NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   35 / 41

102K to 105K   out of 120.7K words

cikin dariya.

I miss your kiss, how your soft lips feels on mine, how wet you.....".

"Ya Isa na fahimta yaushe zaki dawo?"

"Ai ban gama maka elaboration d'in ba, sannan sai na haihu zan dawo".

Alamun ya tashi ya zauna naji sannan yace "yauwa dama inaso na tambayeki, wace 'kasa kikeso ki haihu?"

"Nigeria mana".

"A'a Banda Nigeria ki za'bi wata".

"No dear banaso naje ko ina na haihu anan Nigeria nakeso na haihu gaban 'yan uwa da dangi, banaso naje wurin da zan haihu daga ni sai kai".

"Da gaske nake Bilkisu bazaki haihu anan ba, kinsan irin wahalar da matan Nigeria kesha wajen haihuwa? A cikin lokitoci 10 a wannan lokacin bazaki samu 6 da suke yin aiki tsakani da Allah ba, ni hospitals d'in nan yanzu tsoro suke bani gara muje can wata 'kasar, Australia ma nake tunani".

"To Allah ya kaimu lokacin" na fad'a ina hamma, hira mukaci gaba dayi har ya sanyani bacci.

Da 'kyar Mama ta barni nayi sati biyu a gida ta korani bayan naje na gaida Aunty.

Tunda akayi scan aka ce babies d'ina maza ne shikenan family d'in Aliyu suka zama wasu daban, duk wanda ya fita sai ya shigo da kayan babies, har twins idan suka fita sai sun taho da kayan babies, kusan ma sunfi kowa murna za'a samu twins kamar su.

Shigowa Aliyu yayi da leda ni'ki-ni'ki, kafin ma na kalli kayan nace "yau ma kayan baby ka siyo?"

"Eh mana, idan naga kayan ne bana iya wucewa ban d'auka ba duba kigani rigunan sunyi kyau ko?"

'dagamin su yayi na kalla nace "sunyi kyau, amma ya kamata ki barsu haka fa, Mum tana nata ga Raudah da twins suma, sannan gaka ina zamu kai wannan kayan? Duk inda akayi 3months yara sun fara girma sai an canza su".

Maida kayan cikin leda yayi yace "sai a bada su a siyo wasu, ki duba fa ni kad'ai ne namiji a gidanmu, yanzu da za'a samu maza har biyu ki duba farin cikin da family na zasuyi, kar kiga laifinmu".

Daga ranar ma idan ya siyo kaya saidai ya kai wajen Mum, Allah kad'ai yasan yawan kayan a wannan lokacin domin wad'anda ke wajena ma sun cika akwati.

Lokacin da na kai 8months tuni an gama d'inkin suna, kayan ma ba'a bani na gani ba wai na fiye complain ni kuma gani nake asarar kud'i akeyi.

Fita mukayi tare dashi yiwa Dad barka da zuwa yaje umra ya dawo, twins muka samu suna hanashi sakewa Mum tana gefe tana murmushi, Raudah ce ma take yi musu magana.

'ko'karin dur'kusawa na gaisheshi nake ya d'aga min hannu tare da cewa "it's okay my daughter zauna".

Gefensan Aliyu ya nufa ya d'aga amal cak ya ajiyeta a gefe sannan ya zauna dab da mahaifinsa yace "welcome Dad".

Shafa kansa yayi yace "son".

Maganar business suka fara har na gaji da zama, kafin mu tafi Dad ya bani tsarabata akwati guda, shima dai harda kayan baby, kai wannan family are obsessed with my babies.

Tashi nayi da ciwon 'mara da baya, ina sanarwa Aliyu ya kira Mum, kafin wani lokaci sai ga mum, twins, Raudah, jannat harda Dad sunzo, gaba d'aya muka tattara muka tafi asbiti tun  ma ban fara wani labour sosai ba.

Asbitin da nake zuwa anti-natal muka nufa, asbiti me mai matu'kar kyau da tsada, ko da aka dubani akaga da saura amma hakanan suka ri'keni, bayanin painless delivery suka min nace banaso.

Kamar dai ba haihuwa nazo ba haka muka 'kare da 'karamin picnic, mukaci muka sha ko nace suka ci suka sha domin ni abincin ma na kasa ci ciwo yana cina kad'an kad'an

Gajiya nayi muka koma gida, gidan Mum muka nufa inata safa da marwa suna baccinsu, Mum da Aliyu ne idonsu biyu har cikin dare lokacin da labour ya taso sosai.

Muna zuwa muka shiga tare da Aliyu aka bashi kujera a gefena, shafa kaina yakeyi yana min sannu, kamo hannunsa nayi na dam'ke tareda sakin 'kara a hankali, gumi ke ketomin dukda sanyin Ac d'in dake d'akin.

Aliyu kam dashi muke labour d'in indai nayi 'kara sai yayi, ji nake kamar na nausheshi saboda takaici.

Gogemin gumin fuskata yayi da handkerchief yace "well done baby, keep pushing saura kad'an".

Hannu nakai na makeshi ya dafe hannun yace "owww!! Ya da duka kuma".

Ban kulashi ba naci gaba da fama na, bansan adadin da na d'auka ina labour ba na haihu, na farko kenan, gaba d'aya na gama gajiya ji nake tamkar 'kasusuwan jikina sun dena amfani.

Aliyu ne ya tashi ya le'ka ya gano, wani farin ciki ne ya bayyana a fuskarsa ya dawo ya zauna, kissing d'ina yayi yace "we did it baby saura d'aya".

"I did it, na gaji ya Aalee bayan iya ba".

Ina gama fad'in haka sabon labour ya tasomin, cikin 18mins na haihu ya Aalee harda tsalle saboda murna, murmushi nayi ina kallon 'ya'yana idona cike da 'kwalla, na rasa da kalmomin da zan godewa mahaliccina.

Lokacin da aka mi'komin su kasa danne hawayena nayi na fara kuka sosai, Mum ce tayi hugging d'ina ta gefe tana rarrashina.

Sam na kasa samun hutu saboda ina haihuwa aka fara dandazon zuwa, yawanci friends d'in mum ne da Raudah, harda abokanan Aliyu.

Dauriya kawai nakeyi ina murmushi amma ji nake kaina yana juyawa, hayaniya ke tashi a d'akin sosai, maida kaina baya nayi jin yana rinjayata na fara ganin mutane biyu-biyu, bud'e bakina nayi da niyyar na kira sunan Mum sai ganin wasu taurari nayi suna yawo a idona Kafin na fad'a duh I
************
*SALEH*

Shiga gida Maimu tayi fuskarta kamar a d'aure, Hadiyya na zaune tana jiran Hajiya ta gama abincin dare ta d'auka ta tafi.

Sallama tayi Hajiya ta fito da sauri tace "kin samu kud'in? Kinje wajen malamin ne ko yanzu zaki tafi?"

Zama tayi tace "Hajiya ya sakeni fa!!" Ta 'kare maganar tana cillar da takardar gefe, d'aukan takardar Hadiyya tayi ta karanta da 'karfi

*Ni sa'idu Adamu, na saki matata Maimuna saki biyu sakamakon rashin kwanciyar hankali da nake samu daga gareta*

Nad'e takardar tayi tace "uhm, Allah ya kyauta".

Zama Hajiya tayi cikin tashin hankali ta d'auki takardar hannunta har rawa yakeyi tace "me ya faru kuma maimuna?"

Maimuna bata bo'ye komai ba ta sanarwa Hajiya abinda ya faru, shiru Hajiya tayi sannan tace "ni bansan abinda zance ba wannan 'kaddara ce".

"Hajiya abincin baiyi bane yunwa nakeji fa" Hadiyya ta fad'a tana turo baki.

Galla mata harara Maimuna tayi tace "abincin uban me? Ke ta abinci ma kikeyi a wannan tashin hankalin ko?"

Tsaki Hadiyya taja tace "to tame zanyi? Tashin hankali kaina ya hau? Ni ta cikina nakeyi aure dai kin kasheshi me kuma ya rage?"

Kallonta Hajiya tayi tace "wace irin magana kikeyi haka Hadiyya?"

"Maganar gaskiya nakeyi, ai suk wanda yace d'an wani bazai huta ba shima Allah sai ya Hana nashi hutawa, duk wanda yace auren wani bazai zauna ba sai Allah ya hana nashi zama haka kuma aure rai ne dashi, ki godewa Allah ma da ba mutuwa kikayi yayi auren ba".

"Kutumar ubancan, ke yarinyarnan ni kike fad'awa haka?" Maimuna ta fad'a a fusace

Tashi tsaye Hadiyya tayi ta nuna Maimuna tace "an fad'a miki maganar kuma karki sake kirana yarinya domin ina shirin aje yarinya kwanannan, gaskiya ce daga 'kinta sai 'bata auren da kuka had'u kuka kashe shi Allah ya fara hukuntaku tun yanzu, ai hukunci ma da saura sai kin zauna kin rasa mijin aure".

Tasowa Maimuna tayi tayo kan Hadiyya zata daketa, ri'keta Hajiya tayi sannan tace "Ke Hadiyya kar ki 'kara fad'an irin wannan maganar".

"Barta Hajiya, dan ubanki banda an kashe auren ke kin isa ki shigo har kici arzi'kinmu? Ki sani aurennan mu muka so ayi yanzu idan muka so ya sakeki sai ya sakeki".

Dariya Hadiyya tayi tace "da farko dai karki ta'bani ki shafamin gumin zawarci ki kashemin kasuwa a wajen mijina, sannan abu na biyu karki sake zagin ubana zan zage uwarki ne tas kuma ko a jikina, abu na 'karshe aure baki isa ki saka ayi ko a fasa ba, itama wadda kuka kora d'in wa'adinta ne ya cika, nikuwa nan na samu wajen zama, a tunaninki boka da malam su suke zaunar da aure? Ashe girman naki duk na asara ne wawiya ce ke? Da kissa ake siye miji, idan 'yan neman tayin zawarci kike nema sai ki kama ta gefenki gatanan, aure kuma da kike cewa Zaki kashe Bismillah idan baki kashe ba kafira ce ke".

Sakin maimuna Hajiya tayi tace "Hadiyya, zagina kikeyi?"

"A'a Hajjaju na isa na zageki? Uwar miji ai uwace idan akwai so da 'kauna, 'yarki ce dai ya kamata ki sake mata sabuwar tarbiyya inaga ta baya ta zube, sannan ta kiyayi kanta ta dena sako aurena a harkarta domin nafi 'karfinta wallahi, idan Kinga aurena ya mutu to Ni na mutu ko shi".

"Ke Hadiyya Ashe bakida mutunci bakida kunya? Ni kike kallo kike fad'awa wannan maganar?"

"Ai d'a me kuka shi ke janyowa uwarsa zagi, da Maimuna bata ta'bani ba da Babu yanda za'ayi abun ya shafeki, sannan da ace bansan wace irin uwar miji bace ke da bazan fad'i haka ba, sannan da bata ta'bo mijina da aurena ba bazan kulata ba domin babu abinda yakai mijina yanzu a wajena kuma ko ke uwarsa baki isa ki rabani dashi ba wallahi".

Cikin zubewar girma Hajiya ta kalli Hadiyya tace "abinda zai fito daga bakinki kenan? Bayan na taimaka muku na baki auren d'ana saboda na rage muku wahalar da kuke ciki shine zakizo kina fad'an haka? Zamu gani salen zaizo ya sameni, idan kikayi wasa Zaki rasa aurenki ki koma cikin talaucinki na baya".

Dariya Hadiyya tayi tace "talauci ai ya 'kare Hajiya tunda kika nunamin hanyar arzi'ki, yanzu kam mijina ya yanke mana wahala dukda ba a talauci nake ba munada wadatarmu daidai misali sannan aure ai ya gama mutuwa akan 'yarki, kuje kuji da abinda yake damunku ni nan zama daram, shi kanshi d'an naki yanzu zaisan ya auri mace sannan yanzu zan fara mulki a gidannan, idan kina ganin kina juya d'anki to daga yau wannan ya 'kare zaki san wa kika aurawa d'anki, ki zuba Ido ki gani zan gyara miki zama ke da wannan shekararriyar bazawarar domin Idan wannan halin zaki ci gaba ke da aure saidai kiga anayi".

Fita tayi ta barsu cirko cirko, tana fita ta ciro wayarta daga zaninta ta kira Saleh, fashewa tayi da kuka tace "honey ka dawo gida ba lafiya ina cikin matsala, honey na shiga uku mutuwa zanyi shikenan zasu kasheni".

"Meya faru?" Ya fad'a cike da damuwa, kukan 'karya takeyi tace,

"Honey Hajiya ce da Maimuna suke neman kashemin aure, Maimuna ce aurenta ya mutu sai naji suna maganar abinda suka yisa Bilkisu tsohuwar matarka suk turo mata aljanu saboda ta bar gidanka shine nace sai na fad'a maka sai Hajiya tace wallahi yanda ta kori Bilkisu cikin ruwan sanyi haka zata koreni nima sai ta saka ka sakeni ka wula'kantani ni da cikina, honey kayimin rai ko dan cikina ka taimakeni karka sakeni, nasan Hajiya zata fad'a maka abu daban kuma nasan zaka amince da ita saboda mahaifiyarka ce, amma ka sani nima uwa ce a gareni banida riba idan nayi mata wani abun, dan Allah karka sakeni Honey kaji?"

Shiru yayi sannan yace "shikenan ina zuwa gidan yanzu kashe zan d'aga waya".

Cikin 'kan'kanin lokaci sai gashi ya dawo, zuwa yayi ya d'aukota tana zuwa ta dur'kusa kamar mutuniyar arzi'ki, kallonta Hajiya tayi tace "a yanzu zan nemi ka tsawatarwa matarka ne, ace yarinyarnan ta kalli tsabar idona ta zageni? Yarinyar da na haifa ta kalleni ta zageni saboda ka d'aure mata gindi ko? To ka ja mata kunne wallahi ta sake zan d'auki tsattsauran mataki a kanta".

"Hajiya kiyi ha'kuri amma ni Banga abinda Hadiyya tayi ba, Hajiya kiyi ha'kuri ki dinga yi mata uzuri".

Mamaki Hajiya tayi tace "wani sharri da 'karyar ta fad'a maka? Nan tazo tana nunani da yatsa tana cewa ban isaba, ta kalli Maimuna a gabana ta zageta ta fad'amin ban isaba a matsayina na uwarka sannan kace na mata uzuri? Saboda bance ka saketa ba ko? Ka sani ni na aura maka Hadiyya Kuma a yanzu zan iya cewa ka saketa kuma dole ka saketa".

Girgiza kai yayi yace "Hajiya saki masifa ne a al'umma, banaso na Saba da saki sannan Hajiya kiyi ha'kuri da abinda zan fad'a, na auri Bilkisu za'bina kince Bata miki ba na miki biyayya na rabu da ita, kin bani Hadiyya na kar'ba saboda biyayya, dukda Hadiyya ba za'bina bace bazan saketa saboda umarninki ba, idan har Hadiyya tana miki ba dai-dai bane zan nema mata gida na rabaki da ita inaga hakan zaifi".

Cikin fusata Hajiya tace "au laifina ma kake gani ko Saleh? Wato duk abinda ya faru laifina ne, ita Bilkisun da tana haihuwa zan rabaka da ita ne? Sannan babu inda zakaje da Hadiyya anan zata zauna".

Shiru yayi Hadiyya kuwa tunda ta zauna ta sunkuyar da kai ko d'agowa batayi ba, Hajiya ce ta gama banbanminta suka tashi suka fita, suna fita Hadiyya ta 'kan'kame Saleh tace "honey tsoro nakeji, yanzu haka zanci gaba da zama da Hajiya? Honey zata saka ka sakeni ko kusa ko nesa, nawa nake da zan zama bazawara? Honey na ta'ba 'bata maka? Na ta'ba maka abinda zai saka kaji kana son sakina meyasa  Hajiya bata sonka? A tunanina tunda tace na aureka zata soni amma a kunnena naji tana cewa ta tsani taga wata mace tana cin dukiyarka, Honey ma taimakamin ka samamin mafita kar sumin abinda suka yiwa Bilkisu banaso na haukace".

Kuka take wiwi tana ri'ke da Saleh dafata yayi Yana tausaya mata, ga yarinta ga ciki sannan ga matsalar family d'insa, tabbas dole ya nema masu mafita kafin su sanya mata ciwo domin ya amince da duk abinda ta fad'a masa tunda yasan abinda suka aikata ko me aka fad'a amincewa zaiyi.

Rarrashinta yakeyi da kalamai masu dad'i, dukda har yanzu bai fara sonta ba amma tunda tana d'auke da cikinsa dole ya bita a hankali, sannan Idan ya biyema mahaifiyarsa yasan cewa bazai ta'ba zaman aure ba.

Washegari bayan sunyi breakfast da kansa ya samu sultana ya ro'keta ta bawa Hadiyya abinci saboda bata iya girki sannan sun samu matsala da hajiya, tsabar son gulma yasa Sultana yin girki da wuri ta kaiwa Hadiyya, bayan ta zauna ta tambayeta abinda ya faru aikwa Hadiyya bata bo'ye komai ba ta sanar mata, dad'i ne ya kama Sultana tace "inama Bilkisu na nan wannan abu ya faru?"
53

Salati nakeji a kaina ba tare da naga komai ba, idanuna a bud'e suke amma bana ganin komai sai duhu, da 'karfi na furta "Mum!!"

"Bilkisu ganinan".

"Mum bana gani!!"

"La'iaha illallahu..."

"Muhammadur-rasulullahi!!" Na 'karasa domin ni duk a tunanina mutuwa zanyi ake la'kaba min shahada, har yanzu bana ganin komai a idona sai wani shuuuuuuu da nakeji a cikin kaina, ga salati dake tashi a d'akin sannan ga kukan babies d'ina, hankalina 'kara tashi yake wanda hakan ke 'karamin ciwon kan da nakeji, a hankali na fara ganin mutane a dusashe yayin da naji maganar likita tana fad'in a barni ni kad'ai.

Allura aka yimin wadda ta d'an fara dawo dani hayyacina, bayan na d'an warware naga d'akin yanzu daga ni sai Aliyu da Mum.

"Doctor post eclamsia ne ko?"

"I think so amma bari mu gani".

Bp d'ina ya duba naga Mum ta zare Ido tace "Oh God".

"160/90, post eclamsia ne zamu bata magani kafin kuma ayi urine test, for now ta samu hutu sosai saboda zata iya sake samun seizure".

Ni gaba d'aya hankalina ba a kan post eclamsia d'in yake ba yana kan babies d'ina dake ta canyara kuka, dannewa kawai nayi amma ji nake kamar nayi tsalle daga gadon na d'aukosu.

Aliyu ne ya lura da hakan bayan mun da doctor sun fita ya d'aukomin d'aya ya mi'komin sannan ya ri'ke d'ayan Yana jijjigashi a hankali, nayi mamaki da ya iya ri'ke yaro domin yawancin maza basa iyawa.

Jingina nayi saboda yanda kaina yayimin nauyi ji nake kamar zai fashe, matso da babyna nayi 'kirjina na fara bashi nono, bai wani jima ba ya fara kuka na cireshi na ajiye a gefe saboda kukansa 'karamin ciwon kai.

Dafe kaina nayi na cije baki ji nake kamar na fasa ihu, ga ciwon kai ga kukan yara ga babu nono Ina zan saka kaina?

Dawowa Mum tayita d'auki babyn dake kuka a gefena sannan tace "feed them mana Bilkisu".

Muryata a hankali saboda banason magana nace "babu ruwan nono Mum".

"Okay bari a samo musu madara kema ya kamata kici abinci sai kisha magani".

"Mum ya naga fuskarta ta 'kafarta sun kumbura?" Aliyu ya fad'a cikin damuwa, idanuna a rufe suke kuma banida niyyar bud'ewa Mum tace,

"Eh duk alamu ne na post eclamsia, yanzu jeka ka samowa yarannan Madara, SMA zaka kar'bo musu idan ka fita daga nan akwai wani pharmacy zaka samu a ciki".

Yana fita Mum ta had'amin tea, wato murna da farin ciki yasa suka manta ma ya kamata naci abinci, ni kaina farin ciki yasa na manta da yunwar da nakeji, rabona da abinci yanzu nayi 24 hours.

Alamun zamanta naji a gefena ta tallafo kaina ta d'aura a 'kirjinta, a baki ta dinga bani tea d'in saida na shanye duka sannan ta 'karamin pillow na jingina, magani ta bani nasha na dafe kaina nace

"Wai Mum yarannan bazasu dena kuka bane?"

"Ta yaya zasu dena kuka suna jin yunwa? Da zaran sunsha madara zasuyi bacci".

"Nima inajin yunwar amma banyi kuka ba".

Dariya Mum tayi tace "ko kinyi ba mai ganin laifinki".

A hankali na fara 'ko'karin sauka daga gadon, kamoni Mum tayi tace "ina zakije kuma?"

"Fitsari nakeji".

"To muje taka a hankali". A hankali na taka Mum na ri'ke dani, da alamu maganinnan yana da kyau domin har na fara jin dad'in jikina.

Stiches d'innan ba dai azaba ba fitsarin ma saida dabara, bayan na gama da wayyo wayyo na fito na tako da kaina na koma gado, Mum na samu da Aliyu kowannensu na bawa baby d'aya Madara gwanin sha'awa murmushi nayi na kwanta ina kallonsu, ko ina jama'ar da suka zo suke? Su Raudah ma babu su amma naji dad'in hakan.

Doctor ne ya shigo yayimin allura sannan yace sai washe-gari
za'ayi discharging d'ina.

Babu wanda ke yimin magana a cikinsu zuwa yanzu kaina yayi sau'ki, twins ne suka fad'o d'akin babu sallama Mum ta daka musu tsawa tace "bakwa ganin batada lafiya zaku shigo kuna hayaniya?"

Tsayawa sukayi suna kallon Mum da baby a hannunta, wani iri naji a raina domin tunda nake ban ta'ba jin Mum ta

35 / 41