NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   25 / 41

72K to 75K   out of 120.7K words

lokacin da na kasa bacci, yanda nake d'aukan lokaci ina sauraran bugun zuciyarsa a lokacin da nake bu'katar nutsuwa, how his hands feel on my body, ta yanda yake sakani na manta duk wani bacin rai da gajiya by his single touch.....

"Earth to Bilkisu!!!  Tunanin me kikeyi haka?" Cikin sauri na kalli Raudah da tayi tafi saboda ta dawo dani daga tunanin da na tafi, tunanin da na jima da turashi can 'kasan zuciyata domin banason tunawa da wad'annan abubuwan, murmushi na 'ka'kalo nace "babu komai".

Motata muka bud'e ni da twins da jannat muka shiga baya ya Aalee da Raudah a gaba, twins na hirarsu su Raudah ma na hirarsu ni kad'ai ce babu abokin hira, kan jannat na cinyata 'kafafunta na cinyar amal, na ganesu ne saboda mayafansu yau ba kala d'aya bane.

Zubawa window Ido nayi ina kallon fitilun titi, ba sai na nunawa Aalee hanya ba domin ya bud'e GPS yayi searching wurin tafiya kawai muke muna bin hanya.

"Aunty Bilki ba dai bacci kikeji ba ko?" Aalee ya fad'a tareda juyowa ya kalleni, murmushi nayi nace "a'a kaina ne ya d'an fara ciwo".

Cike da kulawa yace "oh, I am sorry mun d'auko ki bayan kinsha aiki".

"Bakomai ya Aalee" na fad'a tareda kallonsa nayi murmushi, bansan meyasa yanzu yake tunamin da Saleh ba, domin akwai banbanci sosai tsakanin su, Saleh mutum ne mai saurin fushi kuma sai nayi da gaske yake saukowa, amma abinda na lura d'azu da Aalee yanada sau'kin kai ko da kuwa a kan 'kannensa ne, sannan yanada fahimta domin tunda muka zauna yanayin hirarsa da Raudah akan wani sukeyi amma yanda yake Bata reply cikin tunani da basira ya matu'kar birgeni, meyasa Saleh bai zama haka ba, da ace ya yarda dani yanda na yarda dashi ya kuma fahimceni yanda na fahimceshi bazai ta'ba sakina ba ko da kuwa laifin da nayi yayi muni, yardar da na yiwa Saleh gani nake ko da namiji ya kamani da idonsa zai ce "na yarda dake Boo-boo na amma kiyimin bayani ya akai hakan ta faru, nasan ba laifinki bane" sai gashi abinda bai taka kara ya karya ba ya sanya ya sakeni, _boo-boo_. Abinda ke ta min yawo a kaina kenan, tunawa nayi da lokacin da na fara kiransa boo-boo, yana kirana babyna lokacin ban ta'ba ambatar sunansa ba saidai nace "umm kaga"

Bazan manta ba ina amarya ya d'auki wayata yaga nayi saving numbersa da boo-boo ni kuma kunya ta hanani fara fad'a masa, pinning d'ina yayi kan kujera ga tsoro a raina lokacin ga alamun munyi ba'ki yace bazai d'aga ni ba sai na fad'i sunan da bakina.....

Memories ke zuwarmin na zamana da Saleh, hawaye naji ya zubomin na goge da sauri, idon Raudah na gani a kaina tana kallona ta gefen kujerarta, a hankali tace "are you okay?"

Gyad'a mata Kai nayi na koma kallon window, ko wace rayuwa Saleh keyi yanzu? Yana nan yana rayuwarsa free 'barauniyar matarsa ta tafi ya huta, hannuna na Sanya a 'kirjina jin ya d'aura, duk lokacin da kalmar 'barauniya taso Raina sai naji 'kirjina yayi tightening, ba abinda nakeso a yanzu kamar na koma gida na 'kudundune a gado nasha kukana na zazzage Saleh da danginsa a raina sannan nayi bacci.

"Yauwa mun iso, Bilki nan ne ko?" Kallon wurin nayi nace "eh nan ne, fita mukayi muka nufi cikin wurin muka kama table, da mutane sosai yawancinsu maza ne wasu kuma da 'yammatansu, lemo mai sanyi aka fara kawo mana da ruwa a take na shanye ruwan tas, idonsu na gani a kaina sai naji duk nayi wani iri, ba dai kunya na basu ba saboda d'aga ruwan da nayi ba ko?

Sunkuyar da kaina nayi na kasa kallonsu har aka kaso shawarma da ships d'in da twins suka ce suna so, fara cin abincinmu mukayi ko nace sukayi domin ni kusan wasa kawai nake da fork da spoon d'ina, wata 'katuwar shawarma sukeyi a wurin da bazaka iya kaita baki ba saidai ka dinga yanka da wu'ka kana ci da fork.

Kallona sukeyi dukkansu cikin damuwa, bayan wani lokaci nawal ta ajiye fork d'inta tace "Aunty Bilki ko cin abinci ne bakyaso kiyi damu? Muma fa mutane ne bazamuyi judging d'inki akan yanda kike cin abinci ba idan wannan ne damuwarki, idan zakiga yanda muke cin abinci kaman kaji a gida bazaki 'ki cin abinci damu ba".

Wani kallo dukkansu suka wurga mata Raudah tace "ina ruwanki?, Sorry Bilki".

Murmushi nayi nace "bakomai Raudah, ba wai banason cin abinci daku bane kawai banajin dad'i sannan wannan ba shine first time da na fara cin abinci a waje ba kuma wajennan na zo almost three times".

"Ya kuka ji shawarman tayi muku?" Aalee ya fad'a tareda kauwa bakinsa, hakan ya d'auke hankalinsu daga kaina suka hau hirar abubuwan da suka ci a waje, irin abincin da suka ci a 'kasashe daban-daban da yanda taste d'in yayi a bakinsu, hira sukeyi suna dariyarsu abinsu, a haka dai na samu naci abinda zan iya ci na bar ragowar nasan ma shara zaibi.

Ko da muka shiga mota wayarsa ya jona da Bluetooth ya fara kunna mana wa'koki, bin wa'kokin sukeyi suna yi suna tsallensu a mota harda shi Aalee, har wani rawa yakeyi da motar idan mun tsaya a haka har mukaje gida.

Ina zuwa d'aki na shige na nufi toilet na wanke kwalliyata na canza kayana sannan na fito, ina fitowa Aunty ta yi min wani kallo tace "Ina son magana dake" tashi sukayi duk suka bar wurin na zauna ina jiran fad'an Aunty.

"Me yake damunki Bilkisu?" Ta fad'a cike da kulawa, wasa nake da yatsuna nace "bakomai aunty". Kallona tayi tace "kinmin al'kawari kin dena barin tunanin Saleh yana shiga raguwarki, meyasa yau kika sanya 'yan uwanki a damuwa suna shigowa suka fara fad'amin akwai abinda ke damunki".

Sunkuyar da kaina nayi nace "Aunty kiyi ha'kuri ni kaina bansan ya akai hakan ta faru ba, yanda na miki al'kawari na cireshi a rayuwata kuma insha Allah zanci gaba da nisantashi da rayuwata, bansan me yasa...." Kasa 'karasawa nayi tace

"Na fahimta Bilkisu Allah ya yaye miki son wannan mutumin domin indai kina sonshi ko kasheki zaiyi ki dawo komawa aurensa zakiyi".

Girgiza kai nayi nace "Aunty bana fatan komawa gidan Saleh a yanzu" cije baki nayi jin marata ta d'aure, a dai-dai lokacin da naji d'umi a 'kasan 'kafata, murmushi nayi nace "a kwanakinnan iddata zata 'kare Aunty".

Tashi nayi na gyara jikina sannan na fito na nemi ruwan d'umi nasha na kwanta, flo app d'ina na duba a 'ka'ida period d'ina saura kwana 5 ma amma Allah yayimin gata da alamu dai aurena da Saleh ba mai komawa bane.

Du'kun'kunewa nayi a gadon da zamuyi sharing ni da Raudah twins kuma a katifa a 'kasa, dafani Raudah tayi bayan ta saka pyjamas d'inta, ji nayi kaman ta jona min shocking na ture hannunta, cikin damuwa tace "Bilkisu meke damunki?"

"Cramps" na fad'a tareda rufe idona ina fatan ciwon ya tafi, bansan dalilin da yasa har bayan aurena nake ciwon Mara ba maybe Yana relating da infertility d'ina, pills Raudah ta bani tace "pain releiver ne kisha".

Karbat nayi ba musu ta mi'komin ruwa nasha na koma na kwanta, dariya naji tayi tace "shiyasa muka ganki kamar a yanayin damuwa kenan ashe hormonal crash kika samu".

Rashin dad'i naji akan yanda nayi musu a waje nace "kuyi ha'kuri Raudah banso na sakaku a damuwa ba"

Shafa kaina tayi tace "bakomai" mi'ka nayi Jin duk ga'bo'bina sun ri'ke sannan na tashi na zauna, kallon wayarta takeyi tace "kikace kinada aure amma maama tace mana mamanki ce zatayi tafiya shine Zaki zo ki zauna anan, ko kwalliyar ce kawai bakyaso kika bamu wannan excuse d'in?".

Girgiza kai nayi nace "ba cewa nayi inada aure ba cewa nayi da aure a kaina, min rabu da mijina ko idda ban gama ba shiyasa nace haka".
38

"oh" ta fad'a tareda maida hankalinta kan waya, bayan ta gama dannawa ta ajiye ta kalleni tace "ya kikaji?"

" me fa?" Na tambaya tareda tashi na zauna, "mutuwar aure, how does it feel?"

Shiru nayi ina tunanin yanda zan bata amsa, tunda aurena ya mutu babu wanda ya ta'ba min wannan tambayar dukda mama da aunty sun kula dani sosai, amma ba sa'annina bane da zasu tambayeni yanda mutuwar aure take, abinda suke tambayata shine kina lafiya? Saboda kar damuwa tayimin yawa.

Zama nayi na had'e hannayena a gwiwata nace "umm to naji abubuwa da yawa ban ma san yanda zan fasalta su ba".

Idanunta na kaina tace "baki ta'ba fad'awa kowa ba kenan". Gyad'a kai nayi alamun eh ta juyo gaba d'aya ta maido hankalinta kaina tace "nima nan da kike ganina bazawara ce na miki ta hausawa, amma bansan zafin mutuwar aure ba saboda ni da aurena ma ya mutu bansan ya mutu ba sai bayan almost 6months, shiyasa nake tambayarki i can see how hurt you are Bilkisu".

Numfashi naja na sauke sannan nace "a wajena it was the worst feeling ever, I feel sad, hurt, rejected, guilty,...I feel so many things at the same time gaba d'aya 'kwa'kwalwata kamar an dakatar da ita daga aiki, ko processing abinda ya faru na kasa yi a kaina kalmar ce kawai ke min yawo, sai bayan na koma gida Mama ta tasomin da maganar sannan na fara jin zafin abinda ya faru, Raudah muna matu'kar son junanmu, mun yarda da juna,idan muna tare gaba d'aya mantawa muke da kowa da komai, abinda ya girgiza ni shine yanda a cikin mintina kad'an shekarun da mukayi suka tashi a banza".

Saurarona takeyi yayin da na bata labarin abinda ya faru itama take sanarmin dalilin nata mutuwar auren, rayuwarta abin tausayi dukda ta tsayawa kanta ta kuma kare , tayi fighting ma right d'inta har 'karshe, kuma ita dangin mijinta na sonta sosai unlike me.

Har 12 muna hira kuma naji dad'i sosai, domin da iddata ta matso 'karewa kullum tunanin Saleh nakeyi, a cikin fargaba nake idan na gama idda wacce irin rayuwa zan fara, ya zanji idan Saleh ya dawo rayuwata bayan na gama tsarata na cireshi daga lissafi na?

Hannun Raudah naji a kafad'ata tacemin "Bilkisu ba laifi bane ka so mutumin da ya cutar da kai, kuma yanda kika bani labarin zamanku zaiyi wuya ace baya missing d'inki fiye ma da yanda kike missing d'insa tunda ke mace ce shi Namiji ne, na sani zai nemeki ko kusa ko nesa, kawai kiyi preparing kanki yanda Zaki kar'beshi, kina son ya koma rayuwarki ko kinaso ki canza rayuwa it's up to you, balle ma kwanaki kad'an suka rage da zarar igiyar aurensa ta sauka daga kanki ke a jikinki sai kinji sauyi, yanzu ragowar hormones d'insa da ke jikinki su ke sanyaki wannan damuwar amma trust me da kin gama idda zaki samu sau'ki insha Allah".

"Thank you" na fad'a tareda share 'kwallar da ta zubomin, banason tunanin rabuwa da Saleh amma abinda Allah yayi baka da ikon canzawa.

Washegari babu wani abu da muka yi, a kwance na wuni saidai nayi bacci na farka na gyara kwanciyata na sake komawa bacci, breakfast ma a d'aki nayi zazza'bi ne sosai a jikina.

Muna parlour muna hira Aunty ta le'ko tace min "ya kamata yau muyi celebration fa".

Juyawa mukayi duk muna kallonta Raudah tace "au Aunty sai yau zakiyi celebrating zuwanmu? Har munyi kwana biyar?"

Zama Aunty tayi a gefena tace "celebrating 'yata ta zama sakakkiyar tsuntsuwa mana ni ina ruwana da ku, celebration zamuyi na fitar Bilkisu daga idda". Hannu biyu na saka na rufe fuskata nace "Aunty dan Allah ki bari mana".

"Da gaskiyar aunty, yau ranar taki ce dan haka ki fad'a mana abinda kikeso". Raudah ta fad'a tareda zama a kusa dani, twins kuwa har sun fara rige-rigen shiga wanka Aalee kuma idonsa na kaina duk jira suke suji me zance, nasan basa son zaman gida sannan nima akwai abinda nakeso na siya, jingina nayi a bango nace "shikenan ku shirya mu fita".

Bayan sun shige d'aki nace da Aunty "aunty ya batun kayan d'akina? Yaushe za'a dauko min su Kinga bani da jaka ko d'aya ban taho da jaka ba".

"Zamu san abinda za'ayi, ko zuwa 'karshen satinnan ne sai a san yaushe za'a d'auko da inda za'a saka su, jakunkuna kuma dama ai an gama yayinsu, idan kin fita sai ki siyo na zamani".

"To Aunty" na fad'a domin banaso na mata musu, dole ne na fara canza rayuwata a wannan lokacin.

**********
*SALEH*

Maida maganar da sukayi da hajiya baya yayi ya maida hankalinsa ga Bilkisu, idan baiyi wani abu ba yana gab da rasa Bilkisu har abada.

Komawa gida yayi ya samu Hajiya ta siyo kayayyaki da dama, kallon kayan yayi yace "Hajiya mene wannan?"

"Kayan lefenka aka fara had'awa". Kallonta yayi cike da mamaki yana tunanin inda ta samu kud'in, kamar ta karanta zuciyarsa tace "kud'in da yake wajena miliyan biyu, na bawa maimuna wasu dai lokacin da zata tafi to saura su muka fara had'a kayan dasu, ka duba kaga sunyi?"

Ko sake kallon kayan baiyi ba ya tashi ya bar d'akin, Hajiya bata damu da fitarsa ba ta kalli Maimuna tace "wannan atamfofin na dubu talatin kina ganin biyun sun isa?"

"Eh to da dai a 'kara mata d'aya, tunda matsiyaciyar can ma hud'u ya saka mata kuma ni ban ta'ba ganin ta saka su ba, shegiya kullum cikin saka kayan da basa cikin lefe takeyi maybe ma a gidansu ake saya mata".

"Ko ma dai mene ai yanzu ya 'kare, iddar tata ma ai ta kusa cika kowa ya huta, tunda nace masa sai yayi aure matar tayi ciki sannan zai dawo da ita ai shi ma yasan zamansu ya 'kare".

"To Hajiya yanzu ga wad'annan laces d'in da akace za'a tahomin dasu daga legas, a 32,000 zasu zo amma gaskiya a 40 zan baki su".

Jere kayan a leda Hajiya tayi tace "ko ma menene ni dai ayi aurennan komai ya dawo yanda mukeso, a kawo guda biyu".

Abun duniya ya taru yayi wa Saleh yawa gaba d'aya zaman gidan baya masa dad'i, tashi yayi ya nufi gidan su Bilkisu yana nocking Jabir ya bud'e, jingina a jikin 'kofar jabir yayi yace "me kakeso Saleh?"

"Bilkisu nake son gani dan girman Allah Jabir".

Bud'e 'kofar Jabir yayi yace shigo to".

Palo suka nufa ya saka key ya bud'e sannan yace masa "idan nace maka bata nan bazaka yarda ba, gashi ka gani da idonka bata nan kuma bansan inda suka je ba".

Dur'kusawa Saleh yayi a gaban Jabir yace "dan Allah Jabir ka taimakamin wallahi bana son rabuwa da Bilkisu nasan nayi kuskure kuma inaso na gyara dan Allah ka fad'amin inda take".

Tausayinsa sosai Jabir yaji ganin yanda duk ya susuce, alamu yayi masa na ya tashi tsaye sannan yace masa "me kakeso ka fad'awa Bilkisu?"

"So nake kawai na ganta Jabir, nasan idan na ganta zata fahimci abinda nazo mata dashi".

Shiru jabir yayi sannan yace "kana nufin ka shirya maidata ne ko me?"

"Eh"

"Hmm lokaci ya 'kure maka Saleh, a lokacin da Bilkisu take jiran zuwanka kana ina? Sai yanzu zaka dawo gareta? In fad'a maka gaskiya har iyayenmu fushi suke da kai ba ma Bilkisu ba, sannan baba zaka samu da wannan maganar ba ita ba".

"Zan ga baba amma inaso na ganta".

Numfashi Jabir yaja yace "tana gidan Aunty Salma?"

Cikin sauri Saleh ya gyad'a kai alamun eh, "tana can amma ka bari sai zuwa Thursday kaje ka sameta, ta fad'amin tanada day off"

Godiya sosai Saleh yayi ya koma gida gani yake kaman Thursday bazata zo ba, ranar Thursday kuwa da wuri ya bar aiki domin yaje ganin Bilkisu, shin Bilkisu zata kar'beshi? Da wane hannu Bilkisu zata amince dashi? Shin Bilkisu zata amince da komawa rayuwarsa? Da wannan tunanin ya d'auki hanyar gidan Aunty.

***********
"Dan Allah ku barni haka idan ba aljana kukeso na koma ba" na fad'a ina dariya, ina jin dad'in kulawar da suke nunamin a yau jina nake wata special.

Tashi nayi nace "na fad'a muku kayannan sun kamani bazan iya saka su da wannan mayafin ba yayi 'karami, idan kuma ba tallan jikina zan yi ba".

D'aukan mayafin nawal tayi ta yafamin shi a kafad'ata ta yanda bayan zai sauka sosai,ta gaba kuma yayi dai-dai yanda jikina zai rufe.

Kallon fuskata nayi a mirror tare da jin wani confidence na daban, ban sani ba ko kwalliyar da aka min ce ta sanyani Jin hakan ko kuma yanke hukuncin cire Saleh daga rayuwata ne?

"Ya kikaga kanki?" Raudah ta fad'a tareda tsayawa a gefena mayafinta na ninke a kafad'arta, "kamar ba ni ba" na fad'a tareda juyi a gaban mudubin, kallonta nayi nace "I feel sooo good".

"Muje muji me ya Aalee zai ce" ta fad'a tareda jan hannuna, yana tsaye 'kofar kitchen suna hira da aunty yana hangoni ya matso da sauri, tsayawa yayi dab dani ya matso da kansa sosai har inajin numfashinsa, ja nayi da baya yace "you look great". Ya fad'a tareda min thumbs up

"Nagode?" Na fad'a kamar a tambaya, dariya yayi tareda girgiza kansa yace "ina zamu je free Bird?"

Murmushi nayi nace "kaima kabi sahun Aunty ko? Ku dena min tsiya fa dama can free nake".

"Amma yanzu kin zama more free, zakiyi abinda kikeso ba tareda tunanin nauyin kowa a kanki ba, kowane namiji zai kulaki ba tareda kina jin dar ba".

Murmushi nayi na d'auke kaina, saidai maganarsa ta sanyani saurin juyowa na kalleshi lokacjn da ya furta "dukda aurenku ya rabu amma da alamu zuciyarki tana tare dashi".

Bansan me ya kawo maganarnan ba saboda bamuyi wannan sabon da Aalee ba sannan hakan da ya fito daga bakinsa sai naji ya 'batamin rai, d'auke kaina nayi nace "babu abinda ya shafeka da rayuwata sannan matsalar aurena ba abinda ya shafeka bane, so please ka san abinda zaka dinga furtawa".

Hannuna ya kama fuskarsa dauke da murmushi ya d'an sunkuya yace "am sorry Aunty B tsokanarki kawai nake".

Janye hannuna nayi lokacin da su  Raudah suka fito, key d'ina na mi'ka ma Aalee ko nace na cilla masa domin haushinsa nakeji, shi kuwa ko a jikinsa abinda ya 'kara bani takaici kenan.

Takalmina mai tsini ne hakan yasa gaba d'aya yanayin tafiyata ya canza ga kuma skirt d'in ya kamani, fita nayi can waje kafin su fito saidai idona yayi tozali da Sam ban shiryawa ganinsa ba, Saleh na gani yana 'ko'karin aiko yaro gidan Aunty.

Tsayawa nayi na zuba masa ido yayin da shima yake kallona, bud'e bakinsa yayi yace "Bilkisu?"

A tunaninku

25 / 41