Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
with Saleh, bansan yaushe zai fita daga bakinta ba, naga anyo beetle sabuwar yayi shape d'in mata, tayimin kyau sosai motar".
"To waye bazai so ki fita daga sahun su Saleh ba bayan wannan wula'kancin da yayi miki? Miliyan biyun banza? Ai motar da za'a siya miki sai tafi miliyan biyu domin ya gane kurensa, ke fa sai kinfi 'karfin Saleh a 'yan kwanakinnan".
Dafe kaina nayi nace "Dan Allah yaya muyi wata maganar da babu saleh a cikinta"
Jingina kansa yayi a kujera yace "ni da nake Shirin fad'a miki a daren jiya yazo nemanki amma nace masa bakyanan".
Wani iri naji a raina amma na daure nace "me yazo nema a wurina? Ko wani kud'in ya nema ya rasa?"
Murmushi Yaya yayi yace "ba kince bakyason maganarsa ba? A barta kawai".
Banyi musu ba nace "okay" na d'auki mayafina da jakata nayi hanyar d'akina.
"Cewa yayi yazo ya baki ha'kuri ne...ya kiraki baya samunki, na fad'a masa kina Kaduna idan kinaso ku had'u zan masa magana idan ya dawo".
Ban waiwaya ba na shige d'akina na rufo 'kofar, zama nayi bakin gado na zuba tagumi, da ace a weeks d'in da suka wuce ne tsalle zanyi saboda murna, amma a yanzu wani irin takaici ya 'karamin, bai zo bani ha'kurin ba sai yanzu? Ya fara gano gaskiya kenan ko kuwa ya gaji da zaman kad'aici?
Kwanciya nayi ina kallon ceiling, inaso na had'u da Saleh? Sadly yes inaso na had'u da Saleh, inaso naji dalilinsa na zuwa nemana bayan sati uku da sakina, inaso na kalli fuskarsa nace "gashinan abinda na fad'a maka ka 'ki amincewa dani" inaso naga Saleh amma duk yanda naso ganinsa nasan ba abu ne da ya dace ba, bazan amincewa zuciyata naga Saleh ba domin kalma d'aya zai fad'amin ya juyar da ra'ayina na koma gareshi wanda a yanzu shine last thing da nake bu'kata, inaso na zauna a gida na 'kara sanin kaina na san muhimmancin kaina, nayi tunani na kuma yanke hukunci ba tareda soyayya ta rufemin Ido ba, Ya Allah katka had'a ni da Saleh a wannan lokacin kar kuma ka bashi ikon maidani har sai na samu nutsuwa.
Bacci ne ya d'ebeni na gajiyar aiki, 'karan wayata ne ya tasheni na duba naga number Aunty, danne wayar nayi na maidata silent naja abun rufa kafin na koma bacci naji muryar mama "tunda kin tashi sai ki fito kiyi breakfast ko?"
"Ummm mama sai anjima har yanzu da bacci a kaina" na fad'a cikin shagwa'ba, matsowa mama tayi ta yaye abun rufar tace "tashi ki karya 11 ta kusa kina kwance, idan kinci abincin kya koma baccin, na rasa meke hanaki cin abinci jiya haka Kika fita bakici komai ba".
Saida ta fad'a na tuna daren jiya banci komai ba, tashi nayi na nufi toilet nayi brush na fito na canza kayana sannan na fita parlour, breakfast nayi ina tunanin me zanyi tunda inada day off yau, hakanan naji I want to have some fun amma babu hali dan bansan ma me zanyi ba.
Wayata na bud'e na hau Wattpad na fara duba litattafai, d'auko books nayi da dama na zauna na fara karantawa, Ina karantawa mama ta fito ta zauna.
"Wani film ne wannan akeyi?" Ta tambaya tareda d'aukan remote, kallon tv d'in nayi naga 'mission impossible 2' da sauri na zauna nace "aikwa film d'innan yayi kyau".
Kallo mukeyi muna dariya mama tace "Babu dai abinda yake damunki ko?"
Girgiza Kai nayi domin banason wannan maganar da mama ta d'auko, indai za'ayi maganar Saleh sai naji yanayina ya canza wanda banason hakan, nayi tunanin Mama zata bar maganar amma sai naji tace "kinaso ki koma Bilkisu?"
Jan numfashi nayi na zubawa tv ido, kasa bata amsa nayi domin a yanzu bansan me nakeso ba
"Na fahimta idan kinaso ki koma Bilkisu, amma ya kamata kiyi tunani akan abinda ya faru sannan ki shiryawa duk wani abu da zai iya faruwa, bazan bo'ye miki ba amma banji dad'in rashin zuwansa ba, idan aka saki mace ko kai miji baka zo ba 'yan uwanka maza na zuwa su bada ha'kuri, amma anci sati uku babu wanda ya le'ko, shi bai kira yaji lafiyarki ba dukda har yanzu baki fita daga matarsa ba, nasan kina son mijinki amma....."
Katse mama nayi nace "Mama ni a yanzu bansan abinda nakeso ba, ban saniba inason zama da Saleh? Banason zama dashi? Gaba d'aya a yanzu bansan me nakeso ba amma bana fata na koma wannan gidan ko dan wahalar da nasha a cikinsa".
Inajin idon Mama a kaina amma na'ki juyawa, shiru tayi sannan tace "to idan zai maidake kenan wani gidan zai kama miki?"
"Bana tunanin zai maidani bayan abinda ya faru, ko yanaso ya maidani Hajiya bazata ta'ba bari ba nima bana sa ran komawa, ina fata Allah yayimin za'bin da yafi alkhairi".
"Alkhairi shine barin gidan Saleh har gaban abada" juyawa mukayi ni da mama muga mai maganar, Aunty na gani na cine bakina, wai ita bata gajiya da yawo ne? Gashi tazo ana maganarnan na shiga uku.
Zama tayi bayan sun gaisa da mama tace "wannan sha-sha-shar ta zauna tana karanta miki irin son da takewa sale ko?"
Dariya Mama tayi tace "a'a muna dai magana ne a kansa tunda ya saketa shiru shi baizo ba danginsa ma babu wanda yazo"
Hard'e 'kafafu Aunty tayi tace "yo wa zaizo? Ai idan kikaga ana zuwa to dama an d'auki dangin mata da daraja itama matar an d'auketa da daraja, ko kuma dangin mijin ba matsiyata bane, amma wannan matsiyatan ina zasu iya zuwa? Ai wallahi na 'kagu ta gama iddar wannan talakan banzan na nuna mata inda rayuwa take, wannan Saleh yake ko wa d'in sai ya raina kansa domin bazai ganta a hanya ya ganeta ba ma, ko ya ganeta saidai yaja da baya domin tafi 'karfin ya kulata tsoro ma zaiji".
"Auntyna ya batun motar tawa?" Na fad'a domin na kauda hankalinta daga kan maganar Saleh, take walwala ta bayyana a fuskarta ta ciro wayarta ta mi'komin tace "gasunan ki za'bi wadda kikeso ki fad'amin".
Duba motocin nayi naga wata fara, tayi matu'kar had'uwa motar, nuna mata nayi ta kalla tace "yauwa 'yar gari, wannan kamar 3 ko 4 yacemin kud'inta".
Zare Ido nayi nace "Aunty miliyan uku?" Hararata tayi tace "idan an cire miliyan uku an siya miki mota me akayi to? Macece miliyan uku? Shiyasa ma za'a 'kala miki sharrin sata kina nuna kamar kin taso a cikin tsiya, bilki dukiyarki dan an cire miliyan uku an siya miki mota wallahi ba'a fad'i ba, kefa Allah ya cetoki ne kawai daga wuta zuwa aljanna, wani dad'in ma sai kin gama idda".
Zuba mata ido nayi nace "wai ni aunty wannan dukiyar tawa da kike fad'a nawa take ne? Meyasa ban fara cinta ba sai yanzu?"
Yanayinta ne ya koma serious one tace "dukiyarki bazan fad'a miki adadinta ba saboda nima ban sani ba, bayan mahaifiyarki ta rasu Mama ta d'auko ki anso a bawa baba Kabiru gadonki, amma ya'ki kar'ba sai aka dan'ka duk dukiyar a hannun 'kanin mahaifiyarki, Allah ya bashi albarka da baiwa idan har kud'i kakeso ka juya ka samu riba Mai yawa da albarka to kabi ta hannunsa, Kar kice ya akai na sani domin a wajen mahaifiyarki yake zaune, tun iyayenki na raye yake juya kud'in mahaifinki har ya rasu, bayan Mama ta d'aukeki babu wani abu da suke bu'kata ba dawainiya dake dukiyar taci gaba da zama a hannun Khalid yana juyawa, lokacin da mukaji shiru babu labarinsa mun d'auka har ga Allah ya cinye dukiyar ne ashe Yana ta juyawa, a takaice dai yanzu kinada hannun jari babba a wani kamfanin mayafi dake Dubai, iya abinda na sani kenan, kuma bamu san da hakan ba sai bayan kinyi aure, yanzu haka yana shirin zuwa ya ganki yanda yace mana sannan za'ayi lissafin kud'inki na yanzu, motar ma shine zai taho miki da ita".
Gyad'a kai kawai nayi domin ban gama fahimtar abinda take so ta sanar dani ba, wani tunani ne yazomin nace "aunty to ya akeyi da zakka ko baya fitarwa?"
"Idan yazo ki tambayeshi, next week zai iso Nigeria da motarki shine kawai abinda zan iya fad'a miki"
Anan muka bar zancen dai amma duk hankalina ya tafi wani wurin daban, hira su mama
suka fara akan iyayena na zuba kunne Ina sauraronsu, irin zaman da ummina tayi da Khalid, irin zaman auren da tayi abubuwa da dama dai, tunani na fara ina hango rayuwata tare dasu da yanzu ina tare dasu ya rayuwata zata kasance?
"Waye yayi miki wannan d'inkin?" Kallon aunty nayi cikin sauri domin ta katsemin tunani ban kuma ji me tace sosai ba, maimaitawa tayi nace "wani tailor ne Saleh yake kaimin yana min d'inki".
Tashi tayi ta shiga d'akina na bita, kayana ta fara cirowa daga wardrobe sai ta bud'e taja tsaki ta cillar a gefe, saida ta gama hargitsemin kaya sannan tace "Allah Bilkisu ke abin tausayi ce, dama baki tsaya kin waye ba sannan shima mijin naki ba'kauye, yanzu wannan sune kayan da zaki saka ki shiga cikin mutane ki fita kunya? Kinada kayan da baki d'inka ba?"
Raina ya sosu da maganarta amma na share na zauna ina ninke kayana nace "inada kusan turmi 20 a gida da laces wad'anda ban d'inka ba".
"To shikenan da sau'ki ai, ni sai nake ga kamar ma duk kayan lefe ne", kallonta nayi dukda auntyna ce ita kuma babba ce ta fara wuce 'kaida, numfashi naja nace "Aunty dukda Saleh talaka ne a wurinki amma ya wadata ni da sutura yanda ya kamata, a cikin kayan lefena baifi goma sha biyu na d'inka ba a shekara uku domin duk abinda za'ayi na taro sabbin d'inki yake min". Bansan meyasa nayi defending Saleh ba amma gaskiya na fad'a, dukda shine talaka a cikin 'yan uwansa amma suturar da nake sawa zatayi dai-dai da tasu har ma ta wuce.
Aunty batace komai ba ta fita, bayan na gama gyara kayana nayi zamana a d'aki ina danna waya, le'kowa tayi tamin sallama sannan ta tafi.
Haka naci gaba da tafiya da rayuwata, a kowacce rana aurena na sake fita a raina ina kuma sake jin haushin Saleh, na 'kagu na cire Saleh daga rayuwata na samu sau'ki, idan naga 'yammatan da basuyi aure ba sai naji Ina ma ina cikinsu, dukda banyi auren wuri ba nayi aure a 21 amma ji nake inama na sake jira, kamar yanda ake fad'a da kayi auren wuri babu kwanciyar hankali gara kayi zamanka a gidanku, gashi dai ni naje na fito Allah yayi 'kaddarar tawa sai na sake jera kafad'a da wad'anda na tafi na bari.
Ranar da Khalid ya dawo tana d'aya daga cikin ranakun da suka sanyani farin ciki a rayuwata, ba wai jin adadin dukiyata ba a'a, sai domin yazomin da labarai na iyayena wanda babu wanda ya ta'ba bani su, dad'in dad'awa ya kawomin kyakkyawar mota ta kamfanin KIA, bayan ya dan'ka min motar sannan ya dan'kamin account da ya bud'e da sunana wanda riba ce kawai zata dinga shigomin nayi abinda naga dama dasu, zakka da sauran juya kud'ad'den duk yana hannunsa, saida idanuna suka kusa fitowa da ya lissafamin kud'in, da alamu dai Aunty ta kusa juyamin rayuwata na koma ajebota.
Har naci wata biyu a gida ban sanya Saleh a idona ba, zuwa yanzu na gama samun nutsuwar da zan iya yanke hukunci, kud'ad'de shigomin sukeyi sosai ga salary na, abin mamaki aunty ta shareni ta manta da rayuwata hakan yayimin dad'i, domin ban shirya tashi daga Bilkisun da nake ba banaso aunty ta cusamin ra'ayin kud'i na zama wata ta daban, rayuwata a haka tana min dad'i banaso na shiga wata rayuwar.
***********
*SALEH*
Aikin da ya kamata ya gama a wata d'aya ko sati uku a sati biyu da kwanaki Saleh ya gama ya juyo, duk yanda yayi Jabir ya had'ashi da Bilkisu ya'ki, yace masa ta koma wajen kakarta a had'eja dukda haka bai 'kyaleshi ba yace ya bashi address d'inta.
'kin bashi address d'in da Saleh yayi ya sanyashi fara gadin gidansu Bilkisu, amma cikin rashin sa'a baya ta'ba ganin shigarta ko fitarta, gashi ayyukansu sun fara yawa.
Saida aka ci wata biyu bai samu ganawa da Bilkisu ba, a watanni biyunnan har an fara kwashe kayan Bilkisu hakan ya d'aga masa hankali sosai, yanke shawarar neman mafita ta 'karshe yayi wato ya samu mahaifin Bilkisu.
Kwalliya yayi ta ganin surukai sannan ya d'auki hanyar fita, kafin ya kai 'kofa ya had'u da Hajiya ta fito, washe baki tayi tace "a'a Saleh dan Hajiya gidansu hadiyya zaka je ne a wannan daren?"
Girgiza kai yayi tareda gyara tsayuwar sa babu amfanin yiwa Hajiya 'karya saboda haka ya sanar mata da gaskiyar al'amari yace "Hajiya zanje na dawo da Bilkisu ne, a yanzu na Gane kuskurena da na saketa kuma nayi nadama, banida matar da ta wuce Bilkisu kuma bana fatan rabuwa da Bilkisu, kiyi ha'kuri ki zauna da ita lafiya Bilkisu batada matsala".
"Waye me matsalar kenan?" Ta fad'a tana kallansa a wula'kance, "Hajiya bance ga Mai matsala ba amma nasan cewa bakyason Bilkisu, amma ina sonta idan kina Sona zakiso abinda nakeso, Hajiya Bilkisu itace farin cikina bazan iya rayuwa babu ita ba".
"Zaka mutu kuwa domin indai cikin gidannan zaka kawo Bilkisu bazan zauna da ita ba".
"Sai na kama gida na sakata, nidai ki amincemin na zauna da ita".
Numfashi taja tace "hadiyyan fa?"
"Hajiya banason auren wata bayan bilkisu kiyi ha'kuri zan dawo da ita".
Hanya ya d'auka zai fita tace "karka fita Saleh".
Juyowa yayi yace "hajiya bazan miki biyayya akan wannan ba, bayan duk abubuwan da Kika yiwa Bilkisu neman yafiyarta kad'ai ya kamata kiyi".
Numfarsa tayi a fusace tace "bani mu'kullin gidanka" kallonta yayi cikin mamaki, maimaitawa tayi cikin d'aga murya babu musu ya ciro wallet d'insa, kafin ya ciro key d'in ta wafce wallet d'in gaba d'aya sannan ta kar'bi wayarsa tace "kaje gidansu Bilkisu, idan kaje ka zauna acan, indai ka Sanya 'kafarka ka fita daga gidannan saboda wata Bilkisu to ka fita kenan".
Tana gama fad'in haka ta juya ta nufi cikin gida, tsayawa yayi ya bita da kallo ya rasa yanda zaiyi da ransa, yana tsaye ta dawo ta shige d'akinta ta rufe, ganin tsayuwar batada amfani ya sanyashi ya juya ya nufi gidansa saidai ya sameshi a rufe, a fusace ya daki 'kofar ya jingina kansa numfashi yake ja yana saukewa har ya d'an sami nutsuwa tukun ya nufi part d'in Hajiya.
A rufe ya samu 'kofar saida yayita bugu sannan ta bud'e "shigo" ta fad'a tareda zama Kan kujera, zama yayi a 'kasa tace masa "me kakeso"
"Mu'kulli nazo kar'ba".
Sunkuyowa tayi tace "bazan baka duk abubuwan dake hannuna ba Sai akan sharudda, zaka auri Hadiyya cikin wata biyu sannan babu kai babu Bilkisu"
Ya gaji da yi mata musu yace "to"
Kashe murya tayi tace "Saleh na gaji da musu dakai kamar ba ni na haifeka ba".
Sunkuyar da kansa yayi yace "hajiya nima banaso na dinga miki musu".
Tashi tsaye tayi tace "zan barka ka dawo da Bilkisu" cikin sauri ya d'aga kanshi ya kalleta, murmushi tayi tace "amma ka yimin al'kawari zaka amince da duk abinda na nema daga gareka ko menene".
Cikin sauri yace "zanyi Hajiya ko menene".
"Zakayi duk abinda nakeso?" Shiru yayi ya kalleta, Anya ba kuskure bane amincewa da sharad'inta? Still dai yace "eh", ajiye masa abubuwansa tayi tace "gobe da safe kazo ka sameni".
36
Kwana yayi yana tunanin abinda hajiya zata nema daga gareshi, bazai wuce auren hadiyya ba amma indai akan ya dawo da Bilkisu ne zai amince da ko mene, yasan Bilkisu ma zata amince da hakan.
9:00am a part d'in Hajiya tayi masa saida yayi breakfast sannan Hajiya tace masa "Zan cika maka al'kawarinka da na d'auka na amince ka dawo da Bilkisu"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da godiya, girgiza kai tayi tace "sharad'in shine...bazaka dawo da ita ba sai ka auri Hadiyya ta sami ciki tukuna ka dawo da ita".
Sunkuyar da kansa yayi yana auna maganar Hajiya, idan har zai dawo da Bilkisu sai bayan watanni kusan biyar kenan zuwa bakwai, d'agowa yayi yace "Hajiya kiyi ha'kuri na amince zan auri Hadiyya amma ki barni na dawo da Bilkisu, lokaci zai 'kuremin".
"Bazai yiwu ba kayi abinda nace kawai, idan bazaka iya ba sai ka ha'kura da matarka".
Sauke murya yayi yace "Hajiya har yanzu da aurena akan Bilkisu kiyi ha'kuri na dawo da ita sai na auri Hadiyya daga baya".
Dariya tayi tace "Haba Saleh kar ka yimin wayo mana, nasan idan matarka ta dawo bazaka ta'ba auren wata matar ba, sai kayi aure zaka dawo da ita".
Tashi tayi ta shige d'akinta, fitowa tayi tace "ban kuma lamince maka kaje gidansu ba indai ba kayanta zaka ce su zo d'iba ba".
Zama yayi ya zuba tagumi a palon hajiya, wace masifa ce haka ta sanyashi sakin Bilkisu gashi tun kafin aje ko ina ya fara nadama, Banda sharrin zuciya ta yaya zai saki Bilkisu? Bilkisu tayi ha'kuri fiye da wanda shi zai iya, ta zauna dashi cikin biyayya ba tareda matsala ba ko rigima sukayi sai tasan yanda ta shawo kansa bata bari ya kwanta da 'bacin rai ko da kuwa laifinsa ne, meyasa bai kwatanta hakan ba a lokacin da zuciyarsa ke kusa? Ko dan darajar iyayenta bai dace ya saketa ba da wani ido zai kalli iyayenta bayan halaccin da suka masa?
Fita yayi duk da maganar Hajiya amma ya toshe kunnuwansa ya d'auki hanyar gidansu, a hanya ya tsaya yana tunanin dame zai tunkareta take jikinsa yayi sanyi ya juya ya nufi aiki.
**********
*BILKISU*
"Mama yanzu idan kika tafi yaushe zaki dawo?" Na fad'a tareda rungume pillow d'in kujera, 'kauye mama zata je bikin wata 'yar 'kanwar mijin waye waye ni bana gane wannan lissafin nata, gashi aiki bazai barni ba ko da ace banida aiki bana son zuwa 'kauye kwata-kwata musamman irin wannan.
"Zanyi kwana biyar".
Kwanciya nayi a kafad'arta nace "ya zakiyi da babyn taki". Dariya tayi tace "tunda bazaki 'kauye ba sai kije gidan Aunty, nayi mata magana".
"Nifa Mama ba wai 'kauyen ne matsala ba, kikace fa 'kauye cikin 'kauye za'aje a lokacin bikin kuma ko band'aki na kirki babu, haka kawai ka tu'be kana wanka wani 'kato yana le'koka".
Dariya Mama tayi tace "shikenan naji, ki had'a kayanki jibi zan tafi, gobe saiki tafi da yamma saboda fitar sassafe zanyi, idan akwai wani abu da kike bu'kata sai ki fad'amin".
Master card d'ina na nuna mata nace "karki damu mama ko