NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 41

9K to 12K   out of 120.7K words

kifi" dayan dake gefen Saleh ya fad'a,cikin say sultana ta ajiye plate din dambunta ta Masa wuri a gefenta tace

"Kai,Amma kuwa na gode Yaya usman,mugani"

Kallon su maymu yayi yace

"Bazan bud'e su cinye mana ba,ki Bari sai mun haura" ya fad'a tareda kashe Mata ido,d'auke.kanta tayi inaga dai yanzu ta tuna ita amarya ce Domin ta dan fara nuna alamun damuwa

Dukka d'akin Babu Wanda ya kula Saleh Banda sultana,tashi sultana tayi da ya Usman suka koma dayar kujerar da zata ci mutum biyu suka bawa Saleh gefena ya zauna,karashe dambun dake plate Dina nayi na ajiye

Sunkuyowa yayi daidai kunnena yace

"Wato bama wuce tayi ko a gaban surukai"

Tamkar ban jishi ba nayi,Domin duk idonsu kaina yake,Kara matso da kansa yayi kafin yayi magana yaya maymu tace

"Kunga Kar ku Mana rashin kunya anan,mama a sallamesu kafin su Mana aika aika"

Gyara zama mama tayi ta fara Mana nasiha kamar gaske

"Alhamdulillah,nagode Allah da ya rayamin ku ya Kuma rayani Naga wannan lokacin da na aurar daku dukkanku,bazan muku dogon bayani ba Domin dukkanku yayana ne,Usman da Hashim,ga Amana Nan na baku,dukda Hashim Kai tsoho ne a cikinsu,Amma inaso ki rikemin yayana Amana,karku cutar dasu karku Bata musu Rai,ki musu duk.abinda sukeso,Kuma sultana da jumana,ki kularmin da yayana tsakani da Allah,ki ri'ke sirrikan mazajenku ku zauna lafiya"

Shiru tayi ta kallemu,daga Ni har Saleh jikinmu yayi sanyi,wato mu ba 'ya'ya bane,kallon saleh nayi ta gefen iso naga yanda fuskarsa ta sauya sosai rashin jin Dadi ya bayyana,cigaba tayi ba tareda ta kallemu ba tace

"Naso ace Rayuwar yayana ta kasance yanda na tsara,ku auri jininku mu zauna Babu bare a cikinmu,Amma hakan batayi ba,Dole mun samu shigowar bare cikinmu,Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba,Allah yayi muku albarka"

Ko Bata fad'a ba na jima da jin Kaina a matsayin bare,kallon da sukemin tsikar jikina tashi take,hajiya kuwa idan ta kalleni gabana yankewa yakeyi ya fad'i

"Ku ku Kira mazajenku suzo su kwasheku ku Kuma ku tafi Allah yayi muku albarka"

Tashi sukayi suka ja sultana d'aki,mu kuwa mun kasa motsi a wurin,hajiya ko kallo bamu isheta ba kamar ma bata san da rayuwarmu a wurin ba

Kusan minti 20 suka fito da sultana,tashi usman yayi suka jera sukace

"Hajiya Bari mukai Yar lelenmu dakinta ko?"

"Ya kamata,Domin banason 'yata ta taka ita kadai"

Ina zaune kamar marainiya,ko da yake ita din ce,tamkar ma dai an kafemu a wurin,muryarsa cikin nuna rashin Dadi yace

"Mu tafi ko?"

Tashi nayi cikin kasala na bishi a baya,tafiya mule duk cikin rashin dadi,shewarsu naji muna karasawa wurin gidan,duk kewar gida ta kamani,da ace sulaiman na aura da haka zamuyi muma

Gidanmu shine na uku a cikin gidajen,muna shiga naji shirun yayimin yawa,kwalla ce ta zubomin na saka mayafina na goge a Raina Ina Kiran mamana

Zama yayi gefena yace

"Kiyi ha'kuri bilkisu,bansan zasu Miki hakan ba"

Murmushin yaqe nayi nace

"Bakomai,ai Yan uwanka ne,mu bar wannan a gefe"

"To mu tashi muyi abubuwan da Allah ya umarcemu sai mu ci abinci ko?"

Gyad'a Masa Kai nayi yayi hanyar wani lungu a babban palon da muke zaune,bene na gani muka hau,alwala nayi shima yayi muka zauna a palo,kazar da ya kawo kasa ci nayi,da kyar naci fukafiki Nasha lemo naja gefe

Kokari ya dinga yi Domin nayi fara'a,saida ya tabbatar na sakin raina tukunna ya fara nunamin hanyar Disney world 😉tuni na fara ajiyar zuciya Ina Kiran mama,lalube yake a duhu na kuwa barshi yayita fama

Wani Dadi naji a Raina ganin y kima gefe,na aza ya yafe ne,wayarsa Naga ya d'auka ya kunna torch light ya koma....zare Ido nayi na rasa ma takaici zanyi ko dariya, gama haske haskensa yayi ya aje wayarsa Kan bedside drawer yaci gaba da ibadarsa.....

Washegari da wuri wuri na tashi,shayi na daura na fara tunanin me zance dafa,da alamu Torchlight ta haska inda ya kamata Domin ban wahalar da nake tunani ba,dariya nakeyi Ni kadai a kicin din 'kasa,Allah ya kaimu lokacin da zan fara kiransa Torchlight guy

Muna Gama breakfast kuwa sai ga hayaniyar Yan uwana,cike da murna na fita Domin tarosu
Shigowa sukayi Niki Niki da kayana,ko ta kan Saleh ban Kuma bi ba na rakasu sama,jera kayan mukayi muna hira sannan muka sauko

A kujera muka na sameshi Yana zaune,muna sauka ya koma upstairs

Abinci muka girka na Kai masa,Yana bacci na ajiye na rufe kofar na fito,wuni mukayi da sisters muna Hira sai can yamma suka tafi

Washegari da safe na fito gaida hajiya,sultana na gani itama ta fito muka gaisa muka karasa tare

D'ar dar nakeji Amma na dake,muna shiga hajiya ta fadada murmushinta ganin sultana,Ni kuwa da ta kalleni saida naji Yar a jikina saboda wani irin kallo da ta watsamin,zama sultana tayi a gefenta ta gaisheta,dur'kusawa nayi Nima nace

"Hajiya barka da safiya kin tashi lafiya?"

"Lafiya" ta amsa ba tareda ta kalleni ba,ra'bewa nayi jikin kujera kaman marar gaskiya,hura suke da sultana wadda ni kwata kwata na hankalina baya Kan maganarsu

"Ke" naji hajiya ta fad'a,da sauri na d'ago cikin tsoro nace

"Na'am"

"Tashi ki fita mana,kin sakamu gaba"

Tashi nayi na fita jikina a sanyaye,wace irin matace wannan?Ina Jin sultana na cewa

"Hajiya da dai kin Mata a hankali"

Wucewa part Dina nayi na d'auko system dita na fara karatu,Domin presentation gareni jibi

Ajiye system din nayi Kan kujera Ina zagaye d'akin Ina yiwa kaina bayani da karfi,a hankali na fara mantawa da abinda hajiya tayimin

Ina cikin bayanin Saleh ya sauko daga bene,wayarsa ya bude ya faramin video nayi kaman ban gansa ba

"Wow, that's my beautiful wife"

Murmushi nayi naci gaba da bayanina ya sake cewa

"I love you my star shine"

Kallonshi nayi cikin shagwaba nace

"Kana distracting Dina"

"To nadena" ya fad'a yana mele Baki wai zaizo kwaikwayeni,hannu na nuna masa alamun yayi shiru naci gaba da bayanina

Maida wayarsa yayi aljihu yayi hugging Dina ta baya tareda pecking Dina a kumatu yace

"Zan fita,sai na dawo star shine"

"Sai ka dawo" na fad'a Ina sunkuyar da kaina

"Me kikeso na kawo Miki?"
Ya fad'a yana ri'ke Dani,murya qasa qasa nace

"Bakomai,Allah ya dawo dakai lafiya"

Kansa ya d'aura a wuyana yace

"Kawai ki fad'a Mana,kice so nake ka dawomin da kanka yanda ka fita"

Hannu nasa na rufe fuskata cikin Jin kunya irin ta amare,dariya yayi yaja kumatunta yace "bye bye ki kulamin da kanki"

Karasa presentation. Din nawa nayi na sake dubawa na tabbatar ba gama editing sannan na daura abincin rana

Washegari ma da wuri naje gaida hajiya,Ina gaidata tace na zauna tana son magana damu duka, Addu'a nake Allah ya sa abin alkhairi zata fad'a

Dukkanmu da mazajenmu mun had'u a d'akin,Saleh na Kan kujerar da nake zaune a kasanta,jinsa nake tamkar kariya ne gareni Domin zaman dakinnan kaman zaman kurkuku yake a wurina,hajiya na fara magana naji tsoro ya kamani

"To Alhamdulillah,da farko dai zan yiwa jumana godiya da irin kokarin da tayi min,Allah yayi Miki albarka Allah ya Baki zuri'a ta gari"

"Bayan wannan kaman yanda ku Kuka sani Banda waccan,jumana tunda ta shigo gidannan take dawainiyar kawomin abincin safe,Rana har ma da dare,kusan shekara biyu kenan"

Tura Baki sultana tayi tace

"Hajiya Nima fa da inanan Ina Miki,ki sakamin albarka Nima"

"Kema Allah yayi Miki albarka,yanzu abinda ya Sanya na taraku anan shine,a tsakaninku Zaku Raba,bazai yiwu a bar jumana ita kadai da wannan dawainiyar ba,tunda ku uku ne wata zata dinga min abincin safe,wata na rana wata na dare"

Nidai bance komai ba,da sauri sultana tace

"Na dau na dare"

Jumana Kuma tace

"Na d'auki na safe"

Dago kaina nayi Naga duk hankali na kaina,kallon saleh nayi sannan nace

"Zanyi na rana"

Cikin sauri Saleh yace

"Hajiya gobe bilkisu zata koma makaranta Kuma zata fita da wuri,sannan sai can yamma zata dawo,Ina ganin sultana ki bata na Daren ke ki d'auki na safe"

Kafin sultana ta amsa hajiya tace

"Idan bazatayi ba ta barshi,da mahaifiyarta ce ai zata iya ajiye makarantar Domin ta Mata girki ko?"

Kirjina naji ya daure saboda ambaton mahaifiyata,baiwar Allah da ko ganin fuskata batayi ba ta koma ga mahaliccinta akan Dan karamin abunnan za'a nemi tozarta min ita

Muryata kasa kasa nace

"Kiyi ha'kuri hajiya zanyi"

Tsaki jumana tayi tace

"Meye kike wani magana kaman an maki Dole?Kinga idan baza kiyi ba ki barshi,mu da take uwarmu ya zamar Mana Dole mu Mata ai zamuyi,Amma ke ai uwar mijinki ce"

Ban to daga kai na kalleta ba nace

"Zanyi hajiya,insha Allah zanyi kiyi ha'kuri"

A fusace hajiya ta kalleni tace

"Au hakuri ma kike bani saboda nace ki ciyar Dani?kina karkashin Dana kina cin arzikinsa?abincin da zakimin shine ya Bata Miki Rai har kike wani daure fuska?ki barshi tunda bazakiyi ba,Kar ma Kimin abinda zai batamin rai"

_ai a cikin garata zan dafa Miki ba wai arzikin danki zanci ba_

Na fad'a a Raina,kwalla naji na kokarin zubomin na danne nace

"Hajiya ba haka bane,kema kamar uwa kike a wajena,zanyi komai Dan na kyautata Miki,ki yafemin idan nayi wani Abu da zai Bata Miki Rai"

D'auke kanta tayi daga gareni tace

"Naji,gobe 12 ki kawomin abinci,wainar shinkafa nakeso da miyar ganye,ki sakamin cow leg a ciki"

Da kyar na amsa da to,sannan nace

"Hajiya Ina neman afuwarki,gobe 12 zanyi presentation a makaranta,kiyi ha'kuri karfe biyu zan kawo Miki duk abinda kike bukata"

"Tunda ba Taki uwar bace Zaki ce haka mana,ki barshi banaso"

Ha'kuri na dinga Bata tayimin banza,shima Saleh ya saka Baki tayi kaman batasan inayi ba,saida sultana da usman suka saka Baki sannan tace ta ha'kura,Amma idan 12 ta wuce Bata bu'katar abincin

Tashi nayi na fita,Ina sanya kafata a kofar d'akin hawaye suka fara bin fuskata,cikin sauri nayi gaba ba tareda na jira Saleh ba

Ina shiga gida na goge fuskata cikin sauri,shigowa Saleh yayi damuwa karara a fuskarsa,kafin yayi magana nace

"Dan Allah ka samo min cow leg yanzunnan saboda na daura yayi laushi kafin gobe"

Hugging Dina yayi sosai a jikinsa Yana shafa bayani,a hankali ya furta "I'm sorry"

Wasu hawayen naji na danne na kakalo murmushi nace

"Laifina ne,itama uwace bai Dace Ina sa insa da ita ba,yanzu dan Allah ka samo min cow leg d'in"

Amsawa yayi da toh sannan ya sakeni ya fita,zama nayi Ina tunanin yanda zanyi,Nan dabara ta fadomin

Jika shinkafa nayi na fara shirya abubuwan da nake bukata na miya,na Gama hada komai Saleh y kawomin cow leg d'in na daurashi a pressure pot

Kafin na kwanta bacci saida na had'a miyar wainar na sanyata a fridge sannan na Nika shinkafar a blender na hadata na rufe

Da safe 10am na fara soya wainar,kafin 11 na Gama kasancewar kad'an nayi,Domin Sam waina ta fita a Raina daga jiyan

Ina Gama soya wainar na bawa Saleh instruction na yanda zai dumama miyar na bashi flask din da zai zuba abincin a ciki na fice cikin sauri

Na kuwa yi sa'a 12:10 na shiga class din,Daidai lokacin da malamin ya shiga, addu'a na dinga yi Domin duk na rude,cikin taimakon Allah nayi Amma ba yanda naso ba,nasan bazaifi rabin mark Zan samu ba

Mun fita sallar azahar Naga text din Saleh. _idan kin tashi ki kirani zanzo na daukeki😘😘_

Ok na tura masa na zauna muna Hira Kan presentation dinmu,cikin hirar kawata Fatima take cewa

"Wato yarinyarnan aure ya rud'aki ko?presentation dinnan da kyar kikasha,Kar fa aure ya fara interfering da karatunki,bakiga yanda Kika shigo ba firi firi kamar an koroki"

Murmushi nayi na d'auko powder na saka na saka lip balm na gyara hijabina nace

"Yanzu fa?"

"Ko kefa,har kinyi kyau dake" sa'eeda ta fad'a, mu ukunnan haka muka fara karatu tun shekarar farko,gamu a ta hud'u muna jiyo kamshin gamawa

Zuba tagumi fatima tayi ta kalleni tace

"Yanzu fa Nan da shekara sai mu ganki da jaririya ko jariri ko?"

"To me Zan jira?karatu ai yazo gangara yanzu ko da rarrafe ma.wuce da yardar Allah,Kuma kinsanni,wallahi banki wata Tara ma na haihu ba,Allah Allah bake kawai na ganni da baby Nima,na gaji da d'aukan na mutane"

Sa'eeda na Danna wayarta tace

"Nikuwa auren nawa ma sai mun Gama Domin bataso na haihu a school wallahi,Dame zanji?rainon yara ko na uban yaran ko kula da kaina ko Kuma karatun?bazan iya ba,da na Masa bayani yace shima yafiso idan na gama na samu nutsuwa sai ayi auren mu more soyayyarmu"

Itama Fatima cewa tayi

"To ai ko ni da zaai aurena next year Kinga dai muna final year,planning zanyi Kuma munyi magana ma ya amince cewa nayi,idan na Gama karatuna sai na haihu na samu lokacin kaina da na baby da na mijina,kema kiyi Mana bilkisu,haihuwa a nursing wahala ce kina ganin yanda suke fama"

Nikuwa ko a jikina nace

"Haihuwa rahama ce wallahi,ba abinda zanyi gara nayi na huta,ko zanyi planning sai na haifi daya,Naga kafin yayi shekara na samu wani cikin to anan ne zanyi planning,Amma for now zagewa zanyi na day ciki Nima na ji Dana ko yata a hannuna"

Dariya sukayi sukace

"Mayyar yara kenan,to Allah yasa 9months ki haihu dai kowa ya huta,na tabbatar ma kina haihuwa idan kikaji wuyar zakice bazaki sake ba sai bayan shekara biyar"

Ban amsa musu ba na Kira Saleh nace na Gama,sanarmin. Yayi Yana cikin school din na fito,kwatantamin inda yake yayi naje Amma Banga alamun motar Yaya ko Kuma adaidaita sahu ba,waiwaye nake nace

"Kana Ina ne ban ganka ba"

"Ganinan kina kallona Mana" ya fad'a cikin wayar Yana dariya,sake waiwayawa nayi ban gansu ba na kalli motocin dake gabana,d'aya ce a kunne wata VIBE,

"Daga Ina kake ne?"

"Ina cikin motar da Kika kurawa Ido matar salihu,matso kusa ki gani" ya fad'a tareda le'ko kansa ta glass din motar,cikeda mamaki na nufi wurin motar,savuwa ce dal Domin ko ledojin kujerar baa cire ba,kallonsa nayi zanyi magana yace

"Shhhhhh,kar kice komai,mota dai tawace sauran bayanin Kuma sai munje gida,shigo muje"

Shiga nayi na zauna da na bud'e Baki zanyi magana sai yace "shhhhhh"

Muna Isa gida ya ajiye motar muka nufi wurin hajiya,ji nayi kaman na zauna a bakin motar Amma na shiga Ina Jin darr a Raina

Daga yanda Naga Saleh ya kalli flask din abincin dake palon nasan da matsala,kallon flask din nayi na gansu Babu alamun an taba,bedroom din hajiya ya nufa ya kwankwasa ta fito fuskarta da annuri,tana ganinmu ta hade rai

Murmushi yayi yace

"Hajiya mota ta ce dama nazo ki saka mata albarka"

"Mota?yaushe kayi mota?"

Sosa keyarsa yayi yace

"Hajiya....yau dai na karbota Amma tun kafin biki na bada kud'inta,"

"Shine Kuma baka sanarwa kowa ba ko?kaje kayi gaban kanka ka sayi mota,Saleh idan kacemin kanada kud'in sayen mota zan kwace ne ko Zan hanaka?"

Sunkuyar da Kai yayi yace

"Ba haka bane hajiya,kawai naso na muku surprise ne,Kuma kud'in na sanar Miki da samunsu,sannan na sanar Miki cewa inaso na sayi mota a lokacin"

Zama tayi tace

"Yayi kyau ai,wadda ta cancanta ta sani ai tasani,jeka Allah ya tsare" ta karash maganar tana kallona

Tsayawa mukayi kaman wadanda aka kafe,bansan kaikayin bakin da ya kaini magana ba nace

"Hajiya kiyi ha'kuri,wallahi Nima yanzu na sani da ya daukoni daga makaranta,Dan Allah kiyi ha'kuri"

Kallo ta watsomin Wanda saida naji fitsari ya kamani,nuna flask din da Saleh ya Kai Mata abinci tayi tace

"Wannan shine abincin da Zaki kawowa uwar mijinki ko?saboda nace ki kawomin abinci 12 shine Kika kawomin sassanyar waina,sannan kikayi Miya da tafarnuwa, saboda karatunki yafi iyayenki ko?ko ni ban haifeki ba ai na haifi mijinki,banacin tafarnuwa d'auki abincinki ki koma dashi"

Dur'kusawa nayi nace "kiyi ha'kuri hajiya,wallahi ban saka tafarnuwa ba ko kad'an,"

"Nayi karya to"

Cikin sauri nace

"Hajiya ba haka nake nufi ba kiyi ha'kuri"

"To me kike nufi?nace abincinki da tafarnuwa kincemin Babu,kin karyatani gaban Dana Kuma mijinki,kinyi daidai ai,ku fice ki bani wuri,idan har kinsan Abincin da Zaki dingamin zai dinga batamin rai Kuma ki Kare da kallon tsufana ki cemin makaryaciya to ki barshi banaso"

Kwalla naji ta zubomin na goge nace

"Hajiya Zan kiyaye,kiyi ha'kuri Kimin afuwa,me Zan dafa Miki gobe?"

"Saboda na fad'a kice na Baki wahala saboda bana sonki?ki dafamin duk abinda ranki keso tunda Naga karatunki yafi Mahaifiyar mijinki,tunda bani da girman da Zaki kawomin abinci da kanki saidai ki baiwa mijinki ya kawomin"
"ku fitarmin Mana kun tsayamin a ka"

Fita mukayi Ina ri'ke da flask d'aya Yana ri'ke da d'aya,ya Usman da uncle Hashim na gani tsaye gefen motar sunata yabawa,gaidasu nayi da kyar sannan na wuce cikin sauri

Ina shiga tsakar gida na ajiye flask din a gaba na zuba Masa Ido nayi tagumi,bud'e miyar nayi na dandana,Ni nasan ban saka tafarnuwa a ciki ba

Kuka sosai na fara Ina tuna maganganun hajiya meyasa takeson saka iyayena a ko yaushe

Maimakon naji Ina bu'katar cin abinci sai naji abincin ma ya fit daga Raina,wainar da na kusa rasa maki Mai yawa a kanta gatanan hajiya ko tabawa batayi ba ta dawomin da ita

Palour na koma na hau kujera na kudundune Ina kuka,yanzu haka zanci gaba da rayuwata?me Zan yiwa hajiya ta Soni ko ta Dena min wannan tsanar

Qarar wayata naji Ina dubawa Naga mamana,goge fuskata nayi na saita kaina sannan na amsa Kiran,dukda haka Ina magana tace

"Mura kike ne naji muryanki haka?"

"Eh mama,yau da safe na tashi da ita"

"To Allah ya sauke,Kisha magani,ya abokan zaman naki?"

Dariya na kakalo nace

"Kai mama kaman wasu kishiyoyina?duk suna lafiya na dai shiga mun gaisa dasu"

"To yayi kyau,a zauna lafiya sannan cikin mutunci,ya ita Mahaifiyar tasa?"

Ambato hajiya da mama tayi kadai yasa naji kwalla na neman zubomin

"Itama Tana lafiya Lau,dukkansu alhamdulillah basuda wata matsala dukda Yan uwane"

"To Allah ya Kara muku zaman lafiya,ga yayanki yace na gaidake"

"Mama ki fad'a Masa fushi nake dashi,tunda yaki zuwa ganina"

Dariya mama tayi tace

"Wannan ragon?to ai yana Nan saura kiris yayi Kuka saboda Babu ke a gidan,har wani rama yayi a kwana ukunnan"

Murmushi nayi inajin kewar gida na kamani nace

"To mama kice shima ya fito da Mata kawai a kaishi ya cika Miki gida,ai na kusa zuwa insha Allah"

Sallama Saleh yayi na amsa,mama na Jin haka itama tamin sallama ta katse Kiran

Gyara zamana nayi ya zauna gefena,hannunshi ya Sanya a kafadata ya Jani jikinsa yace

"Kuka kikai ko?"

Shiru nayi Domin ba sai na fad'a ba daga ganin fuskata yasan Kuka nayi

Shafa bayana yake cikin lallashi yace

"Laifina ne da ban sanar dake hajiya Bata son tafarnuwa ba,I'm sorry,nasan hajiya nada fad'a Amma kema duk abinda zai hadaki da ita ki kauce Masa kinji?"

Gyad'a Kai nayi Domin na lura ya fara goyon bayan mahaifiyarsa,hawaye ne ya sake gangaromin nace

"Baka sanarmin yanayin da zan shigo ba da na shiryawa tararsa tun a waje,kaga fa duk Yan uwanka basa Sona"

Dagoni yayi ya d'aura hannunsa a lips Dina yace

"Karkice haka star shine,Yan uwana Ni suke Jin haushi saboda na'ki karbar zabin da hajiya ta yimin,Amma a hankali zasu karbeki na maki wannan al'kawarin,Dan yimin dariya Mana nagani"

Dariyar ce ta kwacemin yaja kumatuna yace

"Ko kefa Yar matata ta kaina,zanje shago yayanki ya kirani yace ya koma gida,yara ne kawai a wurin"

Tashi nayi na cire hijabin jikina nace

"To saika dawo Allah ya dawo dakai lafiya,Amma Dan Allah ka fita da wannan

4 / 41