Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
Yaya Bilkisu zatayi responding? Idan Kece Bilkisu ta Yaya Zaki fuskanci Saleh?.....sai naji daga gareku?😉😉😉😉
39
Matsowa ya fara yi dai-dai lokacin da Aalee ya fito, dafa kafad'ata Aalee yayi yace "haba sweet B yanzu fushi kikayi sosai? Am sorry kema kinsan da wasa nakeyi bansan cewa har yanzu wannan is a sensitive topic to you ba".
Gaba d'aya hankalina na kan Saleh, Aalee ganin ban kalleshi ya sanya ya saka hannunsa biyu ya tallafo fuskata tareda juyota gareshi, murmushi yayimin wanda ya bayyanar da kyawawan dimples d'insa yace "look into my eyes and say you forgive me baby, bazan kuma ba kinji?" Ya Kare maganar yana turo baki, kallon Saleh na sakeyi da idanunsa a take suka sauya da alamin kishi, wani irin kallo yake ma Aalee wanda baisan ma yanayi ba hakanan naji wannan lokaci yayimin dai-dai.
Cire hannun Aalee nayi daga fuskata nace "na yafe maka, idan kuma ka kuma...." Jan kunnensa nayi ya saki wani 'kara had'e da murmushi, kama hannunsa nayi na nufi 'kofa cikin sauri Saleh ya matso tareda kama 'kofar, a fusace ya kalli hannuna dake ri'ke da na Aalee sannan yace "me kikeyi haka Bilkisu?"
Shigewa gabana Aalee yayi yace "easy man, no one talks to my girl without my permission".
Tamkar Saleh zai daki Aalee yace "malam matsa da matata nake magana".
Bansan lokacin da dariya ta 'kwacemin ba na girgiza kai tareda jan Aalee nace "mu tafi kar mu makara". Shigewa gida nayi na doka 'kofar saida Aliyu ha d'an tsorata, knocking Saleh keyi yayin da nake jingine jikin 'kofar yanda zuciyata ke bugawa abun har tsoro ya bani, ban ta'ba tunanin ganin Saleh a wannan lokacin ba kuma banda Allah ya kawo Aalee bansan ta yaya zan fuskanci sale ba, hannuna na Sanya a 'kirjina tareda sauke numfashi ina jin bugun Saleh har cikin kaina.
Fitowa su Raudah sukayi tareda Aunty tace "waye yake mana bugu a gida?"
"Ba kowa"
"Tsohon mijin Aunty B ne" mukayi maganar a lokaci d'aya, cikin sauri aunty ta nufo 'kofar take yanayinta ya canza, bansan lokacin da na ri'ke hannunta ba.
Girgiza mata kai nayi a hankali nace "dan Allah Aunty a'a". Hard'e hannunta tayi a 'kirji tace "a yanzun ma kareshi kikeyi?"
Muryata tana rawa amma a haka na dake nace "a'a Aunty ba kareshi nake ba, amma bashida matsayin da zaki saurareshi a wurinnan jannat ce kawai dai-dai dashi, ki kyaleshi dan Allah bansan ma da rayuwarsa a wurin ba".
Dafa kafad'ata tayi tareda murmushi sannan ta juya ta koma gida, runtse ido nayi tareda maida numfashina na bar 'kofar gate d'in da murmushi a fuskata, bud'e gate d'in mai gadi yayi duk muka shiga mota bansan yanda na 'kare a passenger seat ba au Raudah kuma suna baya dukkansu, a tsaye naga Saleh ko kallo bai isheni ba muka wuce.
Mun kusa 10mins babu wanda yayi magana, jannat ce tayi breaking silence d'in tace "ya Aalee Ina zamuje wai".
Kallona yayi yace "Aunty B zaki tambaya".
Kaina na window nace "inaso na sayi kayan makeup, takalma da jakunkuna". Bansan inda zan samu abubuwan da nake bu'kata ba saboda haka muka yita yawo a gari har na samu wurin jakunkuna masu matu'kar kyau, guda biyar na siya su Raudah suka sayi d'ai-d'ai, muna zuwa wajen biya Aalee ya mi'ka katinsa, wurga masa harara nayi na kar'bi katin na mi'ka nawa.
Raudah dake bayana ce ta kar'bi katin ta mi'ka tace "kin ta'ba ganin inda aka fita da namiji mace tayi siyayya?"
Cashier d'in har mun fara b'ata rai, kallon Raudah nayi nace "tunda nace zan biya ki barni kawai dan Allah, na dad'e da kud'innan bansan me zanyi dasu ba kuma abin kashewa yazo sai ace bazan kashe ba?"
Ja tayi da baya ta barni na biya, a kusa da shagon na sayi takalma su Raudah suka 'ki saya saboda basaso na biya, da kyar suka amince suka d'auki d'ai-d'ai shima saida nace zamuyi splitting kud'in da Aalee.
Wasu dogayen riguna na hango a shop d'in kusa da su again nan ma muka shiga, kallon kayan muke munata yabawa naji Aalee yace "wannan kuma a 'kafa ake rufawa ko shima belt ne na ciki?"
Juyowa mukayi dukkanmu kawai muka ganshi ri'ke da bra yana jujjuyawa, a tare muka ja tsaki wanda dukkanmu ya bamu dariya babu wanda ya kula shi nan ma dai bamu fita ba saida muka sayi riguna 2pcs kowa jannat kuma 4, wannan karon Aalee ne ya biya, inaso na sayi panties amma idon Aalee ya hanani.
Saida muka gama siyayyarmu sannan nace da Raudah "inaso na sai undie amma wannan yayan naku sai ya kwana Yana min tsiya idan ya gani".
Dariya tayi sannan tace "ba dai tun na lefe baki canza ba". Harararta nayi nace "haba dai, ai an samu matsala kenan".
"Ah to nasani? Dan wannan matsolon mijin naki da na gani a waje ba alamun zai iya siyan panties".
Bata jira na bata amsa ba ta nufi Aalee tareda bashi kayanmu tace gamunan zuwa ya jiramu, kusan gaskiya ta fad'a tunda mukayi aure Saleh bai ta'ba siyamin panties ba ko ya bani kud'in siya wannan aikina ne kuma Banga hakan a laifi ba ko kuwa laifi ne? Indai zai gani a jikina ya yaba ni yafimin komai, too bad ba sake gani zaiyi ba.
Aalee na fita na d'auko wanda suka min kyau, twins na gani suma suka ce sai an siya musu siyayyar lingerie dai harda su jannat, mun sake sosai kasancewar shagon Mata ne a cikinsa, maimakon muna gamawa mu fita sai ga amal ta hango wata bra a lallai tana so, peach colour ce itama nawal tace tanaso Kuma sai peach, haka aka dinga neman peach d'in babu kuma suka 'ki ha'kura.
Dawowa Aalee yayi alamun ya gaji da jira ya samesu suna musu da Raudah, tace ko dai su canza color d'in ko kowacce ta d'auki different colour, na rasa wannan iyayin na twins har undies ma sai kala d'aya?.
Ina zaune a gefe Aalee ya zauna a kusa dani, an samu sun ha'kura sun d'auki light purple, ta'boni Aalee yayi tareda mi'komin bra yace "wannan zata miki kyau fa".
Kallonsa nayi na rasa daga wani baki wannan maganar ta fito? Tashi yayi ya fice ya barni baki a sake na dubata kuwa naga tayimin na siya.
Mun gama kashe kud'i sannan muka nufi inda zamu sayi abinci, Aunty tace bazata mana girki ba gashi mun gaji balle muyi tunanin yin girki, takeaway mukayi muka nufi gida.
Kallon 'kofar gidan nakeyi wani bangare na zuciyata na son ganin Saleh, wani iri naji a raina da ban sameshi ba, "karki damu gobe ma zai dawo" Aalee ya fad'a tareda fita daga motar, wannan yaron da alamu duka yakeso ya fiye shiya rayuwata.
Waya mukayi da Mama ta sanar dani sai bayan 2 days zata dawo, naji dad'in 'karin kwanakin nasu domin zaman gidan aunty Yana min dad'i, sannan kuma 2weeks su Raudah zasuyi kafin su koma.
Bayan mun huta suka ciro kayansu da suka zo dasu zasu kai d'inki, tagumi nayi nace "nima da ace zan iya debo kayana ai da na kaisu d'inki tareda naku".
Tunani ne ya fad'omin na kira Sultana "sai yau kika tuna damu ko Bilki? Wallahi baki ri'ke amana ba Bilkisu ai ko lafiyar yarinyarki kya kira kiji".
Shiru nayi na d'an lokaci tareda Jin rashin dad'i na kiran sultana da banyi ba, tun ranar da na maida Huda ban sake kiranta ba itama bata sake kirana ba, ko babu aure tsakanina da Saleh ya dace nayi zuminci da sultana domin mutum ce, har tafi Saleh a wurina domin ta tsayamin fiye da yanda ya tsayamin.
"Kiyi ha'kuri Sultana abubuwa ne sukamin yawa wallahi sannan banason duk wani abu da zai shafi Saleh....amma yanzu insha Allahu zamuyi zumunci alfarma nakeso daga gareki".
"Wacce irin alfarma Bilki?"
"Umm dan Allah gidana..." Wani banbarakwai naji da nace gidana amma na 'karasa maganata nace "kinga har yanzu ba'a zo an fara kwasar kayana ba, dan Allah so nake ki shiga akwai kayana da ban d'inka ba suka cikin akwati, ki d'aukomin su".
"Okay gida za'a kawo miki su?"
Tunani nayi sannan nace"a'a bana gida, amma...yauwa shikenan ma ki bawa Saleh ya kawomin yasan inda nake".
Dariya tayi tace "kai Masha Allahu, Allah yasa a jone a haka".
"Haba sultana kya min wannan fatan? Ai ni da sake zama da hajiya har abada, kin lahira banaso na tsaya kusa da ita ko haularta".
"Bakyaso ba wallahi, yanzu ma tananan tana had'a kayan auren....". Shiru tayi ba tareda ta 'karasa ba, "kayan auren wa ake had'awa Sultana?"
Shiru tayi nace "MAMAN DEEDAT".
"Kiyi ha'kuri wallahi bansan 'kai'kayin bakin da ya sani fad'a miki ba, kayan auren Saleh take had'awa, shima hira naji sunayi da Saleh Yana neman shawararsa wai tace bazai maidoki ba sai ya auri wata matar itama matar sai tayi ciki tukuna, kiyi ha'kuri bilkisu".
Dariya nayi dariya kuma sosai, hankalin su Raudah duk yana kaina har Aunty ma, saida na gama dariyata sannan nace "lallai Saleh namijin duniya, shi kuma ya amince ko?"
"To Bilki ya zaiyi? Inaga ya gano duk abubuwan da suka faru sharrinsu ne yace zai maidoki shine ta kafa wannan sharad'in, kuma kinsan ba yanda zaiyi wallahi yana son ya dawo dake sosai shiyasa ya amince".
Murmushi nayi ina lissafa maganar, saboda ni banida zuciya a 'kirjina zan zauna jiransa har yayi aure yayita kwanciya da matar har sai tayi ciki, to ciki abin Allah akwai Wanda ya isa ya kawo shi lokacinsa baiyi ba? Wato duk sai anyi wannan budirin sannan a dawo ga Bilkisu wadda ta yar da zuciyarta dangin mijinta sun take da takalmansu, ace na koma kuma na koma, ina Nan a juya ita kuma tayita ciki tana haihuwa na zauna banida maraba da hoto, domin ko shi indai ya fara samun 'ya"ya nasan Dole soyayyata sai ta canza a wurinsa, to kin Haifa ma miji ya raba son da yake miki ya maidawa abinda kika haifa rabi balle ke da ba zaki Haifa ba? Da alamu dai zamana da Saleh har abada, dole ne na fuskanceshi muyi magana mu samu closure kowa yayi hanyarsa.
"Sultana bakin al'kalami ai ya riga ya bushe, idan kikayi tunani a abinda hajiya ta tsara kawai plan ne a wula'kantani har 'karshen rayuwata, kina tunanin idan ya fara samun haihuwa zai kashemin miliyan hud'u domin na haifi d'a d'aya tal bayan yana samunsu a kyauta? Na gama fahimtar plan d'in hajiya da alamu dai ni da Saleh saidai a bada labari".
Muryarta gaba d'aya ta canza kamar zatayi kuka tace "Bilkisu dan Allah ki taimaka masa wallahi Saleh yana bukatarki fiye da yanda kike tunani kuma yana sonki, bakiga yanda ya lalace ba a tafiyarnan taki, ni kaina wahala nakesha saboda rashinki a gidannan ga Huda ga Ahmad wataran na rasa yanda zanyi dasu saidai na sasu a gaba na zuba tagumi. ni abinda nace ma yayi shine ya maida ke ko wani wurin ne ya kaiki ya ajiye kafin iddarki ta 'kare, idan yaso ko me za'ayi dai kina matsayin matarsa".
Dariya nayi nace "Sultana yau na fita daga idda ai, na tashi daga matar Saleh na zama matar...." Kafin na 'karasa Raudah tace "Aalee!!"
Rankwashinta nayi nace "na zama matar mai rabo, saidai ya shiga jerin zawarana".
Da alamu kuka ta fara saboda yanda muryarta ta sauya, a hankali tace "shikenan Bilkisu bazan sake ganinki ba?"
"Zaki ganni mana Sultana zamu dinga zumunci dukda bazan iya zuwa inda kike ba saidai ki dinga ha'kuri kina zuwa inda nake"
"Dukda haka zumuncinmu bazai kai yanda nake so ba, dan Allah Bilkisu ko Huda ki kar'ba nasan cewa muna nan a "yan uwa".
"Sultana ina kewar Huda sosai wallahi, amma a yanzu ne ma lokacin da ya kamata Huda ta zauna dake, dama auren Saleh ne ya sanya kika bani ita yanzu babu wata dangantaka tsakanina daku, ri'kon Huda zai zamarmin damuwa musamman da su Hajiya basa so, zan dinga ganinta dai akai-akai nagode da kulawarku sultana, kece kad'ai farin cikin da bazan manta dashi ba a zamana a gidanku".
Kuka take a yanzu sosai har ta sanyani hawaye nima, cikin kuka tace "na dad'e ina kishi dake Bilkisu na dad'e ina sha'awar zaman da kikeyi da Saleh, idan na zauna sai nayita tunanin meyasa ni da usman bama wannan zaman? Soyayyarku nake kwaikwaya Bilki har na 'kware nima, yanzu duk wannan zaman kin manta dasu?"
Murmushi nayi nace "Sultana abu marar Dad'i d'aya yana kore duk wani Dadi da kaji a duniya, ban manta dasu ba amma bana tuna lokutannan kamar yanda nake tuna ranakuna na 'karshe a gidan Saleh, amma wataran sai labari ki shafamin kan Huda". Ban jira me zata ce ba na katse kiran tareda share hawayena, duk jikinsu yayi sanyi banda mutum d'aya, kunsan waye ba sai na ambaceshi ba, dawowa yayi hannun kujerar da nake yace "yanzu salele yana number one kenan a zawarawanki, please make me number two".
Galla masa harara nayi ya d'aga gira tare da cewa "I am serious, zan Kara dashi naga a cikinmu wa zaici wannan game d'in?"
"Ya Aalee yanzu Aunty B d'in ce game?" Raudah ta fad'a tana kallon yanda naji ba dad'i da ya kirani game, murmushi yayi yace " 'kwarai kuwa, duk macen da tayi aure ta fiti ta zama game a wurin mazaje, musamman mata irin su Sweet B, tamkar gwal ne, mutum yayi amfani dashi ya yar aka dasashi a tsakiyar ruwa kowa yana kallonsa kuma wannan gold d'in na attracting attention na duk wanda ya wuce, saidai a 'karshe ansan dole mutum d'aya ne zai zama mamallakinsa, mai shi bazai gane tsadarsa da kyawunsa ba sai yaga yanda mutane ke rububin d'aukansa, wannan shi ya maidashi game, wa zaka kayar wa zai kada kai? Ke kinsani bazawara tafi budurwa white blood domin har wani shining takeyi".
Duka muka kai masa da ni da aunty da Raudah, dariya yayi yace "oh my God ashe gidan zawarawan nake, nidai sweet B ki sakani a list".
Tashi nayi nace "ai ba ni zan sanyaka a list ba, kai zakayi proving kanka ka isa shiga list d'in ma ko kuwa".
"Game on wifey, na miki al'kawari a 'karshe ni zan d'auki wannan gold d'in, ba zanyi swimming kamar yanda kowa keyi ba, zan bi ta sama ne na d'aukeshi kowa yana kallo".
Juyowa nayi na kalleshi nace "ai ba d'aukan gold d'in bane wahalar, zaman gold d'in a hannunka shine abinda yafi wuya, karka maida hankali wajen samun abinda ka 'kwallafa Rai ka fara duba wannan abun ya dace da kai ko kuwa? Idan har ka d'auki gold din hanyarka ta fita kayi tuntube da diamond, zaka d'auki diamond d'in ne ka had'ashi da gold d'in ko kuwa zaka yar da gold d'in ne saboda diamond ya fishi daraja? Kuma daga kallonka nasan zakayi amfani da maganata ta biyu ne".
Ni kaina bansan ma'anar maganar da nayi ba saida na shige d'aki, sam ban amincewa Aalee ba na farko saboda yana da kyau, ba wai mummunan namiji nakeso ba amma maza irin su Aalee bakada kwanciyar hankali, namiji ne kamar balarabe komai nasa sai ya d'auki hankalin mace, a fitar da mukeyi ina kallon idanuwan mata da dama a kansa amma ko ta kansu baya bi, sharrin matan zamaninnan wata ta dora Ido kansa kin gama yawo, kuma ni ba aurene ma yanzu a gabana ba, namiji ya bani lesson d'in da Zan dad'e ban amincewa wani namijin ba, wanda ka dad'e dashi ya maka haka balle kuma wanda ka gani a titi? Tun ina secondary nake hulda da Saleh amma yayimin haka, Ina ga wanda zamu had'u a titi?
Sallar Isha nayi kafin na fita na jiyo maganar su
"Gaskiya ya Aalee baka kyauta ba" Raudah ta fad'a cikin 'bacin rai.
"Me nayi?"
"Kai baka San me kayi ba? Ta yaya zaka fara wani zancen game a wannan yanayin? Kwana nawa da mutuwar auren nata zaka fara mata wasa, ba sonta kake ba bai kamata ka fad'i abinda ka fad'a ba".
Dariya yayi yace nifa "banga laifi a abunda na fad'a ba".
"Wai ta Yaya zaka ce baka yi laifi ba? Ita Bilkisun abar wasa ce a wajenka? Ta yaya zaka fara tempering da emotion d'inta bayan halin da ta shiga? Ita ba irin wad'annan sha-sha-shan 'yammatan dake binka bane kana yarfa su, Ka sameta ka bata ha'kuri kar kuma ka sake mata magana irin wannan, idan kanada interest a kanta ne ka biyo ta hanyar da ta kamata mana".
"I mean what I say Raudah, babu na ha'kuri da zan bata" alamun fitarsa naji na koma na kwanta, banaso ma na saka Aliyu a lissafina shirme kawai yakeyi.
Bud'e wayata nayi tareda unblocking number Saleh, pics d'in da mukayi na fara kallo naji sallamar Raudah.
"Me kikeyi?" Ta fad'a bayan na amsa mata sallama, nuna mata pics d'in da nake kallo nayi ta kar'ba tana kallo, twins ne suka shigo suma suka zauna gefenta, kallon hotuna suke wasu su nunamin suce waye wannan na fad'a musu, yawancin pics d'in duk na Huda ne, ji nayi na sake missing d'inta.
Rufe ido naga twins sunyi Raudah kuma ta juyomin wayar tana dariya, wani pic ne nawa da Saleh...wanda dai bazan so kowa ya gani ba, "gogeshi dan Allah" amsamin tayi da to ta goge, saidai fa irin pics d'in ne suka yita bayyana kansu, tun ina cewa ta goge har dai na kar'bi wayar tawa na fara gogesu da kaina, duk hotunan akwai memory d'in da suke holding, tun ina gogesu babu wani emotion har saida zuciyata ta fara karaya hannuna ya gagara danna delete, fita nayi na ajiye wayar a gefe tareda nufar toilet nayi kuka na mai isata sannan na fito, duk yanda zan yaudari kaina nace na cire Saleh a rayuwata nasan cewa wani gurbi na zuciyata har abada yana tareda Saleh.
40
A gajiye na shaso kwanar gidan Aunty, yau munsha aiki fatana kawai na samu na huta, mayafin abaya na yafa kasancewar na fito abokiyar aikina na sallah da hijabina kuma bazan iya jira ba, Saleh na hango a tsaye yana juya key a hannunsa sai raba ido yakeyi.
Mamaki nayi ganin Huda a hannunsa, ya kamata ace yana wurin aiki yanzu meyasa jabir ya barshi ya taho? Me yazo yimin ma in the first place?
Idanunsa na kaina har nayi parking, dukda nayi farin cikin ganin Huda amma ban wani nuna ba kar yayi tunanin shi nake farin cikin gani, domin ina ganinsa maganar sultana ce ta fad'omin ta auren da