NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 41

21K to 24K   out of 120.7K words

damu, shi Kuma sale zaizo ya samemu ne, shima da baisan ciwon kansa ba, Dan Allah hanzarta ki fice ganinki ma sake 'batamin rai yake
13

Zuru zuru nayi cikin tsananin kunya da takaici na tashi nayi hanyar fita, hannuna naji an ri'ke na juya naga sultana

"Ke Kuma sha-sha-sha da bakisan ciwon kanki ba, ta rabaki da saleh ta aureshi amma kina nan kina ma'kale mata, sai kace mayya,ke dai lalacewa ta tabbata a kanki wallahi, kuma kina nuna mata soyayya bakisan hakan 'kara sanya mana tsanarta yake ba "

Janye hannuna nakeso nayi amma ta 'kan'kame, cikin fad'a tace

" Wai meyasa kuke haka ne? Meyasa bazaku ja girmanku bane? Yanzu menene amfanin hakan da mukeyi please, na fad'a muku 'karya nake amma bari na fad'i dalilina na yin hakan"

Sakin hannuna tayi tace " Ina sane na had'a wannan 'karyar domin raina na min dad'i idan naga kuna mata haka "

Banyi wani mamaki ba da jin hakan, domin na dad'e ina jin rashin yarda da sultana a raina, komawa tayi ta zauna ta juya min baya tace

" Bayan nayi hakan kuma na sami nutsuwa a raina sai ya usman ke nunamin bayaso ina yin hakan, kenan Ina ri'ke da soyayyar saleh bayan ina aurensa, kenan auren nasa baida amfani, idan kuna ganin ina sonta ne ni ba haka bane, kawai ni nawa hanyar hukuncin ta banbanta da naku ne, idan kunga zaku ci gaba da zubda girmanku a haka......"

Fita nayi kaina na juyamin, ina shiga gida na fara hawaye, Kan kujera na kwanta ina kuka mai cike da takaici, duk halaccin da nayi wa sultana da abinda zata sakamin kenan?

Alamun ana bud'e gida naji ban ko motsa daga inda nake ba, ina jinsa ya shigo ya 'kwan'kwasa 'kofa alamun naje na masa welcome

Da ya tabbatar bazan fita ba da kanshi ya shigo, cikin damuwa ya ajiye ledar hannunsa yace

"Me ya faru "

Cikin shesshe'kar kuka nace

" 'yan uwanka sunyi min gorin haihuwa, dan Allah boo-boo muje asbiti a dubani domin su tabbatar lafiyata 'kalau, sun'ki bani babyn wai naje na haifa nidai muje asbiti kawai...."

Kwantar dani yayi a jikinsa yace

" Haba my boo, ke kika ce kin dena damuwa da abinda 'yan uwana zasu ce miki, yanzu ko munje asbiti za'a ce munyi garaje ne aurenmu baiyi shekara guda ba fa har yanzu, sunyi hakan ne dan kiji haushi kamata yayi ki nuna musu baki damu ba, my boo ni nake aurenki ba su ba, kuma ni ban shirya gintse amarcinmu a wannan 'kan'kanin lokacin ba, sannan haihuwa ta Allah ce, su d'in su suka haifi kansu ne? ki rabu dasu karki sake zuwa gidan sai ranar suna shima karki zauna "

Ban amsa masa ba yaci gaba da rarrashina

"My boo nifa ban sanki da mita ba, nifa kukannan naki ban gane masa ba, ba dai kukan rashin ganin baby bane? to gata nan d'ago kanki ki kalleta "

Mi'komin wayarsa yayi naga pic d'in jaririyar, mi'ka masa nayi na kwanta a 'kirjinsa ina had'iye sauran kukana, ko me sukamin ni naja tunda nakai kaina cikinsu  kaman wata tsiyar zasu min bayan nasan had'uwata dasu bata zama alkhairi, yanda saleh yace bazan sake nufarsu ba sai suna, shima bazan zauna ba zan taho

Share haihuwar nayi a kwanakin na shiga harkata, saidai jaririyar ta tsayamin a raina sosai nakeso na ganta, amma tafi 'karfina.

Ranar suna da wuri na shiga gidan na tafi da kayan barka na, diaper bag na Kai mata da set uku na kayan jarirai da atamfa d'aya.

Sai yau na d'auki babyn, sultana ta kasa had'a ido dani nikuwa na nuna mata kaman bansan me ya faru ba, cikin fara'a nace

" Ya sunanta "

"Surayya, sunan hajiya ne huda ake kiranta "

"Allah ya raya ta yayi Mata albarka"

Mi'ka mata 'yarta nayi na fice, ina tafiya ina tunanin idan Allah ya bani haihuwa sunan da zan sanya, huda ta shiga raina kafin naje gida na tsara fara addu'ar neman haihuwa

Cikin dare na tashi na fara Kai kukana ga Allah ina ro'konsa ya bani zuri'a ta gari me albarka, addu'a nake bana duban time har aka fara kiran sallar asuba

Kafin lokacin sallah yayi na fara bacci, saida saleh ya dawo daga masallaci ya tasheni sannan nayi sallah na koma bacci

Addu'a na maida d'abi'ata, fatana kawai Allah ya bani zuri'a me albarka nima dai na haifa na wuce gori.

Sati biyu da haihuwar sultana sai gata ta shigomin, fuskata ba yabo ba fallasa na sauketa na kar'bi huda, tamkar ba'kuwa nayi treating d'inta kwata kwata na'ki bata fuska, batayi 20mins ba ta tafi ganin babu fuska

Watansu biyu ta kawomin huda cikinta ya kumbura, jikin yarinyar babu kuzari gashi ta sake 'kan'kancewa.

"Sultana ya na ga jikinta babu wani 'kwari ne?ko bata Jin dad'i?"

"A'a lafiyarta lau banda dai kumburinnan da ya fara jiya ta hanani bacci, ni ba wannan ke damuna ba, dan Allah ki fad'amin madarar da za'a siya mata munaso mu fara had'a mata da Madara"

"Okay, ki bata SMA"

godiya tayimin na fad'a mata maganin kumburin cikin ta tafi, tausayin huda ne ya kamani domin nasan zata sha wuyar uwa, sultana bazata ta'ba iya rainonta yanda ya dace ba.

Addu'a nake babu ji babu gani,haka itama sultana shigowa jikina take sake yi tun ina mata kora da hali har na gaji, ko me zata yimin kanta.

*********

Shigowa tayi idonta a kumbure alamun rashin bacci,saura 'kiris ta jefar da huda a 'kasa na kar'beta cikin sauri, kwanciya tayi kan kujera tace

"Wallahi jiya ban runtsa ba saboda kukan huda,kuma lafiyarta 'kalau kukan iskanci ne kawai, dan Allah ki ri'kemin ita idan zaki iya na samu nayi bacci kaina har sarawa yake wallahi"

" Bakomai, jeki kiyi baccinki"

Mutsu mutsu huda ta fara tana kuka 'kasa 'kasa, wuyanta na kalla naga datti ya had'e da powder

Tambayarta nayi nace

"Yaushe rabon ki mata wanka?"

Shiru tayi sannan tace

"Inaga kwana uku ne ko hud'u? ba ke kika cemin ba'a son yawan wanka ba yana sanya yara mura shine kawai bana mata"

Raina naji ya 'baci nace

"Babu wani mura da ta hanaki wankan yarinyarnan, 'kyuya ce kawai wallahi da 'kazanta, huda ta kwana da Pampers kun tashi dashi inaga tun 7, yanzu ki duba 10 ta wuce amma daga tsamin dake tashi a jikinta nasan Pampers din dare ne a jikinta, yarinya sai tsami take tana 'karni  kuma kina complain tana miki kuka, ba dole tayi kuka ba kin had'a mata wahala baki mata wanka ba kuma baki goge mata jiki ba,haka akeyi?"

Bata amsamin ba ta fice ta barni da huda a hannu, takaici ya kaini bango ji nake kaman na bita na mareta, sai lokacin na kula da jakar da ta shigo da ita na bud'e.

Madara ce da kayan had'i da Pampers a ciki babu wasu kaya spare sai pant 'kwaya biyu, mamaki ne ya kamani, wasu basu san ciwon 'ya'ya ba amma Allah ba ruwansa Basu yakeyi.

Wanka nayi ma huda, jikinta har ya d'ad'e saboda yawan sanya pampers, pant na sanya mata na had'a mata madara tasha na goyata, cikin 'kan'kanin lokaci ta fara bacci ba tareda rigima ba, a wata uku har sultana ta gaza ina ga an kai shekara? banda tazo yanzu Allah kad'ai yasan lokacin da huda zata d'auka da datti a jikinta

Har azahar huda bata farka ba taji dad'in wanka da baya, tana farkawa na kira sultana a waya naji wayarta a kashe, kayan da na cirewa huda na wanke na mayar mata jikinta na fita domin kaiwa sultana ita amma bugun duniya ta'ki bud'ewa,haka na ha'kura na koma na sake bata madara ta hau min hira

Sai 3 ta fara kukan gajiya na sake kaita gidansu,naci sa'a sultana ta bud'e ta kar'beta tare da godiya.

Tun ranar hankalina baya kwanciya, a kowace rana sai nayi tunanin me sultana zata mata na kulawa, kwana uku na rasa sukuni naje na dubata

A Palo na samu huda tana ta tsanyara kuka wai sultana na wanka,gashi tabar gidan a bud'e, d'aukan huda nayi na fita da ita ina Shirin masifar da zan sirfawa sultana

30mins shiru bata kirani ba bata le'ko ba,har dai naga tayi 1 hour dole na koma dan naga abin nata yayi yawa

A rufe na samu gidan na kirata a waya, katsewa tayu ta turomin text

_please am sorry na d'an fita ne, 2 hours nayi al'kawarin dawowa key yana 'kasan wannan dutsen na gefen 'kofar, komai na fito dasu suna Kan kujera sai na dawo_

Cike da haushi naja tsaki na d'au key na shiga na d'auko mata kayanta da kayan abincinta, Allah kasan dalilin da ya sanya ka bawa sultana haihuwa amma dai kam haihuwa a wannan lokacin bata kamaceta ba

Daga nan kusan rabin rayuwar huda ta dawo hannuna, hakan yasa daga huda har sultana suka samu nutsuwa, huda har wani 'bul-'bul tayi ta 'kara kyau dake tana samun kulawa, idan na kar'bota da safe wani lokacin sau biyu kawai sultana zata bata nono tace ta gama sai kuma dare,   huda har ta dena damuwa da nono idan tasha Madara ta hau baya shikenan, har banaso naje school na dad'e Domin wujiga-wujiga zan dawo na sameta.

Watan huda shida sultana ta fara sabon laulayi, kuka tayi sosai na sai an zubar da cikin kafin kowa ya sani nace mata ba dani ba, ganin da gaske so take ta zubar yasa na sanarwa mijinta sun samu 'karuwa dole ta ha'kura ta rungumi 'kaddararta, amma saboda naji haushi ta yaye huda a watanni shidannan ta li'kamin ita dukda bata fara wani laulayi mai tsanani ba, ita ta sanarmin jumana ma nada ciki har ya fara bayyana.

Na shiga damuwa sosai na fara tunanin idan suka haihu wani irin hali zan shiga? Yanke shawarar zuwa asbiti nayi na tabbatar da lafiyata tun kafin lokacin da za'a min dole.....

_naso ace yafi haka tsayi hannuna Yana Dan ciwo ne kuyi hakuri da wannan_

15

Na dawo ina laluben key zan bud'e gida na hango jumana tana yowa wurina, d'auke kai nayi kaman ban ganta ba na fara bud'e gidan

Kiran sunana naji usman yayi na waiwaya na ganshi da huda a hannu tana kuka, tun kafin su 'karaso take mi'komin hannu ina kar'barta tayi shiru.

"Ina wuni " ya gaidani tareda mi'kawa huda hannu,kwanciya tayi a jikina ta'ki ko kallansa

"Lafiya lau, an mata wanka kuwa?"

" Anya kuwa? da kayannan na fita na barta dai gaskiya da alamu ba'a mata wanka ba,itama sultanan a kwance take tun safe jikin ya'ki dad'i "

" Sannunku da hira " jumana ta fad'a tareda Kama wuri ta tsaya, amsa mata nayi da yawwa nace

" Ya kamata ka d'auketa kuje asbiti "

"To shikenan nagode". Shafa kan huda yayi yace

"Sarkin rigima sai anjima ko?"

Tafiya yayi ya barmu na bud'e gidan nace da jumana

"Bismillah"

Tafiya take tana turo mitsitsin cikinta da ba wani bayyana yayi ba, amma ta 'karfi da yaji ake turoshi ko ni ake nunawa?

Kama 'kugu tayi ta zauna tana kallon huda dake hannuna tace

" A wajenki take wuni kenan "

" A'a, bakiga yanzu aka kawota ba? Asbiti zasu je ne shiyasa "

Dama nasan gulma ce ta kawota,

"Amma yanda take da 'kyuya naga tazo wurinki kaman kun saba sosai "

Ban amsa mata ba na ajiye huda nace

"Ina wuni, munata surutu bamu gaisa ba"

"Lafiya lau, ya karatu? Ai kwana biyu banji dad'i ba naga baki zo kin dubani ba nace to inaga baki sani ba"

"Allah sarki, ban sani ba, amma jikin yayi sau'ki ko? Koda yake masu ciki ba'a rabaku da ciwace-ciwace"

Ai kaman na kunnata ta fara zuba

"Ai kedai bari, ciki akwai dad'i akwai wahala, yau wancan ciwo gobe wancan, ai ita kam sultee tana da sa'a, nufa ciki na biyar kenan sannan ya zauna, saura kuma ku 'yan hutu"

" Um, hutu ai akwai dad'i dukda haka dai a taskar Allah muke nema, kema gashi bayan shekara da shekaru ana abu d'aya yanzu Allah ya kawo ba zama? Shi plan d'in Allah ai haka yake sai lokacin da yaga dama yake bayarwa, idan ka takura ka samu lokaci baiyi ba ma zubewa zaiyi tayi har sai wannan wa'adin ya kai"

Shiru tayi ta kasa cewa komai, friso na had'awa huda wanda na sayo a hanya, su iyayenta na fad'a su sayo amma sun fiye wasa

" Ashe kin iya raino haka? Kice idan na haihu nima na huta saidai kawai na dire making wuce, wai yaushe zaki gama karatunnan ne? "

Dariya nayi nace

"Ai ba kowane irin d'a nake raino ba, itama lalura ce tasa nake rainonta, karatu na kusa 'karashewa "

Kafin tayi magana nace

" Bari na shiga na yiwa huda wanka, zaki jira ne na fito?"

"A'a tafiya zanyi dama nazo mu gaisa ne sai anjima, sai munji labari kuma "

Rakiya na mata na rufe gidan na yiwa huda wanka na ciro kayanta a wardrobe na saka mata, wasa wasa huda ta zama rabin 'yata domin babu abinda babu nata a wurina

Kwantar da ita nayi ina lalla'bata
tayi bacci har mukayi tare, sai la'asar muka farka shima bugun gida ne ya tashemu duka

Bud'e gidan nayi naga sultana a tsaye, 'kare mata kallo nayi domin ta bani tsoro, tayi masifar rama tayi haske tayi zuru-zuru

Magana take a hankali banji ma abinda tace ba na rufe 'kofa ta shigo.

Zama tayi ta jingina da kujera tace

"Ya huda ya 'ko'kari?"

"Alhamdulillah ya jikin naki"

"Jiki alhamdulillah, shigowa nayi na miki godiya akan d'awainiyar da kike da huda, bilki duk 'yan uwana babu wadda zata yimin haka nagode Allah ya saka da Alkhairi Allah ya biyaki "

" Babu komai sultana Allah ya baki lafiya "

" A'a bilki, abubuwan da suka faru ko ni aka yima indai huda take bazan kalla ba, amma ke kinada kyakkyawar zuciya kulawar da kikeyi wa huda ni bana mata, nagode sosai, akwai maganar da nakeso muyi amma ba yanzu ba, ga wannan "

Ajiyemin leda tayi ta tashi ta fita tana taku a hankali, rakiya na mata huda na binta da kallo, murmushi tayi ta mi'ka Mata hannu tace

"Huda baza kizo mu gaisa' ba?"

No'ke wuya huda tayi tana ri'ke rigata,dariya tayi tace

" Yaro shima yasan mai yimai "

Ri'keta usman yayi suka 'karasa, Allah sarki sultana tana jin jiki sosai, da alamu dai yau huda a wurina zata kwana.

Bud'e ledar nayi naga lace masu kyau guda biyu da kayan huda, ajiyesu nayi domin saleh ya gani.

Ina girki naji sallamar Saleh, shigowa yayi kicin din tareda hugging d'ina ta baya,

" Sannu da aiki maman huda "

Wani dad'i naji a raina da bazan iya misaltashi ba, murmushi nayi nace

"Sannu da dawowa abban huda " tareda pecking d'insa a lips, dariya yayi yace

" Kin gammu zamu kwacewa mutane 'yarsu, anya muma ba hudan zamu saka ba naga sunan ya hau dake maman huda " ya fad'a tareda d'aukan huda dake wasa kan table mat da na shimfid'a na ajiyeta, hannu ta fara mi'komin ya bata key d'in motarsa ta fara wasa dashi, sunyi min kyau sosai, hangowa nayi da ace huda 'yata ce abun zaifi haka bada ma'ana.

Zama mukayi muka fara cin abincin huda sai hannu take kaiwa ina d'aukewa, gajiya nayi na barta taci wanda zata iya ta 'bata jikinta

Tare da saleh muka tafi yi mata wanka, tunda na kunna ruwan take murna, sanyata nayi na barta da saleh na fita d'auko mata towel, kafin na koma duk ya ji'ke itama ya ji'ka mata gashinta

Ri'ke 'kugu nayi nace

"Me kukayi haka "

Cikin sauri ya nuna huda yace

"Itace". Dariya sosai ya bani kaman wani 'karamin yaro, ganin ya nunata itama ta nunashi, cigaba tayi da facal-facal da ruwa na kar'beta na korashi, wanka na mata na wanke mata gashinta.

Shiryata nayi na tufke mata gashinta, gashin baida yawa sai tsayi tubarkalla, kaman ba kan yarinyar wata bakwai ba

Bawa saleh ita nayi nace

" Banaso na fito naga wani abu ba dai-dai ba, kar ka bata komai a 'koshe take, ka ri'kemin ita kawai har na fito "

Ma'kale murya yayi yace

"To mama"

Tsit na jisu ina wankan, kaman dai abin arzi'ki akeyi, dukda haka hanzartawa nayi na fito

A cinyarsa na sameta ya bud'e wayata suna kallon video, ina fitowa video ya katse ta kalleshi, komawa farko yayi naga tana ta ta'ba screen d'in

Kaya na sanya na kwanta ina karatu ina kallonsu har huda ta fara bacci a hannunsa, kwantar da ita yayi can gefe ya dawo wurina, ba tareda jira ba ya had'e bakina da nasa, tattaro rigata ya fara ta 'kasa naji kukan huda,

Cikin sauri ya matsa na kalli inda take, dafe kaina nayi nace

"Allah yasa tun yanzu tayi kukan, kaima fa ka fiye garaje "

'daga gira yayi yace

"Mun dai fiye garaje"

***********

"Jumana ta haihu"  saleh ya fad'a yana shigowa, cigaba nayi da wankina nace

"Allah ya raya, Zan shiga na mata barka "

A cike na samu gidan anata barka itama ta haifi mace, Allah dai ya taimakeni babu idon wadda  ya hau kaina har nayi barkar na fito

Kwana biyar da haihuwar Saleh ya shigomin da had'ad'd'en Kati ya mi'komin wai na sunan jumana, a wani makeken wurin biki za'ayi shi, ri'ke baki nayi ina mamakin wannan sabuwar bidi'a.

Watanni kad'an da haihuwarta itama sultana ta haihu, namiji ta haifa bayan doguwar na'kuda, saida tayi sati guda a asbiti ma tukun suka dawo gida

Ranar da suka dawo na shiga yi mata barka kuma na kai Mata huda, tsautsayi Ina shiga na tarar hajiya da haularta maganata sukeyi.

" Gata nan munafuka, shigo nan"

Zama nayi da dakakkiyar zuciyata na gaidasu, babu wadda ta amsamin Yaya maimu tace

" To kin dai gama karatunnan na masifa, gashinan haihuwar Kuma baki yiba me kike nufi ne? "

" Yaya maimu haihuwa ai ta Allah ce, ni bance sai bayan na gama karatu zan haihu ba "

" Au rashin kunya zaki min? To bari kiji idan ta'kamarki kinada goyon bayan miji ne to shi kanshi mijin naki a 'kar'kashinmu yake, wallahi kinji na rantse sai ya 'kara aure tunda ke bakida mutunci, sai kiyita zama da hutunki "

Cikin 'karfi ta fincike huda, tsala ihu huda tayi maymu ta daka mata tsawa, tsorata tayi kukanta ya 'karu, kallon sultana tayi tace

"Ke kuma yarinyarnan tafiya zanyi da ita kafin ki warware"

" A'a babu inda za'a kaita, tuntuni mukayi magana da ya usman yacemin bayaso a kaita ko ina, da can ba ni nake kula da ita ba? A barmin abata mi'komin ita ma naji d'umin kayata "

Dake hankalinta na kaina bata wani damu ba ta mi'kawa sultana huda, mi'komin hannu huda take sultana na kauda hankalinta

Maman sultana ce ta shigo itama suka zauna suka sakani gaba, Babu wadda

8 / 41