NAYI DACE HAUSA NOVELS COMPLETE BY KITTY.txt

Author :  kitty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 41

24K to 27K   out of 120.7K words

ta sake magana har ina Shirin fita sai ga saleh,nuna masa wuri akayi ya zauna , cikin gadara hajiya tace

"Ke bilki, d'ayan biyu ko bakyason d'ana ko kuma ke juya ce, ki fad'amin wanne ne a ciki? Haihuwa ce bakyaso kiyi da d'ana ko kuwa haihuwar ce bakyayi "

Na d'au mintina kafin na amsa saida ta sake maimaitawa nace

"Hajiya soyayya ce ta Sanya na auri d'anki, kuma inaso na haihu Allah ne bai kawo ba "

" Ki dena saka Allah a abinda kika tsarawa kanki, su ba gashi duk sun haihu ba? Sultana haihuwarta biyu, jumana cikinta nawa kafin ta haihu? Amma ke kina zaune saidai kici ki yiwa mutane kashi aure kusan shekara biyu" maman sultana ta karashe maganar tana jan tsaki

Kallon saleh hajiya tayi tace

"Kai Saleh, d'auki matarka yanzunnan kuje asbiti ayi mata gwajin haihuwa, ba Kuma Kai kad'ai zaka tafi ba, ka d'auki d'aya cikin 'kannenka ku tafi, idan har aka gano tanada wata matsala a yau zamu fitar maka da wata matar ka aura "

" Cikina naji ya juya, ri'ke hannuna yayi yace "

" Idan kuma batada matsala zaku kyaleta da fitintinu muci gaba da zamanmu lafiya?"

" Mu muke fitintinu sale? Ni uwarka zaka kalla kace muna kawowa matarka fitina? "

Shiru yayi sannan yace

" Naji hajiya na amince, idan har an sameta da matsala zan amince da za'binku, idan ba'a sameta da komi ba dan Allah ku barta ta huta tunda ta shigo gidannan batada kwanciyar hankali saboda ku, sannan ni bazan d'auki kowa ba, ai wannan abin daga mata sai mijinta ake zuwa "

Tasowa maman sultana tayi tayo kanmu a fusace, tsayawa tayi tana nunashi tace

" Akan wannan kake kallan mahaifiyarka kana fad'a mata magana? Saboda Kai baka da kunya baka da mutunci? Akan mace? Macen banza macen wofi da ta sameka da girmanka? "

Shiru yayi taci gaba da surfa masifa, dawowa kaina tayi tace

" Dole yayi haka mana, ya d'auko matar da ta shanyeshi, ke wai yar boko ko? To wallahi daidai muke dake, Zaki san kin shigo cikinmu wallahi sai mun......"

" Wayyo mama marata!!" Sultana ta fad'a da karfi, kallonta nayi ta kashemin ido d'aya na mata godiya a zuciyata,

"Ku tashi kuje kuma ku kawo Mana sakamakon nan mu gani"

  tashi mukayi muka fita kursum na binmu kaman jela

Mota muka shiga ta shiga itama muka nufi asbitin da nake internship, bayani na musu zanyi fertility test ne likitan ya rubutamin muka je muka fara da blood test

Wuni mukayi a asbitin a jagwalgwalani nan a jagwalgwalani can, daga 'karshe akace sai bayan sati d'aya naje na kar'ba

Ko da na koma surutu suka dingayi Akan ina sane na'ki kawo result d'in, dole dai suka ha'kura suka barni.

Satinnan gaba d'aya banida sukuni, mafarke mafarke nake marasa dad'i akan haihuwa abin har ya fara sani rama.

Ranar da sati ya cika hajiya da kanta tazo gidana akan yau ne fa zan kar'bo result d'ina,ji nayi banason kar'bowa haka kawai.

Tunda muka d'auki hanya gabana ke fad'uwa, kafin muje 'kwalla ta cika idona, rarrashina saleh yake amma kwata kwallta bana ji.

Muna isa likitan yacemin

"Bilkisu saki jikinki mana, ko bakyajin dad'i ne?"

" Doctor menene result d'ina ya nuna " na tambaya muryata na rawa

Zama doctor d'in yayi ya mi'komin takarda yace

" I am sorry to say this, but bilkisu you have cervical factor of infertility "
*dedicated to all infertile women on Earth, Allah kad'ai yasan yanda kukeji a zu'katanku saidai komai ya faru ga bawa alkhairi ne, fatanmu Allah ya baku ikon cin wannan jarrabawa ta rayuwa😭😭😭😭😭😭😭😭 heart you all*

15

"doctor to me hakan yake nufi?"

" Yana nufin cervix d'inta yana da matsala, mucus d'in da cervix d'in ke producing yana kashe sperm ne kafin ya kai cikin mahaifarta "

Kaina juyawa yakeyi ina zaune, 'kafafuna gaba d'aya sun d'auki rawa, wasu zafafan hawaye ke zuba daga idona, dafe 'kirjina nayi jin tamkar zuciyata na barazanar fita.

'ko'karin fad'uwa daga kujerar da nake zaune nayi Saleh ya ri'koni cikin sauri tareda kujerar, cikin tausayawa likitan yace

"Kaita waccan kujerar ta zauna" cushion chair ce nara tsayi, zama nayi ina maida numfashi tareda zubda hawayen da bana tunanin zai tsaya nan kusa.

"To doctor yanzu magani za'a bata kenan ko me?"

" Eh to gaskiya matsalarta bata da magani, domin da dama daga mata masu matsalar haihuwa suna fama ne da wannan matsalar, saidai ayi mata dashe na IVF amma bazata iya d'aukan ciki da kanta ba "

Cikin sauri saleh yace

" To yanzu a ina ake IVF d'in muje? Nawa akeyi "

" Ana IVF anan kano amma gaskiya cikin 80% ko 20 ba'a samu an dace ba, saidai kuje Dubai wanda sunfi suna a harkar IVF d'in "

" Nawa akeyi a Dubai d'in? "

Wata takarda ya zaro ya mi'kawa Saleh yace

"Wannan asbitin da suka fi suna a Dubai d'inne wajen dashen, akwai website d'insu da zarar ka shiga zaka samu duk bayananan da kakeso sannan akwai wani abu d'aya, still dai ko da cikin bazata iya haihuwa da kanta ba saidai a Mata CS a curo abinda ke cikinta"

Godiya saleh ya masa bai tambayesa dalilin da bazan iya haihuwa ba, ni kaina bazan iya sake d'aukan wani information ba bayan wannan ba'kin labari.

Kwata kwata bana ganin abinda ke gabana domin hawaye ke wankemin fuskata, Allah kad'ai yasan abinda nakeji a zuciyata, babu abinda nake hange sai Huda,

Yana ri'ke dani muka isa mota, bud'ewa yayi ya sanyani shima ya shiga ya zauna, a wurin ya fara browsing asbitin da aka bamu

" Kai 40,000 dirham? Bari muga nawa ne"

Converting yayi naji yaja wani numfashi tareda salati, can 'kasan ma'koshinsa yace

" Miliyan 4?"

A take anan na sake cire rai da samun haihuwa, nasan a miliyan hud'unnan babu kud'in mazauni da transport da sauransu, a 'kalla sai an samu miliyan 5 zuwa shida zamu samu haihuwa wanda nasan mijina bashida su bashida dalilinsu

Tunanin abinda zan tarar a gida nakeyi, idona a rufe Ina zubda hawaye naji yayi parking ya bud'e min 'kofa tare da kamo hannuna, fito dani yayi naganni a gida.

Tamkar wadda tasha ta bugu haka nake tafiya, sallama yayi ya tsaya daga waje na fad'a palo, a kujera na samu mama babu shiri na zube a cinyarta ina tsananta kukana, cike da damuwa tace

" Bilkisu menene? Lafiya? Me ya faru "

Sallama saleh ya sake dokawa mama ta yafa mayafinta ta masa iso, bayan sun gaisa yace mata

"Mama asbiti muka je ne akai mana gwajin haihuwa, to Allah ya 'kaddara bilkisu tana da wata 'karamar matsala, na rasa ta yanda Zan rarrasheta shine na kawo miki ita "

" Allah sarki babu komai, karka damu zamuyi magana da ita "

Tashi yayi ya fita naci gaba da tsananta kukana, kukan da nake tamkar ma 'kara hurawa zuciyata ruwa akeyi, a ta'kaice gaskiya 'yan uwan Saleh ke fad'a ni juya ce, ko yaya rayuwata zata kasance ba tare da haihuwa ba?

Gyaran murya mama tayi ta fara min nasiha:

" Haba bilkisu ki kasance mai tawakkali mana, Allah ba wai baya sonki bane ya jarabceki ta wannan hanyar, Allah yana sonki ne kuma yasan a cikin dubban bayi ke kad'ai zaki iya jure wannan jarabawar shiyasa ya baki ita"

" Bilki na sani rashin haihuwa bashida dad'i, domin ni kaina victim ce, shekarata 13 a gidannan kafin Allah ya bani haihuwar jabir, babu irin maganar da banji ba, duk zaman lafiyar da nake da kishiyoyina saida suka gorantamin, 'yan uwan mijina sunyimin ki godewa Allah da bakida matsala da dangin miji"

Tashi nayi na zauna nace

" Wallahi hajiya tamkar shed'an haka yan uwan mijina suka tsaneni, fad'a miki ne kawai banayi domin karki damu, tsangwama Babu wadda ban gani ba, tun ranar da aka kaini suka fara sanyani zubda hawaye, tunda kuwa wadda akai aurenmu tare ta samu ciki na fara fuskantar matsala akan haihuwa, sukace ina sane na dakatar wannan ya wuce, yanzu ita sultana tayi haihuwa ta biyu shine suka sakani gaba dole nayi gwajin haihuwa, mama labarin da nake d'auke dashi shine labarin da suke so, yanzu haka jirana sukeyi na koma suga sakamakona shine dalilin da ya sanya Saleh ya kawoni nan, mama shikenan bazan ga jinina ba har na mutu ko? "

" A'a bilki kad'an da ikon Allah kiga kin haihu kema kamar kowa saidai idan mahaifarki ce ta lalace duka shine zaki cire rai"

Bayanin matsalata nayi ma mama tayi shiru sannan tace

" To shi nawane IVF d'in? Idan bai gagaremu ba ba sai mu biya maki ayi ba?"

" Mama miliyan hud'u ne, banda kud'in jirgi da na abinci da mazauni da sauran kayan bu'katu "

" Bazata gagara ba bilki, kinada kud'in gado da yawa sannan kinada dangi masu hali, yanzu ana fad'a cikin ikon Allah zakiga an harhad'a miki ki cire damuwa, idan zaku bi shawarata ku nunawa dangin mijinki bakida wata matsala, da zarar kud'in ya had'u sai ku 'kir'kiri tafiyar aiki daga nan ayi abunda za'a yi ki dawo da cikinki ba shikenan ba? "

Nasan mama ta fad'i haka ne kawai domin ta kwantarmin da hankali, cigaba tayi da rarrashina tace

" Duk lokacin da damuwa tayi miki yawa ki dinga tuna ayar 'kur'ani da Allah yace. " _waman yattaqillah yaj'al lahu makhraja, wa yarzukhu min haithu la yahtasib, waman yarawakkal alallahi fahuwa hasbuh,innallaha baligu amrih, Qad ja'alallahu likulli shai'in 'kadra_ "

Tabbas wannan ayoyi waraka ne, a take naji zuciyata ta fara sararawa da mama ta tunamin da wad'annan ayoyi, Allah zai kawomin mafita ya kuma azurtani ta inda banyi zato ba, dukda haka dai wannan rad'ad'in na rashin haihuwa yana cikin raina.

Bawa mama labarin irin rayuwar da nake ciki nayi, fuskarta 'karara ta nuna tausayawa gareni saidai bata furta hakan ba, tacemin

" Ai kad'an kenan daga jarrabawar gidan aure, kowa da kalar tasa, wata zakiga mijin ne baya sonta amma danginsa kamar su cinyeta, wata kuma gaba d'aya da mijin da dangin basa yinta, wata Allah ya jarrabeta da haihuwa amma babu wadatar da za'a ciyar da 'ya'yan, kowa da tata jarrabawar kiyita addu'a Allah yana sane dake da matsalarki, komai watarana zai sama labari kina murmushi Zaki dinga bada labarin abunda ya faru dake a baya"

Na jima a gidan mama tana bani shawarwari da adduo'in da zan lazimta, sai yamma lilis Saleh ya zo ya d'aukeni, muna shiga mota yacemin.

" Banaso mu nunawa 'yan uwana kinada wata matsala, da ace inada hali da babu mai jin matsalarki, bayan wani lokaci muje ayi miki wannan dashen mu dawo, amma my boo banida halin fitar da miliyan biyar zuwa shida, da ace d'aya zuwa biyu ce zan iya tattarowa cikin watanni amma......"

" Karka d'aurawa kanka my boo-boo, munyi magana da mama tace nayi maka magana, nasan 'yan uwana da zarar na sanar musu cikin 'kan'kanin lokaci zasu had'amin "

" A'a bilkisu, bazan kar'bi komai daga hannun 'yan uwanki ba "

Abun ya dameni nace

" Meyasa bazaka kar'bi kud'i daga 'yan uwana ba? Boo-boo idan muka zauna haka kowa sai yaji kuma 'yan uwanka bazasu barni da rai ba suka san inada matsala, ka sani bazasu taimakamin da kud'insu ba ko da kuwa ace mutuwa zamuyi daga ni har kai "

" Boo abinda nake nufi shine, abinda mukeso mu haifa dani dake munaso mu kirashi d'anmu ne, inaso na kasance uba ga duk abinda zamu haifa, idan har na nad'e hannuna aka taimaka miki daga danginki sun fini iko da abinda zaki haifa, kuma banida zuciyar kallon wannan abun na kirashi da d'ana, inaso nasha wahala yanda kowanne uba zaisha akan d'ansa, muyi ha'kuri bilki har na samu arzi'ki na kaina mu haifi abinda zamuyi alfahari dashi muyi tin'kaho da cewar mune iyayensa "

Shiru nayi domin gaskiya ne zancensa, duk son dangina dani idan har Saleh ya nuna ya fisu iko da abinda na haifa to tabbas anan za'a fara samun matsala

Yana driving gabana na fad'uwa, hasbunallahu nake maimaitawa har muka isa gidan.

Ai kamar jiranmu sukeyi duk sunyi cirko cirko a 'kofar gidana, na rasa wasu irin mutane ne wad'annan, magrib na gabatowa su nufi gidan aurensu sun tsaya lalata auren wasu.

Ina fita daga motar Usman ya nufoni da hudaba hannunsa, cikin kuka ta mi'komin hannu tace

*"MAAMA"*

Wani abu naji ya sokeni a cikin zuciyata, before na gama recovering ta sake ambatar "maama", Kar'barta nayi na sanyata a kafad'ata, d'ago kanta tayi ta kalli fuskata ta sake cewa

" MAAMA" sannan ta hau gwarancinta, tana gamawa tayi luff a jikina,

Bansan lokacin da Hawaye ya zubomin ba, banda huda yarinya ce zan iya cewa da gayya tayimin haka, huda bata ta'ba ambatona da wani suna ba sai yau, ban kuma ta'ba lura da cewar huda kallan uwa take min ba sai yau, ban ta'ba fahimtar cewa sha'kuwarmu da huda tayi nisa har ta wuce 'ka'ida ba sai yau, ji nake tamkar ana tsaga 'kirjina ana sake cusamin soyayyar huda bayan ta ambaceni da maama, tsananin tsoro ne ya kamani na 'kan'kameta a jikina ina hawaye.

" Munafuka, sai ku fito kuyima mutane bayani, tunda kike zubar da Hawaye Allah ya toni asirinki sai ku fad'a muji, tasha 'kwayoyi sun lalata mahaifarta ko?" Kursum ta fad'a Tana bubbuga 'kafa

Godiya nayi ga Allah da hankalinsu baya Kan huda da ta kirani da maama, shafa Kai saleh keyi cikin takaici da ba'kin ciki, wani irin kallo ya jefomin na kin 'bata mana aiki

Kwata kwata bansan na fito da result d'ina ba saida naji an fizgeshi, gabana ne ya fara fad'uwa ganin yaya maimu ce ta kwace takardar, karantawa tayi ta bud'e wayarta alamun browsing abunda ta gani, tamkar wadda taga alkhairi ta rangad'a bud'a tareda tafa hannu ta nuna ni tace

" Dama ance rana dubu ta 'barawo Rana d'aya tak ta Mai Kaya, Ramin 'karya dama asalinsa 'kurarrene, gashi dai result baya 'karya ya kuma nuna ke juya ce ba macen da zamu mora bace, dan haka kai saleh sai ka 'kara aure "

Dawowa gefena saleh yayi ya ri'koni yace

" Ni bazan iya zama da mata biyu ba, bilkisu ita kad'ai ce matar da Zan zauna da ita a rayuwata"

" To kuwa saidai ka saketa ka auro wata, Dan bazaka ta'ba zama da macen da bata haihuwa ba, ni bana haihuwar fanko Kuma Babu d'ana da zai zauna da mace fanko, ka saketa ko ka 'kara aure "
Hajiya ta fad'a tareda matsowa dab damu, turani bayansa yayi yace

" Hajiya kiyi ha'kuri, da ace umarninki domin Allah ne Zan miki biyayya, amma kina tilastamin nayi aurene saboda bilkisu ta tozarta kuma iya ganina bilkisu bata miki komai bayan biyayya, hajiya kece babba ke ya kamata ki dinga tsawatarwa su maimuna idan suna muzgunawa bilkisu amma bakya yi, munyi magana da likita matata zata iya samun ciki ta haihu kamar sauran mata, saboda haka zanci gaba da zama da ita kad'ai bazan iya bin umarninki na 'kara aure ba, kuyi ha'kuri"

Tafa hannu maimu keyi tana ri'ke baki, nunani tayi da yatsa tace

" Babu mamaki, an maka barbad'e an shanyeka, har zaka kalli mahaifiyarka ka fad'a mata magana, saboda mace ta shanye tunaninka da hankalinka an kaika wajen boka saboda baka san ciwon kanka ba, to ka sani mune Daidai da ita kuma wallahi zaka zo ka samemu, ke kuma ko kinso ko kin'ki sai kinbar gidannan tunda ba gidan ubanki bane"..
16

Reult d'in tayi tareda tsaki ta bar wurin, saleh kusa yake a jikinsa kamar zasu cinyeni, d'aya bayan d'aya suka bar wurin.

Kasa d'aga ido na kalleshi nayi cikin Kuka nace

" Kayi ha'kuri "

Shafa bayana yake cikin rarrashi yace

" Haba kukan kuma na mene? Please banason ganin hawayenki my boo, zan iya handling 'yan uwana ki kwantar da hankalinki bazan ta'ba bari su cutar dake ba ko yaya "

Kar'bar Huda yayi muka shiga cikin gida, zanina da mayafi na cire zan fad'a kitchen yace

" Karki d'aura komai a 'koshe nake, nasan kema bakyajin yunwa, saidai ko Huda ".

Jiki babu 'kwari nace

" To bari na saka mata noodles"

" A'a zauna na saka mata "

Kallonshi nayi na turo baki nace

" Da can kai kake dafa mata? Banason wani extra attention saboda wannan abun da ya faru, muci gaba da zama normal karka fara abinda kasan bazaka d'ore ba, ko kuwa ka ta'ba tayani girki "

" Na ta'ba tayaki mana "

" A'a kana dai sakani 'kona abinci "

Dariya yayi yace

" To naji jeki d'aura mata abincin ki dawo "

Juyawa nayi na nufi kitchen, ina shiga ta 'kwala min Kira, ko sau nawa Huda zata kirani da maama bana tunanin zan saba, indai ta fad'a sai naji wani iri a raina.

Shigowa sukayi kitchen d'in na korasu dan nasan hali, ban fita ba saida na gama noodles d'in na zuba mata na fita da ita

Bata bari na bata ba ta saka hannunta ciki duk ta 'bata jikinta, wanka nayi mata nima nayi na shirya cikin riga da skirt.

Rigima huda ta fara na goyata ganin magrib ta gabato na zauna na zuba tagumi, wani kad'aici naji ya fara shigata tunanin abinda ya faru ya dawo sabo.

Anya ba mistake akayi wajen bani result d'in ba? Anya ba irin abubuwan da nake gani a film bane daga baya kuma Allah yayi ikonsa?

Maganar yaya maimu ce ta fad'omin, to idan har auren zai haifamin kwanciyar hankali me zai hana yayi? Matu'kar zasu bar rayuwata ta sarara ni zan iya amincewa da auren nasa domin na gaji, furucinta ya tsorata ni da tace zan ga abinda zasu iya.

Tashi nayi na d'auko result d'in na sake dubawa, sunana ne da komai nawa, ga test d'in da akamin nan a jere kowanne da abinda aka samu.

Hawaye naji yana neman zubomin, dama haka mata marasa haihuwa suke ji? Duk yanda zan misalta yanda nakeji a raina bazai misaltu ba, ta'kamar mace a rayuwarta itace zuri'arta, na dad'e ina ma rayuwata plan da 'ya'ya masu yawa, na dad'e ina mafarkin ganinan cikin 'ya'yana 7-8 muna hira, na dad'e ina hasashen gani nan na fita da 'ya'yana muna tafiya, na shiryasu cikin kaya iri d'aya, ashe kana naka ne Allah na nashi.

Hannu naji an sanya ana gogemin hawayen da ya zubo, d'aga kaina nayi naga sultana, cikin sauri na goge hawayen tareda ajiye takardar gefe.

D'aukan takardar tayi tace

" Bilkisu me arahar hawaye, kedai ki sanyawa ranki damuwa ba komai bane, yanzu shima awon cikin kuka yake sanyaki ne ko me? Ko kuma......."

Dakatawa tayi ta d'ago ta kalleni ta sake kallon takardar, mi'komin tayi tace

" Me takardarnan take nufi "

Goge fuskata nayi nace

" Su yaya

9 / 41