NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 41

36K to 39K   out of 120.7K words

Bilkisu sannu ya jikin naki? Yau supervisor yake tambayarki muka fad'a masa bakida lafiya kuma anyi reporting, shi yace bai saniba saboda haka gobe kije department".

Godiya na mata na kashe wayar na koma baccina, wuni nayi ina bacci marar dad'i, dukda bana mafarki ko ganin abin tsoro amma a firgice nake tashi.

Washegari jikina ya d'anyi dama dama amma dukda haka maganata bata fita sosai, muryata ta koma tamkar ta bebaye idona ma ya juye, a hakan na takurawa su Mama saida mukaje makaranta.

Kai tsaye wajen HOD muka nufa yana ganina ya fara tausayamin, Mama ce ta sake masa bayanin ciwona a take ya lalubo takardar da Saleh ya kai masa ya aikata wurin Dean, shima rubutu yayi yace babu matsala tunda dama saura wata biyu internship d'in namu ya 'kare, duk lokacin da na warke na koma kawai.

Wajen magani muka nufa daga nan aka sake min ru'kiyya, na jigata sosai amma a jikina naji alamun shaid'anun dake cutar dani babu su.

Kwana biyu tsakani sai ga aunty tazo, fad'a ta dinga yiwa Mama akan me ba'a raba auren namu an bar musu d'ansu ba? Gashinan na kusa zama mahaukaciya.

Waya ta dinga yi anan tana sanarwa 'yan uwan mahaifina banida lafiya, anan naga gata duk wanda zaizo da nashi kalan maganin, bansan danginmu akwai yawan malamai ba sai yanzu.

An shafe sati biyu ana zuwa dubani, wasu suzo sau uku wasu sau hud'u anty kuwa kullum sai tazo, kayan dubiya kuwa a d'aki nake tarasu lemu da ruwa dashi nake saukar ba'ki, har na warke sosai ba'a dena zuwa dubiya ba.

Ranar da na cika sati uku a gida muka koma Dan fodio, ru'kiyya aka sake yimin amma cikin ikon Allah babu abinda ya faru, magunguna aka bani aka tabbatar mana na samu lafiya.

Huda kuwa jefi-jefi nake ganinta, idan Saleh ya kawota ma kusan a gidan su zulaihat take wuni, da zarar tayi kwana biyu Saleh ke maidata wajen sultana wai hajiya tana tambayar ina take.

Tare da aunty mukaje gaba sukayi ita da Mama inaji mama nace Mata "Dan Allah dai kar kiyi abinda yaronnan zaiji ba dad'i kinga yayi 'ko'kari".

Bata amsawa Mama ba muka shiga d'aki, bayan mun zauna aunty tace "to alhamdulillah jikin bilkisu yayi sau'ki, yanzu komawa gidanka ya rage amma da sharad'in bazata koma ba sai mun tabbatar da lafiyar gidan naku, sannan abu na biyu ya kamata ka shiga tsakanin matarka da 'yan uwanka, ka sani cewa sune silar shigarta wannan hali dukda cewa kaima shaida ne na zaman dake tsakaninsu, Bilkisu bata fad'a mana meke faruwa ba saida wannan abun ya fara samunta, amma ka sani yanzu zamu sanya ido a kanta sosai, matu'kar irin wannan ya sake faruwa to kayi ha'kuri amma zamu d'auki matakin da ya dace ne".

Sunkuyar da kai yayi yace "hakane kuma nagode da 'ko'karin da kukayi a kanta Allah ya saka da alkhairi, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba zan saka ido akan hakan, sannan kamar yanda Mama tamin umarni kullum da 'kur'ani nake wuni a gidan, ko bana nan Zan kunna yayi tayi sannan duk wani abu da zai jawo shaid'anu na kawar".

"Hakane, amma bazamu gane lafiyar gidan ba sai munje da ita, sai zuwa gobe insha Allah zata koma sannan tare dani zamu koma zan kula da ita da zamanta a gidan, idan tayi kwana biyu babu wata matsala zamu barta anan kuci gaba da kula, amma dan Allah a kiyaye".

"Insha Allah". Ya fad'a tareda godiya, sallama yayi mana ya tafi.

Washegari kafin na koma saida aunty ta kimtsani da kyau, ashe da shirinta tazo, sai dare sannan muka tafi gida.

Jikina duk yayi sanyi raina bayason komawa gidan, idan na tuna abinda ya faru Sai naji gidan duk ya fitarmin a raina, ina tunanin yanda zan samu gidan har muka 'karasa.

A bud'e na samu gidan saida nayi adduo'i sannan na shiga, sultana na samu tana kunna turaren wuta cike da farin ciki tayi hugging d'ina.

Gaida aunty tayi sannan ta jani zuwa kujera, waiwaye nake Ina neman Huda tayi dariya tacemin "Huda ta fita da abban Ahmad wai coco pops takeso tasha sun tafi siyowa, ya jikin naki ya su Mama? Wallahi kullum sai na tambayi jikinki sannan nace ya gaisheki amma ban saniba ko baya fad'a, kinsan nazo sau d'aya lokacin da nazo kina bacci an fad'a miki ko?".

"Allah sarki Sultana, jiki yayi kyau alhamdulillah, kullum kuma sai ya fad'amin gaisuwarki ko bai fad'a ba zance sultana tana gaidani ko? Nagode da 'ko'karinki Allah ya saka da alkhairi, gida yayi kyau".

Katsemu aunty tayi tace "Bilkisu babu dai wani abu da kikeji ko?"

Girgiza kai nayi nace "aunty banajin komai"

Hira mukaci gaba dayi kusan rabin hirar akan Huda da tsiyar da takewa sultana, sai bayan 9 sannan ta tafi.

Aunty kuwa tun 8:40 tayi mana sallama ta shige guest room ta barni ni da Saleh.

Hannunsa nayi yana wasa a bayana, ture hannun nayi nace "boo-boo aunty fa".

Zuge zip din rigata yayi yace "za'a yiwa aunty sharri ko? Kima sani ko Mama ce a gidannan yau sai na biya bashina, kinsan kuwa wahalar da nasha bakyanan?"

"To boo-boo naji mu tafi sama mayi zancen acan".

Ina rufe bakina ya d'aukeni bridal style ya nufi stairs dani, a palon saman ya ajiyeni tareda fara kissing wuyana hannunsa na kan cikina yana shafawa, biye masa nayi muka fara raya dare tun yana farkonsa........
21

Da 'kyar na tashi saboda jin dad'in bacci, wanka nayi na sauka na fara had'a breakfast har na gama ko muryar Aunty banji ba.

'Dakinta na nufa na sameta tana zaune kan gado da wayarta a hannu, dariya nayi nace "aunty kema an koya miki chatting d'innan ko?"

"Kedai bari, zamaninnan ai saidai hamdala, yauwa zo ki nunamin yanda aka d'auko abu a utube wani video naji ana zance nima zan gwada".

Zama nayi a gefenta na shiga utube na mata searching, mi'ka mata wayar nayi ta kalleni tace, "kinyi kyau fa".

Murmushi nayi na sunkuyar da kaina ta sake cewa "babu dai wata matsala ko?"

"Babu komai Aunty nayi bacci sosai ma Alhamdulillah" na fad'a tareda fara'a.

Murmushin jin dad'i tayi tace "To alhamdulillah, haka nakeso naji, gobe insha Allahu idan na sake dubaki sai na tafi, yaushe zaki koma makaranta?"

"Inaga goben zan koma insha Allah, Aunty muje palour na gama breakfast".

Tashi nayi tace "a'a ki kawomin abincina nan bazan fito na takura muku ba".

Cikin sauri nace "a'a Aunty wallahi ba takura ki fito muci tare".

Wani kallo ta watsomin ta maida kanta kan wayar gabanta, fita nayi na had'a mata breakfast na kai mata sannan na had'a mana namu na ajiye.

'Dakinmu na koma na fara gyarawa Saleh na wanka, d'aga murya nayi nace "ka hanzarta kar ya huce!"

Fitowa yayi yana goge kansa da towel 'karami, ri'ke 'kugu nayi na zuba masa ido shima kuma 'karemin kallo yakeyi, murmushi nayi tareda juyawa na fara goge mirror nace "ka hanzarta ka shirya mu sauka na fara jin yunwa".

Tahowa yayi inda nake ya hugging d'ina ta baya, iska yake huramin a bayan kunnena a hankali inajin bugun zuciyarsa a gadon bayana, rocking d'ina yake kamar 'karamar yarinya faffad'an 'kirjinsa na gogar bayana.

Cizar kunnena yayi tareda sanya hannunsa yana shafa kafad'ata, dawo da le'bensa wuyana yayi yana kissing tareda furtamin wasu kalmomi masu matu'kar kashe jiki.

Muryata 'kasa 'kasa nace "boo-boo.....yunwa nakeji". Kamar ma tunzurashi nayi ya sanya hannunsa d'aya ya juyoni cikin 'kwarewa, shafa kumatuna yayi yace "kinada ni har kya zauna da yunwa?"

"Umm..." Bai bari na furta komai ba ya had'e lips d'insa da nawa, hannuwana na sanya a bare chest d'insa yayinda hannunsa ke roaming bayana, rabuwa mukayi da juna saboda numfashi  na dafa kafad'arsa nace "boo-boo munbar Aunty fa ita kad'ai, kafin tayi suspecting abu ya kamata mu sauka".

Pecking d'ina yayi a lips yace "hakane, amma kiyi gaba zan biyoki idan na shirya".

Har azahar babu wanda yazo dubani daga mama har haularta, sultana ce kawai ta kirani tamin ya jiki jumana kuwa har mantawa nake tare muke rayuwa da ita.

Ban damu da rashin zuwansu ba, washegari tareda aunty muka fita aka ajiyeni a wurin aikina ya wuce da ita gida, aikin ma basu barni nayi sosai ba sai kar'bar gaisuwa nake ta yaya jiki.

Saida nayi kwana uku a gida tukuna hajiya da jumana suka zo dubani, ina ri'ke da Huda tana cin biscuit a hannuna, zama sukayi bayan sunyi sallama na gaidasu suka amsa da 'kyar.

"Huda zo mu gaisa mana" jumana ta fad'a tareda d'aukan Huda daga cinyata, tuni idon Huda ya ciko da 'kwalla tana mi'komin hannu ni kuma nayi kamar ban ganta ba.

Kuka ta saki tana zamewa tana yun'kurin ta dawo wurina amma jumana ta ri'keta, tsaki tayi tace "wallahi Huda bakida sabo, ji wani kuka kamar ana figar naman jikinta".

Huda kuwa ganin ban kulata ba ya sanya ta 'kara sautin kukanta, cikin d'aga murya tace "MAAMA!!!" Tareda mi'komin hannu, kallonta Mama tayi ta kalleni taga da gaske dai ni ta Kira da maama, wani irin juyi naji cikina yayi yayin da mama tace da Jumana "saketa muga inda zataje".

Wani gumi naji ya karyomin domin d'abi'ar Huda ce indai ta kira sunana ban amsa ba tayita kira kenan sai na amsa, rarrafowa tayi ta dafa 'kafata ta tsaya tana rage sautin kukanta, "maama" ta fad'a tareda mi'komin hannu, d'aukanta nayi na kwantar da ita a kirjina ina shafa kanta cikin rarrashi, "maama" ta fad'a tareda ri'ke rigata tana kallon Jumana, shiru nayi ta sake fad'a ganin dai ban amsa ba yasa ta d'ago daga jikina ta ta'boni tace "maama".

"Um?" Na amsa mata da 'kyar, gwaranci ta faramin nace "to shikenan yi ha'kuri". Su hajiya kuwa sakin baki sukayi suna kallona, biscuit d'in da ta yar na d'auka ina bata a baki, kar'bar na hannuna tayi ta turamin a bakina, dariya tayi tareda d'ago kanta ta had'a bakinta da nawa, murmushi nayi idanuna na kan su hajiya, gaba d'aya jikina yayi sanyi, kallon juna sukeyi suna min kallon tuhuma ni kuma na sunkuyar da kaina.

Da alamu sun manta dubiya ce ta kawosu domin cikin hanzari sukamin sallama suka fice, basu fi minti talatin da fita ba naji bugun sultana cikin sauri na bud'e da Huda a hannuna, cike da damuwa tacemin "me ya faru ne? Su hajiya sunzo suna tambayata tsakaninki da Huda".

Palour muka shiga na fad'a mata duk abinda ya faru, dafe kanta tayi ta girgizashi cikeda damuwa,  ri'ke hannuna tayi tace "Bilkisu dan Allah komai rintsi kar kice kinyi giving up akan Huda, wallahi Huda taki ce Huda bazata ta'ba jin dad'in rayuwa ba idan babu ke, ina ganin lokaci yayi da ya kamata ace na sanarwa su hajiya tsakaninki da Huda".

Numfashi kawai nake ja ina saukewa na rasa ma me zance, kallon Huda nayi da take kamo wuyan rigata tana mi'kewa Kan cinyata, hannunta na kama nace "Huda dan Allah ki zauna kawai".

Tamkar taji abinda nace ta kwanta a jikina, kallonta nayi na shafi kanta tabbas soyayyata da Huda had'in Allah ce, wani yanayi nakeji yana tsirgawa cikin jikina a duk lokacin da na had'a jiki da Huda, zan iya rantsuwa soyayyar da nakewa Huda ta ninka wadda mahaifiyarta take mata.

Lumshe idanuna nayi nace "wallahi ko ni Sultana banaso a rabani da Huda, jin Huda nake kamar 'yar da na haifa a cikina indai bazaki goyi bayan 'yan uwanki ki kar'be Huda ba, nima bazan ta'ba bayar da ita ba".

Girgiza kai Sultana tayi tace "Bilkisu bana goyon bayan rasuin gaskiya ko Yaya yake, kuma ni bana magana biyu, inaso gobe ki tafi da Huda makaranta domin a gobe za'a yita ta 'kare".

'kan'kame Huda nayi a jikina nace "wallahi Sultana da zarar kin furta haka nakejin gabana ya fad'i".

"Addu'a zakiyi komai zaizo mana da sau'ki, abinda nakeso dake kawai ya zamana kin ri'ke Huda kuma kin tsaya tsayin daka akanta, ko mahaifiyata bata isa ta rabaki da Huda ba, Kai ko ni ban isa na rabaki da Huda ba, yanda zakiyi ya'ki akan Yar da kika haifa ki aikata hakan akan Huda".

Na rasa ma bakin yiwa sultana godiya, ranar kasa bacci nayi kwana nayi ina juyi da tunanin abinda zai faru gobe, da wuri na farka na shirya Huda muka fice saidai hankalina ya'ki kwanciya a hakan ma.

Bayan na tashi daga aiki na bud'e wayata, 28 missed calls na gani da 3 messages, 2 missed calls da message d'aya daga Sultana ne sai missed call d'aya da message biyu daga hubbyna sai kuma ragowar daga numbobi daban daban, cikina naji yayi k'ara domin nasan yau akwai 'karamin ya'kin duniya a gidannan,
Me zai faru
Shin Sultana zata ri'ke alqawari na a barmin Huda?
Zan iya cika al'kawarin Kare Huda dukda nasan zansha gori da takaici?
Wane bangare Saleh zai kasance?
Wasu irin maganganu za'a ya'bamin?

Ina irin wadannan tunanin har nakai gida, wata irin hayaniya naji tana tasowa daga 'bangaren sultana, 'kara ri'ke Huda nayi na nufi sashina saidai kafin na 'karasa naji an nufoni cikin hanzari.......

Kuyi ha'kuri da wannan kaina ya fara daukan caji, alot of tests ga exams tana gabatowa

Zanin goyon Huda na ciro na goyata, kursum ce ta 'karaso tana huci kamar zata fashe tace "kizo ana nemanki".

Banza nayi da ita ina bud'e gida, "wai baki jini bane? Cewa nayi fa ana nemanki hajiya ce take so ta miki magana".

"To ina zuwa". Na fad'a tareda bud'e gidan na ajiye jakata da mayafina sannan na gyara goyon Huda, ina 'kokarin fita Saleh ya shigo, murmushin ya'ke nayi tareda hugging d'insa, shafa bayana yayi yace "muje ko?"

Gaba nayi har na fita ya ri'ke hannuna, ina hangosu a tsaye idanunsu na kaina, murmushi yayi tareda shafar fuskata yace "boo-boo na komai zai zo da sau'ki kinji? Just believe in yourself and protect your daughter at all cost, ina tare dake komai rintsi".

'Dage nayi da 'kafafuna na waiwaya na kalli dangin mijina tukun na had'e bakina da nasa, a take yayi responding tareda sunkuyowa, wannan shine ownership sai naga a cikinsu wacece zata iya masa haka duk juyashin da suke so suyi.

Breaking kiss d'in mukayi nace "mint d'in bakinka yayi min dad'i, zan so ace na sake tasting amma kuma na lura idanun surukaina na Kaina".

Ri'ke hannuna yayi yana min wasa da yatsansa a tafin hannuna har muka isa, cikin ladabi na dur'kusa nace "ina wuninku?".

"Yayi miki kyau tambad'add'iya, wato ke gaki mara kunya ke mai miji ke wayayyiya sha-sha-sha mara tunani zaki tsaya gaban uwar mijinki kina wani cakumar bakin mijinki ke a ganinki kin waye, banza....."

Katse anty maimuna Saleh yayi yace "maimuna ya Isa haka, idan zaki zageta ni ya kamata ki zaga domin ni na nuna mata ina bu'katar hakan kuma duk mace tagari abinda mijinta keso takeyi".

"Rufe min baki shanyayye, Dole ka fad'i haka Mana mace ta shanyeka tana juyaka yanda takeso, baka da aiki saidai tayi laifi ka goyi bayanta".

Ri'ko kafad'ata Saleh yayi yace "yanzu menene laifin Bilkisu Dan ta sumbaci mijinta? Meye laifi a ciki? Kuma a 'kofar gidanmu ne ba wai 'kofar gidanku bane please ya isa haka muyi abinda ya kawo mu".

Cikin fad'a Aunty Maimuna tace "baza a bari ba, abinda yarinyarnan tayi dole a mata magana, haka fa zaman hajiya a gidanta ta dinga fitowa rabin tsirara Kuna shashanci a gaban hajiya, sannan yanzu....."

"Wai dan Allah abinda mukazo yi kenan a wajennan? Yaya maimu muyi abinda zamuyi mu tafi kafin nayi abinda yafi wanda kike fad'a muni". Sultana ta fad'a tana kallon Usman, galla mata harara Maimu tayi

"Dalla malama ki mana shiru wa ya sakaki a ciki? Wawiya wadda bata san me take ba, yanzu sai ki maimaita mana abinda kika fad'a a bayan idonta".

Hard'e hannu Sultana tayi tace "Ni ba munafuka bace kuma bana magana biyu, abinda nace shine nasan Bilkisu tana cikin mawuyacin hali na rashin haihuwa, kuma ita yafi cancanta ta ri'ke Huda domin tafi nuna mata soyayya a kaina, sannan nace Bilkisu tana da son yara sosai shiyasa naga ya dace na bata Huda domin bazan iya rainon yara biyu lokaci guda ba, sannan anty Maimuna abinda baku sani ba tun Huda na wata biyu na mallakawa Bilkisu ita ba tareda na sanar muku ba, nidai abinda nakeso dan Allah ku bar Bilkisu tayi rayuwarta da mijinta banida had'i da ita bayan zaman faccalata da takeyi, ku dena sako relationship d'ina da Saleh cikin rayuwata idan ba haka ba zaku kashemin aure a banza domin ya Usman ya fara si'kewa".

Sai yanzu hajiya tayi magana tace "yanzu ke Sultana abinda kikayi ya dace kenan? Huda mun sani 'yarki ce ke kika haifeta kina da iko da ita, amma bakida ikon ki bayar da ita ba tareda sanin iyayenki ba, ke bakiyi tunanin cewa kema 'ya bace kamar kowa? Kinada iyayen da dole sai kin nemi izninsu zaki aiwatar da abu irin wannan amma uwarki bata sani ba balle ni, kinje kinyi gaban kanki kin bawa bare 'yarki wadda baku had'a jini da ita ba".

Tura baki Sultana tayi tace "to Hajiya ai gani nayi ubanta ya amince kuma nima na amince to me muke bu'kata kuma? Idan har na sanar muku zaku amince ne? Kuma nayi imanin a cikinku babu wadda zata ri'kemin Huda yanda Bilkisu ta ri'keta, na riga na baiwa Bilkisu ita saidai kawai kuyi ha'kuri yanzu haka ma maganar nan tana wajen lawyer ko ni banida ikon na 'kwace Huda daga wajen uwarta".

" 'karya kike wallahi bazai yiwu ba, uban wani ya hanata haihuwar da zaki d'auki 'yarki ki bata? Ke sauke 'yarnan" Aunty Maimuna ta fad'a tana 'ko'karin kunce goyon dake bayana, a hankali na ture hannunta nace "Aunty Maimuna bari mana kar ki tasheta a bacci".

Bud'e baki tayi zata min magana Hajiya ta dakatar da ita da cewa "Bilkisu inaso a yanzunnan ki sauke yarinyarnan ki mi'komin ita hannuna"

Bansan ta yaya na samu dakakkiyar zuciya ba nace "Hajiya ki min afuwa amma a yanzu kotu ce kawai keda ikon rabani da Huda domin yarjejeniya ce muka 'kulla akan hakan, Sultana tayi rantsuwar bazata kar'bi yarta daga wurina ba nima nayi rantsuwa duk rintsi bazan maido Mata 'yarta ba, bazan zama munafuka mai karya al'kawari ba ko sultana a yanzu bata da ikon kar'bar Huda a hannuna".

Cikin zafin nama Anty Maimuna tayo kaina, janyeni Saleh yayi cikin sauri tazo dab dani tana kallona, hannunta ta sanya tana nunani tace " 'karya kike baki isa ba wallahi kinyi kad'an, dole sai kin bada Huda ko kinaso ko bakyaso babu ruwanmu da wata

13 / 41