Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
bayyane take 'karara, sai yanzu ya fara komawa hayyacinsa, shin me ya aikata cikin fushi? Me su hajiya suka aikata masa?
Komawa yayi ya kwanta yana sake duba labarin domin ya gaskata, kwanciya yayi kan kujera ya fara tunanin yanda zai tunkari hajiya da wannan bayani, dalili d'aya yake son ji, meyasa suka kar'bi kud'in? Me zasuyi dashi? Da wannan tunanin ya kwanta
*********
*BILKISU*
Banyi tunanin za'a samar min aiki da wuri ba, amma abin mamaki ina zaune sai ga kiran aunty tace na shirya naje gidan ta zata kaini interview na aiki, dama ana bu'katar interview a nursing?
Ina shiryawa ta sake kirana, cikin d'aga murya tace "saura kizo min da jajayen idanu sau na saka a kwantar dake a asbitin na wata hud'u", dariya nayi nace "to aunty" abinda bata sani ba tuni na dena wa mutuwar aurena kuka, dama nasan igiyar aurena bazata zauna ba tun ranar da na saka 'kafafuna a gidan.
Bazan ce Saleh ya fita daga raina ba amma na kaishi can wani wuri a zuciyata, koyaushe yana raina amma bana tunaninsa, bansan ko akwai wanda ya fahimci maganata ba.
Na san halin aunty ko gumi ta gani a fuskata sai ta 'karewa Saleh zagi nima na sami rabona, saboda haka na d'an b'ata lokaci wajen makeup, abinda banyi ba kusan sati biyu kenan.
Powder na shafa na sanya purple d'in jambaki nayi highlighting da jagira, saida na 'karewa kaina kallo sannan na yafa mayafi, i can't believe it, wai ni ke iddar Saleh ya sakeni, Allah yasa ma ba fara wuri.
Ina zuwa gidanta na sameta tana zaune a palour da jakarta da mayafi a gefe, kallona tayi ta saki murmushi tace "haba ko kefa, har kin fito a mace da kina kwance bakida aiki sai kuka akan wancan me......"
"Dan Allah aunty karki 'karasa ki barshi haka, ni ina mamakin ma yanda kalamannan basu 'kare a bakinki ba duk zaginsa da kikeyi a barshi haka". Na 'kare maganar ina dariya, harara ta tayi cikin wasa tace "da kansa kamar banana". Dariya nayi sosai, har mantawa nakeyi aunty ta kai mahaifiyata saboda yanda take abubuwanta, ta iya tafiya da mutane ko Yaya mutum yayi socializing da aunty sai ya sota, idan akayi hutu gidan cika yake da yara, dukda ban ta'ba ganin mahaifina ido da Ido ba amma idan na kalleta tana tuna min dashi, mama tana yawan fad'amin halinsu d'aya da mahaifina, irin mutanennan ne da basa nuna fushinsu, idan kana tunanin basu haushi saidai ma ranka ya 'baci.
"Tashi muje kar mu makara" tashi nayi muka fita a motarta, baifi tafiyar minti 15 ba sai gamu a asbitin, kallon wurin tayi tace "ya kamata a saya miki mota saboda fita", bance komai ba domin zanso nima na fara tu'ka motar kaina, ina yawan driving ta Saleh musamman zuwa makaranta kuma fita a motarka yafi mutunci musamman a wannan zamani na cudanya da 'katti a abin hawa.
Asbitin nada girma ba laifi sannan ya matu'kar had'uwa, tun daga wajensa har ciki, secretary ta wurin naji ta tambaya wani mutumi nan tace mata yana office, babu wani jira taja hannuna muka zagaye secretary d'in muka wuce, 'kwan'kwasa 'kofa tayi kafin ace mu shiga ta bud'e tareda turani sannan ta shiga.
A fusace mutumin ya juyo zai fara fad'a yana ganinta yanayinsa ya sauya, bansan waye wannan ba amma dai naji yanayin wurin ya canza, "ko kujera baza'a bamu ba Abban shaheed?"
Kallona yayi da alamun kunya sannan yace "kuyi ha'kuri ga wuri ku zauna", d'aura 'kafa d'aya kan d'aya aunty tayi sannan tace "sai naga kana nuna kamar baka san da zuwanmu ba bayan dai kai ka kirani ko har tsufa yasa ka fara mantuwa haka, ko kuma kyakkyawar 'yar tawa ce tayi maka?"
Dariya yayi yace "a'a babu ko d'aya, Hafsa banda abinki ina ni ina 'yarki bayan na aureki? Kawai zuwan naku ne....." Katse maganarsa yayi ya kalleni yace "itace Bilkisu ko?"
"Eh 'yar wajen marigayi ba" kallona yayi cikin tausayawa sannan ya janyo file, sunkuyar da kaina nayi domin na tsani wannan kallon, Allah yayimin gata da bana cikin maraici bansan meyasa mutane ke son dawomin da kewar iyayena a koyaushe ba.
Gaba d'aya hankalinsa ya dawo kaina yace "Bilkisu takardunki sunyi kyau, na duba komai naki, amma meyasa kika 'ki amincewa asbitin da kikayi internship bayan sun d'aukeki aiki?"
Shiru nayi na rasa me zance, a lokacin bana so na fara aiki saboda Shirin d'aukan ciki, sannan ban dad'e da warkewa daga ciwon da nayi mai kama da hauka ba wanda har mutuwata bazan manta dashi ba,amma ta yaya zan fad'a masa wannan? Sannan asbitin bana 'kaunarsa dama dai koyan aiki ne ya kaini kuma na aikatu, na kar'bi haihuwa tafi 500 a shekara d'aya da nayi banda aikin emergency da sauransu.
"Nayi rashin lafiya ne a lokacin bazan iya aiki ba sannan basu barmin offer d'in ba bayan sunga yanayin rashin lafiyata sai suka janye offer"
"Wani irin rashin lafiya kikayi?"
Aunty ce ta tari numfashinsa tace "aljanu ne suka kamata a lokacin amma cikin ikon Allah da taimakon su alhaji baba ta warke kamar batayi ba, baban shaheed haka ake interview d'in aikin? 'yata ce fa ka yiwa Allah ka dena mata tambayar ya uwarta ta haifeta ka bata aikinnan".
Dariya yayi, wani abu dana lura shine duk tambayoyin da yakemin hankalinsa na kan Aunty, waye wannan ko dai?..... Kunya naji da tunanin yazo raina, duk girman anty ace wannan saurayinta ne? Au bazawari? Dariya naji ta 'kwacemin na danne, ina kallonta tana min wani irin kallo.
Tambayoyi yayimin akan aiki, tambayoyi ne da sai ka amsa a dabara har tambayata yayi wani 'bangare ne banaso nayi dealing da nace babu, bayan kusan awa guda ya d'aukeni aiki, takura masa Aunty tayi akan sai ya fad'a mata salary na ya'ki yace idan naga alert sai na fad'a mata idan naga dama
Har mun fita ta bud'e 'kofa tace "ka gaida maman shaheed kace mata tsohuwar natarnan taka me naci tana gaidata".
Girgiza kai nayi tareda murmushi, amma nayi mamaki da tunda na taso ban ta'ba ganinsa ba, ina yawan zuwa gidan Aunty amma bana ganinsa.
Kamar ta karanta tunanina tace "gaba d'aya aurena baifi a 'kirga ba yake zaman gida lokacin yana aiki a England sannan ya'ki tafiya dani, a shekara baifi yazo sau biyu ba, zuwansa na 'karshe yazo min da maman shaheed da shaheed ya dad'e da auren ban saniba abubuwa da dama suka faru bayan haka da sukayi sanadin mutuwar aurenmu, wannan asbitin nashi ne yanzu idan ya miki abu komi 'kan'kantarsa ki fad'amin kinji? Allah ya kaimu first salary d'inki ya shigo idan ya sake ya baki 'kasa da d'ari dai ya ciko miki". Ta fad'a tareda had'e girar sama da ta 'kasa, numfashi ta sauke tace "ni ya kamata inci wannan kud'in amma ya zanyi? Yanzu ke zaki ciyo min su kin jini ko?"
Gyad'a kai kawai nayi ta canza hirar, kafin muje gida na sayi yadin uniform sai yanzu na tuna da million d'ita dake wurin Saleh, dole kuwa na kar'bo kud'ina. Bayan mun sayi yadin muka wuce gidan aunty a can na wuni sai dare ta Kira Jabir ya d'aukeni, a hanya nake ce masa "Yaya akwai kud'ina fa a hannun abokinka, almost a million".
"Meyasa kika bashi kud'inki haka? A ina ma kika samu wannan kud'in?"
"Kud'in internship ne da gwamnati ke biyanmu duk wata lokacin da mukeyi, ana bani 135,000 duk wata, ina d'an siyayya shiyasa ma kud'in baikai million ba sannan ya ari wasu".
Murmushi yayi yace "Zan sa ya turo miki kud'inki sai ki kiyaye nan gaba kisan wa zaki bawa kud'i, tunda ya manta da amince masa da kikayi kika bashi ajiyar ma'kudan kud'i yake zarginki da sata".
Jingina nayi a kujerata nace "Yaya dan Allah mu bar wannan maganar kaji?" Amsamin yayi da to mukayi shiru, fruit muka saya sannan muka tafi gida.
************
*SALEH*
Yanke shawarar fad'awa Hajiya yayi, bayan sun gaisa ya d'auko wayarsa yace "hajiya...." Katseshi Hajiya tayi tace "na gaji da kar'bar uzurinka akan zuwa wajen hadiyya, yau bayan Isha zakaje ka sameta na sanar da iyayenta kuma banaso a sami sa'bani".
Maida wayarsa aljihu yayi yace "Hajiya ya jikin Amir" cikin sauri tace "Amir dai to gashinan idan Allah ya yarda wannan asabar d'in zasu tashi zuwa indiya, Allah ya saka maka da alkhairi ka taimaka wa 'yar uwarka".
"Kenan jirgi d'aya zasu hau da yaran da gwamnati ta biyawa aiki".
"Eh..." Shiru tayi ta zuba masa ido tace "me kake nufi? Wannan tsinanniyar bayan ta tafi ma sai ta dinga jan ra'ayinka? Me kake nufi da abinda ka fad'a? Zargina kake da 'karya ko me?"
Tashi yayi tsaye yace "hajiya ba 'karya nake nufi kinyi ba, tambaya kawai nayi saboda naji ance suma asabar zasu tashi na yarda da abinda kika fad'a" fita yayi ba tareda yace komai ba yana jin tana tuna masa da zuwa ganin hadiyya.
Kamar kullum suna gaisawa da jabir suka fara aiki, ya gaji da silent treatment d'in da Jabir ke masa saboda haka ya nufeshi kafin Jabir ya koreshi yace "Jabir kayi ha'kuri da abubuwan da suka faru ka saurareni, nasan nayi kus......"
Dakatar dashi Jabir yayi yace "lokacin da Bilkisu ke ro'kon'ka ka saurareta ka saurareta? Lokacin da take bu'katar ka fahimceta ka fahimceta? Ka saki 'kanwata tsawon sati biyu amma baka tambayi Yaya lafiyarta ba, baka kirata ko sau d'aya ba sannan kace kana so na saurareka kayi kuskure bazan ta'ba sauraronka ba, akwai aikin kitchen da muka kar'ba daga yobe zaka tafi ranar lahadi zan had'aka da mutum biyu saboda ayyukanmu na nan sunada yawa"
Yana gama maganarsa ya bar wurin, cikin 'bacin rai Saleh ya daki katakon dake gefensa dariya jabir yayi yace "Kar ka karya mana katako zaka biya".
Har Jabir ya gama aikinsa ya tafi Saleh na wurin, sai gab da magrib ya tafi gida, ko abinci baici ba ya fita ya nufi gidansu hadiyya, kwatancen da Hajiya ta masa saida ya sake tambaya aka kaishi gidan, kallon unguwar yayi yanda yara keta shige da fice kamar ba dare ba, yaro ya tura aka kirata ta kusa 30mins sannan ta fito.
Sanye take da hijabinta kanta a 'kasa, dur'kusawa tayi ta gaidashi ya amsa, shiru sukayi tana dur'kushe yana tsaye hakan yayi masa wani daban shima ya dur'kusa a 'kasan, 'kwala mata kira akayi daga gida ta tafi da sauri, dawowa tayi da tabarma da fitila ta shimfid'a ta zauna a can gefe, zama sukayi ta had'e kanta da gwiwa tana kallon gefe, haka suka 'kare zaman nasu shine ma ya d'an mata tambayoyi wanda ta bashi amsa da kalma dai-dai, gajiya yayi ya tashi ya tafi.
Ranar asabar baije aiki ba kasancewar lahadi zaiyi tafiya Jabir ya bashi day off ya kintsa, yayi tunanin za'a shirya Amir a part d'in hajiya amma sai yaga hajiyan ma bata nan lokacin da yaje gaidata, gidan maimuna yana zuwa yayi sa'a sun fito, a tsorace duk suka kalleshi ga Amir yasha farar shadda da jar hula, hajiya ce ta dake tace masa "me kakeyi anan?"
Murmushi yayi yace "nazo yi musu sallama ne Hajiya kuma naso mu taho tare naga kin rigani zuwa, muje na kaiku airport d'in".
Gaba yayi da amir a hannunsa ba tareda ya jira me zasu ce ba, haka suka bishi a baya suna jan 'kafafu, babu wanda ke magana a motar sai shi har suka isa,
Takarda maimuna ta nuna aka tafi da ita da Amir inda sauran yaran suke da iyayensu a tsaye, hotuna aka fara sannan suka shige jikin su Hajiya gaba d'aya yayi sanyi domin ba haka suka yi zato ba, tunaninta zaije aiki kafin ya dawo saidai tace masa maimuna ta tafi amma yanzu bata san ma me zata ce masa ba.
Bayan sun shige Saleh yace da kursum "muje na kaiki gida ko? Ko kuma gidanmu kika nufa?" Gyad'a masa kai kawai tayi kamar 'kadangaruwa suka nufi mota, suna shiga Hajiya ta fara kuka, kallonta Saleh yayi yace "Hajiya kiyi ha'kuri Allah zai bashi lafiya su dawo, bakiga wasu daga cikin yaran ba sun fishi jin jiki?"
Goge hawayenta tayi tace " 'yan uwanka suna cikin matsala wanda ni banida yanda zanyi na taimaka musu, ka duba ka gani ace inada 'ya'ya maza masu arzi'ki kamar ku amma 'ya'yana mata suna shan wahala? Daga maimuna har kursum babu wacce take auren mai arzi'ki, ni nawa 'ya'yan suna Shan wahala amma 'ya'yan wasu na cinye arzi'kinku, yanzu Amir har sai gwamnati ta biya masa aiki saboda talaucin mahaifinsa? Kun isa ai ku biya masa shiyasa da jumana tace min taji zancen kud'innan nace to 'ya'yana sunfi matarka bu'kata, na kar'bi kud'in ne Dan na tallafa musu na raba musu suyi jari tunda nasan idan nace ka bayar bazaka bayar ba".
Dam'ke steering yayi yace "Amma Hajiya kinsan me zanyi da kud'in meyasa kika kar'beshi a lokacin? Idan har jari kikeso ni mai basu ne amma Hajiya dalilin wannan kud'in.....na rasa matata".
Cikin 'bacin rai hajiya tace "dama ba matar arzi'ki bace, lokacin da zaka bada kud'in ba hanaka tayi ba?"
Ya kusa dukan mai mashin cikin sauri ya kauce yace "hajiya ba hanani bayarwa tayi ba, gaskiya ta fad'amin cewar gwamnati ta biyawa Amir kud'in aikin, kuma ta fiku bu'kata, tana cikin damuwa na rashin haihuwa sannan ga takurar ku abinda tafi bukata shine ta haihu, nima ina bu'katar naga jinina, hajiya kinsan me zanyi da kud'innan amma kika kar'be?"
Cikin d'aga murya hajiya ke magana tace "dakeni nace tunda na lura dukana kakeso kayi, idan haihuwar kakeso meyasa baka auro wadda zata haihu a kyauta ba sai wadda zata sayi d'a 'kwaya d'aya a miliyan hud'u? Banda hauka irin naka duk matan duniya masu haihuwa kyauta bazaka aura ba sai ita? Kud'i ne na kar'ba idan kanada hali sai ka 'kwata".
Idanunsa tuni suka ciko da 'kwalla nadama ta dirar masa, muryarsa 'kasa-'kasa yace " Hajiya ya akai kud'innan suka koma gidana?"
Saukar mari yaji a fuskarsa saidai rad'ad'in da yakeji a ransa yafi zafin marin, a fusace Hajiya tace "zargina kake ni na kai kenan? Uwarka ce ni idan ka manta ni na haifeka Dan ubanka!! Kuma matarka ta tafi kenan ka dawomin da ita gidana Allah ya Isa ban yafe maka ba, shashasha kawai".
Saleh bai sake cewa komai ba har Allah ya kaisu gida domin tafiya kawai yake baisan inda yake bi ba, a waje su hajiya suka fita ta doka masa 'kofa, jingina kansa yayi a jikin steering Yana dukan sterrin, meyasa ya aikata wannan kuskuren? Anya Bilkisu zata yafe masa idan ya koma? Yasan halin bilkisu da sau'kin kanta zata saurareshi.
Gida ya shiga ya zauna kan kujera, karo na farko a lokaci mai tsayi ya zubar da Hawaye, haka ya zauna Yana tunanin abubuwan da yayi messing, idan har ba sa'a yayi ba ya rasa matarsa har abada....bazai yiwu ba bazai iya zama da kowacce mace idan ba Bilkisu ba.
Yana sallar magrib ya d'auki wayarsa ya fara Kiran number Biliisu saidai gaba d'aya ma kiran ya'ki shiga, Jabir ya kira saida ya kirashi sau hud'u tukun ya amsa, cikin sauri yace "dan Allah ka had'ani da Bilkisu". Shiru jabir yayi masa ya dinga masa magiya, Jin yanda yake magiya yasa jabir yasan an samu matsala, murmushin mugunta yayi tareda gyaran murya yace.
"Saleh Bilki fa bata garinnan tun shekaran jiya suka tafi Kaduna saidai idan zaka bita".
35
"Dan Allah Jabir kar ka yimin haka ka taimakamin na ganta jo da na minti biyu ne".
Jingina Jabir yayi a bango yana kallon Saleh, hannunsa yasa a aljihu yace "yanda na fad'a maka a waya Bilkisu bata nan tana tana KD, Idan wani sa'ko ne ka fad'amin idan ta dawo na sanar da ita".
"Yaushe zata dawo?"
"Friday" jabir ya fad'a Yana kallon wayarsa, cikin rawar murya Saleh yace "Dan Allah Jabir a d'aga min tafiyarnan zuwa wata Sunday d'in inaso nayi magana da Bilkisu kuma na kirata numberta bata shiga".
"Tayi blocking number d'inka ne saboda tace batason wani abu da zai had'ata da kai, sannan tafiya idan har muka d'aga munyi asarar kud'inmu gaba d'aya kenan saboda sati uku ya bamu mu gama masa aikin, tunda kayi aure ban ta'ba bari kaje aiki a wani gari ba shekara uku kenan, yanzu akwai adalci ace tafiya d'aya da zakayi kana dodging? Idan bazaka je bane ka fad'amin nasan abun yi".
Kallon agogon hannunsa yayi dukkansu sukayi shiru, kallo d'aya ya yiwa Saleh yaga alamun damuwa sosai a tattare dashi, amma basjida niyyar bashi abinda yakeso, indai Bilkisu ce sai ya sha wahala kafin ya sameta...idan ma ya sameta d'in kenan.
"Idan ta dawo zan had'ata da kai a waya kuyi magana, saida safe ko? Allah y kiyaye hanya" Jabir na gama fad'in haka ya shige gida ya bar Saleh a tsaye, sake kiran Bilkisu yayi yaji bata shiga ba ya ha'kura ya tafi.
Washegari 6:00 Jabir yaje ya d'auko Saleh domin ya kaishi tasha, ko sallama Saleh baiyiwa Hajiya ba ya fita ya shiga motar Jabir.
"Dan Allah Jabir da gaske Bilkisu batanan?" Saleh ya fad'a yana kallon wayarsa, shiru Jabir yayi masa har sukaje tasha saida ya shiga mota sannan ya Janir ya juya ya koma gida.
A kujera ya sami Bilkisu tana bacci da uniform a jikinta domin night tayi,wayarta ya d'auko ya bud'e ya duba number Saleh ya ganta a blocked, bud'e Ido tayi tareda mi'ka tace "Yaya ina kaje ne da sassafe haka na dawo bakanan?"
Gefe ta matsa ya zauna yace "naje kai Saleh tasha ne zai tafi yobe aiki, nace idan kin tashi ki dinga kirana meyasa zaki dawo? Gari fa bai gama wayewa ba nasan kika fito haka last week kika taho da dare, Bilki yanayin garinnan sai a hankali karki sake tahowa da safe ko dare sai kin kirani kinji?"
************
*BILKISU*
Tura baki nayi nace "to baba" kallo yayimin alamun na tashi ki gudu, aikwa cikin sauri na tashi, ri'ko hijabina yayi ya kama kunnena yace "me kikace?"
Dariya nake sosai da kyar nace "yi ha'kuri yayana bazan sake dawowa ba tareda na kiraka ba, dan Allah sakeni".
Sakin kunnena yayi na cire hijabin nace "ai Aunty ma tace za'a siyamin mota bansan dai yaushe bane".
Dafe kansa yayi yace "au, aikuwa tayimin maganar tace tanaso ki fito gari kema ki shiga cikin 'ya'yan wane da wance, tace na bincika mota mai kyau ta mata me tsada, batason kamfanin motar Saleh komai kyantq".
Had'e 'kafafuna nayi a kan kujera nace "Aunty dai is so obsessed