Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
d'aga musu murya ba banaso ace saboda ni ko abinda na haifa ta fara, murmushi nayi na bud'e hannuna nace "my babies come and hug me".
Ajiye flask d'in hannunsu sukayi suka nufo ni tareda hugging d'ina, turo baki nawal tayi tace "kinga Mum tayi mana tsawa saboda anyi sabbin babies ko?"
Kumatunta naja nace "nawal ai ko babies nawa za'ayi Mum a wajenta ku kad'ai ne babies, kawai taga banajin dad'i ne sannan ga twins sun ishemu da kuka shiyasa amma ai da mace ake auta kune auta".
Ta'be baki suka yi su a lallai an 'bata musu sannan amal ta d'auko plate ta zubamin abinci, mi'komin tayi naga tuwo, wani farin ciki naji domin a yanzu shi kad'ai zan iya ci.
Mi'komin tayi tace "Inna ce tazo da akace za'a miki farfesu sai cewa tayi 'karku kaiwa 'dan jikana 'kazanta baku iya komai ba" amal ta 'kare maganar tana kwaikwayon kakar tasu, dariya mukayi Mum tayi murmushi har yanzu baby na hannunta ta'ki ajiyeshi, na lura family d'innan na son yara maza.
Ina cikin cin tuwon na fara jin bacci da 'kyar na samu na cinye kafin na fara bacci.
Na samu sau'kin ciwon kan sosai domin babu wanda ya sake zuwa wurina a ranar har washe-gari, bayan an duba Bp d'ina anga ya sauka akayi discharging d'ina.
Muna isa gida gida muka samu twins suna 'ko'karin karya 'yat tsohuwa sun hau kanta wai sai ta goyasu, mi'komin baby Aliyu yayi ya nufi inda suke ya kamo kunnensu, 'kara sukayi ya janyo kunnensu yace "kuka sake takurawa Inna had'aku zanyi ta tafi daku sai kunyi shekara a wajenta".
Gyad'a kai kawai sukayi suna 'ko'karin cire hannunsa a kunnensu, sakin kunnen yayi yazo ya kar'bi babyn hannuna muka 'karasa kujera muka zauna, gaida inna nayi tace,
"Sannu ummm Bilkisu ko?"
"Eh Inna".
"Kin sauka lafiya".
"Lafiya lau Inna".
"To barka Allah ya 'kara lafiya". Kallon Mum tayi tace "na saka an d'aura ruwan zafi kafin ku huta nasan yayi".
"Inna jininta ya hau fa baza'a mata wanka ba sai ya sauka".
Tafa hannu Inna tayi ta ri'ke 'kugu tace "lallai ni larai naga sha'kiyancin 'yan zamani, wato dabarar ma ba yara kawai ba harda ku manya, banda wad'annan turawan sun juya muku tunani ai wankan ma zai rage mata hawan jinin yake ko menene? Sai anyi wankannan yau".
"Dan Allah Inna a bari sai gobe dai ko? Ance fa ruwan zafi zai iya ta'ba mata kai zata iya suma, idan tasha magani jinin ya sauka sai ayi wankan". Saleh ya fad'a cikin lallashi, shiru tayi sannan tace "to naji, amma ruwan da aka d'aura baza'a yi asararsa ba, dashi zatayi idan ya huce".
Hakanan aka barta, zama tayi ta kar'bi babyn hannun Mum nidai uwar yara na zama 'yar kallo, kara da kawaici kawai nakeyi amma so nake naji d'umin 'ya'yana.
Yanzun ma banida wani hope domin bud'ar bakin Mum sai cewa tayi "jeki d'akin Raudah ki kwanta ki huta, sai mu ri'ke su kar su dameki da kuka" kallon twins tayi tace "duk wanda yazo kuce masa tana bacci ance kar a tasheta ko da bananan, ga babies d'innan su gansu".
Murmushi nayi na amsa ma Mum sannan na nufi d'aki, gani nake kamar sun fini son yarannan domin har Inna kallonsu take cike da sha'awa, yanzu ma biyun na hannunta ta hana kowa.
Da kewar 'yayana na samu nayi bacci ban tashi ba sai la'asar, ruwan wanka Inna ta kawo min sannan ta yimin wankan, mita take ruwan babu zafi nikuwa dai cije baki nake, har wani tiriri ke tashi a jikina, idan wannan babu zafi na jegon ya yake?
Bayan na fito Mum ta kawomin twins nayi feeding d'insu sannan ta dawo ta d'aukesu, yau naga inda akewa uwa iko da 'ya'yanta.
Kwalliya nayi sannan na nufi parlour, mamaki nayi ganin akwatina a parlour ga twins na ta shan jagwalgwalo.
" 'yata ta kaina" naji muryar Aunty, tasowa tayi da sauri tayi hugging d'ina tace "barka barka 'yata, wallahi naji dad'i sosai".
Murmushi nayi nace "nagode Aunty, amma dai bazaki koma ba sai bayan suna ko?"
"Kwarai kuwa, 'yata ta haifi twins maza ina naga ta zuwa?"
Bayan na gaida sauran mutum biyu dake d'akin muka koma gefe da Aunty, kallona tayi sosai tace "lallai Bilki ciki ya kar'beki, dubi yanda kika 'kara fresh da alamu ma haihuwar bata miki wuya ba".
"Tabd'i Aunty wallahi da wuya, labour biyu fa". Na karasa maganar ina kallon twins.
Dafa kafad'ata Aunty tayi tace " 'ya'yanki sun miki wuya ko? Ha'kuri zakiyi da zaran anyi suna shikenan".
Sosa kaina nayi cikin Jin kunya sannan tace "danginmu Allah ya bamu son 'ya'ya maza sosai kuma Allah da ikonsa bama haifar mazan sosai, dukkanmu matanmu da mazanmu 'ya'yansu maza d'ai-d'ai, mutum d'aya ce mai maza biyu, shiyasa da akace kin haifi twins maza kowa yake farin ciki, ki jira zuwan sauran sisters d'inmu ganin fuskar babies d'in ma sai ta miki wahala, kayan barka kuwa sai kin rasa wajen ajiya".
************
Washegari kafin Saleh ya fita saida yayiwa Hadiyya cefane, yana fita ta nufi part d'in sultana ta ro'keta ta koya mata girki ta tafi da kayan cefanenta.
Miya sukayi tare Sultana ta nuna mata yanda ake tsaftace kayan miya da nama wanda shine abinda ke fara 'bata girki, sannan ta nuna mata yanda ake had'a miya, bayanin dahuwar shinkfa tayi mata tace taje gidanta ta dafa.
Godiya Hadoyya tayi ta tafi da miyarta ta zauna ta dinga maimaita abubuwan da Sultana ta koya mata, a 'karshe ma littafi ta nema ta rubuta domin yanzu da gaske so take ta mallake Saleh ko dan uwarsa.
Sultana kuwa dukda Hadiyya Bata birgeta amma tafi sakewa da ita akan Jumana, ko ba komai dukkansu basa son halin hajiya, kuma musamman yanzu da Hadiyya ke son gyarawa Hajiya zama hakan yayiwa sultana dad'i, a yanzu zasu gane amfanin Bilkisu sai sunyi nadamar rashinta a gidan.
Saleh yana dawowa ta d'auko abincin ta jere masa sannan ta tsuguna a wurin, addu'a take silently Allah yasa abincin yayi masa dad'i.
Shima tunanin ci yake amma ganin yanda ta damu ya sanya ya daure ya kai abincin bakinsa, a hankali tace "yayi dad'i dan Allah?"
"Yayi sosai ma".
Tashi tayi tareda hamdala ta fara rawa, dariya yayi yaci gaba da cin abincinsa, zama tayi gefensa itama ta fara ci sannan tace "Ammyna tana gaida ka, tace gobe zata zo ma tayi maka godiya".
Girgiza kai Saleh yayi yace "a'a ba sai tazo ba godiyar da kika yimin ta isa, itama kamar uwa take a wurina ai".
'ka'kalo hawaye takeyi sannan tace "gani nake koyaushe kamar banyi maka godiya yanda ya kamata ba, ka ceci mahaifiyata saidai nace Allah ya biyaka, samun miji irinka a wannan lokacin akwai wahala".
Shiru yayi baice mata komai ba suka ci gaba da cin abinci, ya lura da canji sosai a tattare da ita fatansa Allah yasa canjin na alkhairi ne.
Anyi kwana biyu babu wata hatsaniya tsakanin su Hadiyya da Hajiya, hakan yasa hankalin Saleh ya d'an kwanta.
Zuwa mahaifiyar Hadiyya tayi domin ganin lafiyarta ta tahowa da Saleh takalmi, hira sukeyi Hadiyya tace "aikwa zaiji dad'in takalminnan dama ina ta raya me zan masa a raina saboda alkhairin da yake miki".
Maida takalmin kwalinsa Ammy tayi tace "gaskiya yaronnan yaron kirki ne, kinga Hadiyya kar kiyi wasa dashi, banaso sha-shancinki yasa ki janyowa kanki matsala".
"Kai Ammy inada hankali ma, kuma abinda nayi laifinsu ne ba nawa ba basuda imani wallahi, nasan dai banda Allah yasa ya saki Bilkisu d'innan ba yanda za'ayi ya aureni amma Ammy asiri fa sukayi mata wai har hauka ta kusa yi, ni tsoro nakeji ma wallahi kar suyimin asirin nima".
Murmushi Ammy tayi tace "mutum me baki ai ana wuyar cutarsa, kiyi taka tsan-tsan dasu sannan ki dage da addu'a, amma kuma duk wadda tayi miki a cikinsu karki raga mata saidai kiyi takunki cikin tunani da basira indai zaki bi hanyoyin da na dad'e ina nuna miki zaki mallakeshi babu boka babu malam da addu'a da dabara sannan kiyi maganinsu idan sun takura miki kenan, idan basu takura miki ba ki fita daga harkarsu".
Ammy na gamawa sai ga Maimuna ta fad'o d'akin kamar mahaukaciya, tsayawa tayi ta ri'ke 'kugu tace "naji duk maganganun da kukeyi munafukai Allah ya kama ku, wato a mallakeshi a raba mu dashi ko? An kawo ki cin arzi'ki zaki fara za'kewa ke kuma uwar banza mai goyawa 'yarta baya ta ya'ki dangin miji, ai wallahi nayi nadamar ma amincewa da aurenki".
"Saboda bakisan cewa naki auren zai mutu ba ko? Maimuna dan Allah na ro'ke ki ki fita daga harka ta ba ni na kashe miki aure ba, ba ni nace kiyi sharri Allah ya kamaki ba, kije kiji da zawarcinki na illa nadiran ki barni naci aurena a kwanciyar hankali".
Kafin su ankara sai ga Maimuna a gaban Hadiyya, kamo wuyan rigar Hadiyya tayi tace "Dan ubanki sai kin bar gidannan, wallahi tallahi sai kin fita tunda ba gidan ubanki bane".
A fusace Hadiyya ta tsinka mata mari sannan ta tureta daga jikinta, dama ji take da 'karfi da cikinnan yau Allah ya kawo abinda zata huce, nuna Maimuna tayi tace "ke idan kina cin 'kasa ki kiyayi ta shuri, ba gidan ubana bane amma zama daram, bakisan wacece Hadiyya ba ko? To kije ki tambayi wacece ni, shegiya mai ba'kin hali 'yar muguwar mace, bakisan wacece".
Ammy Hana Hadiyya magana takeyi amma tuni idon Hadiyya ya rufe saboda 'bacin rai, ji take hannunta har rawa yakeyi duka kawai takeso tayi, maimakon maimuna tayo kanta sai ta nufi Ammy, tsayawa tayi dab da ammy tace.
"Kinji kunya wallahi, a gabanki 'yarki tana nuna bata koyi tarbiyya ba, babu mamaki a jininku yake tunda kema tsabar rashin tarbiyya cikin shege kikayi kika gudu kikayi aure".
A fusace Hadiyya ta kaiwa Maimuna naushi, baya-baya Maimuna tayi Hadiyya ta sake naushinta a ciki saida ta fad'i, ko nauyin cikin jikinta bataji haka ta haye kan Maimuna ta dinga kai mata duka da mari, tuni ta fasa mata baki jini na fita daga hancinta, a tsorace mahaifiyar Hadiyya ke janta amma ta kasa d'ageta daga kan Maimuna, salati kawai takeyi domin dama tasan halin Hadiyya musamman idan aka ta'ba Ammynta.
Saida Maimuna ta kusa suma sannan Hadiyya ta tashi daga kan ruwan cikinta ta 'kudunduma mata ashar tace "idan baki fita daga gidana ba wallahi sai na illataki yanda bazaki sake son kallan kanki a mudubi ba 'yar gidan jakai kawai".
_din din ....to fah ayimin afuwa zanyi tafiya kuma zanyi kwanaki, amma idan na samu rara ki Yaya ne zanyi posting, thanks_
Banyi updating ba saboda I'm broke, nayi typing tun tuni kunsan Dan School da hutu😅😅😅😅but here it is fatan bakuyi fushi ba
Share
Vote
Comment
Follow
54
Kwanaki biyu suka rage kafin suna wanda a lokacinnan duk wasu family d'in Mum na nesa sunzo Abuja.
Shirin suna akeyi yayin da mai jego ta zama 'yar kallo, an rad'a ma babies Abdul-malik da Abdul-hakim, saidai anata musu akan nickname da za'a yi musu nidai na bar musu wu'ka da nama tunda yaran ma na zama 'yar kallo.
A cikin kwanakinnan kullum sai na sanya sabon kaya wanda duk bansan an d'inka su ba, saidai kawai na bud'e wardrobe d'in Raudah na d'auka, ko gida ban bud'e ba tunda na dawo su Raudah dai na zuwa.
Kayan barka kuwa tun ina mamaki har na dena, ranar farko wata friend d'in Mum wadda mijinta abokin Dad ne tazo da baby Walker guda biyu.
Daga nan fa aka fara bajinta kowa yanayi iya yinsa, da masu yi dan Allah da kuma masu yi saboda ace sunyi, da masu yi saboda su kere wasu.
Kud'in barka mafi 'kankanta da na samu shine 20k, daga 50 zuwa sama ake bani banda kayan yara da nawa, kafin suna na samu zannuwa 16pcs, banda masu janyo trolley cike da kayan babies, kai talaka yana shan wuya, wata ma baiwar Allah haka za'a dinga binta da omo 'kullin 10naira da 50 naira, wadda ta fini bu'kata, amma gasunan ana kawomin ko godiyar kirki banayi domin na lura haka tsarin yake, ka nuna cewa kafi 'karfin abin shine girma, tun abubuwan na min wani iri har sun zamarmin jiki.
Gida ya cika da ma'aikata a daren ranar suna, tunani kawai nakeyi me gobe zatayi holding domin kullum Mum na kan waya tana fad'in haihuwar da nayi.
A family d'ina part d'in su Mama basu wani zo ba, domin yanda suka ce sai anyi suna nasu a can, saboda haka 3 days bayan sunan nan zan tafi kano ayi wani sunan na daban, sai ni 'yar gata.
Kwalliya aka yimin kaman wata sabuwar amarya, a bayan gidan akayi decorations tamkar aurena za'a sake yi, ga katifa 'katuwa da zan zauna saidai banbancinsa da aure akwai gadon babies a gefena.
Yau dai na samu na d'auki babies d'ina saboda hoto amma da zaran anyi nake maidasu gadonsu domin sunyi kyau sosai a gadon.
Gado ne guda d'aya amma ta ciki an raba biyu, light blue ne kalan gadon haka ma kayan jikinsu, bedsheet d'in kuma da kayan jikin nasu yazo.
Sai yau na 'kare musu kallo, kamanninsu sak na mahaifinsu saidai kalar ta banbanta, maimakon farin mahaifinsu sai sukayi wata kala mai 'kyau kamar jariran black Americans yawancin mutane idan suka kallesu sai sun sake kallona, seriously munin nawa ya kai haka? Ni abun ma ya fara bani haushi.
Aliyu ne ya matso tareda wani abokinsa ina shirin tashi, zama nayi muka gaisa abokin ya le'ka gadon sannan ya kalleni ya kalli Aliyu, murmushi yayi yace "wow Masha Allah, kayi gaskiya".
"Ah to, ba na fad'a maka ba? Idan kaje ka auri kalarka aljanu zaku haifa dubi fa ka fini haske sannan ka auri irinka? Sorry man".
Dariya nayi na kallesu, kafin su tafi Raudah ma tazo da friend d'inta tana ri'ke da babynta mace, zama sukayi Raudah tace "sannu da zama me jego".
"Yauwa Auntu Raudah sai niyyar tashi nakeyi amma mutane sun hanani, ko zaki zauna a madadina naje bathroom?"
"Babu matsala amma ku fara gaisawa da intisar".
Gaisawa mukayi na kar'bi babynta, da alamu itama bata wani dad'e da haihuwa ba yarinyar fara 'kal, dariya nayi da na tuna wata magana da wata ke cewa kyakkyawa ya auri kyakkyawa su haifi aljanu mu kuma munanan mu haifi me? Domin wannan yarinyar tubarkalla, lips d'inta ja ga kuma gashin kanta ba'ki sosai, dukda nasan basu fi 40 ba amma an gyara mata kanta yayi kyau tana ta baccinta.
Abdul-hakim ta d'auka ta "Masha Allah....Raudah seriously yayanki ya iya breeding" kallona tayi harda marairaicewa tace "dan Allah aunty Bilki miyi exchange ki bani d'aya na baki wannan tsohuwar".
Dariya nayi nace "bakomai, ga mamansu nan Raudah duk abinda tace ya zauna, ki za'bi wanda kikeso".
Shafa fuskar Abdul-hakim takeyi tace "wallahi yaran sun bani sha'awa sosai, haba naji mamma na ta kod'a kalan yaran ashe tubarkallah kalar 'kwai ce dasu, abinka da mun saba ganin farare, ya kamata dai a family a fara samar mana da wannan kalar kai ni na bawa khadija d'aya ma".
Tashi nayi ina murmushi naga wasu sun doso mu, da sauri nabi ta baya na nufi gida domin tun kusan 1hour back nakeso naje gida.
Na fito daga toilet naji wasu na hira a parlour, ma'kalewa nayi Jin an ambaci matar Aliyu na kasa kunne.
"Nifa nayi mamaki da suka ce wai 'yar gidan uncle Ibrahim da ya rasu ce, nasan dai tayi aure a baya amma ban san yaushe ta fito ba har Aliyu ya aureta".
D'aya daga cikinsu ce tace "ni naji labarin ta fito tunda ina yawan zuwa Kano, sannan akwai Aunt d'inta friend d'ina ce, nidai kamar ce min tayi rashin haihuwa ne yasa aurenta ya mutu, amma ba ma wannan ba, yanzu Aliyu duk ruwan idon nasa ya rasa wa zai aura sai bazawara? Ya gama kumfar bakin shi family zai aura amma ya auro wannan, na farko ba class d'insa bace wajen kud'i ji nake inda ake ri'kon ta baifi boys quarters na gidannan ba? Kuma ma ya akayi ta haihu bayan ance bata haihuwa? Sannan maza wallahi duk zatona idan zata haihu ma mata zatam
Haifa tunda kinga Dad shi kad'ai ne namiji sannan mu ma Namiji d'aya ne damu, haka aunty batul ma d'ayan ta haifa"
Tsaki wata taja tace "wai ku meye naku? Tunda yana sonta Aunty batul na sonta, su Raudah suna sonta harda Dad yana sonta, ta haihu kuma ta Haifa musu abinda suke so ko nace abinda muke so har biyu ma, maimakon kuyi murna sai ku dinga gulmarta? Haihuwa ta Allah ce ai kuma Allah ya 'karo musu mazan tayita haifarsu kuma nuna bakuji dad'i ba bazai saka ta dena Haifa ba, idan Aunty Batul taji kunsan abinda zata muku, kamar ba 'kannenta ba? Haba sisters".
Fitowa nayi da murmushina na gaidasu na fice, ni wannan d'in ma dad'i yayimin domin ba kowa ne zai soka ba, idan har dukkan mutane zasu nuna suna sonka to tabbas ka binciki halayyarka ba dai-dai take ba.
Ina komawa na samu Mum tana gadin jikokinta, friends d'inta suna zaune suna hira, gaidasu nayi suka min wuri na zauna tsakiyarsu aka mana hoto sannan suka bani abin barka, bazan iya 'kirga kud'in da na samu a yau ba domin na baya ma nafila ne, banda kud'i ga kuma kaya a gefen katifar da nake zaune, kayan da twins suka samu zasu iya shekara ba tare da na sake sayen tsinke ba, abu d'aya ne babu a taronnan dangina na 'bangaren uwa, Mama ce kawai tazo itama a yau zata koma har na 'kagu a gama taron nan na koma Kano, sai nayi 40 tukun zan dawo domin rayuwar gidannan ta fara isa ta musamman bayan na haihu.
Dukda ina 'ko'karin zama d'aya dasu amma abun akwai wahala, dole tasa na zama fake, banaso nayi saboda a san inada shi, banaso nayi saboda ace nayi sannan a kowane lokaci tsoron kuskure nakeyi domin ido na kaina, 'wannan talakar matar bari mu ga me ta iya?' shine kallon da nake samu daga wasu daga cikinsu.
Idan har zan zauna daga ni sai dangin mijina banida matsala domin sun san wacece ni kuma suna respecting d'ina a yanda nake, duk abinda nayi sa'banin nasu birgesu yake amma wad'annan sabbin mutanen tsoro suke bani.
Suna bai tashi ba sai 9:30, tun a ranar na fara shirin tafiya kano, I can't wait to meet some real people.
*************
*SALEH*
Zubawa Hadiyya ido Saleh yayi ya rasa ma me zaice mata, ita ma kanta a 'kasa tana turo baki gaba d'aya yau tsiwar ce a