Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
"Mama yanzu Ru'kayya na gida amma baki fad'amin ba? Inaso na biki".
Kallona tayi ta kalli Sultana sannan tace "ba'kuwar kuma kiyi Yaya da ita? Ki zauna idan mun dawo sai kuje kuga babyn".
Fita Mama tayi ta barmu ni da Sultana, "wacece Ru'kayya" Sultana ta tambaya, "itace wacce akayi aurenta watanni bayan nawa, Kinga har zatayi haihuwa ta biyu". Shiru nayi sannan nace "ya akai kika fito da Huda bata sani ba".
"Ta sani kawai ce mata nayi zanje gidan friend d'ita ita kuma Bata ta'ba ganin Huda ba tace naje da ita, idan Usman ya dawo zai biyo ya kawo kayanta suna motarsa".
Shiru mukayi na d'an lokaci sannan Sultana tace "Bilkisu kiyi ha'kuri kuma kisani Allah yana tareda mai gaskiya na sani an cuceki amma ki dogara ga Allah, 'kulle kanki a d'aki ba mafita bane dukda nasan rabuwa da Wanda kakeso akwai wahala"
"Bilkisu na sani kuma bazanga laifinki ba, domin a duniya akan Saleh nasan menene so, tun ina 'karamar yarinya nake son Saleh, tun ina 8years nake fad'an Uncle zan aura, haka nayi secondary na tafi saadatu rimi na gama ban bari kowane namiji ya shiga rayuwata ba saboda zuciyata na adanata ga Saleh, ki duba soyayyar da na ri'ke sama da shekara ashirin ina rainonta a zuciyata na ha'kura meyasa ke bazaki ha'kura ba, shekara nawa kikayi kina son Saleh? Gaba d'aya bakifi biyar ba, amma duk yarintata ta 'kare akan Saleh, daga silly crush har takai ga ta zama soyayya, bazan miki 'kary ba har yanzu akwai soyayyar Saleh a raina amma ba yanda zata hanani rayuwa ba, soyayya ce wadda bazata ta'ba barina na aureshi ba ko da kuwa mu kad'ai muka rage a duniya, ranar da Saleh ya sanar mana ke nakeso wallahi ji nake kamar na kashe kaina a wannan ranar, nasan yanda kikeji bazan kuma hanaki damuwa ba amma ki tuna akwai wad'anda suke sonki suke damuwa dake, bakya tunanin kin yanke musu wani 'bangare na farin cikinsu saboda son zuciyarki? Duk abinda zakiyi ya kasance ya shafeki ke kad'ai karki bari akan mutum d'aya ki saka mutane sama da goma a cikin damuwa kiyi tunani".
Sunkuyar da kaina nayi nace "insha Allah zanyi 'kokari na kuma duba maganarki, amma ki duba rabuwata da taki ba iri d'aya bace, ba wai iyakacin soyayyar Saleh bace ke damuna, irin wula'kancin da zargin da yakemin ma yafi damuna bayan yasan a cikin gidan shine gatana bayan mahaliccina".
"Idan Kika yimin kuka ranki zai 'baci kuma zan tafi da Huda bazan sake kawo miki ita ba, a haka kikeso ki zauna da 'yar taki bata da abin kallo sai hawayenki? Ki lura ki san me kikeyi".
33
Sai bayan la'asar Sultana ta tafi ta barmin Huda, bayan tafiyarta na zauna na fara tunani, idan har na ri'ke Huda to kenan inada hope na komawa ga Saleh? Gashi har na kwana a gida bai nemeni ba, idan har inaso na cire Saleh a rayuwata sai na rabu da duk wani abu da ya danganceshi.
Huda na bacci mama ta dawo ta sanarmin Ru'kayya ta haifi mace, d'aukan Huda nayi na fice na nufi babban gida, babu kowa a gidan daga ita sai adda da Yaya dake had'a ruwan zafi ita Kuma tana d'aki tana zaune tana waya sai wani lullumshe Ido takeyi, d'aukan babyn nayi ta ajiye wayar tareda kallona tace "Bilki yaushe kika zo babu labari?"
"Jiya" na fad'a ina gyara Safar babyn, zubamin ido tayi tace "bakida lafiya ne? Naga kin canza". Murmushi nayi mata na girgiza kai alamar a'a, wasa ta fara da Huda ganin banida niyyar magana, ganin shirun yayi yawa nace mata "mun rabu da Saleh jiya na dawo gida".
Kallona tayi cike da tausayawa abinda banaso kenan, banaso ana tausayamin hakan ke sakawa Ina tausayawa kaina, dafa kafad'ata tayi tace "Ayya Bilki kiyi ha'kuri Allah yasa hakan ne mafi alkhairi"
"Ameen nagode" na fad'a tareda 'ka'kalo murmushi, Ru'kayya ta san irin zaman da nakeyi dukda ba komai ta sani ba, ta san dai matsalar rashin haihuwa da kuma 'kiyayyar dangi, da ace ina haihuwa wani wula'kancin ba'a isa a yimin shi ba.
Bansan cewa da 'karfi na furta maganar ba saida naji Ru'kayya tace "a'a ki ma dena wannan tunanin bilki, idan ba'a sonka hausawa suka ce sai ka shiga ruwa ace ka tada 'kura, ko kina haihuwar abinda Allah ya tsara sai ya faru sai ya faru, sai ace kin fiye haihuwa ko ace kin fiye haifar maza ko Mata, ko ace 'ya'yanki basuda tarbiyya ko Basu da kyau ko 'kazamai ne, d'an adam ba'a iya masa ke dai kuyita addu'a Allah yayi miki za'bin alkhairi ya kuma saka miki, amma kuma kun rabu kika taho musu da yarinya?"
Kallon Huda nayi nace "gani nayi kamar idan na taho da ita zata ragemin kewa kuma..."
Shiru nayi Ru'kayya tace "a'a indai gaskiya zan fad'a miki babu fa'idar tahowa da yarinyarnan, kina tunanin watarana zaki koma kenan ko? Kinada hope kwanannan zai maidake ko? Bilkisu na rasa wace irin zuciya ke gareki, ko da tilastashi akayi ya sakeki karki sakawa ranki cewar zaki koma domin mazan yanzu wallahi sun 'baci, duk son da namiji ke miki wuyarta ya furta sakinnan sai Kinga banbanci, idan kika ri'ke yarinyarnan kamar bakyaso kin ri'ke wani sashi ne na 'kaddararki mara kyau, babu ke babu kwanciyar hankali indai Zaki kalleta to zaki tuna iyayenta, ki tuna tsohon mijinki sannan ki tuna irin 'kuncin da kika shiga ta dalilin jininta, indai kece bilkisun da na sani kina dab da fara Jin haushin yarinyarnan, shawarata idan kinaso ki manta da baya to ki maidata wajen iyayenta, bakya ganin wasu idan an sakesu 'ya'yan cikinsu ma barinsu suke saboda basa son abinda zai tuna musu da rayuwar aurensu, ki maidata kya dinga ganinta a hoto zaifi miki gaskiya a ganina, amma kiyi tunani".
Ko da na kwanta bacci tunanin maganar Sultana da Ru'kayya nayi, tabbas inada son kaina a wannan lamari bana hangen kowa sai kaina, ta yaya zan cirewa kaina wannan damuwar domin banaso ta shafi kowa nawa, hawaye ne ya gangaromin na goge, sallamar mama naji da sauri na rufe idona kamar bacci nakeyi, sunana ta kira nayi shiru ina jin takunta tana matsowa dab dani ta d'aura hannunta a kaina, numfashi ta sauke tace "Allah ya kyauta" sannan ta ajiyemin abu a gefen gadona ta fita, juyawa nayi naga pcm na d'auka nasha domin kaina na ciwo na koma na kwanta na rufe ido ina jiran zuwan bacci saidai kamar nasha maganin hana bacci, na san cewa ina gab da bawa kaina matsala idan har bana cikakken bacci da cin abinci, a cikin jikina ma na fara Jin na canza.
Wasa-wasa har nayi kwana biyar a gida Saleh bai le'ko ba balle waya, Ina zaune a Palo na zubawa tv ido naji sallamar aunty, amsawa nayi na gyara zamana, tana shigowa ta ri'ke 'kugu ta zubamin ido take tsoro ya kamani nasan yau zuwan nawa ne na musamman, " 'kaniyarki" ta fad'a tareda yimin da'kuwa, turo baki nayi nace "ni kuma anty me nayi?"
"Uwaki kikayi, yanzu ke akan d'a Namiji kika lalace haka? Amma kinji kunya wallahi dubeki, har namiji ya wula'kantaki ki zauna kina wani damuwa a kansa? Kamar wadda tayi ciwo dubi fuskarki? Wato jira kike ki mutu kawai ki bar mana gawarki saboda namiji ko?"
Sunkuyar da kaina nayi na fara hawaye, tsawa tayimin tace "karki sake ki yimin kuka anan!! Ke da kinsan ciwon kanki ba kece da kuka ba shi wanda ya sakeki shine da kuka".
Ai kamar ta tunzurani kuka na fara sosai, zama tayi gefena ta jani jikinta sai kuma rarrashi kamar ba itace ta shigo take shirin dukana ba "ya isa haka Bilkisu ba kuka ya kamaceki kiyi ba, na sani akwai ciwo amma kin sakamu a damuwa, Bilki zaki d'aura ma kanki ciwo ki barmu da ganin laifin kawunanmu, amanarki mahaifiyarki ta bar mana idan kika sakawa kanki ciwo ai kamar mun ci amanar mahaifiyarki ne, mun sani kina sonshi amma idan ya rabu dake kema ki rabu dashi mana, menene amfanin barinsa a zuciyarki yana haifar miki da damuwa?".
Goge hawayena nayi nace "aunty kuyi ha'kuri banyi hakan dan na saka muku damuwa ba, na kasa controlling hakan ne a raina".
"Tunda kin auri autan maza dole soyayya ta kasheki ko? Ke kina nan kina kuka shi kinsan me yakeyi? Bilki ki dawo hankalinki mana, na zamar miki misali shekara goma sha uku da mutuwar aurena, dai-dai da awa d'aya ban zubar da Hawaye akan sakaran mutumin da ya rabu dani ba domin asararsa ce, ke yanzu bayan zargin da yake miki da kuma sakin wula'kancin da yayi miki har kikewa soyayyarsa kuka? Kukan da bai san kinayi ba? Tunda haka ne d'auko gyalenki maidake zanyi, ai dama a shari'a bazaki bar gidan ba sai kin cika idda, ki koma kiyi iddarki sai ki dawo idan ya maidake kuma shikenan kowa ya huta".
Kallonta nayi naga alamun ko da wasa take amma sam babu alamun wasa a tattare da ita, tashi tayi tace "maza d'auko gyalenki mu tafi domin babu maganin kukanki sai zaman gidan mijinki ko kuwa?"
Girgiza kai nayi nace "Aunty banaso na koma" wani kallo ta watsomin tace "sai kin koma, bazaki zauna kina mana kuka muna kallonki ba, ta yiwu idan kina ganin mijinki zaki dena gaki ga dangin mijinki ga kuma mijinki da alamu wannan zaman yafi miki dad'i".
Hango irin gori da wula'kancin da zasu min na fara, a 'kasa na zube na fara mata magiya ina kuka sosai, gashi mama ta'ki fitowa ta ceceni, da 'kyar da al'kawura Aunty ta barni sannan ta zauna, ba tareda ta kalleni ba tace "Abu na farko shine ki maida wannan yarinyar" babu musu nace mata "to" sannan tace "takardunki suna wurinki ko suna gidan tsohon mijin naki?"
Harda kaurara tsohon mijin nawa, ban nuna mata komai ba nace "suna nan bayan an bani na kawowa baba".
"Zan kar'be su na nema miki aiki ko ya rage miki wani abun sannan idan tsautsayi ya had'a ni da mijinki wallahi sai na yi masa tatas, jinin matsiyata wanda bai gaji arzi'ki ba, shi ko duniya ce dashi ya isa ki masa sata?miliyan biyun banza da wofi? Ko gadonki ba ya tattake arzi'kinsa ba? Zai san ya wula'kanta mana 'ya zai gane cewa kinfi 'karfinsa daga shi har matsiyatan danginsa, daga yanzu kin fara facaka da dukiyarki, Allah ya kaimu ki fita idda a satin zamu bar 'kasarnan, sai munyi yawon duniya dake har kin gaji, Yana can yana fama da tsiyarsa tsautsayi ma ya Sanya yace ya maidake sai na makashi a kotu wallahi".
Shiru nayi da bakina aunty tayi ta banbaminta, tana cikin magana naji 'karan wayata, dubawa nayi naga *my boo* hannuna rawa ya fara aunty ta kar'bi wayar ta duba, mi'komin tayi ba tareda tace komai ba, ina kallon wayar har kiran ya katse, sake kira yayi saidai na kasa d'agawa, meyasa Saleh ya kirani? Ko dai ya fara nadama ne zai bani ha'kuri? Kafin Kiran ya sake tsinkewa na d'aga na kai kunnena "Salamu alaikum"
Tsit nayi saida ya sake sallama sannan na amsa, shiru yayi shima sannan yace "ya kike?" Amsa masa nayi nace "lafiya" Ina jin saukar numfashinsa jira kawai nake naji dalilinsa na kirana kamar ya sani ya fad'a "umm....ajiyar da nake baki ce ina key d'in yake?"
Kallon wayar nayi na sake maida ita kunnena, I can't believe this!!! Yanzu dalilinsa na kirana kenan ba dan duba lafiyata ba? Gaskiya ake fad'amin Saleh baya sona kamar yanda nake sonshi, 'bacin rai ya turnu'keni saidai nace masa "kazo gida ka kar'ba Yana hannuna" na katse kiran, nayi haka ne domin na jarraba shi saboda kud'in da ya bani last ban sakasu a ciki ba suna cikin jakata a can gidan, so nake naji me zaice.
Zubawa wayar Ido nayi har aunty tace "akan me ya kirawo ki? Ko kud'in da kika sace yakeso ki biyashi?" Girgiza kai nayi kalamanta na dukana, har yaushe wannan kalmar satar zata dena bibiyata? Daurewa nayi nace "kud'i yake bani ajiya shine yake tambayata suna ina?".
Gyara zamanta tayi tace "yanzu tunda kikazo gida bai nemeki ba sai yanzu? Shima ba don lafiyarki ba saboda bu'katarsa? Wani irin miji muka aura miki bilkisu? Wace irin rayuwa muka turaki kikayi?"
Gyaran murya nayi nace "aunty ba laifinku bane laifina ne da na kasa ganin gatan da kuka yimin nabi son zuciyata na auri bare, da d'an gida na aura bazai min haka ba, gaskiya kuke fad'amin Saleh baya sona baya ganin mutuncina".
"Bilkisu Saleh yana sonki amma a baya, kawai yanzu wani abun ya canzashi ne shiyasa da ki auri miji danginsa basa sonki gwara-gwara ki auri wanda baya sonki 'yan uwansa kuma kamar su cinyeki (readers ya kuke ganin wannan batu? Ina jiran raayoyinku). Yana sonki amma ya had'u da sharrin mata ne kinsan sharrin mace ki shaid'an ya sarawa mata, Allah kad'ai yasan abinda suka kitsa masa kuma dama shi karkatacce ne sun janye ra'ayinsa, amma gaskiya bata 'buya zai ganota amma lokacin da bazata amfana masa komai ba".
Bamu sake wata magana ba sai ta aikin da za'a nema min da 'kasashen da nakeson zuwa, muna hirar naga kiran Saleh ba tareda na amsa ba na d'auki key ko mayafi baj yafa ba na fita, har na kai gate na koma na d'auko Huda da kayanta, Ina fita na bud'e bayan motarsa na sakata ba tareda na kalleshi ba, cire key d'in nayi na ajiyeshi a kan motar nayi gaba.
"Bilkisu" cak na tsaya wannan shine Karo na farko da ya kira sunana bayan kwana biyar, gabana fad'uwa ya fara yi jikina gaba d'aya ya d'au rawa, ba tareda na juya ba na fad'a gida tareda doko 'kofar, idan aunty taji wannan labari zata iya bani kyautar kujerar maka, domin a yau babu sunan da bata Kira Saleh ba, tun ina jin haushi har ta fara bani dariya, bayan na gama saita kaina naji tafiyarsa sannan na koma gida na fara jiran kiransa akan ragowar kud'in da basa cikin akwatin, abun mamaki har dare bai kirani ba maimakon hakan ya birgeni sai ya bani takaici, wato ma bazai tambaya ba saboda halina ne cinye kud'insa, takaici yasa nayi yun'kurin deleting numbersa sai kuma nayi tunani, idan nayi deleting number dake kaina ai 'bata lokaci ne, editing number nayi nasa EX SALE, daga yau bazan sake grieving rashin Saleh ba zan fara tsarawa kaina sabuwar rayuwa.
*************
*SALEH*
A kwanaki biyar d'in da yayi babu Bilkisu gaba d'aya ya canza, har mantawa yayi da wankin underwear nashi saboda ya saba tana wanke masa, 'bangaren abinci kuwa ya ma dena cin na gida saboda Hajiya batada abinci sai tuwo, idan ba tuwo ba shinkafa da miya ko lettuce babu, a hakan ma shi yake bada kud'in cefane domin da gayya Hajiya zata yi miya babu nama sai yazo ci ya gani, a nan zai bada kud'in naman domin tace baisan kan cefane ba Bilkisu ta lalatashi da cefanen almubazzaranci.
Tafiya yake hankalinsa na kan rayuwar da ya koma, gashi Jabir ko sallamarsa a ciki yake amsawa, baya bashi fuskar da zai masa wata magana, cikin takaici ya daki steering d'insa ga kukan Huda ya isheshi ga damuwar me zai tarar yau a gida, tsorata ta yayi ta sake fashewa da ihu har suka je gida tana kuka, saida ya kaita wajen sultana sannan ya shiga ya gaida Hajiya.
Tana zaune tana cin tuwon dawa da miyar kuka, dan kyau abinci yayi kyau domin Hajiya bata tuwon banza, saidai shi tuwo bai dameshi ba Bilki ce kawai ta san cikinsa, "matso muci mana sai na 'karo mana",
"Hajiya naci abinci ai" ya fad'a tareda gyara zamansa, kallonsa tayi tace "yanzu Saleh fisabilillahi ka d'auki mummunar d'abi'ar cin abinci a waje ko? Wato wannan tsohuwar matar taka me halin yahudawa abinda ta koya maka kenan yawon cin abinci? Wa ya sani ko wanda take baka kullum siyowa takeyi shiyasa bakinka ya saba"
Shiru yayi bai tanka mata ba, ganin haka yasa ta sauya zancen tace "ya maganar hadiyya? Tunda mukayi maganar kai bakace komai ba yaushe zakaje ka ganta ne? Yarinyarnan fa Allah ya bata farin jini shiyasa ma uwarta takeso ka aureta su huta, kullum akwai wanda zaizo wajenta Allah yaso ma mai hankali ce tunda akayi maganarka duk wanda yaje wajenta sai tace an mata miji, yanzu ka saka rana kaga yau lahadi ko? To banaso wannan rana ta zagayo baka je kaga yarinyarnan ba".
Tashi yayi yace "to Hajiya insha Allah za'ayi hakan, aiki ne ya hanani amma zan fidda lokaci naje". Fita yayi ya nufi gidansa, bud'ewa yayi ya kalli uwar 'kurar da TV stand yayi, wucewa yayi stairs ya zauna bakin gado, tun bedsheet d'in da ta bari bai canza wani ba, kwanciya yayi ta baya ya tuna lokacin da suke rige-rigen hawa gadon idan sun fita musamman fitar dare, kawar da tunanin yayi ya d'aga gadon ya d'auko akwatin ajiyar bilki ya bud'e ya ciro kud'in, 'kirgasu yayi yaga babu 140,000, tunawa yayi ta fada masa ya tuna mata ta ajiye kud'in a Jakarta, d'auko jakar yayi ya had'a kud'in ya sanya a jakar fitarsa ya cire kayansa ya nufi toilet, shi kansa toilet d'in ya fita a hayyacinsa haka yayi abinda zaiyi ya fito ya kwanta.
Wayarsa ya bud'e ya shiga WhatsApp, har zai fita yaga wani link yaga an turo *yara goma da kwankwaso ya biyawa aikin zuciya a india*
Cikin sauri ya danna link d'in cikin sa'a kuwa yaga hotunan yaran, tunawa yayi da maganar Bilkisu da sauri ya tashi ya zauna ya fara karanta labarin, bin sunan yaran yake d'aya bayan d'aya yakeyi har yaga suna mai kama da na Amir ZAYYANU ISA, hannunsa har rawa yakeyi ya shiga hoton zayyanu, hoton amir ya gani ga maimuna na ri'ke dashi a 'kasa an rubuta *Babu abinda zamuce sai godiya ubangiji ya 'kara arzi'ki, inji Mahaifiyar zayyanu MAIMUNA ABUBAKA*...... I
'Kurawa hoton kallo yayi ya kasa ko 'kifta idonsa......
34
Tashi yayi cikin hanzari ya fita, a 'kofa ya tsaya ya runtse idonsa idan ya kaiwa hajiya wannan magana ranshi ne zai 'baci bayaso tace ta san wannan zance saidai bayaso ya gaskata hakan, idan har gwamnati ta biya musu kud'in aiki meyasa suka kar'bi kud'insa? 'ko'karin danne gaskiyar yakeyi a bayan ransa saidai gaskiya a