Author : kitty Category : Romantic Hausa Novels
aikin gida babu aikin waje?"
Hannunsa biyu ya saka yaja kumatuna yace "idan munyi tafiyar da zamuyi mun dawo sai ki yanke shawara, idan kinaso ki koma aiki sai mi sanarwa Mum ta samar miki a asbitinsu amma nasan da wuya ma ki amince ki koma".
Nikuwa me zai hanani komawa aiki?
***
A cikin two weeks da nayi a gidan har anyi renewing passport d'ina a yau muke shirin tafiya Saudi da yardar Allah, su Raudah ke tayani had'a kayana.
"Haba Raudah kamar zan bar 'kasar har abada wannan uban kayan?".
Cigaba tayi da loda kayan tace "bakiji yace daga nan zaku tafi wata 'kasar ba? Kika san dad'ewar da zakuyi? Shiyasa nake saka muku kayan da zasu isheki har ku dawo".
"Dukda haka ki barsu dan Allah, wannan ai sai ace abu na sako a akwatin musamman zuwa saudiyya, sai ace goro ne kisa ayita cajeni".
"Hakan ma bazai faru ba"
"Ko a yagamin jakar kayan su zube kowa ya gani na rasa a ina zan sa...."
"Shutup, na barsu haka shikenan?"
Gyad'a mata kai nayi alamar eh sannan muka daddanna akwatin muka rufe, twins suna parlour da 'kawayensu na kalli agogo, saura three hours mu fita, kallona raudah tayi tace "Bilkisu kina son ya Aalee?"
"Meyasa kika tambayeni? Na fad'a ina kallonta.
"Umm saboda wannan maganar tanada muhimmanci kafin ku tafi, har yanzu kina tunanin komawa tsohon mijinki?"
"A'a bana wannan tunanin, sannan na fad'a miki gaskiya Ya Aalee yana burgeni, sannan yana kyautatamin ina kuma 'ko'kari wajen cusawa Raina sonshi, amma dukkanmu bamu fara son junanmu ba, we are taking it slow".
"Zamuga zuwa yaushe hakan zai tabbata, indai kin amince da zama dashi har 'karshen rayuwarki shine kawai abinda nakeso naji".
"Na amince Raudah zan zauna dashi har abada indai zai zauna dani a yanda nake".
Dariya tayi tace "me zai hana kuwa?"
Cigaba nayi da abubuwan da suka kamata har lokacin tafiyarmu airport, bayan mun musu sallama amal tace "ya Aalee amma dai ka bar key d'inka a gida ko?"
"Eh me ya faru?"
Tsalle sukayi tare nawal tace "bakomai, sai ka dawo, gadi kawai zamu yi maka kafin ka dawo".
Munyi umrarmu cikin kwanciyar hankali, Aliyu shi ya dinga nunamin wurare sannan nayo tsaraba mai yawa, domin na shirya da mun dawo zanje naga gida.
Sati biyu mukayi sannan muka wuce Dubai, a cikin raina ko sunan 'kasar banason ji saboda abinda ya faru a baya, har yanzu asbitin suna turomin notification ta email d'ina wanda hakan na tasomin da abubuwa da dama, fatana Allah yasa ba dad'ewa zamuyi ba.
Muna shiga 'kasar na fara kalle-kalle kamar ba'kauyiya, babban abin farin cikin shine mun sauka a best hotel in the world, burujul arab, suite ya kama mana Allah kad'ai yasan kud'in da ya biya, dukda ba VIP bane amma ai shiga hotel d'in kansa abin kallo ne.
"Bakinki ya'ki rufuwa fa tunda muka shigo".
"Ta yaya bakina zai rufu man, ka kuwa kalli garinnan da kyau? Babban birnin 'kasar fa muka sauka kamar dai Abujanmu, wayyo Allah kamar kar na koma gida".
"Hm wani abun ma sai munje skating da bowling".
Tsalle nayi cikin murna shi kuwa dariya yake ta min, le'kowa nayi ta glass d'in da ya kewaye d'akin, kana ganin rufin garin, dan ma rana ce da dare ne nasan sai yafi haka.
Ahmad ne ha fad'o raina a take na kirashi na sanar masa gani a Dubai, cikin murna yace zai hau jirgin 'kasa yazo ya sameni idan aiki ya ragu.
Ranar ban wani huta ba sam banajin gajiya, na dad'e banyi farin ciki irin wannan ba ban saniba ko Allah ne ya albarkaci 'kasar da sanyawa mutum nishad'i?
Ko da muka je ice skating ri'ke hannuna Aliyu yayi shi ya dinga min jagora, sai dare sannan muka koma bayan naga had'add'en ruwannan, Aliyu kuwa ko a jikinsa shi ni yake kallo ma.
Muna kallon ruwan naji kansa a kafad'ata yace "ban ta'ba ganinki kina farin ciki kamar yau ba".
Hugging d'insa nayi sosai ban damu da mutanen dake wurin ba nace "all thanks to you ka sanyani farin ciki, ka bani abinda a rayuwata ban ta'ba tunanin samu ba Allah ya biyaka".
"Hmm to idan wannan kinyi farin ciki haka next surprise da zan miki ai zaki iya suma".
Da sauri nace "Dan Allah mene ne shi".
"It's a surprise"
"Please"
"No"
"Pleeeeaseeeee"
"Noooooooo"..
"Pretty please?"
"Yes you are pretty, mu koma n fara jin bacci".
Duk yanda naso ya fad'amin surprise d'ina ya'ki yace sai na kissing d'insa nayi, yace na Masa massage wanda yayi leading zuwa wani abu daban.....a haka na ha'kura, nifa inada matsalar surprises na tsani ace za'ayi surprising d'ina.
Abin takaicin ma washegari ya'ki fad'amin sannan yace bazamu fita ba sai dare, tuni na yanke shawarar.maybe wani cinema zai kaini ko dai taro haka, lokacin da zamu fita rufemin Ido yayi da 'kyalle ya kama hannuna ya shigar dani mota, kasa kunne nayi naji ya bawa direba address d'in inda zamuje amma naji yayi shiru, nidai inajin mota na tafiya, ko da na fara 'ko'karin bud'e idona sai ya had'a hannayena a kan cinyarsa.
Bayan motar ta tsaya muka fita yace "yi a hankali dai".
Baifi taku goma mukayi ba ya tsaya tareda kuncemin idona, kallon glass doors d'in dake wajen nayi take na lura da asbiti ne, saman asbitin na kalla naga an rubuta IVF CLINIC......
Wani mugun fad'uwar gaba naji yayin da Hawaye suka fara zuba daga idona, wannan shine surprise d'in da ban ta'ba zato ba ...
48
Kuka sosai nakeyi har saida na gagara tsayawa kan 'kafafuna, dur'kusawa nayi shima ya dur'kusa, hannunsa ya saka a kafad'ata ba tareda yace min komai ba, ban ta'ba kawo yin IVCF a gidan Aliyu ba dukda nasan wataran zai nemi haihuwa, amma ban ta'ba tunanin dani zai haihu ba.
Mun d'auki mintina a haka sannan ya bani handkerchief na goge fuskata muka shiga ciki, hankalina sam baya kan abinda yake fad'i har yaja hannuna muka nufi wani office, anan naji yana bayanin appointment da akayi na Bilkisu mustapha, wato shi ya gama shirinsa duk ban sani ba.
Wata takarda aka bamu ya kira nurse yace ta rakamu za'a min gwaji, gabana sai fad'uwa yakeyi na kama hannun Aliyu na 'kan'kame, Saleh ne ya fad'omin rai, da ace dashi mukazo wajennan zanji nervousness haka ko kuwa murna zan dinga yi? Ba wai na tuna bane saboda soyyaya, a'a na tuna ne saboda shine mutumin da nasan bana haihuwa a wurinsa sannan dashi muka fara wannan magana, Allah yayi ba dashi zanzo ba.
Muna shiga ya mi'ka ma ma'aikaciyar wurin takardar, gado ta nunamin tace na kwanta sannan Aliyu ya zauna a kujerar gefena, bayanin test d'in da za'a min takemin, HSG wanda za'a hasko can cikin mahaifata ina kallo a screen, saida aka saka wani abu kamar syringe da ruwan allura tace min sunanshi contrast media, injecting d'insa akayi zuwa uterus d'ina, bayan wani lokaci aka d'auko HSG tool d'in shima ta saka, hannuna Aliyu ya kama yana murzawa a hankali, wani hawayen ne ya zubomin kafin na goge yasa hannunsa ya goge, muka zubawa screen d'in Ido.
Sai ga mahaifata ina gani dukda ba wai komai da komai ba, bayani take mana a hakan dai aka tabbatar inada cervical infertility, komawa wajen likitan mukayi har yanzu ban furta ko kalma d'aya ba, bayan likitan ya gani yace za'a fara aiki next ovulation d'ina, wanda almost 13 days kenan, sannan a d'auki eggs d'inmu a saka a kwalba sai yayi six weeks sannan a maidashi jikina, bayan wasu six weeks sannan a yimin US scan a tabbatar akwai cikin sannan bayan 2 weeks a sakeyi bayan an tabbatar baby na lafiya lau sai a barmu mu tafi.
Godiya Aliyu ya musu sannan doctor d'in yace da zarar na gama period naje za'a min ovulation test, oh ni Bilki naga ta kaina.
Bayan mun fita Aliyu yace "kinyi shiru baki ce komai ba har kin fara bani tsoro".
"Bansan me zance bane...." Wani kukan na fara yace "Allah ya baki ha'kuri ba sai kince komai ba".
"Amma inaso nayi magana" na fad'a ina goge hawayena, murmushi yayi yace "munada sauran lokacin wannan maganar yanzu dai muyi wata maganar".
"Zamu dad'e anan yanzu ya zamuyi da aikinka?"
"Dad ya hau kai, dama shine a kai ya d'aurani, sauran kuma da na fara zan 'karasa anan kafin mu koma".
Shiru na sakeyi har yanzu gani nake abin wasa ne, ranar kamar kurma na koma da zarar Aliyu yayimin magana sai hawaye, kamata yayi ace tsalle nake da murna amma tsananin murna yasa na kasa hakan, farin ciki yasa washegari na tashi da azumin godiya ga Allah.
Kamar wasa har ranar da za'a fara mana aiki tazo, a tare aka d'auki sample d'inmu aka saka a wata kwalba, da yawa suka d'iba wanda bayan 6 weeks d'in wad'anda suka rayu za'a d'auki biyu a ciki a sakamin, sunce zasu yi 'ko'karinsu su tabbatar maza ne tunda munce duk mazan mukeso.
Muna fita nayi hugging d'insa a bakin titi nace "nagode sosai, abinda ka bani Allah ya ninka maka ya baka".
Dariya yayi ya d'agoni kad'an sannan ya ajiyeni, turo baki yayi yace "ya kamata ki rage nauyi fa".
"Kai ya Aalee nawa nake? 58 fa".
"Aikwa kinyi nauyi da yawa sosai, nafiso na d'aukeki cak ya sa'ba a kafad'ata nayita yawo dake a haka".
Dariya nayi yayin da muka tsaida taxi nace "Banda abinka ai jannat ce kawai zaka iya d'aukanta haka laifi daga kai ne ya kamata ka 'kara 'kiba".
"A'a ke ya kamata ki rame tunda fa kin kusa samun babies, ba ma d'aya ba biyu kinga ya kamata ki musu mazauni".
Murmushi ne ya bayyana a fuskata ba tareda nace komai ba, wai ni Bilkisu nice zan haifi 'ya'yana, abinda nayi shekaru uku Ina shan gori akai, dama ance wani hanin ga Allah baiwa ce.
Takura masa nayi muka bar burujil arab domin kud'in da ake kashewa dukda bai fad'amin ba kuma nasan baya damunsa amma ni yana damuna, banaso naji ana lissafin an kashe miliyoyi a kaina.
Six weeks muka koma aka dasa min babies d'ina, tunda muka baro asbitin nake shafa cikina gani nake kamar za'a ce sun lalace kafin lokaci yayi.
Ko da muka isa gida kama hannuna Aliyu yayi, a hankali yake tafiya ina yin sauri kad'an ya tsaidani yace "ki tafi a hankali kar babies d'inmu su samu matsala".
Kallonshi nayi shi kanshi yana cikin farin ciki domin idanunsa sun nuna, jingina kaina nayi a hannunsa ya ri'ko gefen cikina a hankali har muka 'karasa d'akinmu, saida ya zaunar dani kan gado ya d'auko min kayan baccina ya bani sannan ya fita yace "zanyi aiki kar na dameki da 'karan keyboard, duk abinda kike bu'kata ki kirani kar fa ki tashi indai ba sallah zakiyi ba".
Rigar jikina na fara cirewa nace "nifa banji doctor ya bani bedrest ba, dan nayi tafiya cikina bazai samu matsala ba insha Allah, aikin nauyi ne bazanyi ba har sai an tabbatar da zamansa".
"Ke da aikin nauyi sai bayan kin haihu, ya zaki dinga d'aukan nauyi da baby a jikinki salon su gaji? A'a banason haka".
Murmushi nayi cikin jin dad'i na zura rigar baccina, kafin na kai rigar 'kasa ya ri'keta tareda bud'e cikina, hannu yasa ya shafa sannan yace "good night my babies, kar ku takurawa mummy".
Kashe murya nayi nace "goodnight Daddy". Kissing d'ina yayi yace "kiyi sallah ki huta kin sha jagwalgwalo yau".
Banyi masa musu ba na tashi na nufi toilet, saida yaga shigata sannan yace "take care karki fitsararmin da babies!!".
Dariya nayi yanzu kam farin ciki ya yalwata a cikin zuciyata, kullum cikin murmushi nakeyi ga son Aliyu shigata yakeyi, kai ba so kad'ai ba 'kaunarsa nakeyi sosai da sosai.
A six weeks d'in da mukayi wani riritani yakeyi kamar 'kwai, abinda ke damuna shine ban fara laulayi ba gashi a lissafi dai 12weeks idan aka had'a da wancan 6weeks da yayi a kwalbar bature, gani nake ma kamar dai cikinnan babu shi dukda ina shan magungunan da aka bani.
Ranar da mukaje gabana sai fad'uwa yake ina dam'ke da hannun Aliyu, a yau ne zamuji heartbeat na babies d'inmu gaba d'aya hankalinmu na kan na'urar da aka kunna, bayan ta shafa min jell d'in ta fara aikinta, shiru shiru zuciya ta'ki bugawa, murmushi tayi tace "I think your baby is playing hide and seek with us".
Sake shafawa tayi sai wani shuuuu mukeji ta cikin na'urar, bansan lokacin da na fara hawaye ba Aliyu shi kansa yanayinsa ya canza, ya Allah kar kasa wannan cikin ya lalace this is my last hope.
Yanayin ri'kon da Aliyu yayimin shi ya sanya nasan cewa yana cikin damuwa shima, kuka sosai na fara yayin da mukaji bugun zuciyar ya fara fitowa, tare muka sauke ajiyar zuciya Aliyu ya kwantar da kansa a 'kirjina, share hawayena nayi yayin da na farin ciki suka fara zuba, I can't believe this is real, ni Bilkisu da aka yiwa gorin haihuwa nice da 'ya'ya har biyu a cikina, inama Hajiya zataga wannan ni'imar da Allah yayimin tasan cewa ba d'anta ne kawai zai iya bani haihuwa ba, Allah ne yake bayarwa ta hanyoyi da dama.
Mun jima muna sauraron heartbeat d'in babies d'inmu sannan ta nuna mana kan babies wanda shine abinda dai yafi bayyana a yanzu, gender dai da saura amma gasunan twins gwanin sha'awa dukda ba wani ganewa mukeyi sosai ba.
Ri'ke takardar Aliyu yayi kamar ransa ne a jiki muka fita, wasu masoya muka gani suna tafe suna Shan ice cream, kallon ice cream d'in nayi naji amai ya tasomin da gudu na nufi gefen titi, amai na dingayi kamar zan amayar da kayan cikina kafin na gama Aliyu ya Kira emeegency....
49
Bayan zuwan ambulance na sanar musu ba wani abu bane, banda ma shirmen Aliyu kawai daga fara amai zai kira min asbiti?
Bayan sun dubani sun tabbatar babu wata matsala suka bani magani a cikin motar sannan suka sallamemu muka tafi.
Muna zuwa gida zazza'bi ya rufeni gaba d'aya hankalinsa Aliyu ya tashi, da alamun bai ta'ba ganin marar lafiya ni kuwa baisan dad'in hakan nakeji ba nima na fara jina a mutum.
Kashe AC d'in d'akin yayi ya kunna min heater tare da lullu'bata, dafa kaina yayi yace "sannu Bilkisu ya kikeji?"
"Dad'i" na fad'a tareda 'kudundune jikina, wani kallo yayimin yace "lafiyarki kuwa? Ya mutum yana ciwo zaice yana jin dad'i? Wai kinsha maganin da aka baki ma kuwa?"
Tashi nayi na zauna na jingina a kafad'arsa nace "ya Aalee ba dole naji dad'i ba? Wannan wahalar da zan sha itace zata sanyawa 'ya'yana tausayina, ba wannan ba ma wannan shine first and last time da zanyi laulayi this is so important to me, indai maganin zai hanani ciwon ne to bazan sha ba, wannan shine stage na farko a motherhood kuma banaso nayi skipping".
Shafa kaina yayi yace "Bilkisu bansan ya kikeji ba amma cuta ko ya take batada dad'i idan ciwon yayi yawa zaiyi affecting babies d'inmu ko kuwa? Banaso a samu matsala".
"Babu matsalar da zamu samu da yardar Allah, mata da yawa suna shan wahalar da tafi tawa wata sai an kwantar da ita a asbiti, wata tsabar ciwo fita hayyacinta takeyi, nawa me sau'ki ne fa".
Maganin ya d'auko daga kan bedside drawer yace "to ki daure kisha ba lallai maganin ciwon zai miki ba amma zai rage miki ko da zazza'bin ne, tunda muka dawo ko ruwa baki sha ba gashi abinda kika ci ya dawo kisha magani sai kici abinci yanda suka ce".
Kar'bar maganin nayi nace "okay zansha to d'aukomin ruwa please".
Yana tashi na ciro maganin, bayan na duba naga vitamin ne na yanke shawarar sha, d'ayan kuwa 'boyewa nayi.
Bayan nasha ya fara tambayata me zanci, sunayen abincin da yake lissafowa ne suka sanyani amai da gudu na tashi na nufi toilet.
Ko sunan abinci banason naji ga yunwa tana addabata amma ko zakici yacemin sai naji zuciyata na tashi, malt na samu nasha kafin na kwanta, itama ina bacci ta tasomin na tafi na amayar.
Washegari da safe mukayi waya da Mama, ban sanar mata ba so nake na bata mamaki idan na koma gida naje saidai ta ganni da abuna, Mum ma yacemin kar na sanar mata domin basu san za'ayi min aikin ba.
Bayan two weeks muka koma aka duba babies suna lafiya lau, a ranar muka baro Dubai domin 'kasar ta isheni, cikina har ya fara fitowa amma kayan da na saka basu bayyanar dashi ba
Ko da muka shiga jirgi hannun Aliyu na kan cikina, shi gani yake laulayin da nakeyi zaiyi affecting cikina saida na sanar masa yanda abun yake lafiyarsu ce ta sanyani hakan tukuna ya barni na huta.
Muna isowa gida naji wani annushuwa, twins na hango suna d'ago mana hannu muka 'karasa wurinsu, a tare sukayi hugging d'ina suna tsalle na cije baki domin sun danne min babies d'ina amma ban nuna ba, Aliyu yayi 'ko'karin janyesu nace masa a'a.
Bayan sun sakeni muka gaisa da Raudah, itama hugging d'ina tayi tace "lallai Dubai ta kar'beki kinga yanda kikayi fresh kuwa?"
Murmushi na mata ba tareda nace komai ba na nufi Mum, dur'kusawa nayi ya d'agoni tareda hugging d'ina tace "welcome home".
Turarenta ne ya daki hancina naji amai na tasomin, 'ko'karin dannewa nakeyi amma na kasa da sauri na bar jikinta na nufi wurin da zanyi.
Gaba d'aya wurina suka yo cikin damuwa Mum ta dafani tace "sannu Bilkisu dama...." Tsayawa tayi da maganarta ta fara 'karemin kallo, wani faffad'an murmushi ta saki na sunkuyar da kaina, Raudah ganin yanayin mum yasa ta zare ido tace "OH...MY...GOD!!"
Da alamu twins ne kawai a duhu domin sai kallonmu sukeyi, dukkanmu fuskokinmu d'auke da murmushi.
"Muje ko? Ya kamata ku samu ku huta saboda gajiyar tafiya" Mum ta fad'a tareda yiwa Aliyu alamun tana son magana dashi, gaba sukayi nayi hamdala domin turarenta ya dameni, jan hannuna tayi mukayi gaba tace "how many weeks?"
"14" na fad'a ina murmushi, hannu ta saka ta dafa cikina tace "haba, ni naji abu ya tokareni nayi tunanin d'inki ne, I am so happy Bilkisu wallahi bazan iya fasalta miki farin cikin da nakeji a yanzu ba, nasan munyi maganar da ya Aalee yace zai duba ya gani, ashe shammatarmu yayi".
Kawunan twins ne suka le'komu a tare sukace "wai dama ciki ne da Aunty B?"
Tsalle sukayi tare amal tace "Allah yasa twins ne irinmu".
"Ba amin ba wannan rashin jin naku ina zata kai shi? Ku jira ma ya Aalee yasan abinda kukayi sai jikinku ya gaya muku".
Gaba sukayi cikin sauri suna dariya nace "me sukayi?"
"Hm kibar yarannan ai bana fatan ki haifi twins, wallahi shegen neman magana