada masa ba ai, next week zankoma a tsaida ranar aurensu insha Allah, kuma ina fatan hakan baze dau lokaci ba"


Cikin murmushi umma tace "Allah yakaimu"
"Amin" abba yace yana mikewa yace "bari inkoma dama wannan file din nazo dauka".

Umma nazaune anan tayi kiran anty zainab ta shaida mata duk abinda ke faruwa sosai anty zainab tayi murna dajin labarin takuma yi addu'ar Allah yasanya alkhairi.,.............,
'?

Ko yaushe Sabit yazama Doctor???


Gameson shiga group dina seya tuntu6emu ta 07046767662
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam-Ashner*


_*INA MARABA DA KOWA, AMMA DUK WADDA BATA COMMENT/SHARHI ME MA'ANA DAKUMA ADDU'A TABBAS ZAN CIRETA=?L?BANASON STICKER DA THANKS PLEASE TAKE NOTE=?O?*_


*TALLA*
Akwai turaren wuta, humra, kolacca, body spray, musk, turaren mopping dana kaya.
Akwai shadda, laces, atampa, abaya, yadi, mayafai dasauransu.
Akwai kayan kitchen.
Duka muna maraba dame siyan daya kome sari, abinda kawai zakuyi shine kiran wannan number 07046767662 KO tura sako, kokuma chat ta Facebook a wannan account *Maryam-Ashner Isma'l Usman*


Episode 39

Dakyar daddy ya lalla6a Hajjaju tayarda aka maidata gida, tare da sharadin da zaran munnir ya farfado za ayimata waya tayi magana dashi.


Da farinciki da walwala ya wuni a office din, ma'aikatan gurin duk sunyi mamakin sabon sauyin da Abdul yayi domin fara'a yake wa kowa sa6anin da dako murmushin sa bakowa ke gani ba, yini sukayi suna chat da waya da Cutien shi.


Sofiyya kuwa itama murmushi ta yini tanayi, bata damu da halin da munnir ke ciki ba, hasalima batasan meya sameshi ba, kuma bata damu tasani ba.

Sunanan zaune a asibityn har akayi azahar, duk sukayo alwala daddy yajasu sallah, kamar jira yake su idar, sunayin sallama munnir yafara tari da ambaton Sofiyya! Sofiyya!! Sofiyya!!! Duk da a hankali yake kiran sunan nata amma kowa dake dakin yaji me yake cewa sakamakon rashin hayaniyar dake dakin.

Duk juyowa sukayi suna kallonshi, daddy yayi hanzarin mikewa yaje kusadashi yana fadin "munnir sannu bude idonka kaji, duk gamunan harda Sofiyya"

Tunda yafara magana munnir yake jujjuya kai har seda yaji an anbaci Sofiyya sannan yatsaida kannashi cak a hankali kuma yafara motsa idonshi alamun yanason budesu.

Ganin haka yasa daddy yiwa Sofiyya alamun tazo kusa dashi.
Jiki ba kwari Sofiyya tamike tanufe shi tatsaya kusa da daddy fuskarta ba yabo ba fallasa.

A hankali yakarasa bude idonshi ya sauke kwayar idon nashi a kanta, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da mika hannu gareta cikin dakusashshiyar murya irin ta marasa lafiya yace "Kizo gareni don Allah karki barni 'yar uwata" yakarasa hawaye na zubo mishi kan kumatunshi.


Har zuciyar daddy yakejin tausayin yaronnan, mommy kam juyawa tayi daga barin kallon inda yake don harga Allah banda takaici ba abinda munnir ke bata.

Sofiyya kam mamakin furucinsa takeyi dagaske taji tausayinsa amma sam bazata muzgunawa zuciyar ta, ta farantawa tasa zuciyar ba.

Daddy ne yace "bazata barka ba munnir ka kwantar da hankalinka ai gatanan kusa dakai"

Murmushi munnir yayi yana lumshe idanu, tunanin yadda abin yafaru yakoma yi


*daren jiya ne yarasa yadda zeyi inhar Sofiyya bata za6eshi ba, kwakwalwar sa tadena kawo wuta sam, kuma zuciyar sa na fada masa cewa Sofiyya bazata za6eshi ba don haka yakira abokinsa Sabit domin sake nemab mafita, yayi mishi misaed call tafi goma amma bedauka ba, karshe ma idan yakira seyaga number busy hakan yasa yanufi gidansu kai tsaye, domin yasan zuwa wannan lokacin kam sabit na gida, yaci sa'a kuwa yasameshi, da farko kin kulashi yayi sedaga baya da yayita bashi hakuri sannan ya saurareshi bayan yagama zageshi tasss.
Bayanin duk abubuwan dasuka faru yayi masa sannan yakara da "nifa inaganin dakyar zata za6eni kuma wlh inasonta sosai" nan sabit yafara bashi shawarar abinda yadace yayi, duk wani tari da faduwar da munnir yayi duk sabit ne ya shiryo masa sannan suka hada baki da daya daga cikin ma'aikatan gurin aikinsu, shine ke bawa sabit duk wasu information akan asibityn dasukaje har sabit yazo ya taddasu, kuma yabiya doctors din kudi domin subashi aron uniform dinsu dakuma damar kasancewa likitan munnir*

Uwaki naira lol

Murmushi yasakeyi a ranshi yana jinjina kokari da basirar sabit.

Da la'asar ne su mommy sukayi shirin tafiya gida amma munnir yatada ciwon karya dole akabar Sofiyya tare dashi dakuma daddy aka idan yasamu yayi barchi sesu taho koda bayan isha'i ne.

Fal ranta ya 6aci da wannan hukuncin da daddy ya yanke, amma babu yadda ta iya haka tahakura tazauna.

Da magriba daddy yafita masallaci Sofiyya ta kalli munnir dashima kallonta yakeyi tace "yaya munnir inbaka shawara? "


Da murmushi kan fuskarsa yace "ofcourse i'm all ears"

Tace "karabu dani, kafita harkata kafita rayuwata, kacireni a zuciyar ka, kasan meyasa? "

Be amsa mata ba, taci gaba da cewa "banasonka bana kaunarka natsaneka, idan har kabari aka auramin kai wlh tsab zan zuba maka poison kaci ka mutu nikuma infito in auri Abdul dina banda asara" takarasa tana dage mishi girq da bude hannayenta alamun ko ajikinta.

Sabit dake kokarin shigowa yatsaya yaji duk abinda tafada sannan yaturo kofar yashigo, fuskar munnir kawai yakalla yaji dariya tataho masa, yakasa tsaida dariyar kuwa seda yadara sannan yace "my friend just give up"

Mamaki Sofiyya tayi ganin Doctor na dariya kuma ga abinda yake fadawa munnir, zama sabit yayi yace "Sofiyya ko? Let me tell you the truth about all this"................... & ...... " nan yafada ma Sofiyya duk wani tuggu dasuka shirya tun farko har na yau, sannan yakara dacewa "ni dakika ganni inayin komai amma duk inda aka ambaci kisa to ina cire kaina a gurin, naji duk abinda kika fadama abokina thats why nakeso incire kaina cikin wannan plan din"

Sofiyya was shocked at thesame time tasake jin sabuwar tsanar munnir a ranta sosai da sosai.

Munnir kam kukane kawai beyiba amma takaici, bakinciki da 6acin rai babu wanda beji ba don haka yakasa control din kansa yamike ya cakumo sabit yahau naushinsa yana fadin "Allah yatsine maka tsinanne kawai"

Fadane ya kaure tsakanin munnir da sabit a haka daddy yashigo ya taddasu "subhanallah lafiyarku kuwa"

Dakyar yasamu yayi nasarar rabasu se numfarfashi sukeyi kamar wasu zakaru.

Bayan sun nutsune daddy ya bukaci jin abinda yafaru dan ba karamin mamaki yayi ba ganin munnir din da bashida lafiya amma yazage damtse yana fada.

Babu wani gargada sabit yakorowa daddy bayani kamar yadda ya korowa Sofiyya.

Tabbas yayi matukar mamakin jin makirci irin na Munnir kuma yayi Allah wadai da mugun halinsa a karshe dai daddy yakama hannun Sofiyya suka bar asibityn yana jin takaicin abinda munnir yayi.

Itako Sofiyya har kasan zuciyar ta taji dadin faruwar wannan abun, koba komai Allah ya fiddata daga tarkon da munnir yaso dana mata.


Suna zuwa gida kuwa tafara bawa mommy labarin duk abubuwan dasuka faru, sosai mommy ta jinjina al'amari amma ko mamaki batayi ba, don a kallon datakew munnir ma tanaganin ze iyayin abinda yafi haka muni.


Dadare suna waya da Abdul tabashi labarin duk abubuwan dasuka faru yau, shimadai yayi mamaki kuma yayi dariya sosai, sukayi addu'ar neman tsarin daga shaidanu irinsu Munnir sannan suka daura daga inda suka tsaya a babin soyayyar su.


Koda su daddy suka fice Sabit ma ficewa yayi abinsa yatafi gida, munnir kuwa zama yayi ta6as yana cizon yatsa, abin duniya duk yataru masa aka.

Yayi daya sanin abinda ya aikata yafi awa a zaune a gun sannan yatashi yafita, adaidaita ya hau kaitsaye yakaishi gida.

Hajjaju daketa faman sababin rashin ganin kiransu daddy taga mutum kamar aljani yashigo sum sum yanufi dakinsa, aida gudu tabishi tasha gabanshi tana "a'uzubillah nikam menake gani haka? Kodai ifritu ne yatahomin a siffar jikana manniru?" takarasa tana daura hannayenta akai.


Dogon tsaki munnir yaja sannan ya kauce yabi gefenta yashige dakinsa,.

Kuka Hajjaju tasaka tana cewa "nidai da Allah na dogara ba mutum ba, yawwa"

Munnir kuwa kwana yayi yana tunani a karshe dai ya yanke hukunci kawai zekoma kano dazama, ze manta da komai daya faru a jos..............
'?


Gameson shiga group Dina yayimin magana ta 07046767662
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?


By


*Maryam-Ashner*


_*ina maraba da kowa, amma duk wadda bata comment/sharhi me ma'ana dakuma addu'a tabbas zan cireta=?O? banason sticker da thanks*=?L?_


_*TALLA*_
kununamin kauna wurin siyan datana=?O? akwai giveaway karshen wata ga wacce tasiya yakai sau biyar, koda 500mb take siya=?L? tanada kyatar 1GB, wadda tasiya sau hudu kuma tana da kyautar 500MB.
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook =?G?Maryam-Ashner Isma'l Usman

Episode 40

Cikin satinnan Sofiyya da Abdul sunyishine cike da shauki da soyayya da kauna dajin cewa basuda sauran wata damuwa ko matsala.

Koda munnir yakoma kano iyayenshi suka tambayeshi dalili babu abinda ya 6oye musu yayi musu bayanin komai sannan yakara dacewa "Baba nidai nadawo nan dazama domin , kunyar hada ido da daddy nakeyi gsky, so don Allah kanemamin aiki anan kawai don bana son komawa jos wallahi"

Maman munnir tace "ai Sofiyya ita tayiwa kanta wallahi kasha kuruminka 'yan mata gasunan wadanda ma suka fita kyau zaka samu, kayi zamanka anan kawai"

Shidai Alhj Salisu bece komai ba yana dai jinsu ne kawai, kuma yaji dadin rashin daidaiton dasuka samu don yanason Allah yacika mishi burin hada munnir da 'yar wajen zulaikha aure tunda shi Allah beyi ze aureta ba.

Da murmushi kan fuskarsa yamike yabar musu gurin batare da yace komai ba.

Zuly nacan abin duniya duk ya dameta tarasa gurin wa zataje tasamu information kan su Abdul tunda haryanzu aunty zee bata dawo ba takara postponeding dawowar nata.

......


Sati yaxagayo inda Abba yaje yasamu daddy suka tsaida ranar aure nan da wata biyu kacal, murna agunsu SOFDUL ba'a magana, duk bakinsu yaki rufuwa, a inda mommy tashiga gyara amarya tako ina,.

Me gyaran jiki aka dauko musamman tafara aikinta, tana zuwa duk sati sannan idan biki yarage saura wata daya zata dawo gidan dazama domin aikin zezama kullum ne za'a dinga yi.
Nan mommy tayi kiran kawarta domin tanemo mata wadda ta kware wurin hada turaren amarya , kama daga Humra, turaren kaya, turaren wuta, turaren mopping dasaurandu dai nan kawar mommy tashaida mata kwararriya wurin harkar turare wato *Maryam-Ashner*

Tasanar da ita kwarewarta a harkar turare kowani irine, sannan tabata numbern ta 07046767662 takara dacewa "inkin kirata kai tsaye kice amarya ce kike shiryawa, zata yimiki duk sauran bayani"

........

Dangin mommy da daddy duk ansanar da shirin auren Sofiyya kowa se mamaki yakeyi, tayaya yarinya karama 'yar boko iyayenta 'yan boko suyarda su aurar da ita da wuri haka?wasu kuma sukance ai yaran yanzu ba'a yimusu gata dazaran sun taso zakaga sun maida hankalin kan soyayya, daga karshe ma su ajiye karatun suce su aure sukeso, ai gara ayimusu auren tunkafin azo ayi da'ansani.

Abba da iyalansa duka suka shirya suka tafi niger domin sanar da bikin Abdul, duk dcewa Abba bashida 'yan uwa da iyaye amma yana matukar mutunta dangin mahaifi dana mahaifiyarsa, yakan je lokaci zuwa lokaci, a yanzu kam yanada aiki me muhimmancin dabaze iya tsallakewa ba, hakan yasa ya wakilta Abdul yayi musu jagora a madadinsa dama sunjima basuje ba, don haka ya tattarasu duka harda Raliya yayi musu umarnin tafiya suka tafi zasuyi weekend acan sannan sudawo.



Two days later, Zuly ce rike da waya a kunne tana jiran adau kiran datakey "Assalamu alaikum aunty" tafurta bayan andau kiran datakeyi.

Aunty zainab dake tsaka dacin albinci ta amsa sallamar tare da fadin "zulai yagidan?"

"Lafiya klou aunty wai yaushe zaki dawo ne?"

Aunty zainab tadanyi 'yar dariya tace "kinyi kewata sosai haka zulai, wlh abubuwane suketa tasowa, sena gama shirin tafiya sewani abin yakuma 6ullowa, amma insha Allah nan da sati kam kowani abun ya 6ullo zan barshi inyi tahowata"

6ata fuska zuly tayi tace "hmmmm to Allah yakaimu auty ki gaishesu".

Katse kiran tayi tana jan tsaki, sam tagaji dajiran sanin abinda ke wakana tsakanin Abdul, Munnir dakuma Sofiyya don haka zuciyarta tabata shawarar kawai taje gidan dasunan tazo wucewane tace bari tashigo su gaisa.

Murmushi tayi tana meyin na'am da shawarar da zuciyarta tabata, batare da tako shiga gidan ba tajuya tayi gaba, dama aikenta mama tayi, tadawo shine tatsaya kofar gida tayi kiran aunty zee.


Abba daya dawo gida yayi wanka domin yaune su Abdul suke dawowa so zeje ya dauko su, bayan yadan huta sannan yafito yana jiran drivernsa daya zaga, .

Zuly ce ta kwankwasa get din gidan, megadi yafito yana tambyarta ko lafiya, tace "aikoni akayi gurin matar gidan"
Megadi yace "duk basanan sunyi tafiya amma anjima zasu dawo, sedai kidawo gobe"

Yana gama fadin hakan yakoma yaturo kofar, ciza yatsa tayi tace "inanan harsu dawo"

Abba dayaga megadi yadawo shikadai yace "baba lafiya dai ko?"

Megadi yace "lafiya Alhaji watace take neman hajiya shine nace mata ai basanan"

Hakanan Abba yaji zuciyarsa na bugawa da azalzalarsa dayaje yaga ko wacece.

Tahowa yayi megadi nayi masa magana amma bemaji shi ba sakamakon yadda yafarajin yanayin jikinsa na sauyawa, zuciyarsa tafara tuno masa da abinda bayason tunawa ko kadan, dahaka yakai ga kofar gidan yabude, wani irin bugu da zuciyarsa tayi harseda ya dafe kirjinsa da hannunsa yana fadin "subhanallah" ahaka yakarasa fitowa yana karewa yarinyar dake tsaye a gabansa kallo, duk dacewa tajuya bayane baya iya ganin fuskarta amna a ransa jiyake yasanta sani sosai don haka da hanzari yatafi zuwa gabanta.

Zuly dataga mutum a gabanta tadago kai tana kare masa kallo, yayi mata kwarjini sosai dukda cewa batasan wanene wannan ba amma cikin sunku da kai tace "ina wuni?"

Bude baki abba yayi da niyyar yin magana amma numfashinsa ya sarke, nan yafara kokarin janyo numfashin amma inaa yakasa, ganin haka ya tsorata zuly sosai don haka without a second thoght tabar gurin harda kwasawa da gudu, tayi sa'a kuwa da fitarta unguwar tasamu napep yayi gida da ita se uban numfashi take tana fadin "Alhamdulillah nazo gida, masu kudinnan mugayene soyake yayimin sharri ace nice nashakeshi"

Har driver yafito Abba beshigo gidaba, kai tsaye driver yatada mota da nufi idan yafita se Abba yadhigo kawai sutafi.

Yana fita yaga Abba yashe a kasa yanata kokarin daidaita numfashinsa amma abun yacitura, dasauri yayi parking yafito yana kiran "Alhaji Alhaji lafiya kuwa"

Megadi dayaji hayaniyar Drivet yafito dasauri yana fadin "innallillalhi wa'inna ilalihir raji'uun inaga wannan yarinyar mayyace wallahj"

Driver yace "kamashi musashi a mota inkaishi asibity"

Hakan akayi suka sakashi a mota sukayi asibity dashi, dazuwansu aka kar6eshi akayi emergency dashi batare da 6ata lokaci ba..

Su Abdul nata kiran Abba baya dauka daga karshe dai driver yadau wayar yasanar dasu halin da ake ciki, basu jira komai ba dama saukarsu kenan suka dau shatar mota zuwa asibityn da driver yasanar dasu.

Koda sukazo basu samu ganin likitan dayake dubashi ba sakamakon yana can kan Abban haryanzu.

Duk hankulansu yatashi, bama kamar usman harda kukanshi, Raliya kuwa addu'a kawai takeyi duk wadda tazo bakinta, umma kuwa tana tsaye tana tunanin meya sameshi all of the sudden, don ko awa basuyi da gama waya ba, kafin tayi magana Abdul yace "wai mema yasameshi da sauri haka?" Nan driver yabasu labarin abinda yagani dakuma abindal yaji megadi yafada.

Abdul bejira komai ba yacewa driver "ban keyn motar"
Driver yace "ranka yadade ai....."

Wata tsawa ya buga mishi "give the key to me"

Ciro keyn yayi a aljihu yana mika

18 / 26