Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
ta farfad'o, da wani 'karajin ta farka tana zabura da 'kyar Hajiya ta ri'keta tana tofa mata addu'a har ta samu ta lafa.
A haka suka kwana Hajiya na tofawa Maimuna addu'a Maimuna na tashi tana 'kara, kafin safiya ta zama tamkar mahaukaciya duk inda ta kalla ta saki ihu tana fizge fizge, sai rufeta a d'aki Hajiya tayi ta kira taimako.
Ki da Hadiyya tazo bada hakuri komawa tayi babu shiri domin samun Maimuna tayi ana Mata ru'kiyya, ihun da takeyi ya samu sau'ki saidai kuma bakinta ya'ki bud'ewa, kallon mutane takeyi kamar wasu halittu daban cikin kwana d'aya ta zama abin tausayi.
A wannan hali Saleh ya tafi ya barsu wanda hakan ya 'karawa Hajiya nauyi, sauran 'ya'yanta dama basu damu da su dubata yanda Saleh keyi ba, saidai su bata kud'i suyi tafiyarsu suyi watanni.
Daga Hajiya har Maimuna sun koma abin tausayi kowa tsoron Maimuna yakeyi banda Hajiya, Jumana ma tsabar tsoro mijinta tabi sukayi tafiyarsu can wajen aikinsa, Sultana ma le'kowa takeyi tana musu sannu har 'kannenta basa iya shiga d'akin Hajiya.
Tuni Hajiya ma ta manta da batun Hadiyya, saidai Hadiyya bata yi 'kasa a gwiwa ba takan je ta d'ebewa Hajiya kewa har suka sha'ku sosai, Hajiya batada zance sai na Maimuna ita kuma Hadiyya tana zama ta saurareta ta kuma bata baki.
Ana yiwa Maimuna magani kuma cikin ikon Allah ta fara samun lafiya, yanzu ciwon lomaci lokaci yake tashi saidai ta canza sosai.
Hajiya da kanta taje ta d'auko Hadiyua ta dawo da ita domin ta dinga d'ebe mata kewa.
A wannan hali Bilki tazo ganin gida, waya tayi da Sultana ta sanar mata tazo ganin gida.
"Dan Allah Bilki kizo na ganki ke da yaranki Saleh baya nan sai Hajiya, ki yiwa Allah kizo ki nuna mata yaranki".
Amincewa Bilkisu tayi ta d'auki yaranta ta nufi gidansu Saleh, mamaki tayi ganin gidan a rufe tayi knocking.
"Waye?" Taji muryar Hajiya, saida taja numfashi sannan tace "nice, ba'kuwa ce".
Binta Hajiya tayi da kallo daga sama zuwa 'kasa, ta kasa amincewa Bilkisu take gani a gabanta
"Bilkisu?"
"Na'am Hajiya ina wuni, sultana tana nan ko?"
Kasa amsa mata Hajiya tayi tana bin yaron hannu ta kallo ga d'aya a goye a bayanta, kaucewa tayi Bill ta shige har yanzu Hajiya ta kasa furta koda kalma d'aya, tabbas ta cuci kanta da yanzu yarannan a gidannan za'a haifesu, gaba d'aya Bilkisu ta canza jin dad'i ya bayyana a tattare da ita, taso ganin Bilkisu cikin mawuyacin hali bayan aurensu amma saidai Allah ba azzalumin bawansa bane, ga Bilkisu tayi aure ta sake kyau kwanciyar hankali ta bayyana a gareta ga kuma 'ya'yanta har biyu, yayin da ita tata 'yar take kwance bata cikin hayyacinta.
Tsabar murna Sultana harda 'kwalla tana kallon twins, godiya take ga Allah da ya musanyawa Bilkisu da miji wanda yafi Saleh ya Kuma azurtata da haihuwa.
Fitowarta daga gidan sultana tayi arba da Hajiya, murya na rawa Hajiya tace "Bilkisu dan Allah ki yafemin duk abubuwan da nayi miki".
"Na yafe muku gaba d'aya Hajiya, Allah ya yafe mana".
Tana hanyar fita taga Maimuna a 'kofar d'akin Hajiya, riguna biyu ne a jikinta da zani sannan ga wando dogo ga dankwalinta a du'kun'kune, 'kuda ke binta amma ta kifawa waje d'aya ido tana kallo bata damu da 'kudan dake binta ba, addu'a Bilkisu tayi mata a zuciyarta tana neman mata waraka daga Allah.
Watanni kad'an bayan dawowar saleht Hajiya ta tafi d Maimuna 'kauyensu nema mata magani, gida ya kasance babu Hajiya suna rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, saida sukayi wata shida sannan suka dawo a wannan lokaci Maimuna ta samu waraka sosai.
Dukkansu sun hankalta akan ajiga sabgogin surukansu, Hajiya taso su barta ta koma wani gidan suka 'ki amincewa domin zamanta tare dasu ya fiye musu, a haka ta zauna ita da Maimuna da har wannan lokaci babu aure babu maganar aure a kanta.......
*END*
*ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO 'KARSHE WANNAN BOOK NAWA ME DOOOOGON ZANGO😅😅😅INA SAKE BAKU HA'KURI GAME DA JA MUKU LOKACI SA NAYI AMMA ALHAMDULILLAH ITS FINALLY THE END*
*DAMA NA SANAR MUKU I SUCKS AT ENDINGS😂😂😂KAWAI KU RUFE IDO KU KARANTA DUK ABINDA KUKA GANI, INA GODIYA GA MASOYANA A DUK INDA KUKE ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI*
*MY WATTPAD READERS BANI DA KAMARKU, SOYAYYARKU TA DABAN CE*
*SPARKLING SONSORIANS*
*NAYI DACE FANS*
*MARYAM NOVELS*
*MUSHA KARATU 2*
*FEENAT JAAFAR NOVELS*
*DA MA DUK INDA BOOK D'INA YAKAI INA MUKU GODIYA FOR BEARING WITH ME, SAI WATARANA KUMA LOVE YOU ALL*
    Â