Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
yadda hjy batai ba na ya dinga zuwa yana gaida iya amma da kyar yake zuwa tabbas tasan iyar ce take zagin amma kuma ya zata yi jikan ta ne ta zama dolen sa
ganin hakan ne yasa idan hjy zatayi alala aliyu ne me kai markaɗe gidan iya, kuma kullum yaje da zagin da zai sha wajen iyar kafin tayi masa markaɗe
takan zage masa uwa tas, wai ta yada shi ta tafi yawon karuwanci, yakanyi mamaki wacece wannan uwar tasa kuma meye ya haɗa ta da iyar haka da har ta tsane ta kuma tsanar ta shafe haka
kamar kullum yau ma hjy ta aiki aliyu ya kai markaɗe yana fitowa daga gidan sai yaci karo da wani ɗan maƙocinsu bala da ƙanin sa
"alin hjy ina zaka" bala ya tambaya
"zan shiga gidan iya in kai markaɗe ne"
"iya bala'i zaka ce, kai baka gajiya kullum ka shiga gidan matar na sai ta zage ka, kuma ka kasa faɗawa hjy ta dai na aiken ka"
murmushi aliyun yayi be ce komai ba
"kawo ina habu ƙanina ya kai yau ka huta da zagi" kamar aliyu ya ƙi amma sai ya ba habun ganin cewar ai markaɗe ne kawai
"zo muje ka raka ni wani wuri" inji bala ya faɗa yana jan hannun aliyu
"zan taya hjy aikin alalan ta"
"ai ba daɗewa zamuyi ba zan koya wa wani yaro hankali ne" ya faɗa yana jan hannu aliyu wanda shi kuma ya bishi zingwi zingwi ba tare da ya sake yi masa musu ba
sun ɗan yi tafiya sai ya ga balan ya tsaya ya laɓe a ƙofar wani gida shima sai ya biye masa, wani yaro ne ya fito daga wani gida dake ƙasan layin, ko da yaron ya matso kusa da su sai bala ya ɗauko wani dutse ya jefi yaron da shi sannan ya ruga a guje, shi kuma aliyu sai ya tsaya yana kallon ikon Allah
ko da ya ga jini a goshi yaron ga kuma mutane sun fara taruwa sai shima ya ruga a gujen, yana jin wani yana cewa alin hjy ne ya jefe shi gashi can yana gudu
shidai tun daya samu ya tsere kawai sai yayi filin ƙwallo don yasan dole za a je gidan su neman shi, to idan suka je basu ganshi ba ai dole su haƙura ya faɗa, sai bayan la'asar sannan ya kama hanyar gida yasan yanzu ƙurar ta lafa ya faɗa aranshi yasan yau sai hjy tayi masa faɗan zuwa yawo ya faɗa yana kama hanya
yana shawo kwanar gidan nasu yaga ƙofar gidan cike daƙam da mata da yara sai zage zage suke yi, ko da ya lura sosai sai yaga ƴaƴan hjy ne sai mutan gidan iya da ita kanta iyar to me ya faru ya faɗa
ko da idon su ya kai kanshi da gudu aka je aka kamo shi kamar wanda yayi sata kowa yana masa tofin Allah tsine, babbar ƴar hjy wato hauwa itace taiyi masa mari a dukkan kumatun sa guda huɗu ƙwarara
nan suka hau dukan sa wai duk abinda uwarsu tayi masa sakayyar da zai mata kenan, gaba ki ɗaya duk cikon taron wurin nan daga me dukan shi sai me zagin sa, shi ko kaɗan be ma san abin da yayi ba
zagin sa da suka dingayi na tsintacciyar mage itace ta fi ƙona masa rai, duk cikin gurin nan babu me ƙaunar sa, to me yayi musu tabbas tun taso war sa yasan shi ba irin su don shi kana ganin sa kaga balaraben asali fari ne kyakkyawan gaske ga gashi irin na larabawa, ga baƙi ga kyau da sheƙi don ma baya samun kulawar da ta dace shi
tun tasowar sa yake fuskantar kyara da tsangwama su kansu ƴaƴan hjyr a gaban idon ta ne suke nuna suna sonsa amma da babu ita a wuri shike nan shi tashi ta kaɗe, ya rasa me yayi musu me mahaifiyar shi tayi musu me yasa suka tsane shi haka, shi bama sanin mahaifiyar tashin yayi ba amma kullum sai ya sha zagi da tsinuwa sabida ita wai me mahaifiyar shi tayi ne haka da muni da har abin yanzu ya dawo kansa
duk wannan dukan da suke yi masa da zagin nan idon ƙamas yake ba hawaye, sai dai zuciyar sa da ke bugawa tana wani karta masa kamar ana soka masa allura acikin ta, ƙirjin sa kawai ya kama tare da tsugunnawa ƙasa ganin halin da yake ciki be sa sun fasa zagin sa ba sai ci gaba da yi masa gorin hjyr su tayi masa shi kuma da yake tsintacciyar mage ne bata mage sai ya saka mata da wannan
Iya ce ta ɗauka kun manta yadda uwar sa ta kashe min ɗan ran da ya dawo, haka ne iya uwar sa ta lashe kurwar sani don kince ba ki yadda da auren su ba, nan suka fara caccakar mahaifiyata tare da bin ta da munanan addua
kun san ai munmunar ƙaddara ce take bibiyar sa tun haihuwar sa me zai hana duk wanda yake tare da ta shafe shi, inji iya
to wallahi ƙaryar ka mummunar ƙaddara ka baza ta faɗa akan uwar mu shekara goma sha uku hjyr mu tana ta ɗawainiya da kai uwar da ta haifeka ma tun da ta yar da kai ta gudu bata kuma waiwayar ka ba saboda ƙaddarar ka to wallahi tun wuri ka kama gabanka kasan inda dare yi ma don babu abinda ya haɗa mu da kai taimako ne sai ka jefa mana uwa cikin bala'i
to wai wacece mahaifiyata me ya haɗa ta iya da har ta kashe mata ɗa ina kuma hjy tayi me yasame ta ya faɗa a ransa gaskiya doƙe ya bar gidan nan ya bar mutanen tun da sun fito ƙiri ƙiri sun nuna masa basa ƙaunar sa kuma yana gudun kar munmunar ƙaddarar sa ta shafi hjyrsa macen da tafi kowa son sa da tausaya masa hjy ina kika shige nedon yasan inda tana nan basu isa suyi masa wannan cin kashin ba
[7:45PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*wannan page ɗin naku readers ɗin DANGIN SA na sadaukar da shi kacokam ɗinsa gare ku* 😁😁😁😁
page :33🌹
Gajiya sukayi da zazzaga masa bala'in sannan suka kama hanya ko ina zasu oh, na dai ji hauwa tana cewa ku zo muje muga uwar tamu mu ƙyale wannan tsintacciyar magen,
Kafin kace me duk an watse an barni a durƙushe riƙe da ƙirjina wanda zuciyata take bugawa kamar zata tsaga ƙashin ribs ɗina ta fito
tashi nayi don dole ne inje inji me ya samu hjyr, yana shiga gidan a tsakar gida ya tarar da tj yana ta sharɓar kukan sada sauri ya ƙaras kusa da ɗan uwan nasa
"ɗan uwa me ya same ka" ya tambaya yana dafa shi, jin muryar aliyu yasa tj ɗago da kansa tare da kallon aliyun
"ɗan uwa me su aunty hauwa suka yi maka" ya tambaye ni
"babu abinda suka yi min, ina hjyr take"
"ƴen sanda sunzo sun tafi da ita wai ka fasa wa wani kai"
aliyu be sain lkcn da yayi baya yai zaman daɓaro ba, oho sai yanzu ya fahimci dalilin daya sa su aunty hauwa yi masa haka, wai an kama hjy, to ai shi yayi ba
ya kalli tj wanda har yanzu yake shash sheƙar kukan sa
"wane police station aka kai ta"
"nima ban sani ba, amma tace idan ka dawo ka jira ta kar ka fita" gyaɗa kai kawai nayi
wato koda da tana cikin wannan halin amma ta damu da shi wayyo hjy wallahi bani nayi ba, kuka nake son yi sosai amma na kasa don idona a soye yake, sai zuciyata da ke ta bugawa da ƙarfi da kuma sauri kamar nayi gudu
haka muka zauna zaman jiran gawon shanu, hjy sai da akayi magariba sannan sai gata da ƴaƴan ta, tana ganina ta yo kaina tare da tambayar "kaci abinci kuwa" gyaɗa mata kai kawai nayi duk da dai banci komai ba amma ko kaɗan bana ji yunwa
"ya naji jikin ka zafi baka da lfy ne" ta kuma tambaya
"wallahi hjy bani na jefe shi bala ne"
"haba alina ko ba wanda zai shede ka ni zan shaide ka nasan ba kai kayi, ka kwantar da hankalin ka ba abinda akai min asibiti kawai na kai yaron" ta faɗa tana ƙara jawo ni jikin ta, wanda ni kƴma na lefe nayi luf da ni, gaskiya ina ƙaunar matar nan har cikin rai na
ƙiri ƙiri ƴaƴan ta suka nuna ya kamata tayi min faɗa nan ta hau su da faɗan babu ruwan su, ba yadda suka iya haka suka haƙura sai dai saƙon harara da suka dinga aiko min da shi
Sai da na kwanta jinya har na kwana uku kasancewar ƙirjin nawa ya saukar min da zazzaɓi me zafi, tare da ciwon kai hjy ta ɗauka zazzaɓin ne kawai don haka sai tayi ta dura min maganin malaria
aikuwa cikin ikon Allah na ɗan samu sauƙi don ita ma zuciyar ta ɗan rage dukan da take min, ko da naga na ɗan warwaresai na shirya barin gidan, don gwanda in bar gidan nan kar mummunar ƙaddara ta ta shafi hjy da tj mutanen da suke ƙaunata
da safe bayan na gama komai nayi sallama da hjy akan na tafi in gaida iya, hjy tai murna har tana samin albarka, ina kallon hjy ina jin zuciya ba daɗi idan na tune cewar baza ta kuma ganina ba
naira hamsin ce kawai a aljihuna, tun da na fita nake gararan ba na in shiga nan in fita nan har dare yayi min sannan na samu mkrt almajirai na lafe a cikin su nai bacci na
duk da ba wani baccin kirki nayi ba ni da saba bacci a lafiyayyar katifa amma wai yau nine kwance a dandamaryar ƙasa, hana kaina kuka nayi gwanda inyi wannan rayuwar da inyi rayuwar jin daɗi bayan hjy kullum zata dinga fuskantar ƙalu bale saboda ƙaddara ta haka har bacci ya kwashe ni ina tunanina
kashegari da sassafe na tashi na kama gabana tun kafin su fahinci cewar ni ba a cikin su nake ba, haka na dinga yawo kwararo kwararo inna gaji in samu inuwa in lafe inna huta in ci gaba da tafiya inna ji yunwa in tsaya inyi bara har sai na ƙoshi sannan in ci gaba
haka na ci gaba da rayuwa ta har na kwashe wata shida ni ba almajiri ba ni ba ɗa ba in kin ganni a lkcn baza kice nine alin hjy ba don na canza sosai, acikin yawace yawacen nawa ne na haɗu da wani almajiri me suna shapiu, ɗan katsina ne bbn shi ya kawo shi almajiranci amma da malam ya ishe shi da duka sai shima ya tsere, shine muke gararan bar tare
shapiu ya girme ni sosai don haka ya fini wayo nine me barar shi kuma yana zaune sai dai in samo in kawo mana sannan muci tare
rannan yawon mu ya kaimu ƴen kaba kasuwar kayan miya, ana ta loda kayan miya cikin motoci suna fita da shi zuwa garuruwa, abin yabi sha'awa nan nan nima na shiga loda kaya cikin mota, ko da muka gama sai aka bani naira 100
wannan kuɗin da aka bani ba ƙaramin daɗin su naji ba, sai na fara loda kaya a duk motar da tazo domin lodi ina samun kuɗi shi kuma shapiu ba abinda yake daga yaje wacce inuwar ya zauna sai ya je ya nemi wannan majalisar ya zauna ayi hira da shi nine me neman kuɗin
in kaga ya nemi ni to yaki yunwa haka zaizo yana min ƴar murya ni kuma bana iya hana shi ganin kamar shi kaɗai ne ya sanni don haka ina yi masa kallon ɗan uwana, idan kuwa na bashi bana kuma ganin shi sai ya ƙara jin wata yunwar
watan mu uku a kasuwar ƴen kaba shapiu ya kawo shawarar mu tafi lagos wai anfi samun kuɗi a can banyi wata wata ba muka kama hanyar lagos a cikin wata motar kayan miya, tafiyar da ta canza min rayuwata tafiyar da ta maidani abinda nake yanzu.
ayi hakuri da wannan yau na tashi ɗan jariri na walid ba lfy don Allah ku sa a addua 🙏🏻
[7:45PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*ga gode sosai da adduar ku gare ɗana ya ku masoyan dangin sa Allah ya barmu tare ya samu sauki Allah ya saka*
Page:34🌹
Hjy ce zaune a fali ta zuba uban tagumi tana tunanin rayuwa, yanzu aliyu a doshi shekara da ɓata ba shi babu lbrn sa, ta tuna lkcn da ya ɓata da taga har dare be dawo ba kuma tasan be saba yawo ta shiga neman sa
Babu inda basu ba shi ba ita da tj, inda tj ɗin ba abinda yake yi in banda kukan ɗan uwansa itama hjyr daurewa kawai take yi
daga ƙarshe suka biya gidan iyacigiyar sa duk da hjyr tasan bazai taɓa zama a gidan ba amma dai ance in kana neman raƙumin ka ko cikin tandu sai ka duba
nan iya ta kwashe lbrn abinda ƴƴan hjyr sukayi wa aliyun randa aka kulle ta police station tas ta faɗa wa hjyr, wai hjyr tana riƙe da shege bayan ƴaƴan da ta haifa basa son sa
Hjy rasa bakin magana tayi haka ta dawo gida jikin ta a sanyaye, a daren har kuka tayi tai sallah sosai ta roƙo Allah ya kare mata shi duk inda yake, kashegari ta kira ƴaƴan nata bayan sun zo ta wankesu tas da soso da sabulu sannan tai musu albishirin aliyun ya gudu don haka sai kawaccen su hankalin ta ya kwanta
haƙuri suka fara bawa hjyr nasiha tai musu sannan tace su kuma san da cewar duk wani abinda ya samu yaronnan mara kyau su san da cewar da kamashon su a ciki
kowacce sai jikinta yai sanyi bayan hjyr ta gama yi musu kuma ta patattake su, haka ta zauna ta dinga bin aliyu da addua kullum bata fasawa kuma bata mantawa,
****************
mun sauka lfy a garin *yanki* inji mazauna can, directly kasuwar idi yaraba muka wuce acan muka sauka na fara harkar dako, to rayuwar a lagos ba kamar kano bane, komai da sauƙi, don haka ni da shapiu kowa tasa ta fish she shi mukeyi
Wasu ƴen area boys yake bi babu yadda banyi da shi akan mu nemi abinda ya kawo mu wato bugun abuja amma ƙiri ƙiri sai ya nuna min shi ba sune a gaban sa ba babu yadda na iya shi haka na ƙyale shi, tun yana ɗan zuwa harbya koma ma sai in shafe qata bangan shi ba, a haka tarayyar mu da shapiu ta watse
Aikin da nakeyi na ɗaukar kaya sai kai kaya wurare ba ƙaramin samun kuɗi nake yiba kuma bayan abinci ba abinda nake siya tarawa kawai nakeyi don inyi wa hjyta siyayya
yau kusan watana bakwai a lagos kuma ba laifi na waye sosai na san gari kuma na san harka kama kuɗi nake yi dai dai aikina, akwai wani wai shi umar tare muke aikin mu da shi shima ɗan kano ne amma ɗan kurna da iyalen sa akano
ina son zama da umar sosai ko ba komai idan yana hirar iyalin sa sai inji kamar ina gida, rannan katsaham sai gashi wai gida zashi yayi kewar iyalinsa, kawai nima sai naji hjy ta faɗo min rai, gaskiya ban kyauta yau kusan shekara ɗaya kenan da wani abin da guduwata amma ban taɓa leƙa ta ba kuma nasan tabbas hankalinta ba a kwance yake ba
duk dani ma kullum suna raina ita da tj wanda wani lkcn tsabar tunanin su take sawa inji zuciyata na buga min tare da min wani azababben ciwo gaskiya dole ne inje inga hjyta na faɗa araina
Umar na samu na faɗa masa nima ina da ra'ayin zuwa kanon yai murna tare da min nasihar in dinga kula da iyayena barin idan