CUTIE NA BOOK COMPLETE BY MARYAM ASHNER.doc

Author :  Maryam Ashner Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 26

21K to 24K   out of 76.5K words

tayi tunaninta yadda yakamata ba, hakan yasa ta mike tana cewa "I'm tired bari inhaura"

Da ido mommy tabita, dakuma tarin tambayoyi cikin ranta, the Sofiyya she know magananniya, koda yaushe cikin magana take,
The Sofiyya she know a ranar a kuma lokacin data dawo daga tafiya ko Anguwa take baje kolin surutu da labarin abinda yafaru

But see her now wai tagaji, girgiza Kai mommy tayi a ranta tace "zanzo insameki ai"

Siddika kuwa da harara tabita

Itakuwa ko waige batayiba tafiyarta kawai tayi.


Sukuma sukaci gaba da hirarsu.

5pm Abdullah yatashi a office, yadau hanyar gida, harya kusa isowa gidan yatuna da aiken umma zuwa gidan Anty Zainab,
Juya motar yayi zuwa anguwar sukuwa.

Yaukam yagane gidan sarai don haka kai tsaye yashiga yatsaya a zauren gidan sannan yafara kiran layin anty zainab.

Zuly dake tsakar gida tana tsincewa antyn yara wake taji antyn na kiranta.

Ajiye tiren tayi tamike tanufi dakin,
Anty zainab tace "yawwa maza saka hijab dinki bako nayi"

Zuly tace "tom" tanufi dakin don dauko hijab,
Kafin tafito taji sallama, muryar datake kwana da amonta a zuciya, nan da nan ta zura hijab din tayo falon domin tabbatarwa.

Karaf idonta yasauka a kanshi, har sanyi taji cikin zuciyarta.

Gyara tsayuwarta Tayi, sannan ta durkusa tahau gaidashi.

Jiyayi kamar yasan muryar don haka yadago kanshi ya kalleta sau daya yakau dakai yana tunanin inda yasanta, but tabbas yasan ta somewhere.

Anty zainab ce tace "sarkin miskilai bakaji ana gaidaka ba? "

Dan sosa kai yayi sannan yace "lafiya lou sannu"

Dadi Anty zainab taji, jin yadda ya amsa mata a mutunce, sa6anin yadda yake amsawa mutane inyazo gidan ya tadda baki.

"Jeki kawo masa ruwa ko"

Mikewa zulaikha tayi cikin nutsuwa taje kitchen takawo masa ruwan gora da cup

"Thanks " yafurta a hankali

Da ita da anty zainab duk dadi sukaji, bama kamar ita, mikewa tayi tanufi dakin don tabasu damar tattaunawa.

Tana daga daki amma kunnuwanta na falon.

Bayan sungama gaisawane yake miko mata IV din partyn.yana fadin "nawajenki fa angirma"

Dasauri anty zainab takarfa, a zatonta katin aurensa ne, sebayan data gama Karantawa ne ta fahimci na menene.

Cikin fara'a da zolaya tace "nadauka ma na aurenka ne"

Murmushi yayi yace "ankusa ai"

Cikin murna tace "dagaske ko wasa"

Murmushin kawai yayi amma bece komai ba.

Anty zainab tace "amma kam zanso inga wannan yarinyar wlh"

Cikeda kunya yamike yana fadin "nizan wuce anty sekunzo"

Mikewa tayi domin yimasa rakiya tana cewa "Allah yanuna mana lokacin"

"Amin" yace kana sukayi sallama yawuce.

Dawowa anty zainab tayi suka dasa hirar Abdullah itada zuly.

Anan ne zuly tafara fahimtar wanene Abdullah takuma ci alwashin samun soyayyarsa kota Yaya ne.
Don haka tacewa Anty zainab "inason zuwa gurun partyn school wlh abin yana burg???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?eni"

Anty zainab tace "aikuwa kya rakani, dama ina tunanin zuwa nikadai"


A garin kano kuwa, maman zuly ce cikin hotel takasa zaune takasa tsaye se kaiwa da komowa takeyi, dalilin kamshin datake ji tun farkon shigowarta hotel din.

Zama tayi bakin gadon dakin, tagumin tazuba hawaye masu zafi suka fara gangaro mata, tunanin rayuwarta ta baya takeyi


**********

"Anty Zulaikha kekam kinji dadinki Wlh, inaso idan nagirma inzama kamar ke" cewar Hafsat yarinyar dabata wuce shekara 11 ba.

Murmushi zulaikha tayi tace "kekuwa hafsy meyasa kikeson kizama kamar ni"

Caraf Halimatu tace "wai saboda tadinga kwalliya irin nakine fa"

Duk dariya sukayi...,......
Suna tsaka da hirarsu sukaji sallamar Adda maryamah tana kiran "hafsa da halimatu kufito gashinan yadawo"

Hafsat dakamar zatayi kuka tace "I will miss you anty"

Rungumeta zulaikha tayi tace "miss You too baby take care "

Itako halimatu tuni tayi waje dagudunta.

Adda maryamah ce tashigo dakin, ganin duk zulaikha ta canza lokaci daya yasa tace "zulaikha kidaure kiyi aure anan kano kinga su hafsat insunyi hutun school sadinga yimiki acan kafin kuma ki haihu, tunda naga bakyason zaman kadaici"

Nan ranta yasake 6aci tamike tace "nidai don ALLAH ku kyaleni, keda yaya kun takuramin wlh"

Tana gama fadin haka tayi wucewarta tabar Adda maryamah ta sakakken baki.

Hafsat da halimatu kannen Abokin yayan zulaikha ne, suna boarding junior secondary school anan kano, shekararsu ta farko kenan JSS one. Asalin su 'yan jahar adamawa ne.

Tun haduwarsu ta farko suka shaku da zulaikha tana matukar kaunarsu, duk hutunsu anan sukayi, seyanzu dasukayi third time exam shine zasuje gida.

Hakanan takanje musu visiting duk weekend.

Dadare Alhaji mamman yadawo Adda maryamah take labarta masa abinda yafaru.

Kiran Zulaikha yayi yamata kaca-kaca, dama tasan za'a rina, don haka ko a jikinta.

Bayan kwana biyu kuma sesuka shirya kamar basuba.

A satin kuma tashirya zuwa suleja don tace zataje itama tayi hutu kafin su hafsat sudawo.

Tafiyar data zame mata mummunar kaddarar dabazata ta6a mantawa ba.

*******

"Hmmmm" tasauke nannauyar ajiyar zuciya tace "Allah sarki hafsat, ko kina ina yanzu oho"

Dan guntun hawayen daya zubo Mata ta share sannan tamike tanufi toilet jin ana kiran sallar magriba.

Alhaji Mu'az Gallafi kwana yayi babu barchi kuma yakashe wayarsa don bayason yin magana da kowa hakan yasa yaturawa iyalinsa text kan cewa yafasa dawowa a wannan ranar,.

Kwana yayi yana sallah da addu'o'i dakuma istigfari kan kuskuren daya aikata.

A gidan Alhaji.Mu'az Gallafi wurin dinner Usman ne da Abdul don umma bata fito ba, Usman yanata cin abincin shi, shikuma Abdul yanata chatting se murmushi yakeyi.

Kallonshi Usman keyi da mamaki, can yaji yafara voice, nutsuwarsa ya tattara gurin son jin abinda yake cewa amma ko abu daya beji ba.

Girgiza kai yayi yace "I will snatch The phone don wlh inason jin meyake cewa"

Umma ce tafito fuska babu walwala taja kujera tazauna tana kallon Abdul.

Kashe wayar yayi yasa a aljihu yace "barka da fitowa umma"

Hannu kawai tadaga masa, tahau zuba abinci a plate.

Usman kuwa jiran fitowarta yake yaji ko Abbansu ya taho, don yayita kiran wayarsa bata shiga.
Ganin yanayinta kuma seya kasa cewa komai,
Can dai yakasa hakuri yace "Yaaya nace kunyi waya da Abba kuwa? Ni na nemeshi baya shiga"

Kallonshi yayi sannan yace "nima baya shiga but nayi magana da driver bazasu dawo yau ba"

Cikin rashin jin dadi Usman yace "umma wai me...... "

Bekarasa ba umma ta daga masa hannu.

Sum sum yamike yabar gurin.


A gidan daddy kuwa duk sun hallara a dinning ana dinner amma banda Sofiyya, tana daki tana chat.

Mommy nata mamakin sabon halin da Sofiyya tadawo dashi amma dai batace komai ba.

Daddy da yayanshi Alhaji salisu tare da Munnir da shigowarsu kenan kowa yaja kujera yazauna, mommy na zuba musu abinci Munnir ya dudduba be hango Sofiyya ba, hakan yasashi yima ikee magana a hankali

"Ikee ina Sofy? "

Itako ikram babu sirri ta karfinta tace "Yaaya Sofiyya bata fito ba, tace idan mungama inkai mata nata daki"

Se lokacin daddy ya Ankara cewar babu Sofiyya a gurin,.
Cewa yayi
"Auta jeki kirawomin ita"

Mikewa Ikram tayi tanufi upstairs
Siddika kuwa wani murmushin mugunta tayi, don seda sukayi kaca-kaca, kan taki biyota sufito........
'?

[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah please =?O?

Episode 19

Cike da nishadi take chatting tana kwance a kan bed dinta ko yunwa ma itakam bataji.

Knocking taji anayi, dan guntun tsaki tayi sannan ta mike taje tabude, don har key tasawa kofar saboda Siddika.

Tana budewa taga Ikee, jitayi kamar ta wanketa da mari, cike da takaici tace "What!? "

Cuno baki Ikram tayi tana juyawa tace "daddy ke kiranki" tana gama fadin haka tayi tafiyarta ta gangara.

"Lallai yarinyar nan wlh ta rainani" kwafa tayi, batako janyo kofar ba tabi bayanta, dan seta lakadeta yau dinnan.

Da sauri-sauri take taka step din dan tasan sarai tayi laifi, burinta ta iso gaban ya munnir.

Tana step na karshe Sofiyya ta cafkota ta kwada mata mari, wani kara Ikram tayi kamar wadda aka yanka.

Tuni hankalin kowa yayo gunsu, Munnir kuwa hankalinsa gaba daya Yayi gurin Sofiyya Kallonta yake babu kifta ido, tundaga kalaban kitson dake kanta, don ko dankwali babu a kanta, saboda tsabar fusata datayi ta manta dashi.

Kallon jikinta yakoma yi, black three quarter trouser ne a jikinta, se red T shirt, duk dacewa kayan be matse ta ba, amma haka ya kureta da kallo kamar maye.

Alhaji salis ne yazo dasauri ya riko Ikram yana tambayarta meya faru.

Mommy ko ko juyowa ma batayi ba, don tasan wacece Ikram wurin rashin kunya, takuma san wacece Sofiyya wurin hukunci.

Jin bataji muryar Munnir ba yasa tajuyo tana kallon inda yake, gani tayi gaba daya hankalinshi baya kan Ikram ba, kamarma beji ihun datakeyi ba, hakan yasa ta kallon inda yake kallo, rantane ya6aci, gani a shigar da Sofiyya tafito.


"Amma Sofiyya bakisan ciwon kanki bane Kika fito haka? "

Se sannan ta ankara da yanayin data fito, kunyace takamata dasauri ta juya ta haura upstairs takoma daki.

Daddy dariya yayi yace "ba'asan angirma ba"

Munnir sam beji dadin abinda mommy tayi ba, sam shibega wani aibu ba danta fito haka, tunda dai aiduk babu bako cikinsu.

Mommy sam bataji dadin kallon da Munnir yayiwa Sofiyya ba.

Siddika kuwa farinciki fal ranta, Allah-Allah take sugama takoma tamata tsiya.

Shiko baban Siddika bece uffan ba, dama shi sam magana bata dameshi ba.

Hakanan sukayi dinner dinsu cikin farinciki suna hira.

Koda Sofiyya takoma daki tadau wayar gani tayi handsome yasauka bema yimata reply ba.

"Thank god". Tafurta a fili, kwanciyarta tayi tana Karanta chat din dasuka yi, tana kuma sauraron voice din dasukayi, se murmushi take ita kadai.


Bayan sungama dinner Siddika tayi saurin haurawa sama.
Tana zuwa tahau dariya harda kwanciya akasa.

"Mtssssss Allah dai yakawo sauki wlh" inji Sofiyya

Seda tayi me isarta sannan tace
"Wai meya hadaki da Ikee ne? "

Ko kallonta Sofiyya batayi ba balle ta amsata.

Haka ta Karachi maganarta da dariyarta tayi shiru.

seda kowa yagama cin abinci aka watse sannan mommy tayi Kiran Sofiyya a waya tace ta sauko tasa meta.

Hijab har kasa tasaka, tajona wayanta a charge tace "ko ankirani bance mutum yadaukamin ba ehe"

Tsaki Siddika taja tace "like I care"

Tana zuwa tazauna kasan carpet kusada kafafun mommy.

Kallonta mommy tayi tace "hala dazu hijabin 6ata yayi seyanzu Kika gani"

Sunkuyar dakai tayi tace "sorry mommy"

Kan dinning mommy tanuna mata tace "kije kici abinci tukunna, inkuma azumin dare Kika fara se inji"

Bamusu taje tazuba taci, bayan tagama tadawo inda tazauna dazu tasake zama.

Mommy ta tattara hankalinta gan diyar tata tace "so tell me about it"

Kan Sofiyya yadaure, don bata fahimci tambayar ba, tell her about what? Tafada a zuciyarta.

A fili kuma Tace "mommy mene?

Mommy tace "sabuwar rayuwarki mana"

Zaro idanuwa tayi tace "mommy nibani da wata sabuwar rayuwa ai"

Murmushi mommy tayi tace "na lura tunda kikayi waya kikayi sabbin friends ko"

Kunyace takama ta, don a tunaninta mommy tagano suna waya da Abdul ne, dan haka tace

"Mommy bahaka bane fa, kawai dai...... " sekuma tayi shiru

Nan mommy tahau janta da hira har tasake, nan tafara bata labarin Abdul harseda tace taje ta kwanta.

Tana shiga taga several missed calls, nan takirashi suka hau hirarsu as usual.

Mommy kuwa tunani tahauyi, harga Allah tanason Sofiyya tayi karatu sosai, to amma bazata hanata aureba, don ta fahimci tabbas soyayya Sofiyya keyi batare da tasani ba.

Fatan alkhairi tayi mata kawai.


Maman Zuly kwana tayi batayi barchin kirki ba, don kamshin data samu a dakin yasa takasa nutsuwa balle tasamu nutsuwar barchi.

Hakan yasa ana idar da sallar asuba ta tattara kayanta taje reception tabasu key tayi tafiyarta don bazata iya zama inda kamshinnan kenan ba.

Alhaji Mu'az Gallafi ma kwata-kwata bema kwanta ba balle yayi wani barchi, sallah yadingayi har 4am, barchi 6arawo ya daukeshi batareda ya shirya ba.

Hakan yasa ya makara se 6am yatashi, da hanzari yayi sallah, yafito don bincika abinda ya tsaidashi.

Bakaramin 6acin rai yajiba, jin cewa aita tafi.

Cike da 6acin rai yakira drivern shi yace su wuce yanzu.

Ana kiraye-kirayen sallar azahar Maman Zuly tasauka garin jos, direct gida tawuce tayi sallah takwanta ramukon barchin dabata yiba.


Shiko Alhaji Mu'az Gallafi tun 10am yashigo gida dayake jirgi yabiyo, babu wanda yasan yadwo gidan har zuwa azahar yafito zeje masallaci Umma taganshi, shi beganta bama yayi wucewarsa, da ido kawai tabishi har yafice.

"Gsky akwai bukatar muje gurin masu maganin gargajiya, kodai aljanu kedamun alhaji"
Da wannan tunanin tawuce dakinta.

Mummunan mafarki maman Zuly tayi wanda yadada famomata ciwon dake cinta a zuciyarta.
Seda tayi sallar la'asar sannan takira Antyn yara awaya tace mata tadawo.

Da murna Zuly tataho gida domin dan kwana dayan datayi batare da mama ba tayi missing dinta sosai.


Gidan Alhaji Mu'az kuwa bayan umma tagama abincin dare tahada na Abba daban, seda ta tabbatar yatafi masallaci sannan takai masa dakinsa, don tasan ba fitowa zeyi ba, kuma batasob ma suhadu.

Tabarshi yayi jinyarsa tukunna, idan ya farfado dolene suje koda Islamic herbal ne a dubashi, don ta fahimci ciwon nashi bana warkewa haka kawai bane.

Cikin yaran kuwa bata bari kowa yasan yadawo ba, don babu anfanin hakan.



Seconni suna tafiya, awanni suna bimusu, kwanaki sun shude har yarage saura kwana uku bikin graduation dinsu Sofiyya.


Shirye shirye ake bakama hannun yaro, kullum Siddika da Sofiyya suna hanyar shopping.

Yaudai saloon zasuje daga can kuma suje gurin lalle.
don haka suka fita dawuri, domin yaune Sofiyya tayiwa Siddika alkawarin nuna mata handsome.


Zuly ta wata makobciyar su me lalle (farida) take rokonta kan ta rakata Anyi mata hanya zataje tayiwa wasu lalle za'a biyata dakyau domin ta iya lalle sosai.

Dakyar Zuly tayarda zata rakata, don seda mama tasaka baki tukun.

Gun saloon suka fara zuwa bayan angama musune aka fara yimusu lallen,.

Itadai Zuly kallonsu kawai takeyi tana murmushi don azuwan farko taji sun burgeta, suma ta 6angarensu sun sake da ita sosai, harda exchanging numbers.

seda aka kusan gama musu around 5:30pn sannan Sofiyya takira Abdul akan yataimaka yazo yadaukesu.

Duk su hudun suka fito dai dai lokacin da Abdul yayi parking yafito.....................
'?
[8/22, 9:56 PM] Maryam-Ashner Jos: *Cutie Naa*>?p?

By

*Maryam Ashner*

https://chat.whatsapp.com/HRufBytJ0a434oKtSAFLmn

Mata zallah don Allah =?O?

Episode 20

Yafito sanye da shadda blue-black wadda takara haska fatarsa wadda ita ba baka ba kuma baza akirata da bakaba.

Kanshi babu hula se takalminshi sau ciki baki, sumar kanshi ta kwanta dukda cewa bawai yatara bane,.

Zuly farinciki ne yadabaibayeta don har lissafin kwanakin dasuka rage suje walima tasake ganinshi take.

Farida me lalle ma zuba masa idanuwa tayi, aranta kuwa fadi take inama inama.

Siddika dai batama kula dashiba, ita gyara zaman takalminta take a kafarta.

Sofiyya ko itama idanun tazuba mishi, don bata ta6a ganinshi cikin manyan kayaba,. Yamata kyau sosai wlh fiye da kullum ma.

Duk tsayawa sukayi babu wadda tayi magana cikinsu, se kallonshi dasukeyi.

Itako Siddika tayi zaton ita suka tsaya jira tagama gyara takalminta sutafi.
Sebayan data gama ta dago kawai taga sunzama kamar wasu cartoons suna kallon Abdul,

Itama kallonshi tayi taga shi bemasan suna kallonshi ba don wayarsa ma yake dannawa

dogon tsaki taja sannan tace "Allah wadaran naka ya lalace wlh"
Se lokacin duk suka ankara da shirmen dasukeyi, thank god bema gansu ba.

Duk sundan ji 'yar kunya

Zuly kai narawa tace musu "bari inje mugaisa Yaayana ne, kudan jira ni pleace"

Kalllon mamaki sofiyya kebin zuly dashi amma dai batace komai ba.

Seda tawuce sannan tata6o Siddka tace "Abdul nefa"

Zaro idanu Siddika tayi tace "don Allah dagaske shine? "

Tace "wlh shine muje"

Wucewa sukayi farida ma tabi musu baya.

Zuly nazuwa tace "hello"

Dago dara daran idanuwansa yayi yasaukesu akanta.

Dan murmushi yamata yace "sannu"

Wani farrr da ido tayi tace "from where to where"

Mamaki tambayar tabashi, to ina ruwanta dashi?

Kafin ya amsa mata su Sofiyya sun karasa wurin.

Kamshin turarenta ne yasanar dashi cewa tazo gurin, dago kai yayi suka hada ido.

Murmushi duk suka sakarwa juna na yaushe Gamo.

Don rabon dasu hadu tunkafin tace suleja, sedai sukanyi video call.

Da murmushi a fuskarsa yace "Cutie"

Itama murmushin ne kan fuskarta tace "Yaaya" don dama haka take kiranshi indai a gabanshi ne.

Zuly kuwa ranta ne yafara sosuwa, jitayi kamar tafasa ihu.

Siddika ce tace "hello handsome"

Dariya Sofiyya tayi tace "this is Siddka so dont mind her dan akwai yarinta a kanta"

Shidai murmushi yakeyi kana yace "if you are done semu tafi ko, kinga yamma tayi"

Sofiyya tace "sure"

Juyawa tayi tadubisu Farida tace "kozamuje afara saukeku tukunna? Dan naga abun hawa yana wahala anan"

Ba musu suka amince duk suka shiga bayan motan tareda Siddika.

Itakuma Sofiyya tashiga gaba, sukadau hanya.


A hanyane yakula da lallen da aka

8 / 26