DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 33

33K to 36K   out of 97.7K words

motsi ni sai dai in bishi da a a har yanzu, da abinya ishe ahi wai babyn be fara motsi ba ya kwashe ni sai asibiti inda yai musu compain na cewar babyn bai fara motsi ba




an duba ni inda aka tabbatar da lafiyar babyn sannan aka ce mana motsi sai nan da wata uku a lkcn yana da wata biyar kenan sannan hankalin aliyu ya kwanta muka dawo gida, bana laulayi ko kaɗan kuma duk abin da na samu ina ci ina ci ƙamshin turare ne kawai bana so don haka dole aliyu ya hakura da sawa



yau tj ya kawo mana ziyara, ya shigo har part ɗina don mu gaisa, inda naji ƙamshin turaren sa yai min daɗi har wani lumshe ido nake don daɗin sa da nake ji, suka ƙaraci hirar su ba abinda na fahimta tunda yawancin maganar tasun akan harkokin su ne don haka ne ma yasa ban samu baki ba ni dai kawai shaƙar ƙamshin turaren nake yi ina lumshe ido na kamar mai jin bacci



ko da tj ya tashi tafiya sai na ɗan bata raina,
"lfy kuwa madam" Inji tj
"ƙamshin turaren ka yayi min" na amsa, aliyu ne ya doka masa harara
"sai ka cire rigar taka ka ajiye mata kusa da ita muje in baka wasu kayan daga nan ka raka ni nima in siyo irin shi, ba dole ta so turaren ba ka sako turaren mata sai kace wani ɗan daudu"



sai da suka je part ɗin sa ya bashi kaya ya saka sannan suka kawo min wadanda ya cire har wani kai fuskata nake yi kusa da rigar in shaƙa ina jin daɗi


ko da suka daso daga siyan turaren aliyu ya baje jikin sa da turaren ko daya zauna kusa da ni har wani ƙara shishi shige masa nake yi ina shaƙa wannan ne ya bashi damar sauke min nauyin da ke marar sa a sauƙaƙe ba tare da nayi complain ɗin banaso



mijina ya samu dama ta don haka cin karensa yake yi babu babbaka akaina ba dare ba rana da ya bushi iska abinsa sai yaje ya bazo turaren sa ya matso kusa dani yasan cewar ina jin ƙamshin nan zan dinga shishi shige shi kuwa dama abinda yake so kenan sai yaci karen sa babu babbaka



to kunsan abin me ciki ba tabbas don haka Allah ya taimake ni na daina son ƙamshin turare nan, ranar kuwa ya bazo shi ya tinkari gadon da nake kwance zai kwanta da amai ya taso min da gudu nayi banɗaki sai da na amayar da duk wani abinda yake cikina sannan naji daɗi ko da ya tambaye ni ma ya samin amai sai nace masa warin turaren sa ne bana so aikuwa wanka ya je yayi sosai ya fito amma duk da haka bai daina ƙamshin bahi daman sawars mugunta yayi shiyasa Allah ya kama, don haka dole yau angulu ta koma gidan ta tsamiya don kuwa shinfiɗa yayi a ƙasa ya kwanta don bana son warin tj yau ya sha zagi yau sosai wai bai gaya mai ba cewar abin nawa ba permanent bane shi duk ya sakankance, ina jinshi bance komai ba sai ma dai bacci daya dauke ni me daɗin gaske
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Page :22🌹



sai da na wahalar da aliyu sosai sannan na haƙura na cemasa ya daina warin turaren ba ƙaramar kewata yayi ba na gane hakan ne ta yadda ya dinga rawar jiki a kaina hmmm



Cikina ya fara fitowa, nan rawar kan aliyu ya kuma ƙaruwa sai ya zauna yai ta hira da cikin, siyayya kuwa yi yake yi ba kama hannun yaro hatta kayan funitures sai da ya canza min ni kuma na aikawa khadija nawa


Gyaran gidan ya shiga yi da yaga lkcn haihuwa ya kara matsowa, ko kaɗan baya jin kuɗin sa in dai aka zo maganar cikin jikina ne kuɗi kawai yake fitar wa kamar baisan zafin su ba, ko na yi masa magana sai yace bazaki gane bane, yanzu zanga wanda kullum zan dinga tunawa cewar nima yanzu ga jinina a kusa da ni, yakan ƙulle min kai da maganganun sa tare da soki burutsu don haka nake ɗaukar zancen nasa




Lahadi da daddare muka shirya domin zuwa asibiti awo, na ci kwalliyata sosai kamar ba me ciki ba , muka ɗau hanya, ko da muka je asibitin da nake awo sai aka ce likitan bata nan don haka sai dai muga wani, shi kuwa aliyu ba abinda ya tsana da ya wuce ace namiji ne zai ganni don haka tun farko ya nemi likita mace ta zam dr ɗina,



ko da na faɗawa aliyu ceqar bata nan si dai namiji, sai yace shi bai yadda ba bari kawai ya kirata, ko da aka kira ta sai tace mu same ta general hospital



nan muka je don ta duba mu, labour room ta sa na je don tayi min awon a can, ko da naje da mutane don hka sai tace inɗan jira kaɗan, tana cikin duba aka zo aka kira ta emergency don haka sai ta fita, sai ta sa wata dr ɗin ta ci gaba da duba mu,





ko da zo sai ta kalle mu tace
"duk naƙuda kuke yi" dukaan su suka ansa banda ni, ta kalle ni tayi murmushi
"daga gani har yanzu bata matse ki sosai ba shiyas kika ci wannan kwalliyar"


sai da ta gama duba su tsab snnan tace min in zo, kamar zan mata musu sai dai na tafi, ta sani na kwanta ta duba ni
"kina 2cm,nan da 4hrs zaki iya haihuwa, kije kiyi ta zaga yawa" saukowa nayijikina yai sanyi wai zan haihu




ko da na fito na tarar da aliyu yana jira na
"me suka ce"
"nan da 4hrs zan haihu"
"wattttt kina nufin nan da awa 4 ƙwarara ina nan da baby na a hannu" ya tambaye ni gyaɗa mas kai nayi




nan ya rikiɗe sai sunbatu yake duk ya bi ya ɗaga hankalinsa wai ance haihuwa da wuya, shi bai shirya ba kawai mu tafi gida ma dawo nan gaba idan ya shirya, ya kalle ni
"zainab bana son ki wahala wajen fito da babyn nan mu gudu gida kawai kinga dole haihuwar ta haƙura har sai lkcn da muka shirya ko" ya faɗa yana ja min hannu alamar mu bar wurin





ni da nake shirin fito da babyn hankalina ya fi nashi kwanciya
"hubbi, ba komai am alright, we can do together, baby yace yau yake son yazo ku haɗu pls lets grant our babys first wish" na faɗa masa ina mai tallafar fudkarshi don mu haɗa ido, wannan abinda nai masa ba karamin kwantar masa da hankali yayi ba har ya fara rakani takawar




sai ƙarfe 1:30 na dare sannan na shiga cikin labour room din lkcn wahalar haihuwa ta fara damƙata, na sha wahala sosai bini bini naga call ɗin aliyi kon haihu sai ince masa da saura



ba ni na haihu ba sai da asuba, byan ma anshiga masallaci sallah asuba sannan Allah ya suke ni lfy na haifi ɗana namiji kyakkyawa fari tas da shi




ya na idar da sllah y kirani na faɗa masa na sauka, kashe wayar kawai naji yayi, inda daga baya ya kirani yai ta min godiya tare da addua, aka shirya baby nima akai min duk abinda ya dace ai min da karfe 6:00 aliyu ya kira ni
"ga abinci nan na sa an miki za a shigo miki da shi ki ci, naji ance me jego ta dinha cin abinci sosai ko ruwan nono ya zo ko" to kawai nace



na ɗauka abinci ne irin baifi food flask biyu ba, ba sai naga sai shigo da abinci ake yi, dariya abin ya bani ohh aliyu komai naka daban ne na faɗa arai na, bismillah naƴi wa nurses ɗin da kowa da kowa har ƴen uwana masu naƙuda da waɗanda suka haihu sai da suka sa albarka atakaice da ɗan karamar liyafa akai da safen nan





Sai ƙarfe takwasa sannan aka sallame ko da aliyu ya ga babyn har ƴar ƙwalla yayi tare da kissing ɗin babyn, San nan muka kama hanyar gida,muna komawa gida naga duk ma'aikatan gidan sun fito domin tarar mu, naji daɗin hakan da suka yi mana



ɗakina na wuce direct aliyu ɗauke da babyn ko da muka je zama nayi don bansan abin da zanyi ba, kallona yayi yace
"madam lfy ko" ya tambaye ni yana kashe min ido
"ba komai, kawai dai ban iya wankan baby bane"
"oh na ɗauka ma ko har kin fara missing ɗine ne, kar ki damu akwai wacce zata zo"


murmushi nayi masa nayi masa godiya nasan cikin *dangin sa* zai sa wata ta zo min, wataya ta na ɗauka na fara kira ina faɗawa mutane ga mamaki su khadija ma sun sani wai baba ne ya faɗa mu, na kira number mama ban samu ba nasan zata ce zata zo suna mama kenan na faɗa


aliyu ne ya ƙara shigowa ɗakin ɗauke da babyn kasancewar dama ya fita da shi don masu aiki su ganshi
"madam kin ga yaron nan kowa sai cewa yake yi kamar mu ɗaya" ya faɗa ya kallon babyn
"hmmm kawai suna faɗa ne amma ba abinda ya ɗauko naka,sai haske" saboda babyn fari ne sosai
"kina dai baƙin ciki, kin ga yaro jinin larabawa"
"yauwa hubbi, pls ka koya wa babyn nan namu larabci kaji"
"ce miki akayi na iya"
"ba balarabe bane kai"
"mahaifiyata ce balarabiyar saudiya, mahaifina baƙi ne kamar ki" ya faɗa yana lakuta min hanci
"baka girma da ita bane" na kuma jeho masa tambaya, don a gaskiya babu wanda na sani a *dangin sa* tunda muka yi aure sai tj kawai

Kissing lips ɗina yayi sannan yace
"ga lips ɗin nan naki da kyau gashi da tambaya, bari inje inga me akeyi a wajen nan" ya juya ya fice, aliyu ya iya waskewa idan baya son ansa tambaya


ban damu ba saboda yanzu nasan na haihu dole ƴen uwansa su zo suna, na faɗa a raina, daga dukkan alamu baya son magana akan *dangin sa* har ya kai ƙofar fita ya juyo
"wai yaushe zaki gama wannan abin naki ne"
"wane abu" na tambaye shi da mamaki
"ina nufin yaushe zaki warke, don insan kwana nawa zanyi ban same ki ba" ya faɗa yana kashe min ido



oh Allah ni abu yau Allah ya haɗa ni da miji ɗan world nafaɗa araina
"ko da yake ai akwai ƴen dabaru da zamu dinga yi ko,akwai darussa sosai da ya kamata ace kinyi degree akan su a harkar nan, amma ba komai tunda har lkcn yazo zamu fara darasin mu daga yau ba ɗaga kafa" fahinta yayi cewar duk kunya ce ta rufe ni yasa shi fita yana dariyar mugunta tare da cewa
"ki shirya darasin na yau na musammam ne"





Mama ce ta shigo tare da amina ƴar autar mu, mamaki ne ya kamani ganin ta kwatsam a gida na
"mama" na faɗa ina zare ido
"na'am me jego, kinyi mamakin ganin mu ko, ai mijinki yana kira da asuba yace kin haihu baban ku yace min in shirya, shine mijinki ya sa aka samu a jirgi"




murna ce ta kamani na kamo amina da naga tana noƙewa kamar bata saki jikin ta ba, na zaunar da ita kusa dani tare da ɗora mata babyn akan cinyar ta
"ga ɗanki" na faɗa
"au abin ma ɗan wariya ne" mama ta faɗa tana dariya



"mama bari ta ganshi sai ta baki, kin san abin jini" na mayar mata nima da raha
"to ai shike nan"
"bari insa a haɗa muku breakfast" Na faɗa ina fita don bada umarnin na a haɗa musu breakfast





naji daɗi zuwan mama sosai don gaskiya bata da son jiki ko kaɗan duk da dai ina da masu aiki baja baja amma hakan bai sa mamabata zama ko kaɗan, kwanana uku da haihuwa su khadija suka zo da maryam harda ƴaƴan mama wato su iyami da ƴen uwanta da yaran su, na fa gidan ya kuma cika, da daddare sai ga tj ne nan da matar sa ashe baya gari ne shiyasa bai zo ba ni kuwa nayi mamakon rashin ganin sa



ana jibi suna mama ta faɗwa wa aliyu cewar tana son kwatancen gidan don akwai masu tahowa saboda suna, sai yace duk su haɗu a gidan mu gobe da safe zai sa aɗauko su, ai kuwa haka akayi har gida ya sa aka kawo su




da daddare *dangin sa* suka ƙaraso na ɗauka zanga farar fata ko ɗaya ne amma ga mamakina duk baƙaƙe ne yen uwana, a zuciyata nace ko dangin uban sa ne



Sauka ta musammam akai musu inda aka basu ɗaki biyu don su sakata su wala, sai shirye shiryen suna akeyi ba kama hannun yaro, ƴen uwana da abokan arziƙi sin min kara sosai har mutan gezawa sai da na aika musu da kuɗin mota suka zo har ƴen uwan mahaifiyata sai da suka zo kasancewar duk ƴen gezawa ne, gida ya cika danƙam ba masaka tsinke sai shirye shiryen suna akeyi idan na kalli waɗannan ayawan mutanen na gano ceqar duk don ni suka zo sai inji wani daɗi ya lulluɓe ni nakan godewa Allah da ya bani ƴen uwa masu ƙaunata




kashegari muka tashi da sunan aliyu aliyu sani sunan mahaifin shi jariri yaci inda zamu dinga ce masa haidar, ansha hidima, ga ciye ciye ba kama hannun yaro munyi hotuna sosai don tarihi sai dai muce Allah ya raya mana haidar aliyu



kashegarin suna aka fara watsewa inda duk wacce zata tafi da tsarabar sunan ta a leda sannan a biki da kuɗin mota wanda aliyu ne wanda yanzu ya koma abu haidar ya ba mama cewa adinga sallamar baƙi da kuɗin mota kuma za a baka wanda zai kaika gida har da ɗan wanda zai rage




ranar labara mutan kano suka shirya tafiya wato *dangin sa* basu shirya da wuri ba don haka lkcn suka shigo ina banɗaki ina jin khadija tana ce musu ina banɗaki to bari miuj inda aka sauke mu mu jira ta



suna fita na fito daga wankan, zan shirya mama tace min insa hijabi na inje in sallame su ba daɗi jira, na ɗauko zunbululen hijabi na na saka sannan na kama hanyar ɗakin su don muyi sallama, ina shirin tura ƙofar ɗakin naji suna magana tare da kama sunan mijina don haka sai na dakata don in ɗan ji


"ke dai bari hauwa wallahi ko kaɗan baya kyautawa, dubi yadda ya bar *dangin sa* cikin ƙunci da talauci kamar ba abinda ya haɗa su, sai ma kinga ƙannen mahaifinsa da ke unguwar mu su da ƴaƴan su yadda kika san almajirai, wallahi babu wani abinda yake musu" ɗaya ta faɗa, wata ka ta kama
"rannan da naje jakarar gidan mu na shiga dan gaisawa da inna kakar tasa wallahi zanin jikin ta bazakiyi tsimma da shi ba saboda tsabar lalacewar da yayi, tsayawa kawai nayi ina kallon ikon Allah, nace a zuciyata wai jikan matar nan ne yake da maƙudan kuɗin da baisan iya adadin su ba amma jibi kayan da ke jikin ta don Allah"
"ke dai bari zulai nima abinshi yana bani mamaki kome sukayi maka ba sai ka haƙura ba, tunda ko ba komai yanzu ka fisu, Allah kinsan hauwa ko banɗaki basu da shi a gidan nan nasu, langa langa ce aka sa arufe wai shine bayi"





suka ci gaba da tattaunawa akan talaucin da ke tattare da *dangin sa* wanda sukw mamakin rashin kula sun da bayayi, jikina ne yayi sanyi na shiga ɗakin a sukwane, duk sai suka sha jinin jikin su




tsugunnawa nayi muka gaisa
"lfy naga me jego jiki ba ƙwari sai kace bakya shiga ruwan zafi" Inji ɗaya daga cikinsu kasancewar ba sanin su nayi ba yasa na kasa tantance waɗanda sukayi maganar da naji
"da zazzaɓi na tashi yau" na amsa ahankali don duk maganar da sukayi ta gama kashe min duk wani kuzari na jikina
"ayya dahuwar ƙashi ce, Allah ya sauwaƙe" amin na kuma ansawa a sanyaye duk sukai min Allah ya sauwaƙe sannan mukai sallama da su na tafi zuciyata cike da tunanin ta me kenan ya ke faruwa tsakanin mijina da *DANGIN SA*
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN

12 / 33