Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
ni takeyi yawancinsu suna sa min albarka yayin da wasu saidai kawai su kalleni su gyad'a kai, ko kud'i ne ya musu.yawa har ya danne walwalarsu oho.
Abu d'aya na lura dashi wanda ya sake bani tsoro da auren Aliyu, ba 'karamin arzi'ki Allah yayi musu ba nayi zaton motocin da yake saidawa irin ka siyo ka sayar d'innan ne amma inaa, kamfani guda ne dashi motoci harda na had'a titi yake saidawa.
Mahaifinsa ya bar masa business d'in motar a hannunsa tun bayan ya kammala karatunsa, kuma Allah ya sanya masa albarka har wata plaza ya bud'e a can Abuja, duk shagunan dake ciki an kama kuma yanda nakejin labarin suna kar'bar hayar kusan 200k ko fiye da haka a duk shekara, duk wannan labari a yau na sameshi saboda 'kawayen Aunty Aisha basuda abun yi sai bragging akan arzi'kinsu, itama kuma ba'a barta a baya ba.
Tsabar gulma duk matan suka zauna har bayan la'asar lokacin da za'a kaini, gida kam da na ganshi saida na hadiyi miyau domin kyawun gidan da girmansa ya isa ta waje, wani irin gate ne daga waje gaba d'aya baifi tsayin mutum ba, daga nan zaa wuce makeken compound sannan a shiga main house, gabana fad'uwa yakeyi saboda bansan kayan d'akin da aka min ba, Allah yasa ba tsofaffina aka kawo ba domin zanji kunya gaban 'kawayen Aunty Aisha, maybe ma su fara gorantamin ko su fara mata habaici, ugh kad'an daga illar auren me kud'i dukda nima alhamdulillahi ba talaka bace amma maganar gaskiya kaf abinda na mallaka baifi kud'in mota d'aya a kamfanin Aliyu ba.
Ko da muka shiga palour kasa barin lullubin kaina nayi, palour d'in sai ka taka stairs zakayi 'kasa sannan ga kujeruna a wurin, roynd ne shape d'in palour d'in haka kujerun nawa ma round ne sunyi matu'kar kyau, ga wata tafkekiyar tv ta cika bango, d'aga kaina nayi naga wata chandelier wadda tayi yanayi da ta frozen, da sauri na sauke kaina jin Raudah ta makeni a kaina, ban gama kallo ba aka shiga dani d'aki, saida na d'auke numfashina ganin had'uwar d'akin, ni Bilkisu anya zan iya zama a wannan gado? Bedsheet ne fari 'kal a kan gadon sai wasu red flowers a jiki basufi 6 ba, a hankali na zauna naji katifar ta wani lotsa, hmm yau akwai bacci me dad'i.
An gama ganin gida kowa sai zazzare ido yake domin gidan Aliyu ya matu'kar had'uwa, gaba d'aya tsarin gidan na 'kasashen waje ne ga girma ga kyau.
Bayan 'kafa ta d'auke daga Ni sai sisters d'in Aliyu na cire mayafina, hannuna Raudah taja tace "zo kiga"
Wani labule ta bud'e sai ga glass babba ya bayyana, sakin baki nayi ganin wani had'add'en garden ga kujeru irin na gini da akeyi sannan ga flowers masu matu'kar kyau wajen an shimfideshi da grass carpet.
Gefena Raudah ta tsaya tace "anfi shekara goma ana ginin gidannan tun farkon dawowar Ya Aalee daga karatu, shi ya fara bayyana yanda yakeso gidan ya kasance sannan idan har yayi tafiya yaga wani abu da ya birgeshi sai yazo yace ayishi, ai bakiga komai ba ma a gidan da kanshi gobe zai nuna miki sauran wuraren, sai ma Kinga kitchen d'inki wallahi kamar a can, daga kitchen kana hango palour......"
Kafin ta 'karasa mukaji maganar Aliyu yace "au ke aka bari ki mata hudubar? Oya oya a ficemin daga gida yanzu tunda nayi mata banason sake ganin kowaccenku a wannan d'akin".
Shigowa twins sukayi da saurinsu sukace "Aunty B toulet d'inki fa...."
Katsesu Aliyu yayi tareda kama hannunsu ya fita dasu yana cewa "oya oya a tafi gida sai watarana saura naga 'kafar wata a gidannan gobe".
Babu sallama haka ya korasu, Allah yasa gidan babu nisa zuwa gidansu da 'kafa suka tafi ina hamgosu ta glass d'in dake d'akin.
Bayan ya fitar dasu ya dawo, mayafina na yafa na zauna sai yanzu gabana ya fara fad'uwa, yana sallama ya dafe kai yace "shit!!" Na bar abincinmu a office wallahi".
Bance masa komai ba yace "na aika a siyo mana 'yar kazarnan ta zamani da ake kaiwa kowacce amarya to aiki yayimin yawa gashi ina d'okin ganinki na manta, sorry bari naje na sake siyowa, amma da nisa wurin ko na kaiki gida idan na dawo sai na d'aukeki?"
Girgiza kai nayi nace "ba sai ka siyo ba naci abinci kafin na taho".
Ri'ke 'kugu yayi kamar wata mace yace "tabd'i, so kike ace aurena dake baiyi ba sai an sake? Gaskiya bazamu wayi gari ba a gidannan sai kinci kaza".
Lissafi nayi naga nidai bazan iya zama a wannan gidan aljanun ni kad'ai ba, sannan banaso na koma gidan Aunty Aisha sannan na dawo, sake girgiza masa kai nayi nace "wallahi ka barshi banaso na yafe".
Zama yayi gefena tareda dafa kafad'ata yace "da gaske? Dama ana yafe kazar amarci ai na d'auka har biyan bashi akeyi".
Sunkuyar da kaina nayi nace "sai ka biya bashin ai".
"Shikenan amma dukda haka bari na duba mana kitchen ko akwai d'an abin motsa baki".
Bai jima ba ya dawo da champagne da fruit, ajiyewa yayi yace na sauka muci ba musu na sauka, muna Shan fruit d'in yakemin bayanin yanda aka Gina gidan da hanyoyin da yake samun ideas d'insa, yayi yawo 'kasashe da dama har yake cewa nima zai tafi dani wasu 'kasashen idan zaije.
Bayan mun gama cin abinci ya fita, hakan ya bani damar sauya kayana zuwa na bacci, doguwar riga na saka wadda zan kwanta comfortable sannan na haye gado, wata ajiyar zuciya na ajiye jin yanda katifar da bedsheet d'in keda wani laushi na daban, lumshe idona nayi take naji bacci yana neman d'iba na.
"Ba dai kinyi bacci ba" naji maganar Aliyu, bud'e Ido nayi nace "banyi ba". Ya sauya kayansa shima zuwa kayan bacci riga da wando.
Kwanciya yayi ya jani jikinsa ya kwantar da kaina a 'kirjinsa, ban janye ba dukda zuciyata ta fara bugawa da sauri, bayan ya kwanta comfortably yace min "idan zaki had'a aurenki na baya da wannan a ranar da aka kaiki wanne yafi miki?"
Shiru na d'anyi sannan nace "to bansan meyasa kakeson yawan ambato aurena na baya ba amma babu had'i, wannan an kawoni gida na alfarma wanda har na fara tsoron ranar da za'a min gori wancan kuma an kaini family house, mintina na na farko na fara sanin matsayina a gidan gaskiya idan za'bi zanyi zan za'bi wannan dukda Ina jin tsoro".
Tallafo ha'bata yayi muka had'a Ido yace "me yake baki tsoro?"
Tashi nayi daga jikinsa na kishingid'a a gefe, har ga Allah har yanzu ban fara jin Aliyu a matsayin miji ba, nace
"Naga irin mutanen da family d'inka suke mu'amala dasu, mutane ne masu bala'in arzi'ki da wula'kanta mutane, a dinner da akayi I feel so out of place, kayan da na sanya mahaifiyarka ce tayimin su, abokananka sun bani tsoro sannan kud'in da aka zubar a wajen ya bani tsoro, duk ranar da abokananka, 'kawayen Mum, ko ma : kawayen su Raudah sukaga daga inda na fito sai na fuskanci matsalar gori dukda babu talauci a tattare damu muma, sannan irin 'yammatan dake wajen nayi mamakin da baka auri d'aya daga cikinsu ba, ka tabbata kana son aurena bayan duk wad'annan had'add'un matan da kake gani? Sune irinka ni daban ce".
Maimakon ya amsa min sai ganin fuskarsa nayi dab da tawa, kallon lips d'ina yayi sannan ya kalli idona, kasa motsawa nayi take hannuwana suka fara gumi, murmushi yayi kafin ya d'ora lallausan lips d'insa a kan nawa, hannayensa shafar bayana sukeyi a hankali yake isarmin da sa'konni, hannunsa cigaba yayi da shafar bayana a hankali tamkar massage.
Bayan 'yan da'ki'ku ya janye tareda had'e goshinsa da nawa, d'ago fuskata yayi yace "na za'beki saboda dukkansu irina ne ke kuwa daban kike, kowa yanason canji a rayuwarsa ko? Kema ya kamata ki d'auki aurena a matsayin gwada wata rayuwa ta daban".
"Okay" na fad'a tareda sauke numfashi, hannunsa ya sanya ya shafi lips d'ina yace "u smell amazing".
Murmushi nayi zuciyata tana dukan uku-uku, "can I try again" ya tambaya tareda turo baki kamar 'karamin yaro, wow he look so cute, murmushi nayi na gyad'a masa kai alamun eh, had'e gira yayi yace "this time kiss me back otherwise you will break my heart".
Cije le'bena nayi cikin rashin sani, kafin na ankara yayi straddling d'ina yayin da lips d'inmu ke bada wani sauti na daban, hannayensa take suka fara isar da sa'konni daban daban, da alamu dai Aalee so yake ya goge Aliyu daga 'kwa'kwalwata a wannan lokaci kuwa tabbas yayi nasara.......
*********
*SALEH*
Yana kai jollof din shinkafar bakinsa 'karnin kifi ya daki hancinsa, cikin sauri ya maida abincin cikin plate tareda ture abincin gefe, ita kuwa Hadiyya sai cin abincinta takeyi, ganin ya tashi daga dining d'in ya sanyata d'ago kanta daga farantin tace
"Ban gane ba, wai yau ma bazaka ci abincina ba?"
" 'karnin kifi ke tashi a ciki".
Dukan dining table d'in tayi a fusace tace "wannan wani irin wula'kanci ne? Kwanana goma kenan a gidannan amma kullum nayi girki sai kace baiyi ba, nayi miya kace tayi d'anya, na maka farfesu kace 'karni, nayi tuwo kace d'anye, sannan har yanzu baka bani ha'kkina na aure ba wallahi na gaji wajen Hajiyarka zan kai 'kararka".
Kafin ya bud'e baki ta fice da gudu, zama yayi ya dafe kansa dake masa ciwo sosai ga yunwa, da safe chips tayi masa da kwai, 'kwan bai soyu ba ga 'karni, sannan chips d'in ya kusan 'konewa har wani d'aci yake masa a baki, haka ya fita ya wuni yana aiki sai wajen azahar yaci gurasa, sannan yanzu ga wannan pre d'anyar shinkafar da uban 'karnin kifi a ciki.
Hadiyya shiga d'akin Hajiya tayi tana kuka wiwi, a tsorace Hajiya ta fito daga bedroom tace "Hadiyya me ya faru kike kuka haka?"
Zama Hajiya tayi Hadiyya ta zauna a gefenta tareda d'aura kanta a cinyar Hajiya, Cikin kuka tace "Hajiya na gaji da halin Saleh, ba abinda yakeyi sai wula'kantani, duk abinda nayi yace baiyi ba, baya cin abincina".
Cikin rarrashi Hajiya tace "kiyi ha'kuri bari na kirashi".
Tashi tayi ta zauna ta chone baki tace "kuma Hajiya har yanzu bai bani ha'kkina ba".
Hajiya Bata fahimta ba tace "Zan masa magana ai bazai yiwu ya zauna dake yana 'kin cin abincinki ba".
"Nifa Hajiya ba wannan ne yafi damuna ba, ki ta'bani fa bai ta'ba yi ba balle ya sanni a mace, nidai ayi masa magana wallahi ai wannan cin zarafin ne ko?"
Tsit Hajiya tayi ta zubawa Hadiyya ido, wace irin suruka ce zatazo da irin wannan magana kwana goma kacal da aure?
Ko a jikinta Hadiyya taci gaba tace "dukda kwana uku da suka wuce ina fashin sallah har ma yanzu, amma ai ya kamata ace ma tun ranar da aka kawoni ya kwanta dani ya sanni a mace amma dan Allah mutum yayita kallon miji kamar hoto? Yanzu idan na nemeshi Sai ace nayi rashin kunya".
46
Zubawa Hadiyya ido Hajiya tayi domin bata ta'ba tunanin jin haka daga bakin Hadiyya ba, ba ma matsayinta na suruka ba ko dan yarintarta.
Hajiya dai tsit tayi kafin ta d'au waya ta kira Saleh sai gashi ya shigo da sallamarsa, zama yayi a 'kasa ya gaida Hajiya kafin tayi magana ya mi'ka mata plate cile da jollof d'in Hadiyya yace "Hajiya nasan akan na'ki cin abinci ne ta kawo 'karata, ki ci abincin kiji ya yake".
Spoon d'in da ya sako a plate d'in ta d'auka tana kai bakinta ta yamitse fuska a haka dai ta tura abinci, 'kayar kifi ce ta fara mata sallama a bakinta, da 'kyar ta tauna abincin ta had'iye sannan tace "to ai ba wula'kanta abincin ya kamata kayi ba gyara zaka mata".
"Hajiya na gyara mata tun ba yanzu ba amma babu wani canji".
Kafin Hajiya tayi magana Hadiyya tace "kai nifa Hajiya rabu dashi idan bazaici abincina ba yayita zama da yunwa damuwarsa ce, akwai restaurant kala kala a titi idan yunwar ta isheshi yaje can ya ci abinsa ko a jikina, ni matsalata shine rashin bani ha'kkina".
Cikin mamaki ya kalli Hadiyya sannan ya kalli Hajiya, gaba d'aya Hajiya ta ma rasa ta inda zata fara, ganin sunyi shiru yasa Hadiyya dafe 'kirji tace "na shiga uku, kardai ba lafiyayye bane kika had'ani dashi, aikwa bazan iya zama ba wallahi, tabd'i jan".
Jikin Hajiya yayi sanyi shi kuwa ko a jikinsa, maganinta kenan da ta'ki Bilkisu yarinya mai kunya, har take mata sharrin tana yawo tsirara a cikin gidanta, yau gashinan ta samu sirika me kawo mata manyan maganganu.
Da 'kyar ta daure tace "Saleh ya kamata kaji tsoron Allah kayi adalci a kan kanka da iyalinka, idan ka tauye matarka Allah bazai barka ba kuma ha'kkinta zai iya kaika wuta".
"U'hum ko kefa, kaji magana daga wad'anda suka san Allah, to kaji dai kuma wallahi kaci gaba da tauyeni addu'a zan maka balbalin bala'i ya sauka akan 'kannenka suma...." Shiru yayi sannan ta canza maganar tace "Shikenan dai Hajiya ni Zan koma, na tafi da abincin ne ko na bar miki ki 'karashe?".
"A'a jeki dashi".
Bayan ta fita Saleh ya tashi shima, kiransa Hajiya tayi tace ya zauna ta tashi, dawowa tayi da tray da shinkafa akai da miyar kifi sai 'kamshi take ga lettuce ga kuma lemon za'ki me sanyi.
Ajiye masa tayi tace "kaci kafin ka fita, zan sa jumana ta koya mata girki Amma maganar ha'kkinta kaji tsoron Allah ka dena tauye mata, idan matarka kake tunanin zata dawo to tayi aure kuma har abada bazata dawo maka ba". Tana gama fad'in haka ta bar wurin.
Zama yayi ya dinga cin shikafarnan kamar yau ya fara ganinta, saida yaci plate guda da rabi sannan ya kora kunun za'ki ya yiwa Hajiya godiya ya fita, rabonsa da cin abinci mai dad'in na yau kwana takwas kenan, tunda Hajiya ta dena kai musu abinci, gashi ya sayi kayan abinci ya jibge babu abinda babu amma sarrafawa ya zama aiki.
Hadiyya na komawa gidanta ta kira mahaifiyarta "hello ammy"
"Na'am 'yar leleta kina lafiya? Yanzu nake shirin kiranki kuwa yayyenki zasu zo gobe".
"Dan Allah da gaske? Aikuwa nima gobe zanzo".
"To Allah ya kawoki 'yar lelen ammynta, bani labari me dame kikayi?"
"Ammy dan kiji nayi farfesun nama ranar nan sannan kinga yanda nake miya da nama zu'ku-zu'ku? Inanan nayi 'bul-'bul dani ina cin nama ina shan madara".
"Kai lallai 'yar lele kina jin dad'inki, Amma dai bakya mantawa da ammynki ko?"
"Eh mana komai naci sai na tunaki, ai goben ma zan taho miki da abubuwa".
"To ki bo'ye dai kar ya gani yace daga aure kin fara yiwa uwarki guzuri banason haka".
"Kai ammy sai ya fita fa sannan zanzo".
"To shikenan, oh kina ta Shan Madara abinki ni rabona da shayi me madara tun kafin aurenki".
"Karki damu Ammy ai naga ma ba sha yake sosai ba zan d'auko a ta gara ta na kawo miki".
"To Allah yayi miki albarka".
Saleh na yin sallama ta tashi zumbur ta tafi gabansa ta tsaya tace "gobe zanje gidanmu".
"To Allah ya kaimu" ya fad'a tareda nufar d'aki ya ajiye jakarsa, babu sannu da zuwa babu ya aiki babu komai sai gobe zanje gidanmu, inama ace idan taje tayita zama a can, shine abinda ke ran Saleh.
Bata ma yi gigin bashi abincin dare ba indomie ta dafa ta soya kwai taci abarta ita kad'ai.
Washegari ma tea kawai ta had'a masa, ruwa ne zalla sai Lipton da ta jefa a ciki ko rabin cup baisha ba ya tashi ya fita, har ya fita ta bishi da gudu tana 'kwala masa kira, tsayawa yayi tace "nace maka zanje gidanmu baka bani kud'in mota ba balle kud'in tsarabar da zanyi musu".
3000 ya ciro ya bata yace ta musu tsaraba sannan ya bata 1000 kud'in mota, godiya ta masa ta koma gida da gudu.
Shiga yayi gaida Hajiya ta bashi kunun alkama yasha yaci d'umamen shinkafar jiya ya fita.
Saida ta bari ya fita sannan ta d'auko 'karamin buhu, store ta nufa ta d'auki Madara biyu a ta gararta da milo da sugar da Lipton kwali biyu, sannan ta d'auki jarkar mai 'karama.
Fridge ta bud'e tace "tunda ka kawo kai bazaka ci ba akwai masu ci" raba nama da kifin dake fridge d'in tayi gida biyu-biyu ta sakawa Ammynta rabi ta ajiye rabi, kallon kayan tayi tace "yauwa, nasan sai nafi kowa kai abin arzi'ki".
Babu kunya haka ta fita da buhunta Allah ya taimaketa babu wanda ya gani a cikin gidan, adaidaita ta d'auka har 'kofar gida.
"Salamu alaikum!" Ta fad'a cike da murna, amsa mata sukayi ta fara shiga da jarkar mai ta ajiye sannan ta koma ta d'auko buhun sauran kayan.
"Kai kai kai.....me muka samu haka? Wai wai wai...'yar lelena wannan irin gara haka? Kai harda nama? La harda kifi".kallon Hadiyya tayi tace "ba dai kwasowa kikayi duka ba saboda shirme ko?"
"Kai Ammy ya za'ayi na kwaso duka? Akwai da yawa a firiji wannan kad'an na d'ebo ai".
"Dama ga yayarki ta kawomin kayan miya fal bari azo ayi abinci me dad'i kai nagodewa Allah 'ya'ya mata jari, kai 'yar lelena zo nan na rungumeki kinji?".
Rungumar Hadiyya tayi tace "Allah yayi muku albarka yanzu bari nazo nayi miya da abinci dama akwai kabeji sai aci dashi, duk ku zauna ku huta".
"A'a Ammy tsaya kiga" kud'in da Saleh ya bata ta ciro ta mi'kawa Mahaifiyar tasu tace "wannan ya bani yace na siyo miki abu kawai naga gara na kawo Miki".
Kar'bar kud'in Ammy tayi tace "har dubu uku? Kai yau dole na taka rawa na rangada gud'a, ayyiririiii, Allah nagode maka da ka bani farar haihuwa, yo a hankali ai zan maida kud'ad'den da na ranta na aurenki".
Kitchen ta nufa tana rawa abinta su kuwa sai ya'ke baki sukeyi sun farantawa mahaifiyarsu, zama Hadiyya tayi kan tabarmar dake shimfid'e ta kalli yayarta tace "sakina ta kawo kayan miya ke kuma me kika kawo?"
"Ni ce masa nayi adda batada lafiya ai, anjima zaizo dubiya zai taho da abubuwa".
Bayan d'an lokaci Ammy ta fito da bokitin markad'e a hannunta tace "bari na mi'ka wannan ku zauna ku huta".
Cikin sauri Hadiyya tace "a'a Ammy kawo na kai".
Mi'ka mata botikin ammy tayi ta bata hamsin tace "ga kud'in markad'e".
"A'a Ammy ki barshi akwai canji a hannuna".
"To shikenan Allah yayi muku albarka".
Bayan sunci abincinsu suka fara hira, dad'in hira ya sanya Hadiyya ta fad'a musu bayacin abinci sannan har yanzu fa ita ba amarya bace, shawarwari suka bata na yanda zata ja hankalinsa.
*********
"Seriously I am okay ka bani towel d'in