NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   40 / 41

117K to 120K   out of 120.7K words

nima? Duk wanda ya raina uwar wani hausawa sunce bai d'auki tashi da muhimmanci ba, kin bani kunya Hadiyya".

Kuka Hadiyya ta fashe dashi zuwa yanzu hankalinta ya tashi, dur'kusawa tayi tace "Ammy dan Allah ki yafemin banyi haka saboda na baki kunya ba dan Allah kiyi ha'kuri".

"Zanyi ha'kuri ne kawai idan kika amince da laifinki kika sanarwa da Saleh, ki kuma kar'bi duk hukuncin da zai miki, karki manta ke fa uwace kin haifa, ki duba ciwon da zakiji idan uwar mijin tasleem ta dakeki ta dalilin 'yarki, ki kar'bi laifinki da hukuncinki".

Fita Ammy tayi ta barta tana ta share hawaye, sai yanzu ta san cewar ta wuce gona da iri kuma gaskiyar Ammynta ne, uwa uwace ko da mahaukaciya ce bazata so a ta'ba lafiyar Ammynta ba meyasa ta aikata hakan? Ta san saki kawai zai rabata da Saleh shikenan tayiwa aurenta, nadama sosai takeyi tana kuka yayin da ta d'auki waya ta kira Saleh.

Yana d'agawa tace "Honey, dan Allah kazo gida yanzu inada magana dakai ta gaggawa".

"Hadiyya me ya faru?"

Bata amsa masa ba ta katse kiran ta zauna ta fara preparing kanta for the worst.

Yana tashi daga aiki kuwa ya biya, tana zaune bakin katifa yayin da yake zaune a kujerar dake dakin.

"An sanar maka abinda ya faru a gida ko?"

"Maimuna ta sanar dani, amma inaso naji ta bakinki".

Hawaye ke zuba daga idanunta tace "duk abinda suka fad'a gaskiya ne, naje har gidanku na daki Hajiya da Maimuna.....da dorina" ta 'kare maganar tana shesshe'kar kuka "ka yankemin hukuncin da ya dace domin na fahimci laifina na kuma kar'beshi duk abinda ka yanke zan kar'ba Saleh, abinda nayi babu mai hankalin da zai aikata, na wula'kanta mahaifiyarka bana tunanin ni za'a yiwa tawa haka".

"Hadiyya meyasa kikayi haka?"

"Honey banida dalilin da zan kare kaina, dalilina mara amfani ne shine kawai yanda Hajiya ke son rabani dakai, bayan wannan dalilin bani da wani abu sai son zuciya da raina na gaba dani, kayi ha'kuri dan Allah".

Tashi tsaye yayi tareda dun'kule hannunsa yace "bazan sakeki ba Hadiyya banaso na Saba da saki, amma naji rashin dad'in abinda kika aikata, mahaifiyata ce fa wannan sannan kuma surukarki, aminiya ga mahaifiyarki, ina ganin tafiyarmu tare bazata yiwu tare ba zan tafi ni kad'ai, ki zauna kiyi tunani akan abinda kika aikata sannan ki bawa mahaifiyata ha'kuri, zuwa lokacin da na dawo idan har baku samu fahimta da mahaifiyata ba, ina ganin zan d'auki matakin da takeso domin uwata tafi min kowa a duniyarnan, kin bani kunya Hadiyya banyi zaton haka daga gareki ba".

Ficewa yayi ba tareda ya sake kallon inda take ba, fashewa tayi da kukan nadama tana tunanin yanda zatayi wata hud'u wannan laifin yana cinta, mahaifiyarta na fushi da ita shima Saleh Yana fushi da ita, ya zamar mata dole ta canza halayyarta domin samo soyayyar mutum biyu, Hajiya da Saleh.
"kiyi ha'kuri kinji Bilkisu?"

"Mum komai ya wuce nayi tunani naga hakan da sukayi ba dan su cutar dani bane, sannan kuma ta dalilin haka na had'u dake, twins, Raudah da kuma Dad. Ko wannan ya isa nayi alfahari da auren I think I overreacted back then banso na nuna masa hakan ba".

"Banga laifinki ba idan kinyi fushi domin an miki yawo da hankali amma is it true you are not comfortable around us?"

Sunkuyar da kaina nayi nace "sometimes, amma Mum a cikinku banajin komai, kawai idan wasu suka zo ne nakanji am out of place".

Dafa kafad'ata Mum tayi tace "bai kamata ki dinga Jin haka ba Bilkisu, you are one of us, da ace mahaifinki yana raye yana nan kamar mu, ke mutum ce haka muma mutane ne karki bari wani abu namu ya canza miki d'abi'arki, muna sonki ne a yanda kika ba wai yanda zaki koma ba".

"Nagode Mum amma gani nake kamar ina tauye Aliyu, ya aureni ne saboda yana tausayi na kuma hakanan yake treating d'ina tunda mukayi aure, zaman mu zaici gaba da kasancewa haka Mum?".

"Bilkisu dukda ke abinda kike gani kenan amma bayan tausayi Aliyu ya damu dake, kuma ko da bai nuna miki ba yana sonki kai ko baya sonki mu muna sonki, zanyi iya 'ko'karina dan ganin kin zauna tare damu ko da bakyaso, Bilkisu idan kin rabu da Aliyu ina zaki koma? Destiny ya nuna ke da mijinki na baya bakuda 'kaddarar kasancewa ma'aurata na tsawon lokaci just accept it like that, zamu baki duk wata kulawa da kike bu'kata kuma ni a matsayina na uwa a wurinki bazan ta'ba bari wani abu ya cutar dake ba ko da jinina ne, kiyi tunani"

Ina Shirin tada sallar magrib naji sallamar Aliyu, amsa masa nayi sannan na tada salla yayin da ya nufi twins.

Har na idar da sallah banji kukan twins ba abin ya bani mamaki, bayan na idar da addu'a na juya na kallesu, cikin sauri naga Aliyu ya 'boye abu a bayansa na tashi na nufeshi, twins na samu sai tand'ar baki sukeyi na kalleshi nace "me ka Basu?"

"Ni? Bakomai yunwa dai kawai naga kaman suna ji". Ya fad'a yana sake 'boye abinda ke hannunsa, rabuwa nayi dashi na juya ina 'ko'karin cire Hijabina, da sauri na juyo na kuwa kamashi dumu-dumu yana lasawa yarana lollipop, seriously yaushe maza zasu girma?

"Ya Aalee!" Na fad'a da 'karfi tareda buga 'kafata a 'kasa, 'boye alawar yayi harda zare ido yace "menene?"

Ji nake kamar na makeshi amma na danne nace "baka san ma me kayi ba ko? Ya zaka basu sweet?"

"Kallo naga sunayi am sure Abdul-malik har zubda yawu yayi, ai Kinga nayi rashin adalcu idan ban Basu ba ko?"

Dafe kaina nayi na kalleshi, ya had'e hannunsa biyu da lollipop d'in a ciki ya turo le'bensa, kasa ce masa komai nayi na kar'bi lollipop d'in na saka a baki na juya.

Saida na ninke hijabina sannan na zauna nace "ka kaini 'kara wajen Mum ko?"

Kansa ya d'aura a kafad'ata yace "more like na kai kaina 'kara wajen Mum, ki yarda dani Bilkisu ina sonki kwanakin da kikayi bakya kulani na shiga takura sosai, please stay with me Bilkisu kinji?"

"Indai zaka dinga treating d'ina kamar matarka ba kamar abin tausayi ba zan zauna da kai".

"Nagode nagode nagode Allah ya barmu tare" ya fad'a tareda tura ni kan gadon, tickling d'ina ya fara ina dariya a haka Dan hatsaniyar namu ta wuce.

Madara na had'awa twins muka d'aukesu muna basu a tare, waya ya ciro yayi mana pic ba tareda na lura ba, ture wayar nayi ya bo'ye yana min gwalo, bansan yaushe Aliyu zai girma ba.

"Hashtag feeding my babies" ya furta yana danna wayarsa, kafad'arsa na ture a hankali nace "Dan Allah ya Aalee kar ka tura wa kowa pic d'innan kalli fa kayan dake jikina".

Maida wayar tashi aljihu yayi yace "dama babu wanda zan turawa tsokanarki nakeyi amma bakiga yanda kikayi kyau ba fa, yanzu dai me ya kamata mu yiwa wannan wajen ya cika?" Ya fad'a yana shafa 'kasusuwan wuyana da suka bayyana, hannuna na saka na shafa nace,

"Inajin dad'in jikina a hakan banaso na 'kara 'kiba a yanzu, idan lokacin 'kibar yayi sai ka nemi yanda za'ayi na ragu".

Sannu-sannu muke bin relationship d'inmu kamar sabbin couples, mun zama friends sosai ta yanda yake fad'amin sirrinsa nima nake sanar masa da nawa saidai ba duka ba wani sirrin yafi a barshi a 'boye, kamar zamansa a turai wanda banaso ko ambata ayi.

Munada differences sosai tsakaninmu wanda ban fahimta ba sai yanzu, a baya danne komai yake yi saboda ni amma yanzu yana bayyana min komai.

"Ina twins" ya tambaya yayin da na shiga gida, bayansa na haye nace "relax mana beb, twins suna wajen su inna kulu".

'bata rai yayi kafin yayi magana nace "na San cewa baka son ina kaisu amma banida wani choice, banaso na shiga wanka na barsu su kad'ai it's not healthy".

"Zamansu a wannan wurin ma is not healthy, ki duba haya'kin dake tashi a wurin sannan su kansu mutanen.....".

Hannu nasa na rufe masa baki nace "su Inna kulu suna da tsafta fiye da yanda kake zato, sannan da shinfidarsu na kaisu dan Allah ka dena damuwa".

Dukda Aliyu baya 'kyamar talaka amma baya so 'ya'yansa suna ra'bar su inna kulu, ta 'bangarena kuwa tamakamon sukeyi sosai.

Twins na 6 months Mum ta tambayeni ko inason na koma aiki zata nema min nace a'a, domin aikina bashida amfani a wannan lokacin, bu'katuna kafin na fad'a an biya min ga kud'in dake shigomin lokaci-lokaci.

Lokacin da na Tara kud'ad'de na da dama na nufi sansanin 'yan gudun hijra na Abuja, na bawa mazansu da matansu jari sannan na siya musu abin sarrafawa na rayuwa.

*5 YEARS LATER*

"Mace da namiji".

"No baby Mace zallah kawai nakeso".

"To namiji da mace".

Kallonshi nayi na koma aikina, kusan 2months kenan yana takuramin akan muje mu sake IVF wai twins sun tsufa tunda har sun shiga school sannan gidan ya fara rashin dad'i, kaicewa maganar nakeyi saidai ya ma'kale kullum sai yayi nace masa mace nakeso yace shi namiji yakeso, ni kuma na rantse bazan sake haifar twins ba wad'annan har yanzu suna bani headache.

"Babyyyy......nifa ba babyn ne banaso ba nima inaso kawai banason na sake twins ne wancan sun bani wahala, sannan kuma idan har zaka amince.... adopting baby nakeso nayi".

Wani kallo yayimin yace "adopting kuma? Kamar yaya? Bilkisu kinsan bakida matsalar bu'katu ko wani abun IVF d'innan minti nawa ne an gama?"

"Ba wai banason aikin bane kawai ladan nake dubawa, instead of mu 'bata kud'inmu wajen neman 'ya ko d'a gasu suna neman taimakonmu, please reconsider this".

Numfashi y sauke yace "Bilkisu ina tsoron halin mutane sannan da halin rayuwa da kuma bakin mutane, ance tsintacciyar mage.....".

"Itace kuwa take mage domin ka tambayi gidajen da maguna suka tsufa a cikinsu zasu sanar maka asalin magennan tsintuwa ce, baby mu muke lalata komai da tunani marar kyau, ka tsarkake zuciyarka na tabbatar idan muka bawa 'yar da zamu d'auko kulawa tsakaninmu da Allah bazata tashi da mummunar manufa a ranta ba".

Wa'azi na dinga yi ma Aliyu har ya amince da murna ta muka nufi orphanage home na Abuja, baiyi min musu ba akan baby girl da nace inaso.

Tunda muka je na lura jikinsa yayi sanyi, bin yaran yake da kallo amma bai ta'ba ko d'aya ba, wata baby nagani da bazata wuce wata biyu ba tana bacci cikin shinfidarta instantly ta shiga raina na d'auketa.

Muna fita na mi'ka ma Aliyu ita ya'ki kar'barta saidai da kansa ya kaimu wajen kayan yara na siya mata wad'anda zasu isheta.

A gidansu Aliyu ma Mum batayi approving completely ba saboda bamu sanar mata ba sannan bata tunanin it's a good idea, a hankali na shawo kansu suka amince da yarinyar da na d'auko mai suna Aisha.

************

Saleh yana shiga gida Hajiya tayi masa magana tace "ka 'karashe mata saki ukun ko?"

"Hajiya.....".

"Karka yimin wata maganar banza marar amfani, yarinya tazo har gida ta daki uwarka bazaka mata saki uku ba?"

"Hajiya bazan iya sakinta da 'yata a hannunta ba, ban san bayan wannan mata nawa zaki sanya na saka ba sannan na tsani kalmar saki, da ace kinada ikon sakin Hadiyya da na baki kin saketa amma bazan iya sakinta ba".

Kuka Hajiya ta fara tace "wato har wata mace tafi uwarka ko? Tazo ta sameka na gama kiwata maka ita sannan tace zata rabani dakai, ta wula'kantani ta cimin mutunci sannan kace bazaka rabu da ita ba? Me ka d'aukeni Saleh?"

Runtse ido yayi domin a wannan karon ya fara karaya, bai san yaushe Hajiya zata dena masa gorin kulawar da ta bashi ba".

Dur'kusa gwiwoyinsa yayi a 'kasa ya dago idanunsa d'auke da hawaye, karo na farko da Hajiyarsa taga hawayr a fuskarsa tun bayan sakin Bilkisu da yayi, muryarsa so weak yace,

"Hajiya wace irin biyayya zan miki ki amince dani a matsayin d'anki? Tunda na bujirewa umarninki sau d'aya rayuwata gaba d'aya ta canza, kin tashi daga uwar da nake zuwa wajenta a duk lokacin da nakeda damuwa, kin tashi daga uwar da nake zuwa gareta a duk lokacin da farin ciki ya sameni ko nake bu'katar walwala, har ta kai ga idan na ganki gabana fad'uwa yakeyi, dan Allah Hajiya ki fad'amin me zanyi na gyara tsakanina dake? Na gaji wallahi, na gama sarewa da samun farin ciki a rayuwata shekara hud'u da d'ori kenan kina nunamin banbanci a cikin sauran 'ya'yanki, meyasa Hajiya meyasa? Idan har auren Sultana zai sauya tsakaninmu ki umarci usman ya saketa walalhi na miki al'kawarin zan aureta indai hakan kikeso".

Jikin Hajiya yayi sanyi kunya ta rufeta, a dalilin son zuciyarta ta sanya Saleh damuwa ta tsawon shekaru, kallonsa tayi taga gaba d'aya ya tashi daga d'an da ta sani, ya tashi daga salenta mai barkwanci mai yawan walwala a fuskarsa, tsufa ya fara bayyana a fuskarsa dukda bai cika koda shekaru arba'in ba, abunda yafi Mata ciwo shine kukan da yake sanadiyyarta, idan har ciwon da yakeji ya kai ga yayi kuka da girmansa a gaban mahaifiyarsa wani irin ciwo yakeji a ransa haka?

Dafashi tayi tace "Saleh tabbas nayi kuskure na kuma so kaina da yawa, gaskiya ka fad'a na tashi daga uwa mafi soyuwa a wajenka na koma wata iri daban, bana haifa maka komai sai damuwa, amma da yardar Allah komai ya canza, na sani cewa na kasance mai sanya ido a duk abinda zaka yiwa iyalinka saboda wahalar da nayi a kanka, na zama mai son zuciya da son kaina amma ka yafemin d'ana, Ina ganin mafita d'aya ce garemu, ka d'auki iyalinka ka nemi wani gidan ka zauna ni zaifi min kwanciyar hankali kaima haka".

"Amma Hajiya banaso nayi nesa dake, inaso mu zauna a matsayin zuri'a d'aya ni da 'yan uwana".

Murmushi Hajiya tayi tace "na sani amma zamanka a waje zaifi alkhairi, ko da na wani lokaci ne kaje ka huta da matarka a wani waje daban nesa daga gareni idan lokaci yayi sai ku dawo ku zauna tare damu, Allah yayi maka albarka".

Baiyi mata musu ba sannan ya kasa d'ago kansa ya kalleta, yanda hawaye ke zuba daga idanunsa haka suke zuba daga idanunta tabbas ta lalata farin cikin d'anta na tsawon lokaci saboda son zuciyarta, amma Hadiyya ta koya mata hankali.

"Kayi ha'kuri da rabaka da Bilkisu da nayi, a yanzu na tabbatar nayi babban kuskure kuma wallahi nayi nadamar aikata hakan, inama Bilkisu tana tare dakai a yanzu da na nemi yafiyarta, Dan Allah Saleh idan akwai yanda zakayi ka dawo da Bilkisu gidannan wallahi zan fi son hakan, son zuciyata yasa na aura maka Hadiyya gashi a kaina 'bacin ran ya 'kare, tazo tayimin dukan da mahaifana basu yimin shi ba a 'kuruciyata".

"Hajiya Bilkisu tayi aure Allah yayi ba matata bace, kiyi min addu'a Allah ya sanya albarka a cikin aurena na yanzu ya bani farin ciki, Hadiyya tayi kuskure mai girma amma ta nuna min tsantsar nadamarta".

Shiru Hajiya tayi alamun batason maganar Hadiyya shima ya ajiye maganar, idan har da Hadiyya Allah ya tsara zaiyi zaman aurensa dole ya rungumi wannan 'kaddarar, amma zaiyi tafiya ya bata dama idan bata canza ba saidai ya rabu da ita.

Washegari da sassafe Maimuna ta tashi tana Shirin fita, kallonta Hajiya tayi tace "ke Kuma ina zaki je da sassafe haka? Ba na hanaki zuwa gidan mijinnan naki ba saboda rashin zuciyas shine zaki koma?"

"Hajiya ba fa gidan mijina zanje ba, wajen malam zanje ayi mana maganin tsinanniyar yarinyarnan kowa ya huta, sannan daren jiya kwana nayi ina mugayen mafarkai na tabbatar jifana akayi ake rabani da samari, daga idddata zusa yanzu maza nawa ne suka zo suka gudu? Na tabbata baban su amir ne yake rabani dasu dan haka nayi magana da malam a waya yace nazo da sassafe a maida masa mugayen abubuwansa kansa da 'ya'yansa".

Zama Hajiya tayi tace "yanzu ke Maimuna bazaki yi hankali ba ki zauna ki nutsu? Tabbas asiri gaskiya ne amma ba kowa ne zai miki asiri ba, idan ma anyi ki zauna kiyi addu'a ya karye, da ace aikin malaminnan yana ci ba da tuni kin koma gidan aurenki ba? Yanzu gaki nan kina zaune saidai wannan yazo ya tafi wancan yazo ya tafi, sannan banaso ki saka Hadiyya a wannan abin, ba sai da asiri ba zamuyi maganinta tunda yasan me ta aikata shikenan".

Ko kallon Hajiya bata sake yi ba ta fice, tana zuwa wajen malamin ta fara zayyana masa mafarkin da tayi marar dad'i, buga 'kasa yayi yace "tabbas abinda kike tunani gaskiya ne ba'ka'ken aljanu aka turo miki domin su hanaki aure, amma zamuyi maganin abin ga wannan ki shafa bayan sallar Isha sannan kiyi wannan turaren, ki tabbatar shine abinda zakiyi 'karshe kafin ki kwanta, zakiga abin mamaki cikin baccinki Allah zai nuna miki duk wanda yake nufarki da sharri, zakiga shaid'anun dake kanki suna fita da kansu kuma ina tabbatar miki babu makawa a zancena kina gama turarennan mazaje zasu fara zuwa gareki har sai kinyi ruwan ido".

Cikin murna Maimuna ta d'auki sa'kon ta fita.

'bangaren Hadiyya kuwa kwana tayi tana kuka, da safe ta shirya ta nufi gidan Hajiya.

Tana sallama Hajiya ta d'auke mata kai, ta kai 30mins tana baiwa Hajiya ha'kuri amma ta'ki ko kallonta haka ta tashi ta tafi da al'kawarin zata dawo gobe, zata ci gaba da zuwa har lokacin da Hajiya zata ha'kura.

Saida Maimuna tayi sallah ta sanya kayan baccinta sannan ta d'auko turaren malam ta fara yi, cikin 'kan'kanin lokaci d'akin ya turnu'ke da haya'kin amma bata damu ba, saida ta tabbatar ya ratsa jikinta sosai sannan tabi gado ta kwanta.

Mummunar fad'uwar gaba ta fara ji tare da wani wari a d'akin, kanta ne yayi mata nauyi yayin da takeji wani motsi a d'akin, runtse idonta tayi jikinta ya fara karkarwa, meyasa malam bai fad'a mata hakan zai faru ba?

Idanunta a rufe taji an fizge abinda ta rufa dashi, a ckin 'kan'kanin lokaci taji hannu ya Sha'ke mata wuya, a firgice ta bud'e idanunta tayi arba da wata mummunar halitta da bata ta'ba ganin irinta ba, cikin tsananin firgici ta saki gigitaccen 'kara.

A d'imauce Hajiya ta nufi d'akin Maimuna jin 'karan da ta saki, samunta tayi idaninta a 'kafe tana kallon gefe bakinta a bud'e bata motsi.

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Maimuna" Hajiya ta fad'a tana jijjigata amma ko motsawa batayi ba, ruwa Hajiya ta d'ebo ta fara yayyafa mata tana shafa mata a fuska tareda tofa mata addu'o'i, ta kai awa tana yiwa Maimuna addu'a sannan

40 / 41