Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
kawai" na fad'a a karo na boyar tareda matsawa daga gareshi, tunda yayi wanka ya fito ya dameni dole sai ya nad'eni a towel kamar wata yarinya.
"To shikenan ungo".
Kar'bar towel d'in nayi na d'aura sannan na sauko daga gadon, gaba d'aya towel d'in bai wuce rabin cinyoyina ba, zubawa 'kafafuna ido yayi babu 'kiftawa, ba tareda na waiwayo ba na shiga bathroom a take gajiyar da nakeji na nema na rasa, jina nayi kamar nabar 'kasarnan wani had'add'en d'aki na gani na glass sai ka bud'e 'kofar zaka shiga shower, a ciki akwao sitting jacuzzi.
Ruwa na cika na shiga na zauna tuni na fara gyangyad'i, har na manta ma dare ne domin hasken wurin ma na daban ne, na jima ina gasa jikina sannan na d'aura towel d'in na fito, Aliyu na kwance idanunsa na kaina.
'karamin towel na saka a gashina na bud'e wardrobe na d'auko kayan bacci, gefensa na nufa na kwanta ya matso dab dani, hannunsa ya sanya a cikina yace "goodnight".
Da safe bayan munyi breakfast muka fara zagaya gidan yana nunamin wurare, d'akuna uku ne kawai a main house sai kuma boys quarters sai kuma 'bangaren masu aiki da nidai a wurina baida amfani, akwain'karamin gym sai study nashi wanda yake ajiye takardunsa da suk wasu abubuwa da suka shafi aikinsa, bayan mun gama ganin wad'annan sannan ya nunamin kitchen na daban a waje yacemin anan chefs zasu dinga girki, garden ya nunamin yace "da naso ayi mana swimming pool daga can to sai kuma naga akwai wahala sai na barshi".
Zama mukayi sanyin ciyayin wurin na dukanmu nace "naji kace akwao wajen masu aiki da kuma chefs ai Ina ganin babu amfanin hakan ko?"
Girgiza kai yayi yace "a'a wannan gidan nasan bazaki iya gyaransa ba ko zaki iya bazan barki ba, sannan kaman yanda kika gani a gidanmu chefs ke mana girki kema anan bazan barki kina girki ba, ki zauna ki huta idan kinaso kiyi girkin ga kitchen d'inki nan d'an abun kwad'ayi dai idan kinaso sai kiyi da kanki".
"Okay" na fad'a tareda mi'ka domin bayana ya ri'ke, hannuna ya kama yace "muje wancan zaifi miki dad'in zama".
Kujera ce gatanan dai half gado half kujera, kishingid'a nayi akai shima ya kwanta a gefena, idona a rufe inajin wata ni'ima na ratsani, idan kana irin wannan wurin ai ko wula'kancin dangin miji ma ba jinsa zakayi ba.
Hular kaina ya cire yace "twins d'inmu fa akwai rashin ji".
Murmushi nayi nace "nikuma sai nake ganin kamar basuda matsala".
Kansa naji a 'kirjina yanda yana magana inajin vibration na muryarsa na shiga jikina yace "da suna 'kanana so adorable, amma da suka fara girma duk suka ishi kowa, ita dai Mum tace sunfi bata wuya da suna babies amma mukam sunfi bamu wuya da suka fara takawa, duk saida suka bi glass d'in gidan suka farfasa".
Dariya nayi ina hango amal da nawal suna toddlers nace "nikuma twins na birgeni sosai fa, gani nake kamar ba wani wuya, saboda kana kallansu kana Jin dad'i".
D'ago kansa yayi yace "da twins Mata da maza wanne kikafi so?"
Dariya nayi yayin da naji wani abu a 'kirjina nace "Ni da bazan samu ko d'aya ba mene nawa na za'bi?"
'bata rai yayi yace "am sorry idan tambayar tawa ta 'bata miki kawai na tambaya ne".
"A'a baka 'batamin ba kayi ha'kuri, gaskiya dai....to duk inaso saboda kowannensu akwai abin sha'awa, amma dai zanso na fara da maza".
"Nima nafison twins maza, yauwa na tuna kinada passport ne?"
"Eh inada amma yayi expiring".
"Okay za'ayi renewing d'insa kin taho dashi ko? Inaso mu tafi honeymoon amma sai mun biya Saudi sai muje wata 'kasar ko?"
Wani dad'i naji nace "Allah ya kaimu" a take na fara d'okin zuwa saudiyya, tunda akamin passport d'in baiyi amfanin komai ba, tashi nayi da sauri nace "bari naje na duba".
Tare muka tashi Aliyu yayi 'ko'karin d'agani, a lallai sai ya sakani a kafad'a shi kuma ba wani 'karfi ba, a tsorace nake 'ko'karin dukansa aikwa Yana d'agani muka zube tare kan grass carpet d'in, dariya nake sosai shi kuma ya had'e rai, cikin gunaguni yace
"Shikenan zaki d'aukeni rago".
Tashi nayi ina rigata har tayi danshi saboda ra'ba ce kan ciyayin nace "karka damu nasan ba rago bane kai ni d'in ce mai nauyi".
Hannu ya mi'komin alamun na kamashi ya tashi, maimakon ya tashi sai ya jani na fad'a kansa, Ina fad'awa ya had'e lips d'insa, intense kiss ne amma bai wani dad'e ba ya janye, d'aga gira yayi yace "wato ni jarumi ne ko?"
Tashi nayi daga kansa na juya, dariya yayi yace "au sai yanzu kika fara kunyata after you spend minutes moa....."
Kunnena na toshe na bar wurin da gudu, biyoni yayi yana cewa "tsaya mana na 'karasa fad'a miki abubuwan da kikayi a daren jiya"
Ban tsaya ba na shige d'aki da sauri na kifa kaina a kan gado saidai fuskata d'auke da murmushi, bansan meyasa na yada kunyata jiya ba gashi ya samu abin tsokanata.
47
Tashi Hadiyya tayi tace "nidai zan tafi unguwarnan tamu yamma nayi zakiga duhu ya shiga ga wahalar abin hawa, yanzu ma tunani nake yanda sai naje titi zan hau".
Janyota yayarta tayi tace "ke dalla ai shi ya kamata yazo ya d'aukeki, ya za'a yi zuwanki na farko gida zaki tafi da kanki ai ba'a haka".
"Ai bamuyi zaizo ya d'aukeni ba kuma kinga ya bani kud'in mota".
"Dalla malama zauna, ki bari idan anyi magriba sai ki kirashi kice kin fita baki samu abin hawa ba kuma kinga lokacin sallah yayi kin koma gida, idan babu abinda yakeyi ko zai iya zuwa ya d'aukeki? Haka akeyi ai dabara ake kinga kud'inki ma ya huta".
Haka kuwa akayi tana idar da sallar magriba ta d'auki waya ta kirashi, yana d'agawa tace "ina wuni? Umm nace kaga na fita ban samu abin hawa ba har akayi sallah, nakoma gida nayi sallah kuma dare yayi ko zaka zo ka d'aukeni idan ka gama abinda kake?"
"Okay idan anyi sallar Isha zanzo".
"To sai kazo" ta kashe wayar, wani uban dundu taji an mata saida ta gantasare ta saki ihu, kama kunnenta yayarta tayi tace
"Uban waye yace miki haka ake magana da miji? Shegiya me kan dutse kamar bakya ja? Komai a gabanki mukeyi saboda ki koya amma a banza?, Meye wani kaga? Ba wani sweety, darlin, honey, baby da sauransu se wani kaga? Babu kashe murya kice dan Allah baby alfarma zakamin akwai matsala fa? Wallahi kaga na fita kaza kaza amma kina magana kamar gayan tuwo? Inaga ma kagan da kike sakawa basa bayyanar da jikinki ta ina miji zaiyi sha'awa? Ke ki gyara wallahi idan ba haka ba kafin ya kwanta dake yayo miki kishiya, shawara ma ta canza yanzu nasan me zakiyi".
Hud'uba akewa Hadiyya har zuwan Saleh, saida yazo sannan tayi sallah ta shafa powder da janbaki ta saka turare ta fita.
Cikin sauri ta bud'e motar ta zauna, kissing kumatunsa tayi tace "yi ha'kuri honey na barka da jira sallah nayi ne sannan na taho maka da abinci".
Kallonta yayi tareda hadiyar yawu yace "okay" yasan yau zaisha rigima tunda ta samu tsarki.
Hira taketa zuba masa yana binta da uhm har sukaje gida, suna zuwa tace ga abinci dan Allah kaci, nasan baka son girkina amma wannan wallahi ammyna ce tayi da kanta, bari nayi wanka".
Guest room ta shiga ta cire kayanta ta fad'a toilet, jika jikinta tayi sannan ta shafa turare, fitowa tayi ta kurma ihu sannan ta sake, a firgice Saleh ya shiga yana shiga ta d'afeshi tace "tsaka!! Duba ka gani nazo fitowa na ganta wayyo Allah na!!".
Ganin zata fad'ar dasu yasa ya tallafo bayanta ta kuwa sake 'kan'kamseshi, 'kamshin turaren da ta shafa ya Sha'ka 'kamshi mai matu'kar dad'i sannan gata naked ga ruwan dake jikinta.
Ajiyeta yayi ta sake kama hannunsa da alamun tsoro, gyaran murya yayi yana d'auke kansa yace "to nemi abu ki d'aura.
Dukda kunyar da takeji na tsayuwa a gabansa babu kaya amma ta danne tace "meyasa baka sona ne? Ko kallona baka son yi saboda baka sona? Naji bamuyi soyayya dakai ba amma ai ko a matsayin matarka ta aure ka kalleni, ba fa zaman gadi nazo ba zaman aure nazo".
Ja tayi baya ta nufi kayanta dake ajiye ta d'auki d'ankwali ta d'aura a jikinta tace "tunda banida amfani a wajenka zan tafi wajen Hajiyarka na kwana gobe zan tafi gidanmu bazan sake zama a gidanka ba, haba dan Allah dan cuta kwana goma da kawoni amma bansan kaina a matsayin amarya ba? Ya isheni na tafi na bar maka gidanka sai ka biyoni da takardar saki".
Kwasar ragowar kayan tayi ta nufi 'kofa, binta yayi da sauri ya ri'kota ta sake sakin d'ankwalin daga d'aura.
Hannunta ya janyo ta fad'a 'kirjinsa ta saki kuka, tausayinta ne ya kamashi dukda dai akwai rashin ha'kuri da kunya amma gaskiya ta fad'a ya kamata ya bata ha'kkinta domin yanzu ya lura ba yarinya bace sannan shi kanshi yana da bu'katar hakan".
'Dankwalin ya d'auka ya d'aura mata sannan ya d'auketa bridal style, ta kasa 'boye murnarta tayi ta cusa kanta a 'kirjinsa tana murmushi.
A kan gadonsu ya ajiyeta sannan ya bud'e wardrobe d'inta ya d'auko doguwar riga, wanni kallo ta masa yace "ki saka muyi sallah".
Zura rigar tayi ta d'auro alwala suka gabatar da sallah, bayan sun idar ta zauna kan dardumar hannunta na kan cinyarta tana jiransa.
Zama yayi a bakin gado sannan yace tazo ta zauna, a cikin zuciyarta murna take kamar ta zuba ruwa a 'kasa tasha amma a bayyane ta nutsu sosai, d'aga kanta tayi ta kalleshi a hankali ya janyo fuskarta, gani yake duk yanda ya ta'bata zai iya cutar da ita.
Ai kafin ma ya gama matsowa ta rufe ido tareda turo le'benta, murmushi yayi yana tausayin yarintarta, Bilkisu ce ta fad'o masa rai amma ya kawar, indai ta cigaba da rayuwarta shima ya kamata yaci gaba.
Kissing d'inta yayi ta tsaya cak tateda bud'e idonta, ganin nashi idon a rufe ya sanya ta rufe nata idon itama, hannunta taji yana dago rigarta a hankali itama ta tayashi tareda jan rigar zuwa cinyarta, hannunsa ya sanya a cinyarta yana shafawa take ta fara mutsu mutsu.
Tunda kuwa rigar ta rabu da jikinta ta fara shan jinin jikinta, kwantar da ita yayi tareda shiga tsakanin 'kafafunta, take bugun zuciyarta ya canza ta zazzare ido, abubuwa da dama da taji labari ke zuwar mata, ganin ta tsorata ya sanyashi sake kissing d'inta, tashi yayi ya fara cire kayansa tun tana zuba ido tana kallonshi har abin yafi 'karfin jaririyar 'kwa'kwalwarta ta juyar da kanta.
Dakewa tayi saboda kar ya Gane tsoronta amma ta gama.tsorata da ganin wannan 'katon mutumin a kanta, bata gane barno gabas take ba saida ayar Allah ta tabbata a kanta, tun tana cije baki har ta gaji ta saki kukanta mai isarta.
**********
Muna zaune kan couch d'in dake bedroom d'inmu, kallon tv d'in dake d'akin nayi ina tunanin rashin amfaninta, meyasa za'a sanya Tv a bedroom a sanya a sitting room tsabar kud'in yayi yawa?
Netflix ya kai a cikin tv d'in ya fara scrolling yana karantomin sunayen films d'in dake wurin ina girgiza kai, ya fad'i kusan 10 duk ina cewa sunan baiyi min ba, ajiye remote d'in yayi ya kalleni yace "Anya kina kallon American film?"
"Ina kallo amma ba sosai ba".
"Okay to yanzu zan za'ba mana mai kyau mu kalla tare".
Wani film ya kai mana 'golden intelligence', kallo muka farayi film d'in kuwa yayimin kyau, muna kallo naji 'karan wayata, dubawa nayi naga Raudah cikin sauri na amsa, dad'in gida ya sanya na manta ma dasu domin jina nake a wata duniya ta daban, banda gidana na aljanna yafi wannan ai da sai nace a aljanna nace, ga farin fentin d'akin da kujerar da muke kai ya sake haska d'akin.
"Lallai Bilkisu har ya fara hure miki kunne ko? Bazaki neme mu ba to ai gamu mu mun kawo kanmu, malamai ku bud'e mana 'kofa".
Dariya Aliyu yayi ya tashi ya fita nabi bayansa, wani wuri naga ya danna gefen 'kofar palon sai ga camera ta bayyana, kallonsa nayi na zubawa hoton su Raudah Ido suna tsaye a bakin 'kofa, dariya yayi yace "me kukazo min gida?"
"Ka bud'e mana".
"A'a ku koma".
"Workers d'inku muka kawo idan kuma bazaka bud'e ba shikenan sai mu koma dasu tasha aikinta".
Jikin cameran ya dannan naji alamun lock ya fita daga 'kofar, turo 'kofar sukayi twins suka kama waje suka zauna Raudah ta tsaya mana bayanin ma'aikatan da suka kawo.
Mutum biyu ne zasu dinga gyara cikin gidan sai gardener sai kuma sharar compound kace maigadi yace a bashi zai dinga yi ko?"
"Eh, chefs d'in fa?"
Shigewa tayi ta zauna tace "zasu zo anjima tunda sai gobe zasu fara aiki, kaje waje suna jiranka".
Fita yayi na koma wurin twins muka fara d'an hira, kirana Aalee yayi na kar'bi mayafin Raudah na yafa na fita.
Yana tsaye da wasu mata biyu 'yan dattijawa dasu, sai namiji d'aya, kafad'ata ya dafa yace "wannan itace matata Bilkisu, zatayi muku bayanin yanda aikin yake kai kuma muje da kai".
Gaisheni sukayi har 'kasa duk kunya ta kamani sannan muka shiga cikin gidan dasu nayi na nuna musu wuraren da zasu dinga gyarawa sannan na kaisu part d'insu domin damu zasu dinga zama, komi ni kallon sabo nake masa amma dole na saba indai zaman aure zanyi.
Zuwan su Raudah ya sanya Aalee fita, basu koma gida ba saida ya dawo, kama wuri sukayi su fa a lallai yau anan zasu kwana harda Raudah.
Kama hannun amal da nawal yayi ya fara jansu suna da'kirewa nikuwa ba abinda nake banda dariya, kashe murya nawal tayi tace "Dan Allah Aunty B kice ya barmu mu kwana Allah ni gani nake ma yau bazan iya kwana a d'akinmu ba yayi 'karami".
"A'a ku godewa Allah twins d'akinku yanada girma fa tunda kowacce nada gado a cikinku a ciki sannan ga space dukda haka, amma idan zai yarda ku kwana ga d'aki nan". Na fad'a ina dariya.
Girgiza kai yayi yace "muje na siyo muku burger da pizza, indai kwanan gidannan ne har sai kun gaji bari na koma aikina".
Anyi sa'a sun ha'kura yace na shirya mu fita tare, wani pizza joint mukaje ya siya mana family size, gidansu Aliyu muka nufa a can muka ci sannan muka tafi gida.
Washegari da safe bayan mun gama shiryawa sai ga kira ta land line, d'agawa yayi yace "okay, yeah right now.... thanks".
Hannuna ya kama yace "breakfast is ready" muka nufi dining, bansan cewar mutane zasu shigo ba saboda haka ban fito da mayafi ba, wani iri naji ganin maza biyu sun shigo d'auke da tray, jere plates sukayi sannan suka dur'kusa suka bar wurin, suna fita nace masa "Amma baka cemin mutane zasu shigo ba".
"Sorry, next time zance su kawo kafin mu fito za'a kawo abincin hakan yafi ko?"
Gyad'a masa kai nayi alamar eh sannan na fara kallon abincin, abincin kad'an-kad'an ne a plate, kallon Aliyu nayi ya d'auki fork da hannun hagu ya d'auki knife da hannun dama, a hankali nace "babu kyau cin abinci da hannun hagu fa".
Murmushi yayi yace "bakiga na ri'ke knife d'in da hannun dama ba? Hakanan akecin wannan abincin".
"A'a wannan d'abi'ar yahudawa ce annabi bayaso, ko tea da bread ba'aso a ri'ke cup da hagu saidai ka d'auki bread kaci ka ajiye ka d'auki cup".
"Yeah well yanzu zamani yazo da abu na daban? Indai zakiyi yawon duniya dole ki fara cin abinci haka, ko ina hakanan akeyi zamu je 'kasashe da dama zaki ganewa idonki".
Ajiye maganar nayi saboda batada amfani na saka hannu na fara cin abincina, kallona yayi tareda cire hannuna ya ri'ke yasa tissue ya goge hannun tare da mi'komin fork da knife yace "ki kalli yanda nakeyi sai kiyi".
Raina ya sosu kad'an, me yake nufi da hakan? Daga 'kauye ya d'aukoni ko me?, Danne fushina nayi nace "nasan yanda akeyi kawai banida ra'ayin hakan ne, sannan shaid'an ke cin abinci da hagu banaso naci da shaid'an".
"Ni inaci da shaid'an kenan?"
"Ni bance haka ba kayi ha'kuri" na fad'a tareda sunkuyar da kaina, take abincin ya fita daga raina dukda nasan wayewa ke sanya hakan amma wannan ba d'abi'a ce me kyau ba, indai sai nayi hakan zan waye nayita zama da 'kidahumancina.
Abincin na fara ci da fork d'in, abinda sai na yanka sai na yanka sannan na ajiye wu'kar naci, a haka mukaci abincin shiru, sunyimin dad'i sosai saboda haka ban bar komai ba, ina gama ci fara 'ko'karin had'a kwanuka? Ri'ke hannuna yayi tareda girgiza kai yace "ki barsu za'a kwashe".
Gaba nayi inajin jikina ba dad'i, ta yaya mutum zai iya rayuwa babu aikin komai? D'an aikin da nake zuwa ma ya ragemin zaman banza babu shi sannan gashi tun yanzu mun fara samun sa'banin halaye da Aliyu.
Ganin banida abinyi ya sanyani fara goge gogen d'akin dukda babu wani datti, ina goge gogen ya shigo, amsa masa sallamarsa nayi ya 'karaso inda nake sannan yayi wrapping hannunsa a kan cikina, rad'amin yayi a kunne yace "kiyi ha'kuri".
"Nima kayi ha'kuri ina ganin na wuce boundary d'ina, idan haka dabi'unka suke banida ikon canza maka".
Juyoni yayi na kalleshi yace "kinada ikon canzani mana saboda ke matata ce amma ba yanzu ba, mu fara fahimtar juna tukun sannan zanyi duba akan abinda kika fad'a".
Anan muka ajiye maganar, mun sake fahimtar juna kafin ya fita ya barni ni kad'ai, part d'in ma'aikata na nufa, suna waje suna girki su biyun ina musu sallama cikin sauri suka nufo inda nake tareda dur'kusawa.
Bayan mun gaisa d'aya daga cikinsu wadda naji d'ayar ta kira da inna kulu tace "Hajiya alfarma nake nema daga gareki, Kinga jikata ita kad'ai gareni uwarta ta rasu an barmin ita, to na taho na barta wajen kishiyar uwa gashi azabtar da ita takeyi, Hajiya ko zaki iya barina na d'aukota ta zauna dani anan?"
"Babu matsala ki kawota, Allah ya jikan mahaifiyar tasu"
"Ameen Hajiya nagode Allah ya 'kara arzi'ki Allah ya ji'kan mahaifa".
"Ameen, akwai wani abu da kuke bu'kata?"
"Babu, Alhaji ya saka an kawo mana kayan abinci dan Allah ki 'kara masa godiya, babu wani abu da muke bu'kata".
"To shikenan idan akwai wani abun Sai ku fad'amin".
Bayan dawowar Aliyu na sanar masa da abinda ya faru, kissing d'ina yayi yace "to ai kece me gidan duk abinda kikayi daidai ne Hajiya".
Zama nayi jikina duk ba dad'i nace "wallahi nayi missing aikina sosai, yanzu haka zanyi ta zama ba wani