Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
rayuwa Mai tsayi"
"Nagode" na fada ina shafa abin hannun nawa
Sallama mukayi na koma gida yayi tafiyarsa,wani business app dake wayata na bud'e na d'auki hoton abun nayi searching dinsa, sai ga irinsa sak,duba kud'in nayi Naga $42,converting nayi naga ya bani 15k harda wasu Yan canji,Cirewa nayi na saka a akwatin sarkokina Domin wannan ba abun yawo koyaushe bane
Ina kokarin gyara shimfidata na kwanta mama ta kirani tace baba na son ganina,fita nayi na zauna a kasa wurin kafarta na sunkuyar da kaina
Cikin fara'a baba yacemin
"Ya sulaiman Babu wata matsala ko?"
Gyad'a Kai nayi baba yace
"Kidena daga min Kai kamar kadangaruwa,eh ko a'a,akwai matsala ne?"
"A'a baba,Babu komai"
"Kun fahimci junanku?"
"Eh" na fad'a muryata can kasa
Cike da murna baba yace
"To Alhamdulillah,dama munyi magana da habibu Kuma an tsaida ranar aurensu Nan da wata shida idan Allah yayi muna Raye,ku Mata kune kuke shirya komai maman bilki,sai a fadamin abubuwan da ake bukata Wanda za'a fara yinsu a kusa"
Ji nayi gabana yayi mugun faduwa,na ma kasa motsawa day wurin har saida baba yace
"Jeki bilkisu,Allah yayi Miki albarka"
Tashi nayi na tafi a sanyaye,Kiran sunana yayi yace
"Nayi mantuwa,dangin Mahaifinki sun kirani dazu sunce suna bu'katar kije ki musu kwana biyu,gobe sai ki tafi idan Allah ya kaimu ko sati ne kiyi"
Da kyar na amsa da to na shige d'aki da sauri,Ina zama Kan gado Kuka ya kwacemin da bansan dalilinsa ba,saida nayi Mai isata sannan nayi sallar Isha na Kuma yi salatul istihara Domin neman zabin Allah akan abinda zuciyata ke sakamin,son Saleh yayimin kamun da banyi tunani ba
Washegari banje asbitin da nake zuwa ba,Ina d'aki ri'ke da carbi Ina addu'ar Allah ya ciremin Saleh gaba d'aya daga Raina na huta,ya Kuma bani ikon zama da sulaiman zaman aure
Da wuri na had'a kayana Domin yaya ya kaini,ni kaina Ina son zuwa cikin dangin mahaifina Domin yanda suke nunamin soyayya da kulawa,idan naje goma ta arzi'ki suke hadomin,kowa so yake naje gidansa na kwana d'aya,sunso su karbeni daga wajen mama Amma ni nace musu nafison zama a wurin mama,zamana a tare dasu zai had a fad'a Domin kowa so yake ya rikeni daga mazansu har matansu
11:30am na fito daga d'aki ina Jan akwatina,kallona mama tayi tace
"Me ya Sami idonki na gansu sun kumbura?"
Murza idon nayi nace
"Mama ciwo sukemin ne,jiya da dare suka yita ruwa,idan naje can zanje asbiti insha Allah"
Bakin glass jabir ya bani yace
"Sa'ka wannan saboda rana ko?sabo ne yau nake niyyar sakawa Ashe rabonki ne,Kar dai ki manta tsarabarki biyu Zaki kasata"
"Na amince" na fad'a Ina saka glass din a idona,sallama na yiwa mama muka fita
Ina shiga motar Yaya yace
"Kiyi ha'kuri zamu fara biyawa mu d'auko Saleh sai mu kaiki"
Okay na fad'a na gyara zamana,unguwar rijiyar Zaki muka nufa,wani iri nakejin a jikina ji nake Sam banaso Naga Saleh
Horn yaya yayi a kofar gidansu Saleh,wani tangamemen gida ne masha Allah,da gani part part ne Domin Naga gidaje masu bene har uku,iya abinda nake hangowa a jikin gidajen babu banbanci,duk gidajen Ana musu fenti a lokacin
"Yaya gidansu Saleh babba ne sosai Masha Allah"
"Eh gaskiya gidansu nada girma,mamansu da yayyensa biyu maza duk a ciki suke gini,
"Eh gaskiya gidan nada girma,Kinga benayennan,gidajen su Saleh ne da Yan uwansa maza biyu,akwai Kuma bangaren mahaifiyarsa itama Tana ciki,ai kwanannan ma insha Allah zamusha biki shiyasa kikaga Ana yiwa gidajen fenti"
"Bikin wa?" Na fad'a cike da mamaki
"Bikin Saleh da yayansa"
Yaya na rufe Baki sai.ga Saleh ya fito,yayi matukar kyau cikin farin yadinsa,plain Babu wani aiki a jiki,agogo yake makalawa a hannunsa yana tahowa cikin sauri
Shigowa motar yayi yace
"Kanwata sannunki ko?kwana biyu"
Murmushi na kakalo Domin har yanzi Ina cikin shock na zancen aurensa,duk yanda yaso ya Jani da Hira na dinga dojewa har suka kaini
Gidan Yayar mahaifina suka ajiyeni,sallama na musu a gurguje na shige ba tareda waiwaye ba
Oyoyo yara suka.fara min har suka kusa kaini kasa,fitowa yayar mahaifina tayi Cike da fara'a tace
"Sannu da zuwa bilki,wato sai yau ko?"
Hugging dinta nayi nace
"Kiyi ha'kuri anty,wallahi karatu yasha min Kai"
"Ba wani karatu,bayanta tun yaushe kukayi hutu har ya kusa karewa?kedai kice kina San kina soyayya Dan babanki ya sanar Mana an Sanya ranarki muna farin ciki Allah ya Sanya alkhairi"
Murmushi kawai nayi muka.shige tare, d'akin yayanta mata ta kaini duk basa Nan,kwanciya nayi Kan gadon take na hau bacci
Ina farkawa abincina na jirana,ci nayi na sake kwanciya abuna har la'asar sannan ta tasheni,haka tayita dawainiya Dani har dare
Muna zaune da dare muna Hira naji Kira a wayata,dubawa nayi Naga bakuwar numba na daga ba tareda magana ba,coming muryar da tafi komi za'ki a kunnena naji ance
_kanwata Saleh ne_
Sum sum nantashi daga wurin nayi d'aki ina jin dariyarsu,kwanciya nayi Ina Jin wani farin ciki a Raina nace
"Yaya Saleh ya kake"
_ina lafiya,nace dazu ko laifin me nayi ake shamin kamshi?ko Dan kinsan kin Had'u ne dazun?_
Shiru nayi Ina mamakin abinda ya fad'a,bai damu da shiruna ba yace
_ya mutumin naki?_
"Lafiya" na fad'a a hankali
_banason ganinki dashi ko kad'an bilki_
"Meyasa?"
_nima ban saniba,idan na ganku tare ko naji kina zancensa Raina baci yake,ranar da Kika cemin ya tabaki ban iya baccin kirki ba_
"Meyasa?" Na sake tambaya tare da tashi na zauna
_ina sonki bilkisu,Ina matukar sanki,tunda Kika taso naji raina Yana sonki,na Dade Ina adana soyayyata har lokacin da ya dace,saidai kaman ke ba rabona bace bilki,_
Zuciyata bugu take cikin sauri,take hawaye ya fara zarya a fuskata,cike da takaici nace
"Haba Yaya Saleh,meyasa baka fad'a tuntuni ba,saida aka sanya ranar aurena?"
_bilki....ko yayanki baisan Ina sonki ba sai kwanannan,na kasa furta hakan saboda kunyar iyayenki,gani nake kowane lokaci yayi wuri,a wurina me karamar yarinyace bilki,kanwata dukkanmu munsan bakyason sulaiman,ki fadawa iyayenki bakya sonshi kafin lokaci ya Kure maki_
Cikin shesshekar kuka nace
"Yaya Saleh lokaci ya Riga ya Kure,an Sanya ranar aurena bazan iya bud'e Baki na sanarwa iyayena bana son zabinsu ba"
_bilki nasan bakya Sona Nima,Amma kinsan Zaki Sami kulawar da sulaiman bazai Baki ita ba a wurna_
"Ina sonka Mana....." A tsorace na rufe bakina domin bansan na furta hakan ba
_me kikace bilki?_
Da sauri na katse Kiran Ina Kara sautin kukana,meyasa wannan abun zai faru Dani a wannan lokacin,ban saniba Ashe sautin kukana ya fita parlor
Kirana Saleh yake naki dagawa,shigowa anty tayi ta dafani cike da damuwa,ba tareda tace komai ba ta d'auki wayata da keta Kara ta daga ta Sanya a speaker
Cike da damuwa Saleh yace
_bilkisu.....hello bilkisu Dan Allah kice wani Abu Mana,nasan nayi babban kuskure da ban furta Ina sonki ba duk tsawon shekarunnan,karki hukuntani ta hanyar auren wani ba niba,kema kina Sona bilkisu ki sanarma su mama zasu fahimceki_
Cikin Kuka nace
"Saleh Dan Allah mubar wannan maganar,daga ni har Kai aure zamuyi,Allah yayi ba rabon juna bane mu muyi ha'kuri mu rungumi kaddararmu Allah yasa itace Mafi alkhairi"
Danne wayar nayi na kashe aunty ta kalleni tace
"Me yake faruwa?"
Cikin Kuka nace
"Babu komai anty"
Tashi tayi tace
"Bari na Kira mamanki to na sanar Mata"
Cikin sauri na ri'ke anty nace
"Dan Allah anty karki kirata,banaso kowa yasan da wannan,an Riga an Sanya aurena da sulaiman,da ace Saleh na Sona da gaske da tuntuni ya furtamin,sama da shekara goma Yana ganina,kuma shima aure zaiyi"
Fita tayi Bata kulani ba ta Kira mama,can take dawo da cookies da lemo ta ajiyemin,take na cinye cookies din tas Nasha lemon,Amma banji wani sanyi a Raina ba
Dawowa anty tayi ta zauna ta nunamin cinyarta alamun na kwanta,kwanciya nayi hawaye na bin idona,kaina take shafawa cikin rarrashi tace
"Kina sonshi sosai ko?"
Gyad'a Kai nayi Kuka na neman kwacemin nace
"Anty abin yafimin ciwo da ya furtamin shima,a tunanina Ni kadai nake abuna,anty Yaya zanyi Dole na auri sulaiman Dani da Saleh Dole mu hakura da juna"
"Na Kira mamanki na Kuma sanar Mata,zamu San abinyi insha Allah,bilki ke yarmu ce,Kuma baba bazaiji dadi ba ace kin zauna da Wanda ya za'ba Miki ta Dole ne kawai,iyayenki mass fahimta ne komai zaizo da sauki"
Share hawayena nayi Ina tunanin kala kala a raina,a haka har bacci ya kwasheni
Da safe kuwa mama sammako tayi muna karyawa wurin 10 sai gata,fuskarta d'auke da damuwa ta zauna tana kallona
Sunkuyar da kaina nayi na kasa cin abincin na Kuma kasa daga kaina,Ana gamawa kowa ya barmu daga ni sai mama sai anty
Cike da damuwa mama tace
"Wallahi binta bakiji damuwar da na shiga ba da Kika cemin yarinyarnan Tana Kuka,Bata taba fadamin sulaiman nada matsala ba Kuma duk tambayar da babanta zai Mata zata ce Babu komai"
Bayani anty ta Mata na iya abinda ta sani suka juyo kaina,cikin lallashi mama tace
"Bilkisu meyasa Baki fadamin ba?"
Shiru nayi na kasa cewa komai,anty ce ta amsamin tace
"Tayi zaton ita kadai take Sonsa shiyasa tayi shiru,Amma yanzu tunda sun son junansu sai a San abinyi"
Ina zaune kamar kurma suka Gama.tsarinsu suka ce mama.zata tuntuni baba da maganar,sosai naji relief a Raina just nake kaman an saukemin nauyi daga zuciyata
Babu Wanda ya sakemin maganar aure,Amma kullum anty tana daukana muna zuwa shagunan da ake saida kayan d'aki,tana nunamin su,sati na daya a gidanta take sanar dani zasumin kayan gado a matsayinsu na dangin uba,Amma baba yace su Bari,still dai zasu min ko da ace Babu wurin ajiyewa
Godiya na dinga Kora Mata har na bar gidan na koma gidan kakannina wato iyayen mahaifina,kwana biyu nayi a can sannan na tafi gidan kanwar mahaifina itama na mata kwana biyu,saida nayi sati uku cir Ina yawo sannan na koma gida
Ranar da na koma kuwa baba ya sakani a gaba,ya d'auki lokaci kafin yayimin magana Wanda hakan ya bani tabbacin ransa a bace yake,ni nasan zancen Saleh bazai ma baba Dadi ba,kallona yayi yace
"Bilki,kema 'yata ce kamar yanda sai yayana suke,bana banbantashi sa yayana,yanda zan baiwa yayana zabin abinda sukeso kema zan Baki,meyasa Baki sanarmin bakyason sulaiman ba?"
Kaina a kasa nace
"Kayi ha'kuri baba"
"Allah yayi Miki albarka,Saleh yazo ya sameni kuma har ya turo magabatansa,kamar yanda lokaci yake,Nan da watanni shida za'a d'aura aurenku da yardar Allah"
Sunkuyar da kaina nayi Ina godiya a zuciyata,sakamin albarka yayi sosai sannan y sallameni,Ina zuwa daki kuwa sai ga Kiran Saleh
Cike da farin ciki na daga yace
"My angel"
"I'm" na amsa cike da fara'a
"Hmm munso mu cutar da junanmu fa" ya fad'a yana dariya a hankali
Cikin sanyin murya nace
"Yaya fa yacemin ka kusa aure,ya akai haka?"
"Eh to dogon labari,kamar dai or dinnan Nima li'kamin ita akayi,Yar uwata ce a gidanmu ta taso Kuma Allah ya bani ikon kuncewa na barwa tuzurun yayana ita,tare za'ayi aurenmu insha Allah,ke Kuma ya mutumin naki?"
"Ban saniba wlh,Domin banji daga gareshi ba"
"Har yanzu mamaki nakeyi" ya fad'a cikin daddadar muryarsa
"Ni kuma.tsoro abin yake bani,na kasa gaskata abin"
"Mu daiyi fatan Alkhairi" ya fad'a tareda canza hirar,tamkar wadanda suka Dade Nan muka hau zancen kalar fentin gidan da kalar kayan gado da labulaye da kujerun da ya dace a saka,har zancen kayan kicin mukayi dashi
A Daren sulaiman yazo ya sameni yake sanarmin zai koma Russia ya samu aiki,dama aurena ne zai zaunar dashi Kuma Allah ya taimakeshi ya rabamu, bracelet din da ya bani na maida Masa ya karbi abinsa ya tafi
Abu kamar wasa kamar baza ayi ba har watanni shida sunzo karewa,gida ya cika ma'kil da Yan biki na kusa da na nesa,no kuwa tuni na birkice,mutane gareni lungu da sa'ko,duk na susuce wajen aika katin gayyata,Katina 700 aka buga na kamu amma kaf sun Kare,na rasa Dani da mama was yafi gayya
Biki biyi kawai mukayi sai gidansu ango suka shirya liyafa d'aya,an gayyaceni da Yan tawagata mutum 100 kawai
Bikin nasu yayi matukar haduwa,saidai na zama bare a ciki, dukkansu Yan uwane,anan Naga Yan uwantaka,jikina Kuma yayi sanyi yanda wasu daga cikin matan wurin ke wurgomin kallon banza
Anzo wurin da banaso wato li'ki,a rayuwata na tsani zubar da kud'in da ake a wurin biki,daga iyayen amarya har na ango ai sunada bukata,meyasa bazaka kunshe ka Basu ba sadai ka zubar saboda duniya ta gani?
Kiran dayan angon aka fara you da amaryarsa sultana,murmushi ke saika daga fuskarta,oh,da tuni itace matar Saleh,tsayawa sukayi a fili Nan fa yan uwa suka fara musu barin kud'i,
Bayan an gama asarar kud'in aka kirani,danginmu Basu damu da li'ki ba,Nan dangin saleh suka fito suka.fara zuba Masa kudade,shima nashi ya ciro ya fara li'kamin ganin nawa dangin ba Wanda yazo,MC na ta min habaici wai ko baa Sona ne nikuwa ko a jikina,saida wata take ta kar'bi Mike din tace
"Jamaar dake wurinnan Babu mai taimakawa wannan amaryar ne ua fito ya fanshi danginta?da alamu baby canji a hannunsu"
Daga yanda tayi maganar nasan zagina take,gashi sun'ki Dena yiwa Saleh li'ki,ta Dole dai aka Sanya Yan uwana yimin li'ki,Nima kuwa Naga gata ta wannan fannin,saida aka cikawa masu kida aljihu sannan muka bar wurin Raina a dagule,Domin harda masu kallona sumin tsaki,na taorata sosai a Raina Ina cewa wani irin Rami nake kokarin jefa kaina?
An gama taro lafiya har an d'aura aure,bazaka ce Saleh suruki bane Domin bajewa yayi a gidanmu ya cika tumbinsa sannan ya dauki hanyar gidansu,duk yanda zaiyi ya sameni naki Domin Saleh d'aura aurennan naji kamar na fita da gudu nace a kunce,tuni kewar gida ta fara kamani
Nasha nasiha kala kala,na kuma sha gudunmawa,kowa yazo yace iyayena mutanen arzi'ki ne
Iyayena da suka mutu basu barmin komai ba sai gidan da.suke ciki,Kuma.mahaifina yana da arzi'ki,kyauta ce dashi sosai a haka ya karar da duk abinda ya mallaka,sai gashi Naga gatan da nayi zato ba
Kayan gado a aka kawomin set uku kyauta,Banda kayan kicin da bansan adadinsu ba,kud'i kuwa sai godiyar Allah Domin an rubanyamin sadakina kusan biyar
Da akazo kai amarya kuwa Nan na shiga daru,da kyar aka banbareni jikin mama
Tunda muka d'au hanyar gidansu Saleh gabana ke faduwa, innalillahi wa inna ilaihi raji'un naketa maimaitawa a tunanina ma accident zamuyi sai gaahi munje lafiya
Part din mahaifiyarsa aka nufa Dani Domin danka mata amanata
Fuskata a rufe saboda haka Banga komai ba,naji dai sallama da gaishe gaishe,bayan sun gama.bayanansu na manya Mahaifiyar Saleh tace
"To mu a al'adar gidannan idan aka kawo Mana suruka,zata zauna anan har mijinta yazo ya dauketa,ni zan danka Masa amanar da kuka barmin,"
Ba wani ja inja suka barni anan suka fice,suna fita naji ance
"Tashi ki zauna Kan kujera"
Tashi nayi Babu musu na zauna,
"To amarya bud'e fuskarki Mana mu ganki mu gaisa',Domin mijinki ma bazai iso ba sai nan da kusan AWA daya da rabi"
Bud'e fuskata nayi kaina a sunkuye,umarni akamin na daga kaina ba musu nayi,dayar amaryar wato sultana na gani ta hard'e kafa Kan kujera Tana cin dambun shinkafa
Nunani tayi da cokalin hannunta tace
"Yaya maymu,Kinga fa akan abinda uncle ya kasani"
Wadda aka Kira da Yaya maymu tace
"Ai wallahi Namiji butulu ne,ita ba kyau ba,uban me.ma ya gani a jikinta?
Sultana Bata tanka ba taci.gaba da cin dambunta,Mata hud'u ne a d'akin Banda mahaifiyarsu,d'aya daga cikinsu ce ta taso tace
"Ai wallahi sale y badamu,aikin banza aikin wofi ya'ki jininsa akan wannan abar,wallahi hajiya ji nake kaman na shaketa saboda tsana"
Nayi zaton mahaifiyarsu zata musu magana Amma ga mamakina sai Naga tayimin wani kallo Mai d'auke da tsantsar tsana,cikin Isa da gadara tace
"Waye Mahaifinki?"
Daga Nan nasan kaddarata ta zaman aure ta fara
5
Gyaran murya nayi nace
"Mahaifina ya rasu"
"To Wanda Kika taso a wajensa fa?"
"Dan kasuwa ne"
"Kasuwancin me yakeyi"
"Man gyad'a"
Had'a Baki sukayi suka kalleni sukace
"Man gyad'a?"
Ba tareda na d'auki hakan cin fuska ba nace
"Eh,man gyad'a"
Ri'ke ha'ba yaya maymu tayi tace "kinji fa kursum,wai man gyad'a for God's sake,ai duk danginmu Babu mai kaskantacciyar sana'a kaman shi salen,shine zai d'auko mana Yar Mai saida man gyad'a a kasuwa"
Sosai naji zafi a Raina,Domin sana'ar baba tafi karfin a kirata kaskantacciya,shi yake sayen gyad'a ya bayar a Masa Mai,ya saida ga manyan dealers na man gyad'a,a Nigeria jihohi kad'an ne baya Kai man gyadansa,Kuma yana ri'ke iyalinsa Daidai gwargwado harda ni ma Yar karere,Kuma dai a kayan aurena kowa yasan Babu kaskanci
Bance musu komai ba na sunkuyar da kaina,sunata sukar sana'ar baba da ta Saleh,ni kuwa alfahari nake da sana'ar mijina,abin mamaki duk maganganunsu sultana Bata tankawa saidai ta kalleni irin kallon tausayi ta kalli Yan uwanta ta girgiza Kai
A hankali na lura da mutanen dake d'akin,yayan hajiya Mata uku ne a d'akin,Yaya maimu,wadda nasan dai sunanta bazai wuce maimuna ba,sai Kuma ummukursum,sai Kuma wadda take kaman ta shakeni,naji itama sunanta aymana,dayar da na lura Bata sanya baki ba Naga kaman sirika ce irinmu
"Ke Kuma jumana kinyi shiru ko?"
Murmushi jumana tayi tace
"To ni ai sirika ce me zance?aikin Gama dai ya Gama tunda har hajiya ta Masa magana ya'ki ji saidai mu zuba Masa Ido,ni kaina kunyar idon hajiya yasa na amince da auren uncle Hashim,Kuma gashi ta sanyamin albarka yanzu son junanmu muke sosai,Banga abin 'ki a auren danginka ba,dukkanmu fa cousins ne meye abin 'ki a sultana?yarinyar da ta taso Tana masa Ladabi da biyayya,Kuma a gabansa ta girma balle ma ace wani abun,mudai ki sani bilki,bama maraba dake cikin danginmu ko kad'an "
Tashi sultana tayi ta nufi wata kofa da plate din hannunta,da alamu kicin ne,fitowa tayi da plate biyu a hannunta tazo ta ajiye a gabana tace
"Kunga ki barta haka.mana,daga kawo amarya zaku saka mata ciwon Kai,ba Dan ni akeyi ba?to na yafe na yau kwa d'aura gobe,amarya sauko kici dambu,ko zakici shinkafa?akwai kunun aya da zobo wanne kikeso?"
Kallon dambun nayi tuni kwantacciyar yunwata ta taso,Amma ai bazan zage darena na farko a gidan surukai naci abinci ba
Girgiza Kai nayi nace
"Nagode,Amma na koshi"
Ai Ina gama fad'in haka cikina yayi wani Kara alamun yunwa,kunya ce takamani ita kuwa sultana murmushi tayi tace
"Idan kina kunyarmu ne ki ma Dena,Domin cikinmu Zaki zauna,sauko ki cika cikinki Bari na d'auko Miki lemo"
"Um,taci?tun dazu take kallon kofa Tana rawar kafa ita zata shiga daki da miji taci kaza,rabu da ita taci kazar" aymana ta fad'a Tana wani.yatsine fuska
Bansan lokacin da nace
"Kuyi ha'kuri wallahi ba haka bane"
"Kuma dai" kursum ta fad'a tana kallona,Dole na d'auki dambun na fara ci Domin fa Raina ya sosu,idan bankai Abu bakina ba za'a iya samun matsala
Dambun kuwa yayi Dadi,gefena sultana ta dawo ta zauna tana cin dambunta plate na biyu,a hankali nakeci ina jin Yana kokarin shakeni Amma naki daukan zobon Nasha
Ina cin dambun naji sallamar su Saleh,maza uku ne suka shigo d'akin,sune ragowar yayan hajiya kenan,kallona Saleh yayi yace
"Kut,wa ya baiwa amaryata dambu?salan ta shake ko?"
Dariya sultana tayi tace
"Uncle nice,Kuma da bataso ai bazata ci ba"
"Ni amaryata nama zata ci ba dambu ba,ke dai da bakisan dadin nama ba kick dambunki" ya fad'a cikin zolaya,dariya tayi tace
"Ai naji Dadi da baba cin Naman,babu wani abun Dadi a nama nidai a wurina"
"Shiyasa na siyo Miki