NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 41

30K to 33K   out of 120.7K words

na nuna masa huda, d'aga girarsa yayi yace

" To ai bacci takeyi, amma kuma kinyi gaskiya, ma had'e anjima "

Zumbura baki nayi tareda lan'kwashe 'kafafuwana a kwancen nace

" Dama ka saba min haka, aikwa ranar da zan rama bazaka ji sweet ba "

" Haba matata sarkin hanzari, kawai na fara kunnaki ne yanzu kinsan button d'in naki sai ayita dannawa ya'ki kawo wuta, amma idan aka kunna da wuri da zarar an danna saidai aga haske "

Tashi nayi na kai masa dukan wasa nace

" Kai ka sani dai, ba wani button Mai wuyar kunnuwa kai d'inne baka gama 'kwarewa a kunnawar ba, amma karka damu ilmi kogi ne a hankali zaka koya "

" Au haka zaki ce? Yarinya tausayinki nakeyi shiyasa amma idan na kunnaki yanzu sai kinzo kina ro'kona "

" Bismillah " na fad'a tareda gintse dariyata, cikin hanzari ya kaini 'kasa tareda d'age rigata, hannunsa naji ya fara shafa gefen 'kuguna cikin wani salo na daban, bakinsa ya kai ya sumbaci wurin na cije baki, cikin sauri nace,

" Kayi ha'kuri dan Allah, na yarda ka sani "

" Tukuna ma dai " ya fad'a tareda 'kara sama da rigata, cikin sauri na ri'ke rigar tareda girgiza kai, domin kuwa na tabbata Yana kaiwa wajennan zan manta da Huda a palon, dariya yayi ya koma kujera ya zauna kaman baiyi komai ba yace

" Yunwa nake ji fa "

" Sai ka jira na gama recovering "

Dariya yayi sosai yace

" Ba'a raina 'kwazon namiji, sai a kiyaye gaba "

Wayarsa ce tayi k'ara saida ta kusa katsewa ya amsa, yana gama amsawa yace

" Hajiya ce, wai gobe zan kaita unguwa "

*Kuyi ha'kuri da wannan za'ayi program da ni ne, insha Allah na gobe zaifi wannan yawa*
18

"Nima Mama tace zasu zo bansan da wa zasu zo ba dai, na sanar mata zancen Huda ".

" To Allah ya kawosu lafiya, sai ki shirya musu abinci mai kyau ko? Me ya kamata ayi ne? "

" Sai azahar zan dawo fa, kaga ba damar na had'a musu wani Abu idan ba yamma zasu kai ba ".

" Duk da haka dai ayi musu wani abun ko a siyar musu wani abun Kar tazo gidan namu babu komai ".

Amsa masa nayi da to na nufi kitchen na hau girki, saida ya dawo daga masallaci muka ci abincin saidai ina ganin yanayinsa yana cikin tunani, bance masa komai ba domin nasan tunanin fitarsu da Hajiya yakeyi.

Sai 8:30 Huda ta farka taci abinci ta hau yi mana hira, gajiya Saleh yayi ya kwanta ya barni da ita ina fama sai bayan 11 na samu tayi bacci.

Da wuri na tashi na fara aikace aikacena, tare da Huda muka farka na goyata naci gaba da aikina.

9:30 na gama shirya ta na kaita wurin sultana, cikin sauri na ajiyeta da kayanta nace

" Bata ci abinci ba sai kaman 10 haka zataci "

" Dan Allah kawai ki tafi da ita Ni wallahi bazan iya had'a yara biyu ba wahala yanzu kuma na'ki kula da ita sai ace dan ba 'yata bace, nidai kinga dama baki ta'ba zuwa da ita asbitin naku ba yau dai ki kaita a saka muku albarka ".

Duk yanda naso Sultana ta ri'ke Huda ta'ki sam, da na takura mata sai tace bata son abinda zai had'ata da Huda har shaid'an ya fara Mata hud'uba, dole na tafi da Huda wajen aikina inata tunanin ta yaya zanyi aiki da Huda.

Tunda na shiga asbitin Huda ta bar hannuna, abin mamaki duk 'kyuyar da Huda keyi a gida bata yi a asbiti ba, a nutse nayi aikina Huda na hannun mutane har lokacin tashi yayi.

Saleh ne yazo ya d'aukeni saida muka yiwa su Mama siyayya tukun muka je gida, a gidan na samesu domin na fad'a mata lokacin da na tashi.

Bashi kayan nayi muka nufi sashin sultana, tar'bar mutunci tayi ma su Mama kuma ta hanasu godiya nan dai muka sha hira, Sultana akwai surutu cikin mintina ta saba da su mama da aunty.

Kirana Saleh yayi a waya ya sanarmin ya tafi kai Hajiya unguwa.

Bayan mun koma part d'ina nake basu labarin irin zaman da mukeyi da Sultana, cike da mamaki aunty tace "kinga ikon Allah, duk wani tashin hankali ta wajenta za'ayi tunanin zuwansa amma abin mamaki zuciyarta a tsaftace, Allah ya 'kara had'a kanku da ita kuma ya kareta daga rud'in 'yan uwanta".

Tsaraba suka kawowa Huda na kayan ciye ciye da kayan sawa da 'kyar suka zauna suka yi la'asar sannan suka tafi, wai kar Saleh yazo ya same su.

Sai bayan isha Saleh ya dawo, yanayinsa na kalla naga da alamu abun rashin dad'i ya faru amma ban tambaya ba, abinci na kawo ko kallon abincin baiyi ba ya 'kurawa wuri d'aya ido.

"Me ya faru ne boo-boo na? Naga kamar kana cikin damuwa". Na fad'a tareda 'kura masa ido, bud'e baki yayi zaimin magana sai ga mama ta shigo da yaya maimuna, bansan me yaya maimuna keyi a darennan a gida ba ki meye matsayin mijinta da yake barinta wannan uban yawon oho, gabana naji ya fad'i na zame na koma 'kasa na zauna.

Fuskokinsu babu yabo babu fallasa yaya maimuna tace "ya fad'a miki abinda ya faru ko?"

"A'a yana dai shirin fad'a kuka shigo" na fad'a kaina a 'kasa.

"To bilkisu ina so ki bud'e kunnunwanki da kyau ki saurareni, idan baki sani ba yau ki sani, mijinki yana cikin matsala babba, fitar da kika ga munyi wajen malami muka je dashi".

A raina na ambaci 'subhanallah', tunda aka ce wajen malami nasan anzo min da gagarumar magana.

" A 'yan kwanakinnan komai na mijinki yana lalacewa, shagon nasu ma basa samun aiki sosai, gashi kud'i da zarar ya shigo hannunsa kamar wuta ta cinyesu, ke kanki matsalar haihuwarki akwai sa hannu a ciki haka shima matsalarsa hannu aka sanya masa, gashinan a gabansa akayi komai kuma da bakinsa ya furta matsalolinsa".

Kallon yaya Maimuna nayi nayi na sauke kaina, wani irin hannu za'a saka masa? Nasan cewa basa samun aiki sosai a shagonsu amma yanzu ai ba lokacin aure bane, kuma rufin asiri dai Saleh yana dashi tunda zamu ci mai kyau musha mai kyau, rashin kud'in da take fad'a ya sanarmin ya fara tara kud'in IVF d'ina ne.

"Malam ya fad'a mana cewa akwai wani abokin cinikinsu da suke sana'a iri d'aya shine baya son ci gabansu, saboda anfi sayen kayansu akan nashi shine ya jefe kasuwancin nasu basa samu kema kuma an sanar mana jefeki akayi domin karki haihu dashi ya samu albarka, akwai magunguna da aka bayar suna hannun Hajiya, daga ke har shi zaku dinga zuwa kuna sha a can domin munsan halinki, kuma wannan abun dan amfanin kanku za'ayi ke da shi,".

To kawai na bata amsa tare da godiya, bansan me zance mata ba amma maganganunta sam basu gamsheni ba, amma idan ayar 'kur'ani ce zansha domin nayi imanin ba'a cutarwa da ita.

Bayan fitarsu Saleh yace "yanzu kin yarda da Maimuna?"

Murmushi nayi nace "to boo-boo na ai bazasu cutar da kai ba ko? Idan zasu iya min wani abu kai bazasu iya ba dan haka karmu damu kwana kad'an ne an gama ai".

Lura nayi dai hankalinsa bai kwanta ba nace "yau kaga farin jinin da Huda tayi a asbitin mu? Nayi mamaki ma da batayi 'kyuya ba amma fa tayi ciye-ciye, kaga ma abinda su Mama suka kawo mata".

Bud'e kayan nayi ina nuna masa ina yaba kayan har saida naga yanayinsa ya fara dawowa tukuna.

Washegari 7am sai ga kiran hajiya wai muje musha magani kafin na fita school, haka na d'auki Huda muka fita ko wanka banyi ba.

Ina gaida hajiya ta mi'komin wani ruwa a cup, babu alamun magani a cikinsa ba tare da wani tunani ba nayi Bismillah na shanye, saida ta bani abubuwa kala uku duk nasha, biyun dukkansu masu kala ne kaman an zuba wani abun amma hakan nasha a raina inada 'kudurin ba abinda zai sameni sai wanda Allah ya rubuta min.

Kasko ta kawo ta zuba turare ta saka a gabana, Ina sha'kar turaren na fara tari harda hawaye, a haka nayi turarennan na gama ta d'auke.

Shi kuwa Saleh abu d'aya aka bashi yasha shima kuma ruwa ne fari 'kal, take zuciyata ta rayamin zallan ruwa ne a ciki babu komai, jikina yayi sanyi domin tunanina tare za'a bamu komai, zargin Hajiya ne ya shiga raina zuciyata ta fara rayamin cutar dani hajiya takeso tayi.

Na samu na lalla'ba sultana ta kar'bi Huda domin zan kai yamma.

Tunda na fita kaina ya fara ciwo,  magani nasha a asbiti na fara aiki amma ciwon kan ya'ki sakina sai ma 'karuwa da yake, idanuna sunyi ja duk jijiyoyin kaina sun bayyana, wajen likita naje ya dubani yace migraine ne ya kamata na samu hutu gobe ma kar nazo aiki.

Kasa fita nayi na kwanta na jira zuwan Saleh, a hakan ma ni kad'ai nasan me nakeji a jikina gaba d'aya na had'a gumi.

Da 'kyar na taka na fito na shiga mota muka tafi, kaina ke juyawa ji nake kamar ana bugamin guduma a cikin kaina, dafe kan nayi ina addu'ar da duk tazo bakina, bud'e idona nayi naga komai yana juyawa a idona, sunana naji Saleh yana ambata kafin komai ya zama duhu.

Farkawa nayi na ganni kwance a kujerar hajiya, warin turare naji nayi saurin toshe hancina ina kallonsu cikin mamaki, d'agoni Saleh yayi yana min sannu daidai fitowar Hajiya, kallona tayi tace "ai alhamdulillahi da aka fara shawo kan abin tun yanzu ashe da matsala take zaune ba tare da ta sani ba, yanzu banda Allah ya kaimu wajen malaminnan ina zamu san tanada matsalar iska? Gashi ana mata turaren kuma ta wartsake, da ana nuna maka kana ganin cutar maka da mata za'ayi gashinan ka gani da idonka".

A tsorace naja baya daga gareshi, zuciyata ke bugu cikin sauri, me nakeji Hajiya na ambata? Aljanu a kaina? Gaskiya wannan zancen ban aminta dashi ba me yake faruwa ne?

Gaba d'aya na hargitse tsananin tsoro ya shigeni, tashi nayi na nufi hanyar fita hajiya tace "ka ri'kota mana kar ta fita tayi titi".

Jiki a sanyaye Saleh ya nufoni, zuciyata tana fad'amin na rungumeshi ko naji sassauci a raina amma yana kusantoni na tsinci kaina da ja baya daga gareshi, murya 'kasa 'kasa yace "Bilkisu ki tsaya mana Babu abinda zan miki, ki kwantar da hankalinki okay? You are all right dear zo nan".

Bud'e hannunsa yayi alamun naje yayi hugging d'ina amma kamar an kafeni a wajen, wasu zafafan hawaye naji sun zubomin domin bansan me yake damuna ba, zuciyata na muradin Saleh amma gangar jikina bata so ta kusanceshi, wani ruwa hajiya ta bashi tace ya yayyafamin ya kar'ba babu musu ya zubamin ruwannan, banji wani sassauci ko 'karin ciwo ba.

"Ke bilkisu tashi kije gida kai kuma Saleh zauna anan kar kaje ka takura mata".

Tashi nayi ba tareda na sake ko waiwaye ba na nufi sashina, innalillahi wa Inna ilaihi raji'un nake ta ambata a bakina na rasa ma wani irin tunani zanyi.

Kafin na shiga na tuna da huda dake wajen Sultana, Kar'barta nayi jikina yana ciwo na shiga gida, kwanciya nayi ina tunanin abinda ya faru, saidai na kasa tunani mai kyau akan hakan.

Sai bayan isha Saleh ya shigo gidan, ina zaune ina gyarawa Huda gashinta yayi pecking kumatuna, ji nayi gaba d'aya tsikar jikina ta tashi nayi murmushi da 'kyar.

Tare muka ci abinci na saka Huda tayi bacci sannan na tambayeshi me ya faru dani bayan ya d'aukoni, 'ko'karin canza maganar yayi nace "boo-boo na kar muyi haka dakai tun safiya nake fama da ciwon kai sannan kuma naji hajiya tace inada matsalar aljanu, ka fad'amin me ya faru dani".

Gyaran murya yayi yace "bayan na d'aukoki naga yanayin fuskarki ya fara canzawa, idanunki sun juya, ina kiran sunanki kuma naji kin fara wani irin kuka da abubuwa, har muka zo gida kinayi sai na shiga dake wajen mama, kuma cikin ikon Allah tana fara miki turarennan kika farka".

"Boo-boo na ya zanyi? Shekara ta sama da ashirin a gidanmu ba'a ta'ba samuna da matsala makamanciyar wannan ba sai yanzu? Ina ganin na sanarwa Mama domin wannan matsalar tanada illa sosai".

"A'a boo, karki fad'awa Mama hankalinta ya tashi, tunda har Hajiya tana iya shawo kan matsalar alhamdulillah kuma da yardar Allah bazai zamar miki babbar matsala ba".

Shiru nayi masa domin bana son jan zancen, amma har ga Allah ban aminta da Hajiya ba.

"Haba boo-boo na ki dena damuwa mana, kinsan a kowane yanayi ni zan zauna dake ban damu da matsalarki ba, kai boo-boo na ko maita ce ta sameki  wallahi ni zan zauna dake ba tareda naji wani abu a raina ba, ina sonki a kowane yanayi karki damu, kuma idan ma maganin Hajiya ne baki aminta dashi ba ni dake zamuje mu nemi wani wajen banaso ki fad'awa Mama ta tada hankalinta ne".

'karashe maganar yayi yana d'agoni zuwa cinyarsa, ji nayi kaman na zauna akan 'kaya amma na daure na zauna a hakan, wani hawaye naji yana zubomin na rashin dalili, hannunsa ya sanya yana shafa bayana amma tamkar yana shafa min wuta nakeji, juye juye nake a jikinsa na rasa yanda zanyi da raina sai kuka da nakeyi.

Kasa jurewa nayi na sauka nace "boo-boo na jina nake kamar a kan 'kaya".

"Afuwa boo, na fahimta dama Hajiya ta fad'amin hakan kiyi ha'kuri kinji? Wataran sai labari mu dage da addu'a kawai"

Zama mukayi jugum jugum, a cikin raina babu abinda nake bu'kata kamar mijina amma kuma gangar jikina ta'ki aminta da hakan, sallama nayi masa na tafi sama na kwanta ina juyi ni kad'ai har ya hawo shima

Addu'a ya sanyani nayi shima yayi ya shafamin ya kwanta ya rungumeni ta baya, a hankali na janye jikina daga gareshi, can gefe ya matsa ya barni da halina.

Ina jinsa ya fara bacci amma ni bacci yayi 'kaura daga idona, Huda na d'auka na rungumeta a jikina ina jin ciwon kaina na dawowa, agogo yana buga d'aya na dare na fara jin 'karan 'kofa, kuma a sanina Saleh ya rufe mana 'kofa, sannan ko da ace ta bud'e ba irin 'kofar da iska zata dinga kad'ata bace.

D'ago kaina nayi a hankali naga 'kofar tana yawo ita kad'ai, wani irin 'kara 'kofar tayi lokacin da ta rufe kanta, kwanciya nayi na rufe kaina cike da tsananin tsoro ina jin 'kofar na rufewa da bud'ewa da kanta, ban samu runtsawa ba har saida aka fara kiran sallar asuba wannan 'karan ya tafi kamar ba'a yi ba.

Tashi nayi na kasa aikata komai a gidan sai bin kujera, ko breakfast na kasa had'awa balle wankan Huda da nawa wankan, haka ya fita ya barni da kayan bacci a jikina.

Kasancewar na tashi da period bana bu'katar na tashi nayi sallah, ina kwance wuri d'aya har Huda ta fara kukan yunwa, cornflakes na had'a Mata da 'kyar jikina har rawa yakeyi tamkar nayi aikin wahala.

Komawa nayi na kwanta, kamar wasa babu abinda nakejin dad'insa kamar kwanciya, shigowa Hajiya tayi ta bani magani nasha, a yanda Saleh ya fita ya samemu haka ya dawo ya samemu daga ni har Huda.

Tun abu yana 'kan'kani har ya fara zama babba, na koma 'kazama ta 'karfi da yaji cikin kwanaki kad'an, gashi ba sallah nake ba ko alwala banayi balle naji sanyi a raina.

Gaba d'aya na dena girki bana wanka sai Saleh ya yimin dole, sai nayi kwana uku banyi wanka ba har wani wari ke fita a jikina, ga period ga babu tsafta, sannan na Saba na kwana hud'u sai gashi na doshi kwana goma.

Saleh ko sunana ya ambata sai naji hawaye, idan yana zaune a gida na dinga 'kunci kenan amma da zarar ya fita kamar an sakani a aljanna, shi kanshi ya koma wani 'kazami na 'karfi da yaji.

A wannan yanayin hajiya ta sake bijiro masa da maganar aure, ranar tazo bani magani.

Kallona yayi yace "Hajiya idan nayi aure bilkisu na cikin wannan yanayin ban mata adalci ba, na zama butulu ko da ace zanyi auren sai matata ta samu lafiya bazan iya aure tana wannan halin ba".

Kallona tayi tace "kai har yanzu wannan kake kallo a matsayin mace?kwanan rigarnan hud'u a jikinta babu canji, babu abinda ke tashi daga jikinta sai 'karni, dubi gidanka ka ka dubi kai kanka yanda ka koma, hatta wannan yarinyar dake zuwa ta wuni wajenku ta koma kaca kaca da ita, Saleh dole ne ka sake aure a wannan karon ko fishina ya tabbata a kanka".

Dafe kansa yayi yace "Hajiya ki kalli bilkisu a matsayin 'yarki mana, idan ace kursum ce take wannan halin mijinta zai 'kara aure ya zakiji? Idan aurene zanyi ita kanta ta aminta da aurena amma sai ta sami lafiya zanyi auren dan haka kiyi ha'kuri har ta warke".
19

Shiru yayi mata suka kalleni dukkansu, nima idona na kansu kuma ko a jikina zancen aurennan nasa, indai auren zai shafamin lafiya wallahi yayi domin azabar da nakeji ta isa.

Idan d'aya na dare yayi na fara jin iface-iface kenan da wata iska tana yawo a kaina har sai gari ya waye, daren jiya ma wata murya Mai matu'kar tsoratarwa naji tana cemin 'ki tashi ki fita' har asuba sannan na samu salama.

Gari na wayewa kuma zan fara ciwon jiki mai tsanani wanda ko hannuna bana son motsawa, ga bleeding da nakeyi da ko ta kansa bana bi, nidai nasan rabona da sallah 13 days kenan duk a zaman period nake.

Wajen aikina na aika Saleh yayi reporting banida lafiya har ma 'kawayena sunzo dubani, addu'a bata zama a bakina da zarar na kama sai na kasa 'karasawa.

"Saleh, zan sake maka maganar aure a Karo na 'karshe, idan har baka amince ba wallahi tallahi kaji na rantse saidai ka fita ka barmin gidannan domin bazan zauna da d'an da baya ganin darajata ba, na d'auki cikinka wata tara, nayi na'kuda na haifeka na shayar da kai na raineka ka girma, wai har kaine zaka kalleni ina fad'a kana mayarwa, ka gyara halinka kafin na dawo ko kuma dakai da wannan majnuniyar matar taka saidai ku bar min gida".

Ficewa tayi na bita da kallo hawayen takaici na bin idona, zama Saleh yayi wajen 'kafafuna yace "kiyi ha'kuri boo Allah yana tare damu yasan halin da kike ciki zai yaye maki kinji?"

Gyara kwanciyata nayi yace

"Boo d'an tashi mu gani"

Tashi nayi da 'kyar ya nunamin stain d'in dake kan kujerar, sai yanzu na tuna pad d'in jikina tayi

11 / 41