NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   38 / 41

111K to 114K   out of 120.7K words

zuwa airport hannuna na cikin na Aliyu.

Kallona yayi ya kalli hanyar tafiyarsa yace "yanzu bazaki tausaya min ba ki taho tare dani? Su Mama kya dawo daga baya ki gansu".

Murmushi nayi nace "a'a na fa dad'e banga gida ba, tunda akayi aurena sau biyu nazo nan, sati biyu dai ai ba yawa ni da naso nayi arba'in?"

"Tabd'i da wallahi sai na biyo ki, watannin da nayi babu ke fa jurewa kawai nakeyi but I really miss you".

'karashe maganar yayi tare da hugging d'ina, banyi hugging d'insa back ba da farko saboda Mum tana kallona, daga baya dai nayi hugging d'insa nace "I'll miss you too".

'ko'karin kissing d'ina yayi na d'auke kaina, iya kunyar da zanji gaban Mum na jita banaso na 'kara wata.

Saida muka ga tashinsu sannan Jabir ya d'aukeni muka koma gida.

A gidan ma bata sauya zani ba, domin Yaya ke min wanka sannan ta wuni tana kula da Abduls, da dare kuma ni da Mama muyi fama domin kukan dare garesu.

Tunda naga sun wuni suna bacci na san yau akwai hirar dare, saboda haka na samu nima nayi baccin rana.
.
12am dai-dai suka farka saidai Basu tashi da rigima ba, 1:30 suka fara kuka gaba d'ayan su, 'ko'karin had'a musu madara na fara saidai gaba d'aya na rikice, yau ne rana ta farko da zan had'a musu madara.

Karanta instructions d'in na fara saidai kukansu gaba d'aya ya gigita ni, ga Mama yau tana wurin mijinta.

Ruwan zafin na zuba bansan lokacin da na cika feeder da shi ba, ragewa nayi yayin da ruwan ya zuba a hannuna da 'kyar na samu na had'a musu madara ba yanda ma ya kamata ba, ina fara Basu suka 'ki sha suka fara sabon kuka, Abdul-malik nayi Abdul-hakim na amsawa, rasa yanda zanyi dasu nayi na saka su a gaba na fara hawaye, daga hawaye sai kuka sosai dama haka raino yake? Meyasa na kasa controlling 'ya'yan da na haifa a cikina? Yanda nake da son yara gani nake zan iya kula da 'yan biyar ma, saidai gashi tun kafin ayi nisa na fara gazawa.

"Wai yaya nake jin kuka ne ko bacci kikeyi?" Zubamin ido tayi ganin na saka yara a gaba ina kuka, matsowa tayi kusa dani tace "Bilkisu lafiya?"

"Mama bansan ya zanyi ba". Kuka sosai ya 'kwacemin tace "to ki basu nono mana".

"Tun 12 nike basu har na gaji, kuma na basu madara sun 'ki sha".

'Daukan madarar Mama tayi ta kalla tace "ruwa yayi yawa ta yaya zasu sha? Saidai a zubar a had'a musu wata".

Abdul-hakim ta d'auka ta goyashi sannan ta nufi toilet ta zubar da madarar, dawowa tayi ta fara had'a musu madara tana min bayanin yanda ake had'awa.

Abdul-malik na d'auka na fara feeding d'insa haka yasa kukan ya ragu, tana jijjiga Abdul-hakim ta gama had'a madarar sannan ta saukeshi ta fara bashi Madara, bayan d'an lokaci ya kar'ba muka samu d'akin yayi shiru.

Goge hawayena nayi tare da sanya ma Abdul-malik feeder shima, bacci suka fara mama ta kalleni tace "yanzu ke bakiji kunyar kuka ba?"

"Mama na rasa ya zanyi ne, tuj 12 nake fama dasu sama da awa kenan fa sannan suna kuka sosai a tare, sun rikita ni gaba d'aya na rasa me zanyi".

D'aura yaron hannunta tayi a kafad'a tace "Raino nutsuwa yake bu'kata Bilkisu, idan kina freaking out bazaki iya komai ba, tsaida hankalinki zakiyi wuri d'aya kar kiyi focusing a kan kukansu, kiyi focusing akan yanda zaki sama wa kanki nutsuwa ki sama musu".

Kwantar da shi tayi ta tashi tace "saida safe". Ta fita ta barni, na jima ina tunanin yanda zanci gaba da kula da su har bacci ya d'aukeni.

Kwanaki sunyi gudu sosai kamar yau nazo wai har sati biyu sun cika.

Aunty naje yiwa sallama a gidanta na wuni, muna zaune Aliyu ya kirata bayan sun gaisa ta tashi, hakanan naji yau ina son yin gulma saboda haka na kasa kunne domin jin abinda zasu ce.

"Ita ta fad'a maka hakan? A'a Aliyu kar ka yanke hukunci babu bincike, kowace 'ya tana son ganin gidansu ba Bilkisu kawai ba, sannan na tabbata rayuwarku na birgeta kawai sakewa da hakan ne bazata iya ba........ a'a kar ka sake ka mata wannan zancen wannan tsakanina da kai ne, tunda yanzu kana sonta wannan batu a barshi dan Allah saidai idan har ita tace bata sonka, idan har ka lura bata sonka sai muyi yanda muka ce amma idan har kaga akasin hakan to wannan magana ta zama tsakanina da kai, mu binneta har abada babu wanda zaiji ta, na tabbata hakan bazai wa Bilkisu dad'i ba dukda saboda 'karuwarta akayi".

Gabana naji yana fad'uwa, me Aunty da Aliyu suka aikata da basa so kowa ya sani? Shin hakan ya danganci aurena ko kuma haihuwata? Zuciyata bugawa take cikin sauri yayin da abubuwa marasa dad'i ke min yawo a raina, Aliyu ne kawai mutumin da ya dace nayi wannan maganar dashi fata na bazai 'boyemin komai ba.

*************
*SALEH*

Hajiya da Maimuna na ta zuba ido su ga fitar Hadiyya suka ji shiru, gashi Saleh ya dawo tun kafin lokacin dawowarsa shima ya shige yayi zamansa.

"Hajiya ko na'kuda shegiyar nan ta fara ne? Tunda ya kamata ace ta d'auki hanyar tafiya gida".

"Da na'kuda take ai zai fito ya fad'a mana, kawai dai wani munafurcin take sa'kawa kanta amma zata gani ne, matu'kar ta Sanya 'kafa ta bar gidannan ta tafi kenan domin na gaji da ita".

Sai magrib Saleh ya fito tafiya masallaci, tareshi Hajiya tayi tace "Yaya dai har yanzu baku fita kaita gidan ba? Dare fa zaiyi muku a hanya".

"Ai Hajiya ta fasa tafiya gidan Mahaifiyar tata tace ta zauna anan sai ta kawo mata wadda zata zauna da ita".

Takaici ne ya ishi Hajiya tace "akan me zata zauna? Kowace mace tana son haihuwa a gidan iyayenta domin anfi samun kulawa, ita tsabar rashin sanin ciwon kai ya sanya tace zata zauna? Wannan ai shashanci ne".

"Hajiya ni nace ta zauna fa, amma idan na dawo zan miki bayani".

Bai jira me zata ce ba ya fita, ko da ya dawo duk yanda taso ta juya ra'ayinsa akan ya tura Hadiyya gida ya'ki har ta ha'kura.

A gida ta zauna Ammy ta kan ziyarceta tayi mata kwana d'aya zuwa biyu sannan ta samo yayarta take zama da Hadiyya kullum.

Hakan ya bawa 'yan uwanta damar zuwa cin rice, yau wannan tazo kwana yau waccan tazo Saleh kuwa baya gajiya da yi musu hidima dake Allah yayi musu baki, basu da zance sai nashi kullum cikin saka masa albarka suke yi, shi kuma namiji da son ganin an yaba duk abinda yakeyi musu ko a jikinsa.

Haihuwar Hadiyya tazo da sau'ki domin a gida ta haihu sai bayan haihuwarta sannan suka tafi asbiti, ta haifi 'yarta kyakkyawa kamar ita, a nan fa hankalin su Hajiya ya sake tashi.

Kullum Saleh sai ya shigo da gara leda-leda ga gida kullum cike da mutane, ranar 'kauri ma rago Saleh ya yanka musu.

Kiransa Hajiya tayi ta zaunar dashi tace "wai kai me kakeyi haka ne? Kud'innan kamar ha'kosu kakeyi kullum sai ka kashe kamar baka san ciwonsu ba? Ban ce kar ka yiwa matarka hidima ba amma ya kamata ka san me kakeyi, idan ka biyewa matarnan taka sai sun tatseka tas su barka babu ko sisi na san Halin mahaifiyarta sarai domin na zauna da ita, babu abinda take koyawa 'ya'yanta sai yanda zasu yaudari samari su ci kud'insu, Bata da aiki sai koyawa 'ya'yanta kissa yanda zasu cinye kud'in mazajensu, ka rage abinda kakeyi".

Mamaki sosai Hajiya ta bashi yace "Hajiya a tunanina kin fini murna da samun haihuwarnan kuma duk abinda nakeyi bana yin sama da kima, na yanka rago ne saboda miyar suna da sauransu sannan ga mutane a gidan bazai yiwu a barsu haka ba".

"Mutanen kai ka kawo su!! Banason maganar banza kaji ko?!! Ta tara 'yan uwanta ciyar da su da kake yi ma ai 'ko'kari ne har sai ka 'kara da wata d'awainiya ta daban? To bari kaji idan kai bazaka koresu ba ni zan koresu tunda ba gidan ubansu bane, sai sun talauta min kai sannan ka dawo kana dur'kushe min a gaba? Bazai yiwu ba wallahi".

Da 'kyar Saleh ya shawo kan Hajiya ta amince bazata kori dangin Hadiyya ba, saidai a zuciyarta ta 'kuduri niyyar sai tayi maganin wad'annan mayun.

Ranar suna Hajiya taci kwalliyarta ta sanya shaddarta Ash ta nufi gidan Hadiyya, hidima ake ta yi mutane kad'an ne suka gaisa da ita kowa kai ya shiga caji.

Tabbas Aliyu ya wadata su da kayan cefane abinci kala-kala akayi, waina, funkaso, sinasir, alkubus, tuwo, gurasa, snacks, drinks.

Kasancewar Hadiyya me surutu ce hatta makwabta ta saba da su, mutane sosai sun halarci sunan nata.

Bin abincin Hajiya keyi da kallo tana yatsine fuska, fitowa Hadiyya tayi tayi shigar lace yayi mata kyau.

Da murmushi ta nufi Hajiya tace "sannu uwar mijina" .

"A tunaninki wannan 'karamar 'kwa'kwalwar taki da jahilin tunaninki da wanda uwarki ke nuna miki ya isa ya saka ki rabani da d'ana? Baki isa ba wallahi..."

Katseta Hadiyya tayi cikin walwala tace "Hajiya muna magana a gaban mutane mu d'an shiga ciki mana"

Kafin Hajiya tace wani abu Hadiyya taja hannunta, duk inda tayi sai tace "ga Mamansa ku gaisa ko tace ga uwar mijina ku gaisa".

Saida ta samu inda babu mutane sannan ta kar'bi plate d'in abinci da miya tace "Hajiya kina magana, ko kuma sai kin fara cin abinci ne?"

"Wannan 'kazantar taku zan ci? Na fi 'karfin naci abincinki".

Tuntu'ben 'karya Hadiyya tayi ta juye kaf miyar da ke hannunta a jikin Hajiya, kama baki tayi tace "na shiga uku".

Tsumma ta janyo mai daud'a da alamu ma tsane ruwan dattin girki aka yi dashi ta ya'ba shi tun daga fuskar Hajiya har rigarta da zimmar goge miyar da ta zuba, murmushin mugunta tayi tace "kad'an kika gani Hajiya matu'kar baki fita daga gonata ba sai na kwantar dake wallahi".

Tana gama fad'in haka ta shiga gida tana ihun a taimako mata tayi 'barin miya a jikin surukarta.



*57*

Ina goye da Abdul-malik yayin da nake ri'ke da Abdul-hakim, tunani nake tunda na hau jirgin har na sauka gani nake tamkar minti biyu nayi a hanya.

Ina fita Raudah ta kar'bi yaron hannuna twins kuma suka fara kokawar kwance na bayana, bansan dalilin da ya sanya ma Aliyu ya taho dasu ba kaman wadda nayi shekara a gida?

Mum tana aiki hakan yasa kai tsaye muka nufi gidanmu tare da bar musu twins, naji dad'i da basu biyo mu ba domin yanzu kam lokaci nake so daga ni sai Aliyu.

Muna shiga Aliyu yayi attacking d'ina da kisses, dariya nake ina tureshi amma sam ya'ki tsayawa, kissing fuskata yake ta kowane 'bangare sannan ya gangaro wuyana saidai a hankali yake kissing wuyana, kowanne kiss yana d'aukan lokaci kafin ya tafi wani, kashemin jiki ya fara yi yayin da hannunsa ke bin sassan jikina.

"Ya Aalee" na fad'a da dasasshiyar murya, turani yakeyi a hankali yana ri'ke da hips d'ina har na fad'a kan kujera duk da maganar Aunty na raina amma na barta sai next time.

Straddling d'ina yayi tare da had'a lips d'insa da nawa, rigata ya d'aga ya fara shafa cikina cikin wani salo na daban, wani sauti na saki da bansan lokacin da ya fito ba, janyewa yayi tare da sake pecking d'ina yace "I miss you more".

Kissing wuyana yaci gaba dayi zuwa 'kirjina yayin da hannuna ke shafa gashin kansa zuwa bayansa, slowly yake shafa marata na lumshe ido tare da barinsa yaci gaba da hakan.

Cikina ne yayi 'kara alamun yunwa, dariya Aliyi yayi tare da barin abinda yake yace "ya kamata kici abinci".

Waya yayi cikin minti goma aka kawo mana abinci, muna manne da juna muka ci abincin muna gamawa muka gudanar da natural excercise.....

Sai da na nutsu sannan aka kawomin twins wai sun ishe su da kuka, ganin twins ne ya tuna min da maganar Aunty.

Washegari hankalina ya gaza kwanciya saboda haka na yanke shawarar yi masa magana.

Muna 'kare breakfast ya fita, gashi twins da Raudah duk suna school haka na wuni ina rainon twins har saida na gaji na mi'ka su wajen su inna kulu.

Sai yamma sosai Aliyu ya dawo, bayan fitarsa sallah na wanke 'karnin twins daga jikina na saka riga 'karama na shafa powder da lip gloss na zauna jiransa, na samu twins sunyi bacci gara naci lokaci na kafin su farka domin tsabar raino wankan ma sai yanzu nayi, har na fara tunanin samun mai tayin raino.

Shigowar Aliyu ce ta tasheni daga zaman da nayi na nufeshi domin yi masa sannu da zuwa, d'agani yayi cak tare da juyani wanda ya bani tsoro da mamaki a lokaci guda, bansan yaushe yayi 'karfi haka ba ko kuma nice na rame?

Ajiyeni yayi tare da saka hannayensa bit 'kuguna, sama yayo da hannayen nasa zuwa 'kirjina sannan yace "kin rame sosai fa Bilkisu ko baki da lafiya ne?"

Kallon jikina nayi nace "lafiya ta 'kalau kuma ni banji ramar da nayi ba, ko kuma kai dai ka 'kara 'kiba".

"Bari mu gani muje mu gwada".

Gym d'in cikin gidan muka nufa na kalla nace "da alamu kana shigowa wurinnan sosai ko?"

"Tunda kika tafi da zaran na dawo daga aiki nan nake shigowa, babu machine d'in da ban hau ba".

"Ai naga alamun haka last night". Na fad'a ina rufe idona, dariya yayi ya cire hannuna daga fuskata yace "ke kuma na lura kin rage kuzari, oya hau mu gani".

Saida naji fad'uwar gaba ganin nauyi na 49kg ni da nake 55-56, sai yanzu na yarda na rame cikowar da boobs d'ina yayi yasa na kasa ganewa.

Kallona Aliyu yayi cikin damuwa yace "Bilkisu ki fad'amin abinda yake damunki".

"Babu abinda yake damuna Ya Aalee kawai Nursing d'in da nakke".

"Please don't lie to me, kinyi lossing weight da yawa sannan kice nursing kawai".

"I'm not lying" na fad'a tare da kallon idonsa, murmushi nayi nace "da gaske nake babu abinda yake damuna saidai idan akwai wani abu da ban sani ba".

"ki sanya skirt muje wurin Mum tabbas akwai abinda yake damunki 7kg fa da yawa, ta yaya zakiyi losing 7kg a 'kan'kanin lokaci?"

Hannuna yaja muka fita ina ta rantse masa babu abinda yake damuna, bai amince ba saida ya kira Mum ya sanar mata gamunan zuwa bani da lafiya.

Yaranmu muka d'auka muka nufi gidan Mum, waya take tana bayanin wani patient saida ta gama sannan ta juyo gareni, cikin damuwa tace "Bilkisu me yake damunki?"

"Mum na fad'a masa babu komai amma ya'ki yarda wai akwai abinda yake damuna saboda nayi loosing 7kg".

"7kg da yawa kin tabbatar ba abinda yake damunki?"

"Mum bana jin ciwo a jikina ko kad'an, ko ciwon kan da nayi tuni na dena nace masa nursing ne ya sani rama ya'ki yarda".

"Gaskiya kam rainon twins akwai wahala, ni da na raini mata ma saida naji a jikina ga 'yan raino ina da balle ke da baki da mai tayi gasu maza, suna shan madarar sosai?"

"Ba sosai ba dai jiya sau biyu suka sha yau ko sau d'aya basu sha ba, ko na had'a basa sha maybe har yanzu ban iya had'awa ba".

D'aukan Abdul-hakim tayi tace "Masha Allah dukda haka da nauyinsu, ko da yake zasuyi 'kiba tunda suna tsotse min ke, ya kamata ki dinga cin abinci sosai....."

Haka taci gaba da bani shawarwari harda maganin da tace zata bani nace mata ta barshi, dukda na rame amma naji dad'in jikina a haka saboda dalilai da dama, kuzari na kawai ya kamata na 'kara.

A hanyarmu ta komawa gida shiru nayi ina tunani, ta yaya zan 'bullo masa da maganar da ke damuna a raina? Wace amsa zan samu?

"Bilkisu".

"Na'am" na fad'a tareda kallonsa, hannuna ya had'a da nasa yace "naga kinyi shiru tabbas akwai abinda yake damunki".

"Hakane, idan munje gida sai muyi magana".

Yana ri'ke da hannuna yaci gaba da driving har muka shiga gida, muna zama yace "ina sauraronki".

Bud'e bakina nayi na rufe, na sake bud'ewa na rufe, cije le'bena nayi ya sunkuya a gabana yace "Babyna please say something mana na fara damuwa".

Abubuwa da dama ne suka fara zuwa kaina, meyasa kake tausayina da yawa? Meyasa ni da kai bamu ta'ba fad'a ba? Meyasa duk abinda nayi dai-dai ne a wurinka? Meyasa baka ta'ba ganin laifina? Meyasa kake d'aukana da muhimmanci foye da yanda ya dace? Kai kake aurena amma meyasa ni nake iko da kai? Wad'annan sune tambayoyin da suke kaina amma na danne nace "Meyasa ka aureni".

Kallona yayi tareda murmushi, zama yayi kan kujerar da nake yace "yanzu wannan tambaya ce?"

"Na sani ni da kai auren had'i ne baka sona lokacin da aka aura maka ni, nasan tausayina yasa ka aureni da kuma biyayya ga iyayenka, nasan dole aka maka..."

Yanke maganata yayi ta hanyar kissing d'ina, rashin responding da nayi yasa ya janye tare da turo baki yace "Bilkisu ni bana kallonki a matsayin auren dole, tun ranar da na ganki kike birgeni dukda ban fara miki kallo a matsayin macen da zan aura ba, saidai a duk lokacin da na zolayeki nakan ji hakan a raina kamar da gaske nake ban ta'ba nuna miki bane".

Girgiza kai nayi tare da tashi na nufi bedroom, bayan na canza kayana zuwa na bacci Aliyu ya shigo da damuwa a fuskarsa yace "Bilkisu wani abu nayi miki ne? Idan laifi na miki ki fad'amin na baki hakuri ban fahimci tambayoyin da kike min ba me suke nufi?"

Kallonshi nayi nace "saboda maganganunka ba gaskiya bane, Ya Aalee naji maganar da kukayi da Aunty so nake ka fad'amin dalilin ka na aurena banda wanda na sani".

"Me kikaji? Ni bansan wani abu ba bayan had'amu da akayi saboda ganin mun dace, bansan maganar da kika ji ba".

Dur'kusawa nayi a gabansa nace "dan Allah ka fad'amin gaskiya wallahi na san cewa akwai wani dalili na daban, naji abubuwan da Aunty ta fad'a ka fad'amin menene real dalilinka na aurena?"

Hawaye na matso ina kallonsa da kalar tausayi, d'agoni yayi yace "ki min al'kawari bazaki gujeni ba idan na fad'a miki gaskiya".

Nasan maganar babba ce amma banida wani za'bi nace "na maka al'kawari, babu inda zani".

"Bilkisu.....am sorry to say this Aunty ta bani aurenki ne a matsayin contract".

Zare ido nayi nace "ban gane ba".

Tashi yayi tsaye tareda sanya hannunsa cikin lallausan gashinsa, cije le'bensa yakeyi saidai gaba d'aya kaina ya 'kulle, contract? Wani irin contract? Me Aliyu yake nufi da hakan?

"Ka yimin bayani mana dan Allah".

Zama yayi saidai da ganinsa ya shiga

38 / 41