NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   33 / 41

96K to 99K   out of 120.7K words

amma zaiyi maganinsu ne, mota suka d'auka ba'a saniba ita kuma Mum bataso ta musu fad'a kinsan sune auta".

Ko da muka je gida jansu Mum tayi tace "ku barsu su huta anjima sai kuje".

"Mummy dan Allah labarin Dubai kawai zata bamu".

"Saboda baku ta'ba zuwa ba? Ku wuce mu tafi gida" Mum ta fad'a tareda jan hannayensu, gidanmu muka nufa muna zuwa Aliyu ya shiga wanka, kwanciya nayi kafin ya fito na fara bacci.

Tashina yayi na shiga wanka saidai gaba d'aya 'kamshin toilet d'in baimin ba, sabulun da na d'auka ma sai naji yana neman sani amai, wankan gaba d'aya banason yi haka na watsa ruwa a fuskata na fito na zura kayana na koma bacci.

*********
*SALEH*

Bacci ne ya d'ebeta bayan ta gama koke kokenta taga Saleh yayi mata banza, tunda yayi mata sannu sau d'aya yayi kwanciyarsa sai bacci, takaici ya mata katutu domin ita fa ba haka taji ana yi ba, kamata yayi ya rungumeta yayi ta rarrashinta bazaiyi bacci ba ma har sai tayi, yana shafa ta Yana I love you thank you, amma dan wula'kanci ya kama wuri ya kwanta sai baccinsa yakeyi.

Kafin tayi baccin ya juyo sai d'aya ya dubata, bayan ya tabbatar ba wani matsala dake bu'katar kulawa ya koma baccinsa, tunaninsa idan ya ta'bata zata tsorata ne shiyasa ma ya barta baisan hakan haushi ya bata ba.

Da safe shi ya shirya musu breakfast sannan ya tasheta yace zai fita ta tashi tayi breakfast, amsa masa tayi da to ta koma baccinta ya fita.

Haka yayita hidima da ita kusan kwana uku har saida ya gaji ya rabu da ita, zamansu ya canza sun fara treating juna a matsayin mata da miji amma babu wata soyayya ko sha'kuwa.

Saleh ba shirin fita taje ta sameshi tace "honey zan fita zanje asbiti".

Kallonta yayi gata dai lafiyarta 'kalau yace "meke damunki zakije asbiti".

"Jikina ne nakejin ba dad'i sosai kamar dai ciki ne dani shiyasa nakeso naje asbiti a dubani".

Tashi yayi cikin sauri yace "muje na kaiki".

Suna tafe Bilkisu ce kawai a ransa yana tuna irin gwagwarmayar da sukayi a kan samun ciki, ji yake ina ma Bilkisu ce ta kawo masa wannan labarin, hango murmushinta yake yayin da take sanar mana wannan magana, hango kansa yakeyi suna celebrating tare, meyasa 'kaddara zata masa haka?

Bayan an dubata aka samu positive, dukda cewa Saleh yayi farin ciki amma ba kamar dai ace Bilkisu bace.

Suna biyo hanya ta fara nuna abubuwa tana cewa ya siya mata, a 'kofar gida ya ajiyeta ya juya.

Shiga tayi da ledarta cike da kayan kwad'ayi suka had'u da Hajiya, fara'a Hajiya tayi ita kuwa Hadiyya ta sha kunu.

"A'a ina kukaje haka da safiya?" Ta fad'a tana kallon ledar hannun Hadiyya, matsar da ledar Hadiyya tayi tace "asbiti mukaje ance inada ciki".

Yage baki Hajiya tayi tace kai masha Allah alhamdulillah, ga inda ake abun arzi'ki yaje ya mannewa juya gara ma da na rabashi da ita gashi kafin aje ko ina Allah ya bashi arzi'ki, akwai wani abu da kikeso ne na miki?".

"Bakomai amma idan inaso zan miki magana". Tana gama maganar tayi gaba, ledar hannunta ce ta yage rake da d'ata da gyad'ar da aka siya mata suka zube, tana ganin Hajiya na kallon d'atar ta kau da kanta ta kwashe abinta a mayafi tayi gida.

Part d'in Sultana ta shiga ta sameta tana yiwa Huda kitso, gaisawa sukayi ba sakin fuska dukda haka ta zauna har aka gama yiwa Huda kitso.

Sultana na 'ko'karin tashi ta fara aikace aikacenta Hadiyya tace "um maman Ahmad tambayarki nazo yi".

"Akan me?"

"Akan tsohuwar matar Saleh, ina son nasan komai a kanta".

Dariya Sultana tayi tace "nidai abu d'aya zan fad'a miki, matar Saleh macece mai ha'kuri da kirkin da ban ta'ba ganin wata mace dashi ba tunda nake, a gidannan nice aminiyarta sauran kuma kije ki tambayi jumana ko Hajiya da kanta inada abin yi".

Shigewa Sultana tayi ta barta a zaune, tashi tayi ta nufi part d'in jumana itama dai bata sakar mata fuska ba domin bata son raini, bazata tsaya tana kula wannan 'karamar yarinyar ba.

Ganin dai babu biyan bu'kata ya sanya ta nufi wajen me gayya me aiki wato Hajiya, tayi sa'a kuwa kursum tazo.

Bayan sun gaisa ta tambayi Kursum wacece Bilkisu, gyara zama tayi tace "wannan munafukar? Ai Allah ne yayi mana maganinta tazo ta nemi ta mallake Saleh saida muka nuna mata muma fa ba a zaune muke ba, ga masifar naci duk abinda ake mata saboda ta fita da kanta ta ki saida ya saketa dan dole....."

Babu pull stop ba comma Kursum ta dinga zayyano ba'kin Bilkisu, duk wannan labarin abubuwa biyu Hadiyya ta fahimta, irin tsananin soyayyar da Saleh ke yiwa Bilkisu da kuma tsanar da Hajiya tayi mata, hakan na nufin yanzu ita ce 'yar gaban goshin Hajiya, sannan ta lura da yanda Saleh ke jin maganar mahaifiyarsa wanda ta d'auki hakan a abinda ya Sanya baya sonta yanda ya kamata, zata san yanda zatayi ta janyo Saleh gareta ita kad'ai ba tareda ta hadashi da wata ba ko da kuwa mahaifiyarsa ce.
50

Ranar a wurin Hajiya Hadiyya ta wuni, saida taci abincin rana tayi takeaway na dare sannan ta koma part d'inta.

Washegari da wuri ta tashi ta zauna ta saka tv a gaba har Saleh ya tashi, saida taji tashinsa sannan ta nufi toilet ta fara kakarin amai kamar da gaske.

Fitowa tayi cikin kalar tausayi tace "Honey bazan iya girki ba, ina saka 'kafata a kitchen nake jin amai ko zaka kar'bo mana a wurin Hajiya? Gaba d'aya banason ganin kitchen d'in ma dan Allah".

Rufe kitchen d'in yayi ya fita kar'bo musu abinci a wurin Hajiya, dawowa yayi da d'umamen tuwo ta kalla a yamutse tace "wayyo Allah na d'aukeshi daga gabana banason gani".

Kallonta yayi shi dai baiga wani alamun ciwo a tattare da ita ba saidai maybe haka masu cikin suke, duk 'ko'karinta na yin kalar ciwo ta kasa.

D'aukan tuwon yayi yaci yace "me kikeso?"

"Koko nakeso da 'kosai".

"Shikenan bari na duba waje idan akwai sai na siyo miki".

Tashi yayi zai fita tace "a'a dan Allah banason na waje na Hajiya nakeso, na waje amai zai sakani".

Kallonta yayi yace "Hadiyya aikin 'kosai aiki ne mai yawa sannan kinga gari ya jima da wayewa, ki bari na siyo miki gobe sai na fad'a mata da wuri idan kinaso".

Hard'e hannayenta tayi ta turo baki tace "barshi banaso".

Komawa gefenta yayi ya zauna yace "kar kiyi fushi mana, naga Hajiya ta tashi da shirin funkaso ne kar na sake had'ata da wani aikin".

"Shikenan naci funkason kaje kayi wanka saboda lokaci ko?"

Yana tafiya wanka ta fita harda saurinta, tana shiga part d'in Hajiya ta fashe da kuka.

"A'a Hadiyya me kuma ya faru kike kuka?".

Cikin kuka tace "Hajiya Saleh baya sona ko kad'an, na fad'a masa 'kosai nakeso kuma na gida amma wai saidai ya siyomin, kuma ni banason na waje, a 'karshe ma cewa yayi saidai naci kaina bazai ro'ke ki kimin ba yayi tafiyarsa ya barni gashi yunwa nakeji".

"Kai Saleh me yake damunsa ne? Anya asirin da yarinyarnan ta masa kuwa ya sakeshi? Kiyi ha'kuri zan masa magana kuma indai 'kosai ne kin samu yanzunnan zan wanke waken dama an 'barzo min shi, zauna anan zaizo ya sameni, ace amanar Allah mutum ya kasa ri'keta? Ko ba dan ke ba ko dan wannan juna biyun ai ya tausaya miki, zaizo ya sameni ne". Hajiya ta fad'a tana nufar kitchen, kwanciya Hadiyya tayi akan kujera tace

"To Hajiya tun yanzu ya fara nunamin haka ina ga ciki ya tsufa? Idan na haihu ma zai iya kashe jaririn tunda ya nunamin shi baya son cikinnan".

Dawowa Hajiya tayi a fusace tace "shi yace bayaso?"

"A'a Hajiya kawai naga yanayinsa, amma dan Allah Kar ki fad'a masa sai ya 'kara jin haushina".

"Shikenan zauna ki huta zanyi magana dashi".

Tana zaune hajiya ta wanke waken ta markad'a a blender duk 'yar lele na kwance, ta gama markad'awa Saleh ya shigo.

Yana sallama Hajiya ta balbaleshi da masifa "Allah ya wadaran halinka, shekara nawa kayi kana neman haihuwa Allah ya hanaka yanzu da ka samu shine zaka fara wasa da damarka ko? Saboda kaga yarinya mai ha'kuri kake wula'kantata, me yarinyarnan ta tsare maka? Meyasa kakeson azabtar da rayuwarta, kai kenan daga wannan sai wancan ko imani baka dashi? Ka duba juna biyun dake jikinta ki dan shi ai ka tausaya mata, daga yau yarinyarnan tace tana son abu ka hanata wallahi sai na 'bata maka".

Shiru yayi har Hajiya ta gama banbanminta sannan ya fita yana tunanin me yayi da za'a masa fad'a haka? Ko dai 'kosan da tace tana so ne ya janyo haka? Hadiyya dai bata rabuwa da drama.

Yana fita Hadiyya tace "Hajiya wannan bilkisun da ya aura a baya anya ba 'yar shed'anu bace? Nifa gani nake ita ta mallakeshi wallahi ta hanashi sakat, wani lokacin yana bacci saidai kiji yana ambatarta na rasa dalilin hakan, ko kuma idan zai kira sunana ya ambaceta, ni fa gani nake sallah ma ba dai-dai yake ba saboda sai inji kamar yana fad'an sunanta a sallah, anya baza'a nema Masa magani ba? Indai ya zauna a haka zaiyi ta wula'kantani ne".

Kafin Hajiya ta amsa maimuna ta shigo a gigice, a firgice suka kalleta Hajiya tace "menene hakan? Lafiya kuwa?".

Wayarta ta ciro daga jaka hannunta na rawa ta danna ta nuna musu, zubawa wayar ido Hadiyya tayi tace "nifa banga komai ba".

"Hajiya wai tsabar wula'kanci sa'idu aure zai 'kara? Ashe duk wahalar da nasha akan Amir yana cemin baida kud'i kud'in aure yake tarawa, jiya na d'auki wayarsa ina bincike kawai naga hoton wata a take ya sanarmin ita zai aura kuma ba wanda ya isa ya hana auren".

zama Hajiya tayi tace "to meye abin tashin hankalin?".

"Hajiya ga tashin hankalin nan kina gani? Kishiya bala'i ce masifa ce wallahi, mutumin da watarana yake fita ya barmu babu abinda zamu ci shine yake zancen sake aure? Rashin lafiyar Amir gaba d'aya dubu biyar ya kashe duk sauran ku kuka biyamin a hakan zaiyi aure? Wallahi Hajiya a san abin yi bazan bari yayi aureba, kuma wadda zai aura da gani tangararriyar 'yar iska ce".

Tashi Hadiyya tayi ta nufi kitchen tana 'ko'karin fara suyar 'kosai, maganar Hajiya taji ta fara faking amai tare da fita daga kitchen d'in, zama tayi gefen Maimuna da ke ta sambatu ita kad'ai amma batace mata komai ba.

Bayan d'an lokaci Hajiya ta dawo da 'kosai a faranti, zama Hadiyya tayi ko a jikinta ta fara cin 'kosan yayin da suka ci gaba da maganarsu, cikin 'kaguwa Maimuna tace "Hajiya wannan mutumin da mukaje wajensa yayi mana maganinta mayyar can da farko wajensa nakeso naje, amma banida kud'i shiyasa nazo ki bani".

Shiru Hajiya tayi tace "to ai nima d'an kud'in dake hannuna a aurennan duk ya 'kare, amma anya zaki koma wajensa? Kina gani dai itama aikin nata babu wata riba tunda bayan cutar da tayi saida ta dawo".

"Hajiya shiyasa nace miki mayya ce amma yanzu ba ta fita dan kanta ba? Kuma bazata ta'ba dawowa ba? Nidai ko wajen su usman ko zayyad ki tambayarmin su bani dan Allah".

"A'a usman Usman shekaran jiya ya kawomin kayan abinci sannan shima zayyad d'in ya kashe kud'i sosai, kuma sun bada gudunmawa 150k dukkansu a aurennan, bazai yiwu na tambayesu kud'i yanzu ba kuma zayyad yayi tafiya usman kuma aikin nasa sai a hankali, bari Saleh yazo mu gani".

Wani takaici Hadiyya taji jin ance minjnta ne zai bada kud'in, duk yanda zatayi ta hana a basu kud'innan sai tayi, ko da kuwa hakan zai janyo rasa abinda ke cikinta ne sai tayi, zama tayi ta fara tsara 'karairayi a ranta har ta samu shawara tsayayyiya, tashi tayi ta nufi band'aki ta fito tace da Hajiya  "Hajiya zanje asbiti banajin dad'in jikina, marata ciwo kuma yanzunnan ya fara".

"Subhanallah to bari na d'auko mayafina muje Allah yasa dai lafiya".

"A'a Hajiya kiyi zamanki wallahi yanzunnan zan dawo nasan ba wani abu bane babba, sannan ga Maimuna ya kamata ki zauna da ita".

Bata jira me Hajiya zata ce ba ta fita, part d'inta ta nufa ta zari mayafi ta d'auki kud'i a ma'ajiyar Saleh ta nufi gidansu, da uwarta suka gama tsara abunsu.

Wani 'karamin asbiti suka nufa wanda suka san za'a musu abinda sukeso, asbiti ne da ya shahara da zubar ma da mata ciki, bayan sun gama yiwa likitan bayanin abinda sukeso yayi da kuma kud'in da zasu bashi Hadiyya ta kira Saleh, likitan ne ya kar'ba yace.

"Good afternoon sir, matarka ce Hadiyya Bello tazo asbiti tayi complain ciwon mara, da na duba sai naga tana critical condition babynta a bayan mahaifa yake yanzu haka tana tsananin zubar da jini, mun shiga da ita theatre za'ayi aiki saboda muna gab da rasata idan ba'a yi aiki an maida babyn cikin mahaifa ba, ana bu'katar 110,000 naira, mahaifiyarta tayi signing kawai ana bu'katar amincewarka ne".

Cikin tashin hankali saleh yace "wani asbiti ne? Ganinan zuwa".

Kafin ya masa kwatancen asbitin ya kashe wayar gaba d'aya, kira Saleh yakeyi amma ta'ki shiga hankalinsa yayi matu'kar tashi, kiran Hajiya yayi itama tace bata san ina taje ba, kiran number Ammy yayi itama not reachable babu.ahir.

Sai bayan awa d'aya sannan Hadiyya ta kunna wayarta ta sanar masa tana gidansu har an mata aikin ta koma gida.

Cike da damuwa yaje ya sameta tana kwance a lullu'be, zama Ammy tayi ta dinga shirga masa 'karya sannan tace ya kamata da sun fita su wuce gida domin Hadiyya ta jigata, kud'in kuma ga account number d'in likitan ya tura masa.

Haka kuwa akayi a take ya tura kud'in sannan ya d'auki Hadiyya suka tafi gida sai dafe ciki takeyi, saboda abin nasu yayi dai-dai saida aka d'an yanka cikinta kad'an aka nad'e da bandeji duk dan ya yarda, murna Hadiyya keyi a cikinta domin burinta ya cika, yanzu sai ta gani idan Hajiya nada rashin imanin da zata kar'bi kud'i a hannunsa.

**********
Da'kirewa nakeyi yana 'ko'karin jana zuwa bathroom, tuni idona ya ciko da 'kwalla amma yau Aliyu bai ko tausayamin ba, kwanana hud'u kenan babu wanka kafin kuce 'kazama ba laifina bane, na tsani 'kamshin sabulu, man shafawa, turare kai hatta towel d'in wankan na dena d'aurawa, saboda haka idan na shiga sai an d'anyi kwaskwarima da ruwa na fito, yau dai dubuna ta cika Aliyu ya kamani.

Tattaro 'karfinsa yayi sai gani a kafad'arsa for the first first time, tsoro ne ya kamani yace "kina motsi zamu fad'i fa".

"Dan Allah ka bar wankannan yau Allah gobe nayi al'kawari zanyi kaji? Wallahi gaba d'aya 'kamshin bathroom d'innan bana sonshi ka fahimceni mana".

Ajiyeni yayi ya rufe 'kofar da key sannan ya zubamin ido, hard'e hannunsa yayi a 'kirjinsa yace "haba Bilkisu kwana uku ba wanka bai isheki ba sai kin 'kara da na hud'u? Wato shiyasa kika koma wanka da hijab saboda ki wanke fuskarki ki fito ban ganeba, sorry to say amma a kwana biyunnan naji jikinki ya d'an fara canzawa, look idan kikayi wankannan yau gobe na amince kiyi fashi sai kiyi jibi, amma ko d'an deoderant kina shafawa mana".

Wani kallo na wurga masa, a ta'kaice dai so yake ya cemin ina wari amma ni ba abinda nakeji, dukda daud'ar na damuna amma sam banajin wani odour a jikina.

Had'e rai nayi nace "ka fito kace min wari nake kawai".

"Kai Bilkisu you are making this hard, ko ma mene dai idan kinyi wanka sai muyi idan ma rufeni da duka zakiyi sai kiyi amma bazaki fita daga bathroom d'innan ba sai kinyi wanka".

Hawaye ne ya fara bin fuskata abinka da hormones d'in me ciki, kuka na fara nace "duk zamana dakai baka tsiri cewa ina wari ba sai yanzu, sai yanzu ka tsiri ka fara wula'kantani ka kirani da 'kazama".

Dur'kusawa yayi a gabana ya saka hannunsa ya goge hawayen yace "bance ke 'kazama bace Bilkisu kinada matu'kar tsafta, kawai cewa nayi ya kamata kiyi wanka ko dan kiji dad'in jikinki".

"Ni inajin dad'in jikina a haka meyasa kakeso dole sai nayi wanka? Wallahi na tsani sabulunnan da man da nake shafawa da turaren da komai ma me 'kamshi".

"Duk yau zan canza miki su dake zamu fita ki za'bi wanda kikeso, for now kiyi wankan tukuna please".

Towel ya mi'komin nayi cilli dashi domin banason 'kamashinsa, shiga yayi ya kunna shower ba fara kici kici da 'kofar fita, kamoni yayi ya turani a cikin shower d'in ya janyo 'kofar, ruwan dukana yake ina dukan glass door d'in har na ha'kura na tsaya ruwan na dukana tun daga kaina banyi yun'kurin d'aukan sabulu ko sponge ba.

Idona a rufe naji alamun ya bud'e 'kofa, ban bud'e idona ba naji yayi wrapping hannunsa a cikina yana shafawa a hankali, kansa na wuyana, kissing wuyana ya fara tareda shafa cikina zuwa 'kirjina, ajiyar zuciya na sauke na sake manne bayana da jikinsa, abinda ya kamata yayi kenan ba wai ya cicci'boni ya kawoni ba.

Hannunsa ke descending zuwa 'kasa-'kasa, cikin kunnena yace "sorry baby" sai jin soso nayi a jikina, struggling na fara na gudu amma ina, ya kamani ram.

Saida ya wankeni tas har round uku, ji nake kamar bazan iya numfashi ba domin sabulun ya gama shiga kaina, ganin haka yasa ya ha'kura da wankan a hankalin nace "mugu".

"That's me" ya fad'a tareda fito dani daga shower d'in, towel ya yafamin na cire na yar na d'auki zanina na d'aura, shi kansa zanin rabonsa da wanki.....Kar dai a tona domin 'kamshin omo da sabulun wankin ma matsala ne a gareni.

Bai ma yi gangancin cewa na shafa mai ba, wardrobe na nufa na fara laluben kayan da zan saka wanda suke sababbi, jikina har wani sakayau yayimin gaskiya

Ina d'auko kayan ya kar'ba ya ajiye a gefe, kallonsa nayi ina 'ko'karin fara mita ya had'e lips d'insa da nawa, zanin ya kunce ya ri'ke gefe da gefen a hannunsa yace "ko baki so na 'karasa abinda na fara a can?"

Amsarsa itace pushing d'insa da nayi zuwa gadon, dariya yayi yace "I love this side of you".

"Ba wai na huce bane ba, I will deal with you later". Na 'karashe maganar ina attacking lups d'insa.......

Washegari da kewar gida na tashi sosai na kira Mama muka sha hirarmu, har yanzu ban sanar mata inada ciki na so nake saidai ta gani kawai, Allah yasa ranar da zanje naga Saleh, I will rub it on his face domin a yanzu cikin ya fito sosai bazaka

33 / 41