Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
kotu".
Hannunta ta sanya tana kunce goyon Huda na ri'ke hannun nace "Aunty maimuna tun ina girmamaki ki d'auke hannunki daga jikina, banaso kiyi abinda girmanki zai zube a idona, ku da mahaifiyarku kun nunamin tsana iya tsana na danne na jure, kin shiga rayuwar aurena na ha'kura, yanzu kuma so kuke duk wata hanya ta farin cikina ku toshe? Bakwa tunanin kuna cutar da d'an uwanku a haka? Muna son junanmu ku rabu damu mana, Sultana tana Sona after all the circumstances da ya faru tsakaninsu da mijina, wannan kad'ai bai isheku izna ba? Sai dole kun rabani da 'yata meyasa kukemin haka ne?"
Kursum ce tayo kaina cike da tsiwa tace "kar ki sake na sake jin kin ambaci hakan a bakinki, Huda ba 'yarki bace babu abinda zai had'a jininmu dake, baki haifi Huda ba baki shayar da ita ba, babu abinda kika sani game da ita kuma dole ne ki bada ita".
Dariya nayi na shafa Huda dake bayana nace "alhamdulillah ban haifi Huda ba balle naji zafin haihuwarta, ban shayar da ita ba amma tun kafin Huda tazo duniya nake d'awainiya da ita da mahaifiyarta har Allah ya kawo ta duniya, ban haifeta ba amma na haifar mata soyayyar da duk wajennan babu wadda zata iya bata ita, Mahaifiyar Huda ta aminta dani ta bani ita dan haka babu komawa baya".
Hannu kursum ta Sanya a k'ugunta tace "bazaki bayar ba kenan?" Gyara goyona nayi nace "bazan iya ba gaskiya", hannu maimuna ta mi'komin tace " idan na k'irga uku baki bani Huda ba zan miki abinda sai kinyi dana sanin ja-in-ja dani".
Dariya nayi cikin takaici nace "to ni kuwa a zamana na gidannan menene ban ganiba? Tun daga day one nasan matsayina a gidannan bana tunanin akwai abinda zaku yimin na jishi a jikina, babu wadda ta isa ta rabani da Huda wallahi ko da kuwa Sultana ce"
Kallon Hajiya Maimuna tayi tace "Hajiya kiyi mata magana mana"
Daga inda take tsaye tace "Bilkisu, umarni nake baki idan har jin haifu ki sauke 'yar nan ki bani ita a hannuna, idan kuwa bakiyi hakan ba to tabbas bakya ganin darajar wad'anda suka haifeki".
Wani abu naji ya tsayamin a raina a hankali na kunce Huda, Kar'barta Saleh yayi tana bud'e idonta ta Kira sunana tare da mi'komin hannu, dogon tunani nayi a wannan lokacin ba kalli Sultana, girgiza min Kai takeyi na rungume Huda nace. "Hajiya ni 'yar halak ce kuma ina ganin darajar mahaifana duk da banzo duniya na samesu a raye ba, amma duk d'an halak ya san girman al'kawari, bazan iya baki Huda ba har sai anje kotu mun tsaya ni da Sultana ta fad'i cewar ta canza maganarta da dalilin canzawar, sannan nima zan goge nawa al'kawarin ba baki Huda amma a yanzu Huda mallakina ce, bazan iya....."
Saukar wani mari mai gigita tunani naji a fuskata, saura 'kiris na yar da huda saboda tsananin firgici da zafin marin, d'agowa nayi idanuna a take suka sauya, zuciyata ta sake 'ke'kashewa, Raina ya kai 'kololuwar 'baci nace "Maimuna wannan ya zama karo na 'karshe da zaki kai hannunki jikina, na d'auki iya abinda zan iya d'auka daga gareku, na gaji da zama daku Banda ina 'kaunar mijina babu abinda zai zaunar dani a cikin wannan gidan, Huda ce bazan bayar ba duk wadda take ganin tanada iko da ita tazo ta 'kwaceta"
"Da wa kike?" Maimuna ta fad'a tana kallon tsakanin ni da Hajiya, tsaki naja nace "duk wadda take ganin girmanta ya isa ta zubar dashi tazo tana kishi da matar d'anta ko Kuma matar 'kaninta saboda matar tana samun wadatar da ita bata samu a gidan aurenta, ina magana ne da duk wadda ta gaji da zamana a gidannan, Huda tawa ce haka ma Saleh nawa ne duk duniyarnan Babu Wanda ya Isa ya rabani da wad'annan mutane biyu, idan kun rabani da Saleh kuna tunanin zaku bashi abinda nake bashi ne? Ni nake baiwa Saleh walwala na bashi farin ciki na kuma raba dare ina masa hidima, duk soyayyar da kuke masa kuna tunanin zaku iya masa hakan ne? Meyasa kuke kishi dani? Meyasa bakwa son farin cikina? Meyasa? Banida lokacin tsayawa cece kuce daku amma kusani ku tsaya ku kula da aurenku domin aure Rai gareshi, idan kana tunanin raba wani da nasa Kai baka san wa'adin da Allah ya d'ebarwa naku ba, na gama maganata anan duk wadda take da ikon kwace Huda daga gareni ta sameni a mazaunina".
Cikin sauri na bar wurin na nufi sashina zuciyata tamkar zata fita saboda 'bacin rai da tsoro, tunda nake ban ta'ba tsintar kaina a irin wannan yanayi da aka Kai hakurina nesa ba, yanzu me zai faru tsakanina da Huda? Me zasu aikata next?
23
Sauri nake saboda hawayen da naji yana zubowa daga idona, kiran sunana Saleh yakeyi amma Sam na 'ki tsayawa, tura gidan nayi na shiga cikin sauri kai tsaye kujera nabi na ajiye Huda na kifa kaina ina matsanancin kuka, dukda cewa a yau na 'kwatarwa kaina 'yanci amma dukda haka rad'ad'in maganarsu yana damuna.
Dur'kusawa Saleh yayi a gefena yana shafa bayana ba tare da yayi magana ba, ha'barsa ya d'aura kan kafad'ata yace "I am so sorry boo-boo na, kiyi ha'kuri kinji?"
'Dago jajayen idanuna nayi nace "meyasa hakan yake faruwa ne boo-boo, meyasa 'yan uwanka bazasu barni nayi rayuwar aure mai dad'i ba? Meyasa......" Sar'kewa magana ta tayi na sake kifa kaina, hannunsa ya sanya ya d'ago fuskata yace "babyna kalleni nan, ki fad'amin dalilin zuwanki gidannan, saboda su kike zama ko saboda ni? Soyayyarsu kike so ko tawa?".
Hannuna na Sanya a kan nasa nace "komai da nake yi saboda kai ne, amma soyayyarsu tana da matu'kar muhimmanci a wajena domin zata bani damar zama kamar kowacce mace, nima naji dad'in zaman aurena amma aure anfi shekara babu abinda ya canza? Yaushe zan bar wannan 'kangin walahalar saboda bana haihuwa? Ni na d'aurawa kaina? Su suke bada haihuwar ko kuma su suka haifi Huda da zasu nunamin iko da ita? Wallahi a duk lokacin da hakan ta faru sai na tsinci kaina ina nadamar......".
Bai bari na 'karasa ba ya had'e bakinsa da nawa, cikin zafin rai nake tureshi amma ya ri'ke kafad'ata sosai, wani abu naji yana min yawo a cikin raina, zuciyata ta sake raunana wasu sabbin hawayen ke zubomin.
Shafa kafad'ata yakeyi zuwa wuyana zuwa saman bayana, sake deepening kiss d'in yakeyi tareda sanya hannunsa yana goge hawayen dake zuba, a hankali zuciyata ta fara rinjaya zuwa ga aikin da yakeyi saidai wani 'bangare na jikina yana fad'amin na dakata.
Ban maida hankali ba na biye masa, daga yanda nake maida masa martani yasan Ina cikin tsantsar 'bacin rai, so nake kawai na samu hanyar da zan fidda zafin dake cikin raina gashi kuma Saleh yazo min da hanyar da tafi sau'ki gareni.
Idanuwana sun rufe, hanya kawai nake nema da zan cike emptiness d'in da nakeji a raina, kwanciya nayi kan carpet d'in yayi rolling kansa bisana, cikin da'ki'ku kad'an komi ya fara heating up
HUDA, cikin hanzari na tureshi na kalli kujerar da na ajiye Huda, tana kwance tana bacci yau dai kamar tasan me zai faru bacci take ta faman yi, ajiyar zuciya nayi nace "kwata-kwata na manta da Huda a wurinnan Allah ya taimakemu bata farka ba".
Murmushi yayi ya kalleni yace "har kin huce kenan, God you are so sexy when you are angry, Zan tabbatar ina 'bata maki rai akai-akai domin wallahi I love this demanding you".
Duka na kai masa cikin wasa sannan na 'karasa zuge rigata na cireta ba tare da nace masa komai ba, 'kurawa 'kirjina ido yayi yace "wannan ban Santa ba sabuwa ce ko?" Ya 'kare maganar yana nuna bra d'in jikina, kai na gyad'a masa nace "amma ai ta dad'e tun kafin na fara rashin lafiya fa, baka dai kula bane".
Skirt d'in jikina na cire shima na ninke na zauna da underwear, camo bra ce a jikina saboda haka so comfortable nake jina tamkar na saka riga, ajiyar zuciya nake tayi amma abin na bani mamaki yanda lokaci guda 'bacin raina ya
yaye saidai zuciyata ta fara rayamin abinda nayi ban kyauta ba.
"Humm Bilkisu kenan, ki ma dena tunanin yanda wannan genie d'in mijin naki ya kawar miki da damuwa nan da nan, na sanki fiye da sanin kanki na san yanda kike da abinda kikeso when you are exhausted or angry, na sani cewa kina jin rashin dad'in abinda Kika ma 'yan uwana a gabana ko? Bilkisu na san ke wace irin mutum ce, kinada tsananin ha'kuri da kawarwa sau da dama zan miki abu nasan ranki ya 'baci, amma saidai kawai kice hmm ko ki nemi abin ci ki kai bakinki, ina sane da yanda kike d'ebo wanki ki fara saboda damuwa ko bakyaso kiyi magana akan abu, Bilkisu ina lura da yanda kike d'aura girki da zarar mun shigo gida a duk ranar da akayi taro saboda bakyaso abinda ya faru ya dameki, ina karantar yanda yanayin idanunki ke canzawa a duk lokacin da aka maki wani abu, tunda nake dake ban ta'ba ganin wannan side naki ba, kuma zan fad'a miki gaskiya a yau na sake tabbatarwa nayi sa'a da mace ta gari, ba wai fad'awa Yan uwana magana shine abinda ya dace ba a'a, amma yanda kike kauda kanki saboda ni shine abunda ya birgeni, kiyi ha'kuri bilkisu a yanzu hakan shirye shirye barin gidannan nake ko dan ki huta, saidai hankalina ya rabu zuwa haihuwarki da sama maki sabon mazauni".
Cushion na d'auko daga kujera na kwanta nace "boo-boo na na matsu na haihu wallahi, ni ko cikin kara zan iya zama indai zan haihu, Kar ka takura ma kanka wajen neman wani gida na daban nidai ayi abinnan na haihu naji me akeji da akemin gori kaima ake maka gori akai".
Mi'ka nayi domin jikina duk yayi tsami, hannu Saleh ya Sanya ya shafi inda Maimu ta mareni bud'e baki yayi zaiyi magana nace "Kar ka tunamin da wannan, a rayuwata 'karshen 'kas'kanci shine mutum ya mareni, amma babu komai ai rauwa ce, baka yi ba ma an maka balle kayi"
Dariya yayi ya fara matsamin 'kafafuwana, rufe idona nayi nace "ya akai kasan abinda zai saukarmin da 'bacin rai? Ai nayi tunanin baka iya rarrashi ba".
Pecking d'ina yayi a lips yace " 'kwarai kuwa ban iya rarrashi ba, amma nasan matata sarai itama ba kowane rarrashin take ji ba, sannan na lura a duk lokacin da kikayi full week kina zuwa makaranta kinfi zama active ban saniba ko gajiya ke 'kara maki kuzari ko kuma motsa jikin ne? So I just guess bari na baki abinda bazaki iya resisiting ba ko nima naji sau'ki a raina".
Shiru nayi ina tunanin mijin da Allah ya bani, gashi dai Babu wata doguwar magana amma har na fara cire abinda ya faru a raina, wato Saleh ya karanceni fiye da tunanina, idan naga abu kuma inason abun kuma Ina Jin nauyin na nauyin na tambaya, saidai kawai na ganshi da wannan abun idan nace ya akayi ya san inaso sai yace zuciyata ce ta sanar masa, haka nima na karanci mijina iya yanda ya kamata na san abinda yakeso da wanda bayaso, nasan yanda zan sanyashi dariya na kuma bashi haushi in a good way, Ni nasan Allah ya haliccemu dan junanmu ne domin ba mata da miji kawai ba, mu 'kawa da aboki ne, abokan shawara ne, ya zamarmin tamkar babban yaya wajen tsawatarmin ni Kuma na zamar masa tamkar 'yar uwa wajen bashi shawara, tabbas nayi Dace da miji nagari.
"tabbas nayi dace da mace ta gari, wato Bilkisu Allah kad'ai yasan 'boyayyen al'amarin dake cikin aurenmu, wallahi baby girl ni nasan halin da na shiga da kina gida ji nake tamkar an yanke 'barin jikina bana iya bacci saidai na tashi nayita sallah ina ro'kon Allah ya baki lafiya ya 'kara karemin ke daga fitintinu"
Rub da ciki nayi yaci gaba da massaging bayana, bacci naji yana neman d'aukata nace "boo-boo na mu 'kara ha'kuri, babu wanda ya ta'ba dawwama a wahala ko damuwa wataran zamuyi farin ciki mai tsawo, ai duk rayuwar da babu 'kalubale a cikinta to dama ku binciki imaninku, yanzu dai mu zuba Ido muga abinda zai biyo baya".
Shiru mukayi dukkanmu yaci gaba da massaging d'ina cikin 'kwarewa, hamma nayi nace "Allah ya maka albarka mijin 'yar aljanna"
"Ameen matar d'an aljanna", ya fad'a Yana dariya, ganin zanyi bacci yasa ya dena yace na tashi yamma tayi nayi ko adduo'i ne.
Kwana hud'u da faruwar wannan al'amari naji bugun gida, zani na d'aura akan short d'in dake jikina na fita na bud'e gida, ajiyar zuciya na ajiye ganin Hajiya, Sultana da kuma mahaifiyar sultana.
Sunkuya nayi na gaidasu Mahaifiyar Sultana tace "ba wannan ya kawomu ba, ina yarinyar take fito da ita".
Kallon Sultana nayi da idanunta sukayi ja alamun tayi kuka, tausayinta ne ya kamani duk wannan damuwar da take ciki ta sanadina ne, palour na nufa suka bini a baya sai ga Saleh ya sauko da Huda gashinta a cukurkud'e ya saka mata jeans da yellow shirt, mi'komin ita yayi a hankali yace "ba na fad'a miki zan iya shiryata ba? Gatanan kin gani ki dai gyara gashin nata na kasa gyarawa".
Gaida su Hajiya yayi amma cikinsu babu wadda ta amsa, kallon sultana mahaifiyarta tayi tace "ke Sultana, ina baki umarni ki kar'bi yarinyarnan yanzunnan".
Runtse idonta tayi tace "Mama Dan Allah Dan girman 'kur'ani, Mama dan soyayar da kikewa manzan Allah idan kina Sona da gaske ki 'kyale Huda a wajen Bilkisu, Mama bana son Huda na fad'a maki tun farko, sannan bazan iya kar'bar Huda ba idan Huda ba rabon Bilkisu bace da kanta zata dawo wajena".
"Ba shawara nake nema ba Sultana, a matsayina na uwarki na baki umarni ki kar'bi huda daga hannun Bilkisu ta dawo gareki, ko kuma wallahi tallahi a yanzunnan na miki baki".
Wata mummunar fad'uwar gaba naji na ambaci innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu akan wannan abun Mahaifiyar sultana ke ambatar wannan kalma marar dad'in ji?
Hannu Sultana ta Sanya ta rufe fuskarta, shesshe'kar kukanta kawai ke fita, a hakan tace "Bilkisu.....dan Allah kiyi ha'kuri".
Dama ko bata bani ha'kuri ba nayi niyyar bata 'yarta, bazan zama silar shiga tsakaninta da mahaifiyarta akan abu na son zuciya ba.
Tana dur'kushe a 'kasa na mi'ka mata Huda, girgiza min kai tayi ta nuna min su Hajiya, a sanyaye na mi'ka musu Huda muryata na cracking nace "bari na d'auko kayanta".
Danne zuciyata nayi na fara kwaso kayan Huda, Saleh bansan dalilin fitarsa ba amma a halin yanzu ina bu'katarsa a kusa dani, shikenan zaa rabani da farin cikina Huda.
Kayan da hannuna zai iya d'auka na fita dasu na ajiye a gabansu, dakewa nayi nace "duk abinda ya rage zan aika dashi part d'in sultana idan Saleh ya dawo".
Kuka Huda keyi tana mi'komin hannu na kauda kaina kamar bansan tana yi ba, tashi maman sultana tayi ta kai mata Huda amma ta'ki kar'barta, tsawa tayi mata ta kar'bi Huda Wanda hakan ya sake gigita Huda ta fashe da kuka, hannu sultana ta Sanya ta ri'keta amma fizgewa takeyi tana nufo wurina da hannunta.
Sakinta Huda tayi, rarrafowa tayi cikin hanzari ta nufo inda nake tsaye ta kama 'kafata ta tsaya.
"Tashi ki d'auketa" hajiya ta fad'a Tana kallon Huda, ko da sultana ta ta'ba Huda wani matsanancin kuka ta saki tana 'kan'kame 'kafata, bakinta baya ambatar komai sai maama.
A hakan babu tausayi babu imani Hajiya ta cire Huda daga 'kafata suka fita da ita, kukan Huda har cikin raina nake jinsa, Huda tayi wayon da ko makaranta zanje saidai na fita a 'boye da hijabina a jaka nake iya fita, sautinta nakeji Yana amsawa a kunnena tana ambatar maama, dafe 'kirjina nayi saboda yanda zucoyata tayi zafi, wasu hawaye ne suka zubomin nace "ya Allah idan har Huda rabona ce ka dawomin da ita, idan kuma Huda ba alkhairi bace a garenj Allah ka.za'bamin abu mafi alkhairi".
*kuyi min afuwa da abinda Zan fad'a, Ina tunanin wannan shine last post da zanyi sai kuma nan da kusan wata guda, next week insha Allah zamu fara exams, I'm gonna miss you guys😥*
24
A wurin da nake zaune na zuba tagumi, Ina jin kiran sallah amma na kasa motsawa tunanin Huda kawai nakeyi, ki wajen mahaifiyarta taje kwana da sassafe ake dawomin da ita ta ishesu balle kuma wurin bare, tunda na dawo daga gida wata sabuwar sha'kuwa ta shiga tsakaninmu, ya zanyi babu Huda? Ya Huda zatayi idan babu ni?.
Tashi nayi jikina babu 'kwari nayi sallah na had'a kaina da gwiwa kukan Huda kawai nakeji a cikin raina, har lokacin bacci na kasa aikata komai.
Batun girki kuwa babu, Saleh tun yana rarrashina har ya dena domin da zarar yace nayi ha'kuri tamkar ya sake tunamin abinda ya faru ne, wace irin masifa ce wannan ta dangin miji da zasu raba uwa da 'yarta? A jikina ina ji cewa Huda na cikin damuwa.
8:30 Sultana ta shigo da food flask ta ajiye gabana, bata ce komai ba ta d'auko plate ta zuba abincin ta saka spoon ta mi'komin, kallon macaronin nayi irin dogayennan ce mai kama da taliya saidai gajeru, tayi mata jollof mai cike da kayan had'i gata ruwa-ruwa gwanin sha'awa saidai sam banida appetite da zanci abincin.
Girgiza Kai nayi nace "Sultana bazan iya ci ba". A tunanina zata tursasani kawai naga taja plate d'in ta fara ci, tana ci Saleh ya shigo ta 'kara musu suka cigaba da ci ina zaune a gefensu.
Saida suka cinye tukun ta sake zubawa tace "Bilkisu idan zaki kwantar da hankalinki kici abinci kici, wani irin azabtar da kai ne haka? Akan Huda zaki hana cikinki abinci tun safe? Ki dubi fuskata Mama ta har mari na tayi akan Huda, babu irin abinda basu ce ba to amma ya zanyi? Idan akwai abinda Huda zata so shine ki zauna da kuzarinki domin 'kwato mata 'yancinta, inada tabbacin Huda bazata jima ba zata dawo gareki, wallahi na dad'e ina mafarkin wata mata mai yalwataccen haske tana ri'ke da yarinya suna zagaya wani lambu mai matu'kar kyau, ina zaune daga gefe ina kallonsu dukkanmu fuskarmu cike da annuri, Bilkisu tun kafin na haifi Huda nake wannan tunanin kuma a hankali Allah ya nunamin kece uwar da ta dace da Huda, tunda Huda ta'ki zama