Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
mi'komin kud'in, zare Ido nayi ganinsu da yawa na bud'e na 'kirga, 250,000, d'auko bankin 'karfen nayi na saka key na bud'e padlock d'in sannan na saka kud'in na rufe na maida, harkokinmu muka shiga kamar muka manta da wannan ajiyar saidai na rasa nutsuwa bana son harka da kud'in mutane sam.
Washegari tare muka fita ya ajiyeni a gidan mama na jima banje mun gaisa ba,anan na na wuni sai dare tukun muka koma gida.
Kujera na kama cikin sauri na Kai MBC action, ban ta'ba kallon wrestling ba sai yau abin mamaki ya shiga raina, talla nagani a gidan mama kawai naji inason kallan wrestling.
Huda tayi bacci tana kujera tana kwance, zama Saleh yayi ya Sanya hannunsa a kafad'ata yace "da gaske wrestling zaki kalla?"
"Eh mana, kaga wancan? To last week anyi dashi wancan me Jan gashin ya 'kwace masa trophy d'insa, shine fa yau ya dawo ya kar'bi abinsa, kuma kaga fa wannan mutum uku akan mutum biyu sannan wancan......."
Dariyarsa ce ta katseni nace "menene?", "Yaushe Kika kalli wannan har kike bada labari?"
" Jabir ne ya bani labari ai, yanzu dai yi shiru Muji me suke cewa".
Shiru yayi saidai Ina jin idonsa a kaina maimakon a tv, hannu ya Sanya ya shafi gefen fuskata nayi murmushi ba tareda na kalleshi ba, "side view naki kinada matu'kar kyau Bilkisu, kinga yanda bakinki ke motsawa idan kikayi murmushi? Gashin idonki gwanin sha'awa, ga lebenki a duk lokacin da kika motda bakinki.......gaskiya nayi dacen mace a duniya, Kai har lahira ma da yardar Allah".
Kwanciya nayi kan kafad'arsa nace "nagode sosai".
Sake matso dani jikinsa yayi muka fara kallon wrestling d'in, duk na cikwikwuye Masa riga saboda tsoro, wad'annan mutane akwai mugunta, rufe idona nayi tareda 'kan'kame Saleh ganin wani ya d'auko kujera ya Sanya kan opponent din nasa cikin kujerar had'a kan opponent d'in da garu a cikin kujerar, jini ke zuba, inada tabbacin wancan ya mutu.
Jikina duk ya d'auki rawa shi kuwa Saleh dariya yakeyi, d'ago kaina yayi yace "kalli kigani, paramedics sun d'aukeshi yanzu aka rubuta cewa bai mutu ba amma an kori wancan daga wrestling d'in saboda ya karya doka, kinga zai daki wani d'an kallo".
Ban bud'e idona ba kuma ban sakeshi ba, muryata a hankali nace " Dan Allah canza channel banaso na sake gani".
"An gama ai yanzu ma maze runner zasuyi, d'ago ki gani". Daga kaina nayi Naga da gaske an gama, kwanciya nayi na d'aura kaina a cinyarsa na fara kallon maze runner, bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba.
Wani mummunan mafarki nayi, inda naga Saleh cikin wani yanayi mai firgitarwa, tsayawa yayi a kaina cikin tsawa yace "bazaki fad'amin gaskiya ba!!!!" Tsoro da firgici sun hanani magana, hawaye ne kawai ke zuba daga idona gefe d'aya kuma ga hajiya da su maimu fuskarsu d'auke da walwala, murmushi hajiya tayi tace "meye ban sanar maka ba? Gashinan ai yanzu ka gani da idanunka"
Kallona Saleh yayi saidai babu abind nake gani a idonsa face tsana, takaici da nadama, wata takarda ya jefomin yace "kin bani kunya".
Bud'e baki nake amma babu kalmar da ta iya fitowa, numfashina ya sarqe a wuyana, ambatar sunansa nake amma babu Wanda yakeji sai ni, da kyar na furta da wuri Wanda ya sanyashi juyowa a firgice, dawowa yake gareni da sauri saidai maimu tazo ta tsaya a gabana tareda dafa kafad'ata, ji nayi tamkar an sakar min kibiya a wurin, kallona tayi ta kalli Saleh tace "lokaci ya 'kure" tareda murmushi a fuskarta.
Bansan me ya faru ba da ya sanyani tsorata, cikin firgici na tashi inaja da baya tareda fara gudu, muryar Saleh nakeji Yana kirana saidai na kasa tsayawa, zuciyata rayamin take idan har na tsaya zai cutar dani, matsowa yake dab Daniel saidai ba tareda na waiga ba nake ambatar "karka matso kusa Dani, banaso Kar ka cutar dani ka bari!!!"........
A firgice na farka tareda Jin kiran sallar asuba, fuskata ta ji'ke da gumi ga bugun zuciyta da ninka kusan sau hud'u, har saida na dafe kirjina saboda yanda nakeji bugun zuciyata, wani irin mafarki ne haka? Me yake nufi?.
Kar kuce yayi kadan banajin dad'i ne, luv u all😘😘😘😘😘
26
Tashi nayi jikina babu 'kwari, mafarkin da nayi sake dawomin yakeyi tamkar da gaske ya faru, girki nake amma hankalina sam baya wannan duniyar.
Tsorata nayi jin muryar Saleh a bayana, hannunsa ya zuro ya ri'ke cikina tareda juyani a hankali, "ina kwana" na fad'a cikin sanyin murya.
"Kin tashi lafiya?" Ya fad'a tareda kissing kumatuna, "you look stunning as ever".
'ka'kalo murmushi nayi domin ji nake kamar hawaye zai zubomin, meyasa mafarkinnan ya razanani haka? Me ke Shirin faruwa damu ne? Tabbas mafarkin yayi min kama da zahiri, sannan naga alamin laifina ne, to me zai faru tsakaninmu domin tashin hankalin da naga mun riska a mafarkin bana bu'katar na ganshi a zahiri.
"Bilkisuuuu!!" Naji Saleh ya ambaci sunana a saitin kunnena tareda d'aga muryarsa, kallonsa nayi nace "um?", Juyoni yayi ya zubamin ido yace "meke damunki? Bakida lafiya ne?".
"Lafiyata lau inaga baccin ne bai isheni ba kasala kawai nakeji".
Kallona yayi alamun bai yarda ba yace "kasalar ce ta sanya inata miki magana bakisan inayi ba? Me kike tunani ne haka?".
Shiru nayi na d'aga kaina, had'a Ido mukayi cikin sauri na sauke kaina, hannunsa ya Sanya a kafad'ata yace "me ya faru Bilkisu? Idan akwai wata damuwa ne ki fad'amin, me aka miki? Waye yayi miki? Mama ce?".
Girgiza kai nayi inajin zuciyata babu dad'i, gaba d'aya na karaya ji nake tamkar wata katanga ke gina kanta tsakanina da Saleh, meyasa bayan mun samu kwanciyar hankali zuciyata bazata huta ba? Wannan illusion d'ina ne kawai mafarkine mara ma'ana, idan har na kalleshi ta hanya mai kyau komai zaiyi daidai, idan kuma naci gaba da kallonsa ta hanya marar kyau tabbas Ina cikin matsala.
Saidai zuciyata ta gama rayamin tabbas fa akwai abinda zai faru marar dad'i, mafarkina gaskiya ne ba tunani bane, ya zanyi idan wani abu ya Sami Saleh a dalilina?.
"Ya Isa, ya isa babu abinda zai faru kinji? Ko ma waye ya miki laifi zanyiwa mama magana kiyi ha'kuri, banaso kina zubar da hawayenki boo-boo na wallahi" Saleh ya fad'a bayan yayi hugging d'ina, cikin sauri nace masa "babu abinda aka min boo, mafarki nayi da mahaifiyata kawai kayi ha'kuri idan na sanyaka a damuwa".
Cigaba yayi da shafar bayana har saida hawayena ya tsaya sannan yace "Allah ya ji 'kan mama ya mata rahama"
"Ameen" na fad'a tareda kakalo murmushi, hannu na Sanya a na shafa hannunsa nace "ganina zuwa saura kad'an na 'karasa". Ya lura so nake kawai ya barni ni kad'ai baice komai ba ya fita, 'ko'karin kauda mafarkin nayi a raina, idan ma Abu ne zai faru ai future ne, abinda ya kamata shine nayi cherishing farin cikin da nake ciki.
Cikin wasa da dariya muka gama breakfast na shiga ayyukan gidana, ina gamawa na kira mama muka gaisa, mun d'auki kwana hud'u Banga alamun wata matsala ba na saki jikina
Bayan sati biyu Saleh ya sake kawomin kud'in ajiya, 'kirgasu nayi nace "wasa-wasa fa boo-boo kun kusa had'a 500, indai yakai 1million inada 200 a ciki".
Dariya yayi yace "duka ma zai iya kasancewa naki ne".
"Asbitinnan na Dubai...." Shiru yayi ba tareda ya 'karasa maganar da zaiyi ba, murmushi nayi domin nasan dalilin da ya hanashi 'karasawa, na sanar masa banaso muna maganarnan akai akai har sai lokacin yayi, domon duk ranar da mukayi maganarnan sai yanayina ya canza, ji nake kamar ban cika mutum ba, tamkar akwai halittar da ta ragu a jikina.
" D'azu na shiga website d'insu har munyi magana da wani likita, tunda kinga nan da watanni kad'an da yardar Allah kud'in zai had'u, likitan ya sanarmin mu tura picture na result d'in gwajinki recent one, kuma yacemin zamu iya zuwa a hakan, ayi miki aikin daga baya sai mu bada sauran kud'in".
Shiru nayi kwakwalwata na processing abinda ya faru, na kasa had'a pieces na maganar Saleh, hakan na nufin cewa cikin satittika ko watanni kad'an zan Samu ciki?.
"Kwarai kuwa boo-boo na, insha Allah nan da sati uku zamu fara shirye shiryen tafiya"
Dariya nayi nace "bansan cewa da 'karfi na fad'a ba".
Shirye shirye na fara na tafiya, duk yanda naso na rufe bakina kar na fad'awa mama murna ta hanani, a 2nd week na kirata, tana amsawa ban jira mun gaisa ba nace "mama albishirkinki, farkon July dai insha Allah muna Dubai".
"Masha Allah tafiyar ta taso kenan". Ta fad'a cike da farin ciki
"Eh mama, tun last two weeks ya fad'amin yace zamu fara shiri nan da sati uku, dama wasu kud'i yake jira kuma a satinnan ma har sun shigo, next week ,zuwa dai July d'in mun gama shiri sai tafiya"
"Masha Allah, Allah ya kaimu lafiya ya bada sa'a, kuma duk ya gama hada kud'ad'den?"
"Eh kusan dai an had'a, dama tun watannin da suka wuce ya had'a miliyan 2 da abubuwa, to kud'ina na internship na bashi ya had'a a ciki, idan ya kar'bo wannan kud'in kusan 5m kenan, zai ishemu har iya zaman da zamuyi a can".
Ina rufe bakina naji alamun mutum a 'kofa, tun ban juya ba gabana ya fara fad'uwa, bansan tsautsayi da ya sanyani waya a palour ba.
Juyawa nayi naga jumana a tsaye, sallama tayi min a hankali da Sam muryarta bata fitoba, "mama zan kiraki anjima" na fad'a tareda katse wayar na amsa Mata sallamar nace "ya akai".
Dariya tayi ta kama kujera ta zauna tace "haka kuma kika koma saukar ba'ki bilki? Ko kuma duk canjin na an samu kud'i ne?"
Ban tanka mata ba ta girgiza kanta tace "zanso naga yanda su mama zasuyi idan sunji zancennan, ana can ana fafutukar had'a kud'i Ashe ga inda kud'i suke, har an rasa abinda za'ayi dasu ana shirin tafiya yawon duniya ko?".
Dukda na tsorata amma na danne nace "jumana kud'in mijina kud'insa ne, baku da damar yin iko dashi, kuma abinda zamuyi ba abinda ya shafeki bane, kud'innan ko zubar dasu zaiyi a kwata babu ruwanku a ciki".
Waya jumana ta ciro, dukda zuciyata na ingizani na ro'ki jumana kar ta Kira ko ma waye take son kira amma na gaza yin hakan, lokaci yayi da ya kamata na tashi na nemi 'yancina da kaina, ha'kuri na yazo 'karshe sun Riga sun kaini bango, wannan shine kad'ai opportunity d'ina babu Wanda ya isa ya hana wannan tafiya tamu sai mahaliccinmu.
"Hello yaya ya mai jikin?..... Yauwa Allah ya 'kara sau'ki, mu had'u anjima a gidan mama akwai magana babba ma kuwa.... a'a kedai kizo mana magana ce mai muhimmanci sosai wallahi.....yauwa to sai kinzo....eh duk su zo....to Allah ya 'kara sau'ki".
Tana katse wayar naji tamkar an zaremin laka, me zai faru idan jumana ta sanar musu? Me zasu aikata? Bazan ta'ba bari su sake wargaza min rayuwata ba.
Tashi tayi tace "dama zuwa nayi na sanar miki d'an gidan yaya maymu bashida lafiya, ita munafukar taki nasan Bata sanar miki ba tunda tana fama da kanta itama, sai mun had'u anjima ko?".
Binta nayi da kallo har ta fita, zagaye d'akin na fara na kasa yanke shawarar komai, cikin sauri na laluba number Saleh a wayata na kirashi.
"Hello boo-boo na ya akayi ne? Har kin fara missing d'ina ne? Domin ni ban fara ba".
"Boo akwai matsala, jumana tasan da tafiyar mu".
"Kai boo-boo kefa akwai tsoro, wa zai fad'a mata? Ya akai ma Kika san ta sani?
Fad'a masa komai nayi, shiru yayi na d'an lokaci sannan yace "ba matsala karki damu kinji? Zan san abin yi idan na dawo".
Hankalina gaba d'aya ya tafi part d'in mama, idan suka zo me jumana zata ce musu? Me zasu yi?, Kwantarwa da kaina hankali nakeyi dukda nasan matsala dole ta faru, saidai ina fatan kar ta zama babba.
Tunawa da mafarkina nayi wanda ya sake tsorata ni, me zai faru idan mafarkinnan ya zama gaske?
3:00 naji shigowar motar Saleh, jikina a sanyaye na fita, hugging d'ina yayi ta gefe yace "hajiya ce ta kirani tace na dawo yanzu-yanzu, bari naje duk yanda akayi zan sanar miki".
Gyad'a kai nayi na koma na zauna ina tunanin abinda yake faruwa, ko dai hajiya cewa zatayi ya kawo kud'in, to me zai sanya maganar kud'i ta zama babbar magana?
4:10 ina idar da sallah saleh ya kirani a waya yace naje, takalmi na sanya na tafi cikin sauri ko rufe gidan banyi ba.
Muryata 'kasa-'kasa na gaidasu babu wadda ta amsa, kafin na zauna hajiya tace "kud'in da kike bada labarinsu a waya na waye?"
Kallon Saleh nayi ya kalleni kawai ya d'auke kai, "tambayarki nakeyi kud'in waye?". Kasa cewa komai nayi domin bansan me Saleh yace ba, saida ta sake tambaya nace "hajiya kud'ina ne".
"Ina kika samu wannan kud'ad'den?" Shirya 'karyar da zanyi nake saidai naga meye amfanin hakan? Dole dai gaskiya zatayi halinta idan lokacin tafiyarmu yayi, gyara zamana nayi cikin confidence nace "mama kud'ina ne amma Saleh ne ya bani su, mun tara ne ba don muje yawon duniya ba, aiki zamuje ayi min na haihuwa".
Tsaki maymu taja tace "idan Allah bai baka haihuwa ba akwai shegen da ya Isa ya baka ne? Masu bijirewa ikon Allah, haka zakuje ayi aikin kizo ki haifi d'a kamar aljani".
Kallonta nayi nace "ko me na Haifa ai yafi babu ko? A tunanina abubuwan da kukemin saboda ban haihu bane, idan na haihu nima kuka tabbata mahaifata tanada lafiya sai hankalinku ya kwanta".
"Wace lafiyar mahaifa? Ai lafiya kuma babu zancenta tunda babu ta yanda zaki samu ciki ki haihu saidai wani 'katon banza yayi miki cikin, abinda ma gashinan malamai na fad'a zina ce wannan dashen cikin shine zakuje ayi miki, saboda shi mijin naki bai san ciwon kansa ba". Kursum ta fad'a cike da 'bacin rai, nunata Saleh yayi yace "ki iya bakinki, Bilkisu matata ce kuma ra'ayi na ne wannan, babu ruwanku a ciki".
"Ba wannan ne ya Sanya na taraku ba" hajiya ta fad'a cikin iko "yaron maimuna bashida lafiya kuma kana sane, tunda aka haifi yaronnan suke yawon asbiti akan matsalar zuciyarsa gashinan shekara hud'u Babu wani ci gaba, a asbiti an fad'a mana cewa sai an masa aiki, kuma indiya za'a kaishi aikin,babansa ka sani bashida 'karfi kuma aikinnan yakai miliyan biyar, zaka bada miliyan biyu 'yan uwanka su bada sauran tunda kai kanada kud'in a 'kasa".
Kallona juna mukayi ni da Saleh, shiru yayi ya kasa cewa komai, raina yayi matu'kar 'baci a wannan lokacin, mijin jumana yafi Saleh da mijin sultana 'karfi, a cikinsu ma Saleh ne mai 'karamin 'karfi meyasa zasu mana haka? Na tabbata mijin jumana da Usman zasu iya had'a kud'innan, idan so suke ya taimaka meyasa zasu masa iko da abinda zaiyi?
"To uwar Saleh, kin amince ya bayar da kud'in ko kuwa kinfi so d'an ya mutu tunda ke baki haifa kinji yanda ciwon d'an yake ba?" Maimuna ta fad'a Tana kallona cike da tsana, sai yanzu na lura da yaron dake Kan kujera da cannula a hannunsa da wani Abu a hancinsa, ya rame kana ganin 'kashin kansa da 'kirjinsa.
Bansan dalilinta na yin magana ba saida mama tace "kun zauna kamar kurame, yaushe zaka kawo kud'in domin ance aikin imagency za'ayi masa a indiyan.
Runtse Ido na nayi, nasan d'ayan biyu ne, idan har bamu bada kud'innan ba yaronnan ya mutu to tabbas bazan yafewa kaina ba, idan har na hana bada kud'innan to naso kaina da yawa, ko kuma mu bada miliyan d'aya in yaso ko su mama sa cika mana.
"Shi...shikenan zamu kawo zuwa gobe" na fad'a muryata na rawa, tashi nayi na fice ba tareda na jira me zasu ce ba, hawaye ke bin fuskata a raina ina tunanin Anya alkhairi ne wannan abin? A duk lokacin da ya taso sai wani abun yazo ya toshe mana hanya, "Allah ka za'ba min abinda yafi alkhairi" na fad'a cikin raina.
Saida na shiga gida sannan Saleh ya shigo, zama yayi gefena ya d'aura kaina a kafad'arsa Yana shafa gashina, cikin rarrashi yace "duk Wanda ya dogara ga Allah to tabbas Allah zai kawo masa mafita, ta yiwu wannan tafiyar tamu a yanzu ba alkhairi bace shiyasa hakan ya faru karki sawa kanki damuwa kinji?"
Cikin shesshe'kar kuka nace "to boo-boo na, amma meyasa zasu yi mana haka? Sun k'wace mana dukiyarmu cikin iko da isa da gadara, da ace ro'ka tayi ma da sai yafi amma dole fa aka mana, idan mun hana wani abun ya samu yaron kuma shikenan zaace laifinmu ne".
Baice komai ba yaci gaba da shafa bayana har na samu nutsuwa, shiru mukayi dukkanmu har lokacin sallar magrib yayi, yana fita masallaci na Kira mama na sanar mata abinda ya faru,
"Babu komai Bilkisu ai taimako kukayi a hakan, idan Allah ya bashi lafiya mafi yawan kason ladan naku ne, wannan ba abun damuwa bane kawai abinda za'ayi zan baku kud'in ku cika a matsayin rance tunda yace baya son kyauta, idan anyi aikin an gama lafiya sai ku biya".
"To mama Zan fad'a masa mungode Allah ya saka da alkhairi".
"Bakomai bilkisu kiyi ta ha'kuri dai, insha Allahu komai mai wucewa ne, babu abinda yake dawwama a duniyarnan kinji? Wataran da kansu zasuyi nadamar abinda sukeyi su nemi yafiyarki".
Shiru nayi Ina jin kalaman mama masu kwantar da hankali, muna cikin wayar Saleh ya Kira na katse Kiran mama na d'auki nashi "nayi mantuwa akwai fura da nono a booth d'in mota ki d'auko kar yayi tsami sai ki dama mana, ai akwai kwakwa ko"
"Eh akwai kafin ka dawo na dama insha Allah"
Fita nayi na bud'e motar na d'auko nonon, dariya naji daga bangaren jumana har nayi gaba na tsaya domin naji akan me suke magana, wajen duhu hakan yasa basa hangoni sannan da alamu hankalinsu baya kaina.
"Dan Allah da gaske ko wasa?" Jumana ta tambaya
"Wallahi jumana da gaske, asbitin ne sun ganemu sun kuma san amir yana Shan wuya kuma bamuda Hali, ban ma san da zancen aiki kyautan ba sai last week da kwankwaso yazo asbitin 'bangaren masu matsalar zuciya yara, anan ya zabi yara goma harda Amir ya biya musu kud'in aikin kyauta a indiya".
Saura kad'an na jefar da ledar hannuna, wannan wasu irin marasa imani ne?
"Lallai ma Yaya maimuna, to Hajiya ta sani?"
"Ta sani mana, kursum ma ta sani, ke kowa ma ya sani ranar 23 ga wata zamu tafi, har kud'in guzuri ya bamu fa kyauta".
"Lallai Yaya maimuna ke bala'i ce, to me zakuyi da miliyan biyun?".
"Ni bala'i ce ko hajiya bala'i ce? Ai