NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 41

27K to 30K   out of 120.7K words

maimuna basu fad'a miki ba kenan "

" A'a, ba wanda ma ya shiga part d'ina a cikinsu, tunda suka cemin ke suke jira suka ga zan hanasu zuwa suka fice, amma me ya faru kinsa gabana ya fara fad'uwa "

Bayanin matsalata nayi mata, dafe kanta tayi tace

" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya Allah ya akai haka ta faru dake? Yanzu kenan bazaki ta'ba haihuwa ba ko me?"

" Eh haka dai suka ce, indai ba dashe za'a min ba bazan ta'ba haihuwa ba "

Shiru tayi ta zuba min ido, d'auke kaina nayi nace

" Ki dena kallona haka bana so"

" To bilki bansan me zance miki bane, wallahi kaina duk ya 'kulle bansan ya ake rarrashi a irin wannan yanayin ba, saidai nace Allah yasa hakan ya zame miki mafi alkhairi kiyi ha'kuri, nasan 'yan uwana zasu kafa miki 'kahon zu'ka akan hakan amma dan Allah karki saka hakan a ranki, nasan sunce ya 'kara aure ko? "

" Eh "

Tashi tayi ta dawo kusa dani tace

" Bilki, dan Allah ko ta yaya karki bari yayi aurennan, wallahi idan yayi aurennan kina cikin matsala, nasan su waye 'yan uwana sarai, nasan kuma irin macen da zasu aura masa, bilkisu ba munafurci ba amma wallahi bana fatan kiyi kishi da d'aya daga cikin danginmu "

Jan numfashi nayi ba tare da nace mata komai ba, mutanennan danginta ne, duk yanda zata soni matar tsohon saurayinta bazai Kai son da zata yiwa danginta ba

Tashi Huda tayi na saukota na ajiyeta tareda kar'bar Ahmad, shafa 'kafarsa huda tayi ta kalleni tace

" Maama "

Kallonta mukayi a tare sultana ta kalleni tace

" Kai, ikon Allah dama yarinyarnan tana magana? "

Mamaki ne ya kamani nace

" Huda tana magana mana, ko nace gwaranci,amma d'azu naji ta fara cemin maama na d'auka ma ke take kira haka "

" Tabd'i, to ni huda banda ihu me take min? Idan ta kwana wajena wallahi bana iya bacci, idan kika fita school ma ta dinga kuka kenan saidai idan ta gaji tayi bacci "

" Laifinki ne ai, bakya kula da huda yanda ya kamata "

Sunkuyar da kanta tayi tace

" Bilki wallahi ni kaina bana jin dad'in hakan kuma nasan ban yiwa huda adalci ba, kinsan Allah kwata-kwata ji nake kaman ba ni na haifi huda ba, kuma ban fahimci haka ba sai da cikin ahmad, kinga cikin huda banyi d'okinsa kaman na Ahmad ba, wallahi tunda huda ta fita daga jikina naji kaman an ciremin 'kaya, bani da sha'kuwa da huda yanda ya kamata uwa ta sha'ku da 'yarta, idan Huda tana wajenki mantawa nake da ita, ni bansan ya zanyi ba "

" To ai sultana tun farko baki d'auko matakin zama uwa ga sultana ba, dukda nasan da cikin ahmad da ya sakaki gaba, amma huda fa tun tana wata biyu kika fara fita kina barmin ita, wata shida kika yayeta kuma a wannan lokacin shine yaro yake fara fahimtar uwarsa, to lokacin kika yakiceta daga jikinki, bata taso ta sameki a uwa ba, kema kuma lokacin kina fama da kanki , amma dukda haka da dai kin jata a jikinki lokacin da take bu'katar ki "

Cije baki tayi tana kallon huda, tashi tayi zata tafi nace

" Bazaki tafi da ita ba? "

Langa'bemin wuya tayi tace

" Idan ba damuwa ta kwana a wurinki kawai "

Amsawa nayi da to na d'auki huda muka raka sultana.

Washegari muna breakfast sai ga hajiya ta shigo, tana zama naji abincin ya fita daga raina, zuba mana ido tayi har na kwashe kwanukan na koma na zauna

Kallona tayi tace

" Tashi zamuyi magana da d'ana "

Tashi nayi na shiga kitchen na fara wanke wanke, muryarta na jiyo tana cewa

" Saleh, nazo na baka umarni ne ka 'kara aure, duk namiji me hankali bazai zauna da mace mara haihuwa ba, duk d'an adam yana so yaga zuri'arsa, kuma cutarwa ce ace bazaka yi aure ba matarka kuma tana juya, yanzu haka zaka mutu ba tare da yaga zuri'arsa ba, idan har matarka zata hanaka aure to bata sonka tsakani da Allah, aurennan idan kayi ita kanta zata amfana, ko ba komai zata ga 'ya'yan mijinta "

" Hajiya nifa bilki bata hanani aure ba, ni ne naga rashin dacewar hakan, hajiya bilki zata iya haihuwa, likitan ya fad'a mana za'a iya Mata dashen haihuwa a 'kasar waje kuma zata haihu, yanzu haka ina tunanin had'a kud'in ne da za'ayi hakan, hajiya bazan iya zama da mata biyu ba saboda bazan iya adalci ba "

" To saidai ka saki bilkisu, Kai kenan da d'a d'aya zaka zauna a rayuwarka? Ko kuma duk lokacin da kuke bu'katar haihuwa zaku dinga zuwa ne ana mata dashen? Kaga na gaji da halayenka akan matarnan, tunda ka aurota ka dena kallona a matsayin uwarka, ka fara manta cewa ni na haifeka, to a yau umarni nake baka wanda dole kabi, dole kayi aure ko kana so ko baka so, bazan zauna da juya a matsayin sirika ba, kaje ka sami 'yar gidan habiba munyi magana ku daidaita "

Fitowa nayi zan tafi sama yace

" Hajiya 'yar gidan habiba kuma? Bazan iya auren yarinyarnan ba hajiya, bata da halaye masu kyau bata ganin darajar mutane, hajiya dan Allah ki barmin aurena muna zaune da matata lafiya, hajiya ba dai jika ba? Zata haifa miki bansan meyasa bakwason bilki ba duk biyayyar da take muku "

Harzu'ka hajiya tayi tace

" Ubanka, akan mace kake fad'amin magana? Ita zata kalli uwarta ne ta fad'a mata haka? An cuceka an had'a ka da mace juya, na fad'a 'karara bana son matarka bana 'kaunarka, kuma duk d'a na gari zai kasance Yana son abinda iyayensa suke so yana nisantar abinda basa so, ka sani, idan har bazaka yi aure ba kuma bazaka rabu da wannan yarinyar ba to ka ficemin daga gida, banason ganinka bazan kuma zauna da d'a wanda baya bin umarnina ba bayan d'awainiyarka da nayi na shekaru sama da ashirin, ka fice ka barmin gida kaje ka zauna da matarka duk inda kaga dama, karka sake kallona a matsayin uwarka kaje ka zauna da matarka ta zamar maka uwa "

Ficewa tayi na sauko na zauna gefensa, kama hannunsa nayi ina murzawa a hankali, ajiyar zuciya ya sauke nace

" Kaje ka bawa hajiya ha'kuri, idan har auren zai saka ta sauko dan Allah kayi kawai, boo-boo na ba abinda yakai mahaifiyarka a rayuwarnan, ka tuna fa shekaru da dama ta d'auka tana wahala dakai, mahaifinka ya rasu ya barku a hannunta ita taci gaba da wahala daku, yanzu da kayi hankali ka kawo 'karfi ka nuna Mata kana appreciating abinda tayi maka, ta baka umarnin aure a baya ka'ki, yanzu kayi mana fushin iyaye masifa ne, boo-boo na ban taso na Sami mahaifiyata a raye ba, amma inada tabbacin tayi min umarnin rabuwa dakai zan bi, bazan so kaina nace ka bijirewa hajiya ba, ka bata ha'kuri kuma kayi auren wallahi har zuciyata na amince ko wacece ka auro "

Muryarsa har rawa take saboda 'bacin rai, hannunsa biyu ya sanya ya ri'ke hannuna yace

" Ban bijirewa umarnin hajiya saboda komai ba sai domin tayi hakan ne domin ki cutu, mahaifiyata ce nasani, amma ya kamata taso abinda nakeso, boo ki duba fa, kallon idona tayi tace bata sonki, boo kinsan yanda nakeji a raina da furucin da tayi na bata 'kaunar abokiyar rayuwata? "

" Come on.....'bacin rai ne ya saka ta fad'i haka na sani, amma dai ka bata ha'kuri, idan muka bar nan ina zamu je? Kana ganin hankalinmu zai kwanta ne? "

Numfashi yaja ya juyar da kansa, hannu na sanya na juyo fuskarsa gareni tare da sauke murmushi, shafa fuskarsa nayi nace

" No matter what ina tare dakai mijina, kuma inaso kaima komi rintsi karka bijirewa mahaifiyarka, zaman lafiyarmu shine samun amincewarta, I love you boo-boo na "

Hannunsa ya d'aura kan nawa dake fuskarsa ya sakarmin murmushi mai d'auke da abubuwa da dama, kwanciya nayi a kafad'arsa ina karanto masa kalamai masu kwantar da hankali "

Washegari na fita asbiti tun kafin na dawo sultana ta kirani tace tana son magana dani, inata tunanin abinda zata fad'amin.

Da hanzarina na shiga gida, a bud'e naga gidan na shiga inata mamaki, sakin baki nayi ganin palon cike da tarkace.

Kayan Huda ne ko Ina a d'akin, ga gadon jarirai, ga baby walker, akwatuna biyu, kayan wasa cike da gadon ga kuma jakunkuna da cereals d'inta

Huda kanta wata kwalliya ta daban aka mata cikin riga da wando, rigar takai gwiwarta fara 'kal sai wandon tight ne light pink, gashin kanta an mata two babies da pink ribbon, takalminta kuma fari, tana ri'ke a hannun usman sultana Kuma na zaune gefensa.

" Zauna mana kin zuba mana ido, waye sabo a cikinmu hudan ko kuma mu?"

Ina zama Huda ta zamo daga cinyar usman ta taho wurina, had'a Ido sukayi usman da sultana sukayi murmushi, rad'a tayi masa ya gyad'a kai

Kallon saleh nayi yayimin alamun baisan menene ba, gyaran murya sultana tayi tace

" Da farko dai bilki ina baki ha'kuri akan abinda ya faru dake, nasan kinada 'karfin zuciya shiyasa ma Allah ya miki wannan jarabawar, Abu na biyu ba tareda 'bata lokaci ba Zan sanar miki dashi amma kafin na fad'a akwai dokoki, bakida ikon cewa a'a, idan kinsan ba amincewa ce zata fito daga bakinki ba to kiyi shiru "

" Bilkisu tunda na haifi huda Kika zamar mata uwa, kece komai nata ni kawai haihuwar Huda nayi, amma idan za'a sakamin wu'ka bansan lokacin da take bu'katar abinci ba, bansan lokacin baccinta ba bansan komai akanta ba, bilki ina jin kunyar na Kira Huda 'yata domin bamuda sha'kuwar uwa da 'ya, ranar da naji Huda ta kiraki da maama kwana nayi ina tunani a raina, anan na gane Huda aya ce gareni, ba kaina na haifawa ita ba ke na haifawa, huda bata ta'ba zuwa hannun wani a cikin ni da ya usman ko yan uwana ba tareda tayi kuka ba, ke kad'ai Huda ke amincewa ta zauna dake, saboda haka muka yanke shawara ni da ya Usman, bilki mun baki Huda halak malak, har abada na tashi daga Mahaifiyar Huda ke kin zama mahaifiyarta, idan so samu ne ko girma huda tayi banaso tasan nice mahaifiyarta, wallahi da zuciya d'aya na baki ita har abada "

*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭I don't know what to say har Raina wannan kyautar ta tabani*

*NEXT UPDATE: SATURDAY INSHA ALLAH,KU TAYANI DA ADDU'A INADA TEST*

17

Zuba mata ido nayi na rasa me zanyi, ban sani ba farin ciki nake ko ba'kin ciki? Tabbas zan fi kowa farin ciki da samun Huda a matsayin 'ya, amma ta yaya dangin sultana zasu kar'bi hakan?.

Runtse ido nayi tare da d'aga kaina sama, 'kwalla ce ta zubomin na goge cikin sauri ganin idon Huda a kaina.

" Kar kiyi kuka ki sanya 'yarki damuwa mana "

Ambaton 'yata da tayi ne ya karyar min da zuciya, kuka sosai na saki, 'kirjina naji yana d'aurewa gaba d'aya na rasa inda zan saka kaina saboda emotions, sultana tayi min ba zata.

Gefena sultana ta dawo tana rarrashina, zubamin ido Huda tayi take idonta ya ciko da 'kwalla.

" Ki dena dan Allah bilki karki saka Huda kuka, kinsan ba'a so kana nunawa d'anka damuwarka ".

Shesshe'kar kuka nake tareda sha'kuwa nace,

" Dan Allah ki bari sultana, ki dena fad'amin haka ba komai zuciyata zata iya d'auka ba ".

'Daukan Huda tayi ta ri'keta a hannunta, mi'komin hannu huda tayi ta fara kuka, d'aukanta nayi tare da danne kukana, kwanciyar da huda tayi a jikina saida na jita daban, na d'auki kusan mintina biyar kafin na dawo hayyacinta, duk hankalinsu na kaina na kalli sultana nace

" Meyasa kika min wannan kyautar sultana? Kina tunanin Zan kar'beta da zuciya d'aya ba tare da gudun faruwar wani abu ba? Sultana kyautar d'a ba 'karamar kyauta bace ko 'yan uwana ba kowa ne zai iya bani ba, kuma 'yarki ta fari? Dan Allah sultana kar mu fara abinda bazamu iya 'karasawa ba, kar gaba kizo kice na baki, sultana ko kin bani danginki bazasu bari ba ".

Tsaki taja tace,

" Bilki idan akwai wadda zance ta haifarmin Huda kece, nasani dole zakiyi kokonto akan hakan saboda abinda 'yan uwana ke miki saboda ni, amma wallahi abinda suke yi ba dan ni bane kawai son zuciyarsu ne, na sani saleh tsohon saurayi na ne kuma na soshi kaman zan mutu ".

Usman ta kalla tace,

" Kayi ha'kuri yayana amma inaso na goge zargina daga zuciyar bilkisu ".

Juyowa tayu gareni tace,

" Bilki nasan 'kaddara na kuma yarda da ita, na amince da auren ya usman ne kawai don huce takaici, amma yanzu na godewa Allah domin dalilin auren ya usman na sami gata da soyayyar da inada tabbacin da saleh na aura bazai bani ba, wallahi bilki da zuciya d'aya nake sonki tunda na tabbatar da zuciyarki a tsarkake take, furucin da nayi kwanaki saboda kawai hankalinsu ya kau daga kanki ne, amma hakan bai samu ba, bilkisu idan ban baki Huda ba cutar da ita zanyi, wallahi kinji na rantse tunda nayi cikin huda bana son cikin, laulayin da nayi takaici ne duk ya cikani, ranar kuwa da na haifeta kamar an rabani da 'kaya, ban san isharar da Allah yake son isarmin ba, amma babu soyayyar huda a raina kaman yanda uwa zata ji ga 'ya'yanta, nayi 'ko'karin naga naso huda kamar yanda sauran iyaye ke son 'ya'yansu amma jinta nake kamar bare, ke nifa banda naji zafin haihuwarta zan iya rantsuwa ba 'yata bace, Huda 'yarki ce tunda na haifeta kike bata kulawa, Huda dake ta dace ki taimaka ki kar'beta dan Allah ko na sami nutsuwa a raina, na miki al'kawari ko zan rasa duk 'ya'yan da na haifa bazan sake kallon huda a matsayin 'yata ba, dangina kuma ki barni dasu ni nasan yanda zanyi dasu, amma naki dangin ki musu shela su fara kiranki da maman Huda, har rubutu ma munyi saboda tsaro gashi zaki sanya hannu a takardarnan ".

Bugaggiyar takarda ta mi'komin a ciki an rubuta,

_ Ni Usman Abubakar, tareda matata sultana jibril, mun bawa saleh abubakar da matarsa kyautar 'yarmu surayya abubakar, kyauta ta har abada, bisa ga sharad'in zata ri'keta amana, bazata cutar da ita ba_.

Wurin signing na iyayen aka bari sannan aka sake rubuta.

_Ni Usman abubakar tare da matata bilkisu Ibrahim munyi al'kawarin ri'ke surayya abubakar bisa amana, bazamu nuna mata banbanci ba bazamu cutar da ita ba, komai wuya komai dad'i bazamu maidata ga iyayenta ba_.

Daga kai nayi na kallesu na saka hannu a takardar, kar'bar takardar tayi ta mi'kawa usman tace.

" Gobe sai kayo photocopy guda biyar haka ko? A bata d'aya a kaiwa lawyan d'aya, sauran mu ajiye saboda halin 'bata ".

Cikin mamaki nace,

" Me ya kawo lawyer kuma? ".

Murmushi tayi tace,

" Saboda iyayenmu mana, dole sai mun danganta da kotu, yanda ko sun 'ki amincewa kotu zata ce musu babu halin hakan ".

Shiru nayi sannan nace,

" Sultana na kasa furta godiyafa gareki, bansan me zance miki ba, saidai nace Allah ya biyaki da aljanna ya 'kara miki zuri'a masu tausayi da jin 'kai, Allah ya baki zuri'ar da zasu ceceki su sakaki a aljanna ranar 'kiyama ".

" Ameen nagode da wannan addu'ar ".

Godiya saleh yayi suka fita shi da usman muka hau hirarmu, nan nake bata labarin yanda mukayi dasu akan rashin haihuwata da kuma zuwan hajiya, bani baki tayi hankalina ya d'an kwanta.

Tana fita na kira mama na sanar mata wannan babbar kyauta, d'if naji mama tayi sai can tacemin,

" Wannan maganar ba ta waya bace gobe zamu zo gidan, ki fad'a min lokacin da kike nan "

Fad'a mata lokacin da zan dawo nayi na goya huda tare da d'aukan kayanta na fara kaisu d'akin sama ina jerawa, saida na yiwa komai wuri gadon nata kuma yamin nauyi na barshi saleh ya d'auka

Saida na gama shirya kayanta tsaf tukun na sami nutsuwa na zauna ina tunanin sabuwar rayuwar da zan shiga da Huda, ina zaune a gadon d'akin naji sallamar Saleh a palo, sauka nayi na sami fuskarsa d'auke da murmushi

Cikin sauri na sauka tareda hugging dinsa, hawayen farin ciki naji ya sauka a fuskata, ha'barsa ya d'aura a kaina yana shafa huda dake bayana.

Sauke Huda nayi muka zauna ya kar'beta ya zuba mata ido, kallona yayi yace

" Kinga kyautar Allah ko? Dama ance yana azurta mutum ta hanyar da baiyi zato ba, daga ni har ke bamu ta'ba zaton huda zata zama mallakinmu ba amma kalli, cikin mintina kad'an kin haifarmin 'ya, Allah mungode maka "

Murmushi nayi na d'aura kaina a kafad'arsa ba tare da nace komai ba, duk kalmar da zan yiwa Allah godiya da ita gani nake tayi kad'an, azumin godiya nayi niyyar yi tare da sadaka domin sune hanyoyin da nake ganin zan fi nuna farin cikina ga Allah.

Kamar ance na d'aga kaina, had'a ido mukayi muka sakarma juna murmushi, kwana biyu munyi missing juna saboda damuwarmu ta fara yawa, amma zuwan huda kaman wani sassauci yazo

Hannunsa ya sanya ya tallafo fuskata tare da sumbatar goshina yace

" Ina 'kaunarki bilkisu, ke kad'ai nake mafarki a rayuwata ina addu'ar Allah ya barni daga ni sai ke sai 'ya'yanmu bana so kowace mace ta sake shigowa rayuwarmu "

Hannu na sanya a fuskarsa nace

" Allah ya amsa addu'ar ka mijina, Allah ya barmu mu biyu har aljanna "

Sunkuyo da kansa yayi tareda had'e goshinsa da nawa, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya sannan ya d'ago kansa, saida ya kawo bakinsa saitin nawa na d'auke kaina tareda cije le'bena "

'daga girarsa yayi yace

" Me kenan? "

" Aha, abinda nakeso kayi kenan, na dad'e banga ka d'aga girarnan ba, wow I miss it ashe haka kake kyau idan ka d'aga gira?"

Kwafa yayi yace

" Zan rama ne "

Kujerar gefe ya kai Huda dake bacci ya nufoni, da gudu na tashi ina dariya kafin nayi nisa ya ri'ko cikina,d'age 'kafafuwana nayi domin na sakar masa nauyi amma ko a jikinsa.

A tsakiyar palon ya kwantar dani tare da yimin rumfa, lumshe ido nayi ina jiran naji kiss naji cakulkuli, dariya nake sosai ina bashi ha'kuri saida nace masa zanyi fitsari tukun ya 'kyaleni

Dariyar bata gama sakina ba naji bakinsa a nawa, lumshe idona nayi hannuna na bayansa, hannunsa naji yana shafa kafad'ata zuwa wuyana na tuna da huda, a hankali na bubbuga bayansa ya d'ago yace

" Yaya dai "

Numfashi nake maidawa

10 / 41