NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 41

54K to 57K   out of 120.7K words

zama ina shiga d'akin. "Boo-boo ya kamata muyi magana".

"Kallona yayi idanunsa har yanzu na nuna 'bacin rai, murmushin takaici yayi yace "wace magana zamuyi kuma? Ai mun gama magana".

Kujerar mirror naja na zauna nace "zamuyi magana ne irin ta masu hankali ba maganar da zamu dawo daga baya muna nadama ba"

"Sunce zakiyi haka ai" ya fad'a can 'kasan ma'koshinsa da alamu baisan naji ba, controlling kaina nakeyi kafin na fashe domin Nima na fara zuwa bango, had'e hannuna nayi nace "su waye sukace zanyi haka? Bayan wannan 'kazafin kuma me sukace na aikata? Boo-boo meyasa bazaka gane intension d'insu a kaina ba? Burinsu su rabaka dani su rabaka da farin cikinka, idan har suna sonka zasu so abinda kakeso amma dubi tunda nazo suke nunamin 'kiyayya har takai ga sunyimin wannan sharrin, meyasa ba zakayi tunani irin na masu hankali ba kaga inda wannan abun ya dosa?"

"Kina nufin duk abinda nayi a cikin hauka ne? For the last time Bilkisu stop dragging my family into your mess, danginka danginka, komai dangina har a yanzu da suke fafutuka da mara lafiya laifinsu kike gani, sai yaushe zaki fara hangen laifinki ki dena ganin na dangina?!!"

Ya fad'i maganar cike da bacin rai saboda haka na maida masa martanin da ya dace dashi "saboda danginka sune matsalata a rayuwa!! Na taso ba uwa ba uba amma ban ta'ba jina cikin maraici ba saida nazo na zauna dakai, kuma danginka sune damuwata sune laifina, wa kakeso nayi pointing a matsayin mai laifi? A wajensu har abada kai mai laifine indai kana tare dani, Kai kasan me sukacemin farkon zuwana gidannan? Kuji tsiya wai 'yar gidan masu man gyad'a ya d'auko, bayan tsiya da son duniya ya 'kare a kansu, gata da dukiya inada su fiye da tunaninka, kud'inka sunyi kad'an na 'boye domin nafi 'karfinsu, ninkinsu za'a iya bani meyasa kake tunanin zan wula'kanta kaina akan wannan tsiyar? Menene miliyan biyu? Me akayi aka yisu?"

"Me akayi aka yisu da kika 'boyesu kika kunyatani a gaban dangina ko?!! Bilkisu duk actions d'inki suna sake fito da rashin gaskiyarki ne, sannan kina min gorin dukiya ai Allah ne yake bada ita, kuma cikin ikonsa sai ya baka dukiyar ya hanaka wani abu na jin dad'in rayuwa, dukiyarku ba komai bace tunda bata yi miki maganin matsalarki ba, sannan kika sake ambato dangina a wannan maganar zan miki abinda baki ta'ba zato ba, nasan duk zaman da kikeyi a gidannan a gaban idona ki nuna you are innocent a bayan idona kina wula'kantani".

Tuni 'bacin raina yayi exploding, dama ance ba'a kai mai ha'kuri bango abin baya 'karewa da kyau " me kuma sukace? 'karshen magana suce Ina kawo maza gidanka Wanda a wannan state din da kake zaka amince da komai da sukace, ka kasa ganin greediness nasu, kayimin gorin haihuwa Wanda Allah ne yake bayarwa kuma kud'in iyayena bazai ta'ba bani 'ya'ya ba, a wannan lokaci na fara nadamar shigowa ahalinka Wadanda basu san darajar mutane ba, na godewa Allah da ya hanani haihuwar ya bani iyaye da dangin da sukasan darajata da mutuncina, wad'anda Basu da son zuciya da son kansu, domin akan na zama uwa mai son zuciya irin mahaifiyarka gara na mutu ban haihu ba".

Ban ta'ba tunanin wannan maganar zata fito daga bakina ba saidai babu damar canzawa, illar magana kenan ba'a maidata ciki idan ta fito ta fito kenan, kuma illar da zatayi ya ninka zafin fitarta, saidai ban ta'ba tunanin maganar da zata fito daga bakinsa zatayi muni haka ba...

"Ki tafi gidanku NA SAKEKI".

Tamkar ya sakar min bomb a kaina naji, ja da baya nayi cike da tsoro da fargaba, babu abind nakeso na gani a fuskarsa sai nadamar abinda ya aikata amma sam babu wannan, saidai muryarsa 'kasa-'kasa yace "bazan zauna da matar da zata dinga cin zarafina da na iyayena ba, duk abinda nayi miki ki rasa dame Zaki sakamin sai zagin mahaifiyata". Yana fita na zube a wurin, ko a mafarki ban ta'ba tunanin Saleh zai iya sakina ba ko da kuwa na mari uwarsa, Ashe nayi kuskure.

Ko d'igon hawaye bai zuba daga idona ba, gaba d'aya gidan ya fitarmin a raina banaso na kwana a cikinsa dukda 9:30 ma ta gota, akwatina na janyo na fara zuba kaya saidai yanda nakeji a raina bazan iya fasaltawa ba, a lokaci d'aya ina Jin takaici, bakin ciki, nadama, da tausayin Saleh, me yake damuna ne bayan dun abinda yayimin tausayinsa nakeji? Idan har hakan zai sanya duk mu dawo hayyacinmu musamman shi....Allah yasa hakan ne yafi alkhairi".

Na gama d'aukan iya kayan da zan bu'kata sannan na kira jabir, ko Dan dangantakarsu da jabir bazai ji kunyar sakina ba? Yanzu bazaiji kunyar kallon mama da baba ba da auka zamar masa tamkar iyaye? Har d'inki iyayena ke yiwa jabir da Saleh, Banda kud'in makarantar da aka taimaka Masa dashi amma Dan Adam butulu ne.

Saida na kirashi sau uku a na hud'un ya katse ya kirani, sai yanzu naji kuka na tahomin amma na danne, muryarda naji cikin zolaya yace " autar mama you miss me ko? I miss you too kiyi ha'kuri na kwana biyu ban kiraki ba wallahi abubuwa sunmin yawa shi kuma Saleh bakya barinsa yayi abinda ya dace, dama inaso nazo na ja miki kunne mijinki ya fara wasa da aikinsa".

Numfashi naja nace "Yaya dan Allah alfarma nake nema, ko zaka zo ka d'aukeni?"

Tuni salon muryarsa ya canza yace "nazo na d'aukeki kuma bilki? Me ya faru? Bakida lafiya ne? Meyasa mijin naki bazai kawoki ba? Ko motar ta samu matsala ne?".

"Yaya idan kazo duk zan maka wannan bayanin, dan Allah kayi sauri kaji".

"Bani minti ashirin ganinan" yana fad'a ya katse wayar, kayan jikina na fara cirewa Wanda yayi dai-dai da shigowar Saleh, kallo d'aya yayimin ya kauda kansa Ni kaina jinsa nayi tamkar ba muharramina ba bayan ya furta kalmarnan, yanzu su mama da maimuna sai a kama efficient ayi party 'karfen 'kafa ta tafi, Domin banajin idan su mama sukaji labarina zasu bari na dawo wannan gidan ko sun bari bana sha'awar sake dawowa wannan Rayuwar.

After dress na sanya na saka 'karamin hijabi, Saleh tuni y fita bansan inda yake ba ban kuma damu da inda yake ba, a cikin wuni d'aya rayuwarmu ta turning upside-down.

Parlour naja akwatina snnan n d'auki wani na sake cikawa tunda d'aukana za'ayi gara na debi duk kayan da nake bu'kata.

Ina rufe 'karamin akwatin sai ga kiran yayana, d'aukan 'katuwar hand luggage d'ita nayi naja akwatunana zuwa gate, abin takaici part d'in hajiya shine dab ba gate, a 'kofar d'akin na gansu kursum harda sakin gud'a, banbi ta kansu ba na fuce inajin maganganunsu na biyoni amma banida lokacin saurara......
30

Cikin sauri jabir ya 'karaso tareda d'aukan akwatina d'aya, 'kare min kallo yayi kafin ya Sanya akwatin a mota yace "me ya faru Bilkisu".

Wani azababben ciwon kai nakeji sannan banida niyyar bashi amsa, kalar tausayi nayi domin na sanshi da takura nace "Yaya idan munje gida mayi maganar yanzu dai muyi mu bar wannan wurin".

Bai sake tambayata komai ba har  muka d'au hanya, saidai lokaci lokaci idanunsa na kaina yayin da nawa idon ke titi, ciwon kaina 'karuwa yake saboda tunanin da nakeyi Wanda baida amfani.

Tsayawa naga Yaya yayi ya fita ba tareda yace min komai ba, dawowa yayi da ice cream da cake ya mi'komin su ta window, godiya nayi masa na bud'e ice cream d'in na fara sha, fata nake sanyinsa ya kashemin zafin da nakeji a cikin jikina, dukda ya sanyayamin raina amma zuciyata tana nan yanda take sai ma 'ko'karin kuka da ba fara, meyasa Saleh zai yanke wannan hukuncin a irin wannan lokacin? Meyasa banyi ha'kuri har ya huce ba na takura masa akan ya yarda dani har yardar ta kawo wannan ga'ba? Akan wane dalili ma nake baiwa kaina laifi? Ba laifina bane ya sakeni zuciya ce kawai ta d'ebeshi, idan har inada zuciya ya dace na cire Saleh tun yanzu daga raina.

Bansan lokacin da na shanye ice cream d'in ba, jifa nayi da robar ta window na maida kaina ina kallon waje, har yanzu ganin sakinnan nake kamar 'karamin abu ne, kamar yana zuwa yana cewa nayi ha'kuri ya wuce, gani nake tamkar zai biyoni a baya yace yayi kuskure nayi ha'kuri na koma d'akina Amma nasan duk wannan ba abune Mai faruwa ba, yanda naga fuskar Saleh a yayin da ya furtamin wannan mumkunar kalma bnaso har mutuwa ta na sake ganin wannan yanayin.

Muna isa gida na d'auki 'karamin akwatin na shige na bar Yaya a waje, sallama nayi sai naji tamkar an manne min 'kafafuna a waje, tsoron haduwa nake da mama na fad'a Mata wannan abun, ban sake tabbatat da saki babban Abu bane sai yanzu.

Amsa sallamata mama tayi tareda ambatar sunana, Jan jikina nayi kamar wadda 'kwai ya fashewa aciki na shige kaina a 'kasa, shiru mama tayi ta zubamin ido har na zauna, tun kafin ta tambayeni nace "ya sakeni".

Wasu zafafan hawaye naji sun zubomin Wanda na danne tun farkon faruwar wannan abun, sam ban shirya amsa tambayoyin da nake tunanin zasu fito daga bakin mama ba, nasan abinda zata tambayeni shine me ya faru? Meye dalili? Akan me?......saidai ga mamakina jin mama nayi a gefena tana rarrashina.

Hakan na nufin ya sanyamin nutsuwa amma sai na sake karaya, Kuka nake sosai a kafad'ar mama tana bani ha'kuri, abinda ya kamata mijina yayimin lokacin da aka min sharri amma sai ya goyi bayansu, ta yiwu rabuwata da Saleh shine alkhairi.

Sallamar Yaya naji shima ya shigo ya zauna, abinka da namiji yana zama yace "wai ke meke faruwa ne?"

Cikin sanyin murya mama tace "jeki ki ajiye kayanki a d'aki ki huta".

Tashi nayi ba tareda na kalli Yaya ba na shige d'aki, ajiye jakata nayi da akwatin da naja na kwanta kan gadona, 'karewa d'akin kallo nakeyi fatana wannan d'akin ya sanyamin nutsuwar da nake bu'kata amma Ina...tunanin gidana nake ko nace gidan Saleh, the more nayi tunanin gidan the more yake sake fita a raina, idan na tuna da Saleh kuwa tamkar zuciyata zata fito.

Cire kayana nayi na shiga wanka na dinga sakarwa kaina ruwa har saida na gaji, fitowa nayi nai shafa'i da wutri da rashin nutsuwa ya hanani yi a gidana.....afuwa gidan Saleh, sai yanzu Huda ta fad'omin a Rai, ji nayi Ina matu'kar kewarta.

Duk abubuwannan da suka faru Huda sun fita da ya Usman, al'kawari yayi mata cewar zai kaita ta hau lilo saboda na daketa shine suka fita yau, bansan lokacin da ya dawo ba ban kuma ga alamar Huda ba, alamun dai ya samu labarin abinda ke faruwa ya barta wajen Sultana kar taga halin da muke ciki.

Wayata na d'auko na kira sultana na tambayeta lafiyar Huda, sanarmin tayi Huda nata tambayata, ban sani ba ko tasan abinda ya faru saida naji ta sanarmin zata baiwa Saleh uta ya kawomin, cikin sauri nace "a'a Dan Allah ki baiwa usman ya kawomin ita banason ganin Saleh yanzu".

Shiru tayi sannan tace "kiyi ha'kuri bilkisu komai mai wucewa ne, dukda bansan duk abubuwan da suka faru ba amma bai kamata kiyi yaji ba Zaki basu abinda sukeso ne, gobe za'a kawo miki ita amma Dan Allah kiyi ha'kuri ki dawo,bansan ya zanyi rYuwa a wannan gidan Babu ke ba kinsani kowa ya tsaneni".

Shiru nYi na rasa me zance mata, ha'kura tayi ta katse wayar Nima na d'auki cajata na fita, zuwa yanzu na d'an samu nutsuwa kad'an a yanayina amma cikin raina Babu wani banbanci da lokacin da na baro gidan Saleh....Saleh, synannan ya zama tamkar magani a bakina, duk lokacin da na tuna da sunan sai naji wani d'aci har cikin bakina.

Fita nayi naga mma tana yiwa jabir kashedi kar ya sake ya yiwa Saleh magana ko ya nuna masa wani Abu ya faru,

"Wannan abun tsakanin Mata da miji ne idan ka shiga ka zubar da girmanka ne da darajarka, sannan Kai bakasan me ya faru ba menene amfanin d'aukan hukunci akai? Mu jira muji ta bakinta Amma inaso ka sani, ko me ya faru kar ya ta'ba ala'karka da Saleh musamman ta bangaren kasuwancinku".

Zamana ne ya dakatar da mama ta kalleni tace "ya kikeji yanxu?"

"Dan dama-dama" na fad'a tareda 'ka'kalo murmushi, harga Allah Babu abinda nakeso nayi a yanzu kamar Kuka, sannan inaso na sanarwa mama abinda ya faru Ina Jin tsoron me zata ce?, Kamar Yaya ya karanta tunanina yace "bilki....ki fad'amin me ya faru ne wai? Meyasa Saleh yayi gaggawar sakinki ki nacw gangancin sakinki?"

Har na bud'e baki mama ta katseni tace "jabir ka bar yarinyarnan ta huta tukuna, jeki d'auko abinci kici".

"Banajin yunwa mama".

"Yaushe rabonki da abinci?"

Shiru nayi domin yau tea ne kawai a cikina shima Babu Madara, d'okin zuwa wajen mama ya hanani cin komai sannan bala'i ya hanani lunch, a takaice dai daga tea sai ice cream nasha yau kuma banajin yunwa, numfashi naja nace "nasha ice cream a hanya banajin yunwa".

Tashi mama tayi tace "ice cream ba abinci bane, daga alamunki tun safe baki ci komai ba ni Bari na zubo Miki tuwo Kuma banaso ki sake min musu".

"Mama Dan Allah ki bar tuwonnan bazan iya ci ba, Yaya ya siyamin cake zansha da tea".

Zama tayi ba tare da tace komai ba sai kalle kalle muke, kafin kowa ya tambayeni na fara magana nace "Mama akan wannan kud'in ya sakeni".

Kallona tayi cike da mamaki naci gaba, Basu labari nayi ban cire komai ba a zagin da yayimin, Wanda yan uwansa sukamin da martanin da na maida Masa, lokacin da na Gama har sha'kewa nake saboda kuka, kallonsu nayi idona dishi dishi Amma naga alamun bacin rai a tattare dasu musamman ma Yaya da yake alamin zai iya kashe mutum, dukkanmu munyi shiru sautin kukana kawai ke tashi...
31

''Allah ya kyauta Kuma Allah yasa haka ne mafi alkhairi". Mama ta fad'a bayan min day lokaci shiru, amsawa nayi da amin ina goge hawaye na, ledar cake d'in da na shigo da ita na d'auka na bud'e na fara ci dukda Kuka nake, dariya mama da jabir sukayi Wanda ya sanyani murmushi, har na manta da wannan bilkisun mai sauke 'bacin ranta a kan abinci, wadda bata ri'ko Bata bari abu komai girmansa ya dameta, matu'kar Zan kai abu bakina zance ya 'kare.

Kallona sukeyi yanda nake sauke 'bacin raina kan junk food d'in dake gabana, a duk loma idan na kai maganganu nake a zuciyata Wanda bazan iya furtasu ba, janye ledar mama tayi tace "Kar Kuma kici wanda zakiyi amai".

"Amma mutane basuda halacci, duk taimakon da na yiwa Saleh baiji kunya ba ya sako 'kanwata? To mama ko dukansa takeyi ya saketa? Ai ya duba girmanku da mutuncin dake tsakanina dashi, sai ya san ya wula'kanta 'kanwata".

Girgiza kai nayi cikin sauri nace "a'a Yaya Dan Allah Kar kayi haka ba girmanka bane, ko dan abotar dake tsakaninku ka rabu dashi dan Allah Kar kayi masa magana ka nuna tamkar ba abinda ya faru,wannan tsakanina dashi ne banaso ka shiga da kansa zai san yayi kuskure".

Wani irin kallo jabir yayi min yace "har kin fara tunanin komawa gidansa kenan ko?"

Shiru nayi na zubawa hannuna ido, banaso ko hanyar gidan Saleh na sake bi, amma tsabar rashin zuciya irin nawa akwai tiny hope na gobe da safe Saleh zaizo ya bani ha'kuri mu koma zaman lafiya, me yake damuna ne? Wannan itace soyayya? Wani irin so nake ma saleh haka? Wace irin zuciya ce dani?

"Amma bilkisu kin bani mamaki bakida zuciya ko kad'an wallahi, mutumin da ya zageki ya zagi iyayenki ya sakeki ba tareda tunawa da zaman da kukayi dashi ba, ba tareda tuna zaman da nayi dashi ba har shi kike tunanin komawa gidansa? Bilkisu da nasan abinda zai faru kenan da ban goyi bayan aurensa ba, da Abdul Zaki aura ko kinaso ko bakyaso, ko ba komai d'an uwane bazai ta'ba wulakantaki ba musamman yanda yaga gatan da kike ciki".

"Yaya ni ba so nake na koma ba fa, kawai banaso ne wannan abin ya shiga tsakaninka dashi banaso hakan ya ta'ba ala'karka dashi".

Tashi tsaye yayi yace "idan har bakyaso hakan ya ta'ba ala'kata dashi ki barni nayi magana dashi, idan har na kauda kaina bazan ta'ba yafe Masa ba".

Fita yayi ya barni a zaune, mama kuwa tunda muka fara maganar ta tashi, jikina a sanyaye na shige d'aki na shimfid'a bedsheet na kwanta, Saleh zaizo bikona kuwa? Shin zaiyi nadamar sakina? A Daren yau zai iya bacci babu ni a gefensa? Nima zan iya bacci babu Saleh a gefena? Tambayoyin da suketa yimin yawo kenan har nayi bacci.

************
*SALEH*

Wani numfashi ya sauke bayan kalmar saki ta fita daga bakinsa, bai ta'ba tunanin ko da wasa zai saki Bilkisu ba amma gashi yau lokaci yayi, yasan cewa su hajiya basa sonta amma wannan karan bazai ta'ba yiwuwa ya goyi bayanta ba bayan yaga laifinta da idanunsa sannan ta d'aura laifin kan 'yan uwansa har ta kai ga zagin hajiya, tunawa yayi da maganar da hajiya ta fad'a masa wadda kusan ita ta tunzurashi ya saki bilkisu

Bayan sunyi hayaniya ya fita part d'in hajiya ya nufa, Hira ya samesu sunayi akan abinda ya faru, tsayawa yayi a inda yake tunanin bazasu hangoshi ba, baisan cewa zuwansa ne ya Ssanya suka fara maganar ba, ji yayi maimuna na cewa "Wallahi nayi mamakin bilkisu, nasan Bata sonmu bata son rayuwarmu, amma me zai kaita aikata haka? Ita kenan kowa ma ya mutu idan zata samu haihuwa , bata tunanin cetar ran amir zai iya sanya Allah ya kawo mata komai cikin sau'ki, Kuma babu kunya babu tsoron Allah tace Bata san ya kud'in suka shiga gidan ba".

"Hm, ai da ace ma yasan me tace mana da ta kawo kud'in da bai tsaya tantama akai ba, kin tuna kallon tsabar idon hajiya tayi tace "idan har Kina haka ne Dan ki rabani d'anki idan ya rabu Dani ya aureki sai kije kiyita haihuwar dashi, wace macece mai tarbiyya zata fad'awa uwar mijinta haka?" Kursum ta fad'a Tana murmushin mugunta domin duk motsin Saleh sunaji.

"Ai kad'an kikaji ma da kinsan zagin da takewa hajiya da bakiyi mamaki ba, idan hajiya tace a fad'a masa sai nace a'a domin a wajensa Babu mai gaskiya sai ita, wataran da kansa zaiji ta zageta a gabansa ai, anan zai nuna kansa idan

19 / 41