DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 33

1 to 3K   out of 97.7K words

[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
Marubuciyar, *tawa kaddarar* da *uwata* 😜😜😜



Page :1🌹



Bismillahir rahmanir rahim, WA sallallahu ala nabiyyir Kareem



Saurin nake tayi in ƙarasa wanke2n da nake yi don inje in ɗebo ruwa nasan yanzu mama ta kusan dawowa daga yawon ta kuma duk irin hidimar nan da nayi mata a gidan ta ba lallai ne ta gani,



Khadija ce ƙanwata wacce take bina suka fito daga ɗakin mu ita da maryam cikin uniform ɗin islamiyya,
"yaya haryanzu baki gama ba, zaki makara ma yau kinga jiya sai da aka miki dukan latti"
"hmmm kudai tunda kun shirya ku wuce ku tafi karku makara ni ba lallai bane inje" alamar tausayi na gani a fuskar ƙannan nawa
"me yasa" suka haɗa baki




Tashi nayi ina goge hannu na da riga ta ina kaɗa su don in ba korar su nayi ba ba lallai ne su tafi ba sai suma su makara, wucewa sukayi dukkanin su rai a jagule ni kuma na dawo na ƙarasa aiki na




ko dana gama na ɗau botiki na fara ɗebo ruwa sai da cikawa mama robobin ta tas sannan na samu na huta, ba ita ta dawo gidan ba sai karfe 5:30 yadda ba yadda za ayi nace zanje mkrnt don lkcn tashi ya kusa




tana shigowa sai ga ƴaƴanta sun biyo ta ko da yaushe suka fita oho ni dai nasan lkcn da suka dawo daga schl ita kuma ta daɗe da ficewa
"sannu da zuwa mama" ko kallo na batayi ta hankaɗa labulen ɗakin mu tai shigewar ta




A ƙofar ɗakin dai na cigaba da zama don banga alamar sakin fuska a tattare da ita, *zainab* naji an ƙwala min kira da manyan harufa
"na'am"





cikin ɗakin na shiga asukwane ta cire kayan jikinta daga ita sai zani ga ƴaƴanta nan a zaune a ƙasa suna cin gyaɗa, ɗakin da na gama shan wahalar gyaransa
"to uwar munafunci baki ga alamar na dawo bane baza kizo ki karɓi abinda zaku dafa bane don tsabar kinibibi kina zaune kina kallo na ko ni zan dafa muku" ta faɗa a hasale




Bance komai ba "ɗauki garin kwakin can kije ki tuƙa eba sai kije kasuwa ki siyo ewedu kiyi miya tunda muna da dage dage" too kawai nace na ɗauka na fice




sai da na tuƙa ebar na kwashe sannan na shiga ta bani kuɗin ewedun da daddawar, ina fitowa na ci karo da su khadija har sun taso,a tsatsatsaye nayi musu magana sannan na wuce don kasuwar ba laifi da ɗan nisa



kasuwar agege naje kasancewar tafi kusa da mu na siyo, inda magariba ce ta shigo dani gida ina shigowa sai da na ɗaura miyar sannan nayi alwala na shiga ɗakin mu, bayan naa idar na ƙarasa miyar ewedu ta na sauke ɗakin mu na shigar da abinci inda na tarar da mama da yaran ko shirin tashi sallah basu ba saboda suna kallo kai Allah ya kyauta baga uwar ba baga ƴaƴan ba




ana sallar isha muka ci abinci su khadija suakyi wanke wanke mukayi shinfiɗa a nan falon mu muka kwanta gajiyar da ke jikina baisa ma naji dawowar bbn mu.





************


sunana zainab mahaifina ɗan gezawa ne dake garin kano, mahaifiyata wadda muke ce mata iya Allah yayi mata rasuwa shekara tara kenan da suka wuce mu uku ta mutu ta bari, ni sai ƙannena biyu khadija da kuma maryam, sannan baba ya auro wata bazarawa me wacce muke ce mata mama ita kuma ta haifa masa yara huɗu maza uku sai auta mace



a agege muke da zama a unguwar ruwa haya muke yi a gida me ɗakuna barkatai inda muke cikin ciki da falo, mama ta hana mu shiga ɗakin ta ko da wasa yasa muma iyakacin mu falo ba abu namu da ke cikin ɗakin, baban mu mutun ne mara zuciya ko kaɗan be damu da harkar mu balle ya kula da rayuwar sana'ar kayan gwari yakeyi a kasuwar gatan kowa, amma sai ya shafe sati be kawo komai gida ba don muci sai yace wai ba kasuwa, ita kuma mama a nata ɓangaren Allah yai ta masifaffiyace don in ƴen abinta suka motsa har wajen gidan mu ana iya jiyo su da baban mu barin ma in ta tashi bata da ko sisi kuma babu abinda zamu sa a bakin saƙatin ranar baba yana da bomb ɗin kamawa da hannunsa



ko kaɗan bana jin haushin abinɗa mama take yi mana da ƙannena don nasan cewar ko me tayi mana laifin babanmu, kuma duk jarabar mama bata taɓa barin mu da yunwa ko baba bai kawo ita sai tasan yadda ytayi muka ci muka ƙoshi wannan dalilin ne yasa nake ɗaga mata kafa




mama Allah yayi ta me shige shige ce gidajen mutane don haka kullum sai ta fita ko babanmu ya sani ko be sani ba ita dai oho shima baya damuwa idan ya dawo be ganta be wani nuna damuwa ko kaɗan


***********


Tun kiran farko na asuba na tashi kasancewar yau mune da wankin vandakin gidan kuma ni nake wankewa in turn ɗin mu ya zagayo tun mutanen gidan suna ƙorafin mama bata wankewa saini har suka haƙura tunda mama ba mutum bace da zaka taɓa ta ta kyale, da sauri na zundimi ruwa nayi banɗaki na fara wankewa amma ikon Allah kafin in gama har a cika a ƙoafar banɗakin a a layin shiga



haka na gama na futo wasu ma har sun ƙagara sun fara mita, ni dana wanke komawa nayi gefe na zauna don banga ranar shigana ba, sai da gari yai shaaa sannan aka ragi ya rage sauran iya temitope ce kawai a layi sai ni komawa nayi ɗaki na taso kannena suka fito




Sai da tabbatar da sunyi wanka sannan nima na shiga nayi wankan nawa muka zo muka shirya mama haryanzu bata buɗe kƙfar cikin ɗaki ba ragowar ebar nan na dumama mana muka ci sannan na jaa kƙoar falo muka kama hanyar schl Wacce ta kasance ta gwamnati ce dake unguwar dopemu a ƙafa muke zuwa kullum sannan in an tashi ma mu dawo a ƙafar



k
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By mmn walid nd walida(mrs aliyu)



Page: 2🌹





Shekara tana ta tafiya muna ƙara zama ƴan mata lamarin baban mu ba sauƙi don kuwa haryanzu be canza sai ma ƙara taɓarɓarewa da yayi, don yanzu sai yai wata be kawo komai gidan ba wai don muci mama ma on d other hand lamarinta na nan, amma ita tana ƙoƙari sosai damu in dai banda zagi da gorin da muke sha a wajen ta to gaskiya bata da matsala



A yanzu nayi graduating daga secondary amma babu maganar ci gaba yo ina ci gaban abinda har yanzu banje na karbo result ɗin da ya dade da fitowa ba saboda tsabar babun da baban mu ya ɗorawa kansa, don haka ne ma na kama sana'ar taimakawa wata maƙociyar mu sai da abinci



Iyan amina muke ce mata yar ghana ce da ke zaune a lagos ita da mijinta da kuma ƴaƴanta biyu shapi'u da kuma amina, tana saida wance (abincin ƴen ghana wake da shinkafa wadda ake ci da tankwa, zaku ga wance din baƙi amma sai daɗi)



Da kuma dukunu shima kamar tuwo ne na ghana wanda ake yinshi da masara sannan a naɗe shi cikin ɓawon masara, kullum take biyana wannan ba ƙaramin taimaka mana yayi duk wasu ƴen ƙananan matsololin mu ni da ƙannena ina iya biya mana, mama ma wani lkcn in abin yai mata yawa takan sakar min ciyar da mu nida ƙannena, haka rayuwa take ta ci gaba sai godiya Allah




Kullum ni nake zuwa kasuwa inyo cefanen girkin da muke siyar wa, sannan inna dawo in haɗa girkin in ɗora, duk wannan abinda nake yi bai hanani aikin mu haka zan haɗa aiki kamar wata jaka, in su khadija suna nan sukan taya ni amma idan basa nan sai godiyar Allah



************


Bayan shekara biyu

Rayuwar dai bata canza ba ɗan cangin da aka samu shine yanzu baba yana kawo kayan abin sai dai kuɗin cefane sai ankai ruwa rana da shi, shima kayan abincin bai fara kawowa ba har sai da mama ta gaji tayi yaji da yaga abin ba daɗi sai ya dawo da ita tare da alƙawarin zai dinga kawo kayan abinci haka kuwa ake yi har yanzu



Su khadija a yanzu suma sunyi candy tunda dama shekara ɗaya ne tsakani na da khadijar, mun zo mun haɗu mu ukun muna zaman gida su suna yin aikin gidan ni kuma ina sana'ar sai da abinci, wanda yanzu ba laifi nima ina samu sosai




Baban mu ya tara mu yace dukkan mu mu fito d miji aure zai mana, abinda nake gudu kenan don ni tunda nake zan iya cewa ban taɓa yin saurayi ba, gwanda ma khadija akwai wani hadi shine yake son ta amma yana da mata don dai matar tasa bata taɓa haihuwa ba ne




Bayan mun keɓe ne nake cewa khadija "kiyi wa hadi magana ya fito mana tunda naga da gaske yake" ta kalle ni ido rau rau kamar zatayi kuka
" yaya ke fa" murmushi nayi na dafa ta nace "khadija kowa lkcn sa na aure idan yayi zai yi, kinga ke yanzu Alƙah ya haɗa ki da wanda yake sonki ki yi auren ki kawai kin huta da wannan rayuwar da muke ciki mara tabbas"


ba irin lallami da ban bakin da banyiwa khadija ba amma ƙiri2 tace fafur bata yadda ba ita dai in ban riga ta ba to sai dai muyi tare ba yadda na iya da ita don na san inna na matsa mata sai ta sa min kuka




sai da bari dare yayi hadi ya zo zance sun daddage suka zuba soyayya na je nayi musu sallama suka amsa khadija tana ganina ta sha jinin jikinta sai naga ta haɗe rai, ban kula ta ba na koma wajen hadi nai mai bayanin komai da ake ciki, ya nuna jin daɗinsa sosai sannan ya ce in shaa Allah yana komawa zai yiwa magabatansa magana akawo kuɗi ina ganin khadija sai zumɓurar baki take tayi ni dai na bar su na koma gida abina su ƙarata




hadi kuwa kamar yadda yai alƙawari haka kuwa ya aiko da magabatansa suka kawo kuɗi inda aka sa ranar wata biyar, kuɗin hannuna da nake tarawa wanda nake samu a wajen siyar da abinci shi na ba khadija muka je tare ta siyo ƴen kayan kitchen wanda muka ɓoye a ɗakin iyan amina don in mama ta gani ba lallai bane ta bari baba yayi mata wasu ba




Bikin khadija yana gabatowa inda ni kuma a ɗayan ɓangaren nake shan habaici a wajen mama wai nayi kwantai na rasa mijin aure, shima a ɓangaren baban mu ba sauƙi sai kace nice zan bawa kaina miji, wannan hali da na shiga yakan ɗaga wa khadija hankali don wani lkcn har kuka zaka tsince ta tana yi, na kan ɗige da bata haƙuri, ince mata kowace mace da irin yadda rayuwar auren ta yake farawa






************
Da bikin khadija ya zo Allah ya taimake mu baba yai mata gado dama auren lagos mace gado kawai zata tare da shi sai kayan kitchen duk ragowar hidimar gida su gyaran falo da komai duk na miji ne, munyi shagalin biki lfy mun gama ƙalau sai dai fatan Allah ya basu zaman lfy, flat aka kai khadija duk da dai ba ita kaɗai bace akwai kishiyar ta kowacce ta ɗauki ɗaya shima mijin ya ɗau ɗaya,



Da bikin khadija Allah ya haɗa jinin maryam ɗin mu da wani cousin ɗin hadi mai suna sadiq, shima kamar yawancin matasan agege ɗan chanji ne, haka shima mijin khadija chanji yake yi



Soyayya suka dinga zubawa sun so ma suyi aure kasancewar maryam akwai rawar kai amma baba yace har yanzu be huta daga auren khadija ba gani ni ma har yanzu ba wani motsi,




haka ta haƙura, suka zubawa sarautar Allah ido nidai in don ta nine ban ƙi a aurar da maryam ɗin ba amma baba ya ƙi, khadija bata daɗe ba ta fara laulayi, kafin kace me sai haihuwa, ta haifi ɗan ta namiji kyakkyawa kamar ubansa,



Ansha shagalin suna inda hadi ya ɗauko ƙanwar mmnsa daga kwatano tana kula da mai jego, hadi ya kashe kuɗi sosai a wajen sunan khadija inda ɗanta yaci sunan baba sa ibrahim ana ce masa khalil, haihuwar khadija ce ta taso da zancen auren maryam, inda iyayen sadiq suka samu baba da zancen har da kuɗin zancen su da na sa rana baba baiyi wata wata ba ya karɓa aka sa musu rana




kawo kuɗin maryam ya sa na kuma takura a gidan ba wanda yake tausaya min sai ma wulaƙanci da musgunawa danake fuskanta daga kowane ɓangare na naƙi kawo miji nayi kwantai,



ni dai ba abinda nakeyi sai miƙawa Allah kuka na akan ya zaɓa min na gari, sallah dare nake tashi nayi amma randa mama ta ganni inayi har safiya tana mitar wai ina tashi ina son in asirce mijin wata da daddare, haka ina ji ina gani na daina ko kuma inyi a ɓoye,



da bikin maryam ya gabato sai aka haɗa da na ƴaƴan mama wanɗanda ta haifa a gidan ta na fari su uku duka mata dama ƴaƴa huɗu ta haifa acan ta aurar da ta farin ta, kuma duk kayan ɗakin da aka kai su da shi babanmu ne yayi musu gaba ɗaya da maryam ɗin





na so harga Allah in samu miji ko da bikin maryam ne amma hakan be yuba haka na dawo na cigaba da ruwata ina ta miƙa roƙona ga Allah ubangiji (swt) akan ya dubeni da lamarina


Mijin maryam sadiq irin mutanen ne masu sakin hannu, don kullum in dai yaga ƴen gidan mu a gidan sa to da saƙo na musamman da zai ba akawo mana, don haka mama take kiran shi da ɗan albarka, bata sati cikakke sai ta je gidan shi kuwa baya gajiya da hidima saɓanin miji khadija, itama maryam ɗin in ta tashi zuwa haka zata zo da kaya ciye ciye lodi lodi, baba kuwa yai ta sa mata albarka hmmm iyayen zamani




ko da lkcn da maryam ta haihu mama ce da kanta take zuwa har gidan maryan ɗin don kula da jariri da kuma mai jego, nidai tunda naje barka sau ɗaya ban koma ba, sai ƴar autar mu amina da aka kaima ta wai ta taya ta aiki don anga mijinta da ɗan maiƙo



ana gobe suna mama ta koma gidan wai saboda aikin miya, ban yi niyyar zuwa sai da khadija ta biyo min sannan ta sani a gaba muka je, wai don kar ace inayi wa maryam ɗin baƙin ciki




a gida aikin miyar maryam na sha habaice habaice kusan agege da sa ido tun ina danne wa ina nuna ban san dani ake har abin ya dame ni na koma uwar ɗakin ta nai ta kuka na khadija ce kawai ta san halin da na shiga har ta iya lallashina ita kuwa me jego ba abinda ya dame ta hidimar ta kawai take yi
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By mmn walid nd walida (mrs aliyu)




Page

1 / 33