Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
NAYI DACE
KITTY
©Maryam Aminu Musa, wannan document din na kudine kuma mallakina ne ban yarda wata ko wani su juyamin ko su fitat dashi ba tareda iznina ba, masu son document su tuntuɓeni 08121957799
I
Na kifa kaina cikin littafin da nake karantawa bana ma so na dago wani abun ya daukemin hankali,idan na Fadi wannan semester Ina cikin matsala,domin a yanzu ne na fara dandana me nursing ke nufi
Ina jarrabawar 2nd semester level 3,dukda a baya nayi school of nursing Amma karatun Babu sau'ki
Sunana bilkisu Abba adam,iyayena sun rasu,mahaifina ya rasu kafin zuwana duniya,sannan mahaifiyata ta bishi a ranar da ta haifeni,bazance banyi maraici ba Domin da iyayena nake kwana dasu nake tashi dukda ban taba ganin fuskokinsu ba Banda a hoto
Saidai banyi maraici na gata ba,Domin mama ta d'aukeni ta zamarmin uwa,shekaruna ashirin da biyu a hannun mama,kasancewarta yayar mahaifiyata yasa ta rikeni tamkar ita ta haifeni
Mama d'anta d'aya a duniya jabir,sai Kuma ni bilkisu,na samu gata a wajen mama,baba da jabir da ko iyayena iya abinda zasumin kenan so am so grateful
Kira naji mama ta kwala min,fita nayi daga d'akin Ina bitar abinda na karanta na sameta da waya a hannu,kafin tayi magana nasan dalilin kiranta
Cikin shagwaba na fara buga kafata a kasa nace
"Mama gobe fa exam gareni 8:30,Dan Allah kice Yaya kawai ya sayi takeaway idan nayi girki akwai matsala"
Ina maganar Ina sake duba littafin hannuna,murmushi umma tayi tace
"To ni da zaici nawa girkin ai sai nayi ko?Kuma karatunnan tun Friday kikeyi,yau lahadi,ki godewa Allah fa kinyi iya abinda Zaki iya,ya kamata ma ki huta hakan,Amma jeki ki karasa ni nayi girkin"
Kallan umma nayi yanda take smirking,ta sani Sarai bazan barta tayi girki Ina zaune ba,kicin na nufa da littafin nace
"Bari na musu jollof din macaroni kawai me bushasshen kifi Dan aikin Naman ma wahala ne"
Mama Bata tankamin ba har na Gama hada abincin inayi Ina karatuna,gaskiyar mama ce,Domin duk abinda na karanta alhamdulillah Ina jinsa a kaina,inada confidence a wannan exam din insha Allah
Ina juye abincin a flask naji tsayuwar motar su yaya,cikin sauri na baro kicin din Domin d'auko gyalena,d'aya d'aya abubuwan da suka Sanya banason zuwan su Yaya da Rana kenan,bana sakewa saboda abokinsa Saleh
Fitowa nayi na gaishesu na d'auko kayan abincin na ajiye ba tareda na kalli fuskarsu ba
Tafa hannu Yaya yayi yace
"Yauwa kanwata Yar albarka,Allah dai ya Raya Mana ke musha biki"
"Ameen Yaya,Allah yasa kaima ka tsaida Mata Nan kusa mu huta"
Dariya yayi ba tareda ya cemin komai ba,yayana playboy ne Amma fa na hausawa,yanada yammatan da bazan iya kirgasu ba,na rasa menene abin burgers a Tara Mata
Banji maganar Saleh ba Kuma nasan Yana wurin,daga Kai nayi Domin mu gaisa' nasan shi dai ba miskili bane
A baje na ganshi Kan kujera ya hada gumi idonsa yayi ja,kallon Yaya nayi nace
"Yaya me ya sameshi?"
"Kanwata zazzabi yake tun jiya da muka bar gidannan,shi Kuma bazai je asbiti ba,na manta ma.yace na bashi extra idan munzo gida"
Tashi nayi na taba goshinsa,jikinsa yayi zafi sosai,kallon idonsa nayi da hannunsa nace
"Malaria ce Yaya,Kuma allura zata fi saukar dashi da wuri,Bari na Masa pcm injection sai kuje asbitin daga baya"
"Bazamu iya tafiya asibitin a haka ba?" Saleh ya tambaya Yana kallan jabir,girgiza Kai nayi ganin yanda idanunsa ke kokarin juyewa nace
"Sai anyi allurar tukuna aje asibitin,Domin zaka iya galabaita kafin aje"
Tashi nayi da sauri na d'auko first-aid kit Dina na had'a allurar,zama nayi a hannun kujerar da yake nace
"Ba wani zafi zatayi maka sosai ba idan ka tsaya...."
Kafin ma Nakai allurar hannunsa ya janye cikin sauri,t-shirt ce Mai karamin hannu a jikinsa,hannunsa yasa ya rufe wurin yace
"Wai Dole sai allurar bazan Sha magani ba?"
"Ha'kuri zakayi,allurar tafi saurin gauraye jiki ne Kuma jikina yayi zafi,ka Bari nayi yanzunnan"
Babu kunya yake kokarin guduwa,yau Kam naga Namiji me tsoron allura,murmushi nayi nace
"Haba Yaya Saleh,bafa wani zafi zatayi ba ka daure ka tsaya Mana,minti kad'an ne"
Kallan allurar yakeyi kamar wata adda,girgiza Kai yayi yace
"Nifa banaso"
"Yaya Saleh allurarnan sai anyita ka tsaya kawai,Yaya Dan ri'keshi kad'an"
Ri'keshi jabir yayi,wani kallo ya watsa masa ya sakehshi yana dariya
Runtse Ido yayi ya kankame hannun nasa tareda cije baki,sakin Baki nayi Ina kallonsa,allurar Tana rufe a hannuna ko bud'eta banyi ba
Ri'ke wurin nayi tareda Bismillah na saka allurar,wata irin firgita yayi yace
"Wayyo!" Tareda Jan hannunsa wanda yasa allurar gaba d'aya ta goce
Zareta nayi nace
"Yaya Saleh Ashe Kai ragon Namiji ne?common allura ce fa,Allah ya taimaka da tuni ka jiwa kanka ciwo"
Dayan bangaren na koma nace
"Kayi ha'kuri,Amma sai Yaya ya rikemin Kai"
Ai jabir kamar kiris yake jira ya ri'keshi Gam Gam,allurar na saka a hannun yayi Kara kamar karamin yaro,kankame jabir yayi harda tura kansa a kafadar jabir,wincing yakeyi nikuwa dariya ta Gama cina kawai na danne ta ne,Amma zabgegen saurayi kamar wannan da tsoron allura
Wayyo yaketa nanatawa har na cire allurar,tashi nayi nace
"Kayita lailaya wurin kafin kuje asibitin"
D'aki na shige ba tareda waiwaye ba naci dariyata na gode Allah,kowane mutum akwai abinda bayaso Amma ban taba kawo Namiji zai tsoron allura ba
2
Kaina naji ya fara sarawa na rufe littafin na ajiye,lokacin hutawa yayi kenan Kar Kuma naje na rubuta rubbish
Wattpad na bud'e na duba littafin da nake karantawa nayi cigaba da karantawa,a half har bacci ya debeni
Washegari cikin doki na nufi makaranta, confidence sosai nakeji akan jarrabawar yau kuma alhamdulillah,na sameta yanda na shirya Mata
Mun Gama exams lafiya na Kuma ci gaba da jigilar yiwa su Yaya girki,har yanzu Saleh kunyata yakeji tun allurar da na Masa ni Kuma bana nuna masa wani Abu dukda Yana bani dariya idan na ganshi
A Dan hutun da muke na nemi makaranta ta bani takarda Domin na ziyarci wani asbitin na Karo ilmi kafin mu koma,a take aka bani approval,asbitin sharad'a na shiga na Basu takardar suka Kuma amince zan dinga zuwa Ina practicing acan
Ina da matukar son karatu sannan ina kaunar field Dina,na samu matsala a shekara ta biyu wadda ta janyomin maimaita dukka shekarar,hakan ne ya karamin karfi gwiwar da na zage dantse da karatuna
Tare da su Yaya muka fita suka ajiyeni a asbitin, bangaren haihuwa aka kaini Wanda nafi tsoronsa akan kowane bangare
Labour room muka fara zuwa babbar nurse din na ordering Dina nayi abubuwa,zuciyata ta karaya ganin yanda Mata ke Shan wuya tun kafin ma haihuwar tazo
Tsayawa mukayi Kan wata Mata dake jijjiga,hankalina ya tashi sosai da kyar na zama calm na tsaya a wurin
Matar ta galabaita sosai,bleeding take Wanda har nurse din saida ya Bata tsoro
Tun safiyarnan ake fama da wannan baiwar Allah sai biyar ta haihu,zuwa yanzu Kam na Gama karaya Dan naga iya ganina,Mata suna Shan bakar wahala wajen haihuwa
Kallo d'aya matarnan ta yiwa jaririnta tace
"Allah yayi maka albarka"
Kalmarta ta karshe kenan wadda ta fito sarari Bata sake cewa komai ba,a gaban idona yau mutum ya mutu,mace ta mutu bayan haihuwa
Fita nayi cike da tsoro,hawaye ke zuba daga idona Ina hango matarnan a cikin kwakwalwata
Yaya na Kira Ina Kuka nace yazo ya d'aukeni,Ina shiga motar na fara musu sambatu
"Yaya ta mutu,sanadin ta kawo Rai wannan duniyar ta rasa nata,Yaya yaronnan zai tashi maraya,a gaban idona ta mutu bayan Tasha wahala,Yaya...."
Katseni yaya yayi hankalinsa na Kan tu'kinsa yace
"Bilki,idan fa mutuwa ce kinyi sallama.da ita kenan,Babu abinda Zaki iya kiyi ha'kuri kawai shine,Allah da ya kawo jaririnnan duniya shi yasan yanda zaiyi dashi,kedai Baki kashe ta ba,Kuma tunda bazaki iya kasheta ki Raya ta ba mene na damuwa?muje na siya Miki shawarma kinji?"
Takaici ne ya sake isata,maimakon naji sassauci sai naji zuciyata ta sake karaya,cigaba nayi da Kuka Saleh yace
"Haba man,wannan wani irin rarrashi ne?mace ce fa Dole taji daban a ranta,kuma wannan rarrashin naka ai kaman kace ta sake yin Kuka ne,tsaya ka gani"
Bude gaban motar Saleh yayi ya dawo baya inda nake,saukar da muryarsa yayi yace
"Kiyi ha'kuri kinji kanwarmu, addu'a Zaki Mata da jaririn nata,Kinga ita fa tayi shahada aljanna straight zata tafi,Kuma Allah bazai bar abinda ta Bari ya wulakanta ko yasha wahala ba,ki zama mai juriya tunda haka yanayin aikinki yake,idan kina d'aga hankalinki bazaki dinga bawa marasa lafiya kulawar da suke bukata ba,nasan Zaki damu Amma ki takaita damuwarki"
Naji Dan sauki a Raina da maganar Saleh,cikin shesshekar kuka nace
"Yaronnan kamar ni yake fa Saleh,Nima haka mahaifiyata ta rasu,ya zai taso yaji?"
"Ke me kikeji?akwai wannan kewar iyayen nasan Zaki jita a ranki,Amma gata dai kinsamu,kin Sami iyayen da suka maye Miki gurbin naki,kin samu gata daidai misali,ki sanyawa ranki shima wannan yaron zai samu gata fiye da naki ma,kiyi ha'kuri mutuwa ba Dadi Amma ki jure,kina aikin asbiti kinawa marasa lafiya Kuka ai Korarki zasuyi,share hawayenki muje kici shawarma,zan Baki labarin wata amarya da akazo da ita wajenmu ta zabi kayan gado"
Jana ya dinga yi da Hira yana fadamin labaru na ban dariya,kafin muje sayan shawarma har na fara dariya
Ana bani sharmar tawa na bud'e na fara ci,tayimin Dadi sosai,lumshe ido nayi Ina cika bakina da shawarmar,Domin tafi Dadi ka jita full a bakinka
A jikina naji kaman Ana kallona na bud'e Ido na kalli Saleh,kallona kuwa yake Yana murmushi,ko a jikina na tura sauran shawarmar a bakina
Yar da takardar nayi ina lashe hannu nace
"Yaya Dan Allah mu koma Bata isheni ba wallahi,Kuma bamu siyowa umma ba"
"Ba inda zamu koma,saidai mu sayi biredin a hanya muje gida ki had'a ni dama ba son sayenta nake ba gani nake asarar kudi ce,Kuma idan Kika Mana tafi dad'i"
"To mu sayi biredin,ni yunwa ma
Ta karamin" na fad'a Ina jingina da kujera,Saleh ne ya mikomin tashi yace
"Nan gefen bakinki ki goge"
Gogewa nayi na'ki karbar shawarman nace
"Ka ci kawai idan munje gida zan had'a ai"
Bata Rai yayi yace
"Saboda na saka yawu shine bazaki kar'ba ba?"
"A'a wallahi ba haka bane,kaci kaima naci ai,Kuma ta isheni"
Hannu ya saka ya gutsire inda yaci yace
"Yanzu Kam idan Baki kar'ba ba nasan kyankyamin hannun nawa kike Kuma na wankeshi a hanya"
Kallonshi nayi na kalli shawarmar,naga ya Bata Rai,Mika hannu nayi na kar'ba tareda godiya na fara ci,Ina Jin idonsa na kaina nayi kaman bansan dashi ba,ita shawarma ba'a Mata cin gayu
Tas na cinye na goge hannuna da bakina,a hanya muka tsaya muka sayi biredin kasancewar inada duk kayan hadin shawarmar
Biredin shawarma
Cabbage
Naman kaza,rago ko Kuma minced meat(Amma minced meat bai fiye Dadi ba,ki yanka Naman rago kanana ki tafasa kiyi dashi tafi dad'i)
Attaruhu
Mayonnaise
Ketchup (optional)
Albasa (dafaffiya)
Zaki hada nama da attaruhu da albasa a cikin sauce pan,da sauran kayan hadinki,sai ki shafa mayonnaise a jikin biredin shawarman da ketchup idan kinaso sai ki d'auko Hadinnan naki ki zuba sai ki saka cabbage ki rufe,anaso a saka kayan Hadin da zafinsu yanda zasu rage taurin cabbage din ko Kuma ki saka a microwave idan kin Gama
Shikenan,all done abin 350_600 a sau'ka'ke
Idan kaza Zaki saka Zaki cire Naman a tsaitsaye ne d'aya jikin kashin
*Hadin mayonnaise*
Kwai guda biyu
Mai gwangwani biyu
Leman tsami
Vinegar
Gishiri
Zaki zuba kwai a blender ki kunna har sai yayi fari,sai ki saka lemon tsami da vinegar da gishiri kici gaba da blending,idan suka hade kwan yayi fari Kal,sai ki d'auko Mai ki dinga zubawa a hankali har sai yayi kaurin da kikeso sai ki juye,a sau'ka'ke Babu kashe kud'i
********
Shawarma tayi Dadi,Kuma kasancewar kananu nayi ni kaina naci kusan biyar,su Yaya da Saleh kuwa ba sai an kirga ba
Lemon na'a na'a na had'a Mana (wannan sai next page zan bada shi insha Allah😋),muna ci muna korawa muna Hira har dare yayi
Bayan sun fita na zauna Ina tunanin Saleh,a rayuwata inason Namiji Mai barkwanci Wanda na lura halin Saleh ne barkwanci da surutu,dadin dadawa Kuma gashi da iya magana da rarrashi
Duk zuwan da sukeyi bana ma zama dasu balle na sauraresu,Amma zamana da Saleh yau yasa na fara Masa kallo na daban,yau Saleh ba ragon Namiji bane,cikakken namiji ne a wurina,Wanda yasan yanda zai tafi da mace
Mamakin yanda ya rarrasheni cikin kankanin lokaci nayi na kwanta Ina dawo da maganganunsa,irin kallon da yakemin Ina cin shawarma da Kuma gentle man din da ya zama sanda ya mikomin tashi
Tashi nayi zaune na zare Ido,meke damuna ne?Anya garau nake?na zauna Ina tunanin Namiji har na kusan minti biyar?
Ba shiri na tashi na fita Palo,a zaune na samu mama Tana kallo nace
"Mama zanje gidan Yaya"
Amsawa tayi da to na fice
Ina zaune a unguwar d'ambare,unguwa ce Mai karancin mutane saidai Tana da kyau
Baba kabiru, mari'kina kenan sannan mijin mama,matansa hud'u,duk matansa guda uku gidajensu na hade da juna a bayan layinmu,mama ita kadai ce macen da aka Ware a gefe sannan itace mace ta.uku a cikinsu
Hajiya itace matar baba ta farko,tanada 'ya'ya goma dukkansu Mata ne,ta aurar da takwas saura biyu da Kuma tarin jikoki a gidan
Adda itace mace ta biyu,tanada yara bakwai,maza biyar Mata biyu,maza uku sunyi aure sauran duk sunanan
Sai mama,ita Kuma d'anta d'aya tall jabir
Maman dije itace amarya,Yayanta Kuma biyar,Mata uku maza biyu,duk kananu ne
Gidan adda na shiga Domin shine da saannina,yayanta Mata biyu zulaihat da rukayya
Samunsu nayi suna cin tuwo dumame,wanke hannuna nayi na zauna muka ci na tashi na Karo,a wajen abinci bana kunya ko a Ina ne,Domin a wurina wayewa shine na cika cikina na baiwa bakina hakkinsa
Bayan mun Gama ci nake basu labarin Saleh,da Kuma abinda ya faru a asbiti,kallon juna sukayi zuka tafa sukace
"Mukam Allah ya kaimu musha biki,Ashe ruwan idon da ake mijin na gida"
Kwanciya nayi ba tareda nace musu komai ba,idan nai magana ma surutu zan karawa kaina nasan halin abuna
Kuma nasan ba gskiya suke fad'a ba,ni ban yarda da love at first sight ba,yaushe ma nasan Saleh da zan fara tunanin aurensa,lalube ne nake a duhu bansan da wa zan Kare ba,nasan dai Saleh ya fara birgeni kuma zan daukeshi a matsayin abokina.....Amma me kuke tunani?
Insha Allah zan dinga posting sau uku kawai a sati,Amma ya danganta da yanda zaku min votes and comments,idan na samu votes da yawa zanyi sau hud'u ko biyar ma,idan kuwa Babu zan dinga sakinsa sau daya a sati
Littafi ne da zai tabo bangarori daban daban na rayuwa,girke girken zamani kala kala da yanda ake yinsu,kayayyakin gyaran jiki,yanda Zaki tsuma kanki ba tareda illa ba da sauransu,
Vote
Comment
And tell me your opinions,tnxxx
3
Washegari male ward aka kaini,na aikatu sosai na gaji,Ana sallar azahar na d'auki hanyar gida
Ina zama Kan kujera mama tace
"Babanku yace yau zakiyi ba'ko"
Maida numfashi nayi nace
"Layi yazo kaina kenan,Amma kin sanshi mama?"
Zama tayi kusa Dani tace
"Eh to na sanshi,Amma shekararsa 7 a Russia Yana karatu,kamar ance engineering yake karanta,Dan gidan baba habibu ne bai Dade da dawowa ba,tun wancan satin babanku ke min zancensa yau dai zaizo"
"To Allah ya kawoshi lafiya,yanzu fa ko bamu yiwa juna ba shi zan aura ko mama?"
Dariya mama tayi tace
"Eh to,ya danganta,idan mazan sukace basa so yawanci Ana ha'kura,Amma dai gaskiya duk Hadin da su baba keyi ba'a canzawa Kuma haka ake zama lafiya ba wata fitina"
"To muma Allah ya had'a jininmu,Ina dai tsoron Yan kasar wajennan kad'an"
Tashi nayi na shigo harkokina Ina tunanin irin mutumin da baba kabiru zai turomin
Nayi mamaki ma da yakai yanzu bai min miji ba,yanda ka'idarsa take shi da baba habibu shekara 17_19 an yiwa yarinya miji,wasu ma tun suna secondary har su gama tukun ayi auren
6:00 naji Kira a wayarta da number da ban sani ba,Kai wayar kunnena nayi tareda sallama
Da wani Ascent na daban naji an amsamin,irin bakinnan ya gaurayu da wani yare na daban,tamkar ma kamo hausar da zaimin yakeyi
Da kyar ya samu yace
"Nine baba ya turo Ina tsaye a waje"
Riga da skirt ne a jikina na atamfa,mayafi na yafa na saka powder da man Baki na nufi d'akin mama
Sallama nayi daga waje sannan na shiga nace
"Mama wai yazo"
"To jeki a dawo lafiya,a Kuma kula"
Har na fita na dawo nace
"Mama a kofa zamu tsaya ko?"
"Eh d'auki kujerun robarnan ki ajiye muku daga gefe"
Tafiya nake ba tareda Jin wani d'ar a Raina ba,ni dama tsoron fidda miji nake duk mazan tsoro suke bani,gara a zabamin ko banaso nasan su baba baza su min zaben da bai Dace ba,Kuma soyayya a wajena ba komai bace nidai naci na koshi nayi karatu nabi lafiyar katifa na Danna wayata.
Kokari nake na maida fuskata neutral,ba yabo ba fallasa,karasawa nayi Ina murmushi na bud'e gate din ya shigo
Wani irin kallo yakemin,irin kallon da zaka ji duk tsikar jikinka ta tashi,he was checking me out
Matsawa nayi Amma dukda haka idonsa na bin duk motsina,gyaran murya nayi Domin na dawo da hankalinsa Kan fuskata Amma Ina...
Kallona yake kaman Wanda aka bashi Riga akace ya 'kirga yawan zaren da aka sa'ka rigar dashi,banason kallo Sam,dukda kokarina na iya magana gaban mutane Amma da zarar hankalin mutum ya sauka kaina bana sakewa
Kafata naji ta fara rawa nace
"Sannu da zuwa,Bismillah mu zauna ko?"
Hannu yasa ya shafi kujerar alamin yaga ko da 'kura,dukda Babu kurar saida ya Sanya handkerchief ya goge tukun ya zauna, murmushi yayi yanakallona Ido cikin Ido,a hankali na sauke kaina nace
"Ina wuni,ya gida?"
"Lafiya....so.....kene bilkisu?"
"Eh" na amsa da kyar
"Ni sunana sulayman,Kina da 'kirar jiki me kyau"
Mamaki ne ya kamani da takaici,abinda zai fara fitowa daga bakinsa kenan?bance komai ba yace
"Shekarunki nawa?"
"22" na fad'a cikin sauri,sunkuyo kansa yayi sosai wurin kujerata,ji nayi kaman na gudu sai kuma na tuna a cikin gidanmu ne na dake
"Baba yacemin kina karatu ko?me kina karanta?"
"Nursing" na fad'a ina jin kaman zanyi Kuka,na takura sosai
Dariya yayi yace
"Oh nursing?kune masu dealing da su jini su fitsari,duk wannan kazantar ko?ugh,banason wannan aikin.kin kusa gamawa?"
Cije bakina nayi nace
"Saura shekara biyu"
"Sai kin Gama kenan za'ayi aurenmu"
Shiru na Masa yace
"Ops sorry Ashe fa ku Nigerian girls bakwa zancen aurenki saboda mene ake Kiran abun?"
Shiru nayi bance Masa komai ba ganin yaso ya fara da cin fuska,Banda ma ya Raina ni shi shekarunsa nawa a Nigeria?maybe ma irin kazamannan ne da Yana saurayi
Bai kwantamin a Rai ba ko Dan yanayin kallon da yakemin min,tashi nayi nace
Bari na kawo maka ruwa"
Kallon hannuna yayi ya kalleni ya girgiza Kai yace
"No dear,bakomai Nasha ruwa a hanya,tafiya zanyi sai wani lokacin ko?"
Amsawa nayi da okay na d'auki kujerun nayi gaba,waiwayawa nayi na ganshi ri'ke da gate yana kallona ta baya,waving Dina yayi na kakalo murmushi nayi gaba
Ina shiga naga mama na yanka kankana,zama nayi ba tareda nace komi ba na fara huce haushina Kan kankanar
Fam nake cika bakina da kankanar,idan Raina ya back dama kan abinci nake hucewa,idan ba fruit ba to na samu snacks
Kallona mama tayi tace
"Me ya faru?" Domin tasan idan Ina tura Abu bakina haka to an ta'boni ne
Hadiye kankanar nayi na Danna banana,Ina cin bananar nace
"Mama yaronnan inaga Russia ta 'batashi,kinji