Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
basu da hali sosai
kuɗin da hannuna na haɗa muka tafi kasuwa nida umar, siyayya sosai mukayi, buhun taliyar nan irin ta damage na campany guda biyu, sai jan wake na san hjy ta na son sa, akwai wata madara da ake siyar wa daɗi gare ta, da bourntiva ɗinta a haɗe kawai sugar zaka sa sai ka haɗa shayi,botikin penti biyu na siyo sannan na samu gwangwani manya manya na madara na juye su a ciki, su hjy su sha shayi mu more,
sai kayan gwanjo masu kyau da sai wa tj, ita kuma hjy na sai masa lesis masu kyau guda uku marasa nauyi
muka kamo hanyar kano, a hanya ne na dinga ba umar lbrin abinda na sani game da rayuwata da dalilin guduwata, ya tausaya min sosai daga nan bai kuma cewa komai ba
mun tsaya a hanya muka sai doya da manja, tj kawai na hango don masoyin doya ne, a kura muka tsaya muka sai shinkafa ƴar hausa me kyau, ta dafawa da ta tuwo sai gero, sannan muka ƙaraso cikin garin kano
munyi siyayya kamar ba gobe barin ma niduk abinda na gani sai na siya, don haka muna sauka kano muka ɗau akori kura sai kurna gidan umar muka sauka don nace masa bazan je gidan hjy ba sai dai in masa kwatance
kasancewar da safe muka sauka sai da muka huta sannan da yamma muka kama hanyar gidan hjy don so nakeyi a ranar in koma lagos ɗin
taxi muka ɗauka aka loda mana kayan nawa har layin da za a shiga gidan hjy sannan muka sauka muka samu almajirai suka ɗau kayan, nai masa kwatancen gidan sosai sannan nabi bayan shi don in laɓe don ina son ganin hjyta sosai
dubu biyar na bashi tare da wasiƙar kwantar mata da hankali tare da nuna mata inanan lfy wacce na rubutata tun a lagos, sai hotunana guda biya, a ƙofar gidan ya tsaya ya doka sallama
hjyr ce da kanta ta fito sanye da hijabin ta tana nan yadda na barta Allah sarki hjyta na faɗa araina, sun daɗe suna magana tare da hjyr inda daga baya ya miƙa mata envelope ɗin da wasiƙar tawa da pics ɗin wa suke ciki
Hjy tana karantawa tana hawaye ni kaina sai ta bani tausayii amma dole ne inyi haka in tashi don in gina kaina don kuwa bani da gata bani da me yi min don haka dole in san in da dare yayi min, sukayi sallama bayan ya sa an kwashe mata kayan an shigar mata da su ciki
koda muka haɗu sai dinga min faɗan in koma hjy tayi kewa ta sosai tooo kawai nace masa mukayi sallama sanna na kama hanyar tashar sabon gari don komawa neman kuɗina
na koma lagos na ci gaba da neman na kaina, duk wani burina yanzu akan hjy yake da tj, duk wani abu idan na samu sai in tura kano umar sai ya tura ƙaninsa ya kai musu, bama waya amma muna musayar wasiƙu musamman ma tj, duk abinda yake so in dai ya faɗa min sai na siya na aika masa ita kuma hjy babu komai a wasiƙar ta sai nasiha da adduar kullum in zama me gaskiya tare da neman halal kawai
***************
hjy tana zaune tana girki taliya take dafa wa wacce taji kayan miya tare da nama, zuƙu zuƙu tana tunanin rayuwa yanzu komai sun fi ƙarfin sa in dai ta ɓangaren sutura ne da abinci to sai dai ta bawa wani, sallamar da aka doka ce ta katse mata tunanin ta, tashi tayi ta ɗan leƙa sai ta ci karo da nasiru ƙanin umar, ga kayan abincin nan buhu buhu a kusa da shi
bayan sun gaisa ya bata kayan ya kama hanyar sa har kuɗi ta bashi amma ƙiri ƙiri ya ƙi karɓa, haka ta sa aka shigo mata da kayan nan ko waɗan da ya aiko musu da shi wancen watan bai ƙare ba ko rabi basu ci ba amma wai yau gashi yanzu ya kuma aiko musu da wani kamar bai san ciwon kuɗin sa ba
shawara ce ta faɗo mata sai ta raba kayan biyu tasa yara suka ɗaukar mata rabi sai gidan iyababu abinda ba ta ɗibarwa iyar ba harda kuɗi dubu uku
iya ganin ana ta shigo da kaya ɗakin ta yasa ta sakin bakin tana mamakin waye, ganin hjy ya sata ƙara mamaki har da ƴar fara'ar ta rabon da hjy taga fara'ar iya har ta manta
bayan sun gaisa hjy tai wa iyar bayanin irin hidimar da aliyun yake musu sannan tace mata gashinan na raba kayan biyu na kawo miki rabi kema kici arziƙin jikan ki duk da dai kince ba jininki jininki bane amma kowa ya san jinin ki, don haka gashi kema kici arziƙin jikan ki
hjy ta ɗauka iyar zatai bala'in ta da ta saba amma ga mamakin ta sai taji iyar tana bin aliyun da adduar Allah ya kare shi duk inda yake , hjyr sai ta ɓoye mamakin ta tare da ansawa iyar da amin sukayi sallama a mutunce hjyr ta kama hanyar gida cike da mamakin canzawar da iyar tayi
[7:45PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺U☺☺☺☺☺☺☺
page:36🌹
Haka na ci gaba da neman kuɗi tare da turawa hjy duk wani kuɗin daya zo hannuna, ban damu ba idan na zauna banni da ko sisi in dai na tabbatar da cewar gidan hjy akwai abinci to bazan damu ba
Shekara ta biyu a idi yaraba sannan Allah ya haɗa ni da wani bayarabe wai shi balogun, yakan zo kasuwar mu, a haka shaƙuwa ta shiga tsakanin mu, ko da muka shaku sosai sai ya yi min tayin wai in zo in fara aiki da shi a deport, ban wani dogon tunanin ba na bishi a lkcn umar yana kano don haka babu wanda inda na koma
Aiki a deport yana wuya amma kuma samun kuɗin da ake yi a can bama za a haɗa da idi yaraba ba, don haka kan a ce wannan na tara kuɗi ba kaɗan ba
Watana uku a deport na tara kuɗin da ni kaina ban san cewar zan same su ba, kuma har yanzu ban kuma neman umar ba, ranar wata talata ana saura sati biyu a fara azimi na shirya zuwa ganin umar don in aikawa da hjy kayan azimi, don in shaa Allah azimin bana hjy sai ta shana
bayan mun gama aikin mu na shirya sai idi yaraba, umar yai murna sosai da ganina tare da faɗa min yadda hankalin hjy ya tashi da taji lbrin ya bar idi yaraban, nan ya faɗawa umar sana'ar da ya koma yi a deport, ɗin
Umar ya jinjina wa aliyun yaro ne ɗan ƙarami amma Allah ya bashi zuciyar nema, komai wahala yanzu me ya kai aikin deport wahala, akwai samun kuɗi amma akwai wahala kuma, da kaya sun zo daga waje ko cikin dare ne dole ku fito ku kwashe tare da loda su a cikin motacin da zasu kai garuruwa, haka in kaya suka tashi a fitar da su daga nan, nan masai sun kwashe sun loda
sai ayi kusan sati a kan jirgi ɗaya ana kwashe odar daya yo, ya danganta da irin girman jirgin amma wai ita wannan sana'ar ɗan ƙaramin yaron nan yake yi gaskiya Allah ya bashi zuciya
Kasuwa ya rakani ni kaina bansan irin ɓarnar kuɗin da nayiwa hjyta ba amma gaskiya kaya na siya mata kamar za a buɗe wani ƙaramin kanti, shi kanshi umar ɗin sai dana yi masa siyayyan kayan abinci sannan na haɗa don turawa kano
amma sai umar yace in barshi kawai zai kai mana dama shima yana son idan ya samu kuɗi yai siyayyar kayan abinci zai je gida yayi azimi acan amma yanzu tunda na taimake shi gwanda kawai ya gudu
naji daɗi sosai ganin umar zaije kano da kanshi, na bashi kuɗi wanda zai ƙrasawa hjy siyayyar ta acan, irin su ƙwai, dankalin turawa gero, da dai sauran abinda baza siya anan ba
mukai sallamr da niyyar bayan sallah idan ya dawo zan shigo, shi kuma umar ya samu mota guda ya loda kayan na sai kano, direct gidan hjy ya fara zuwa ya sauke mata kayan da ya zo mata su, hjy kasa shiru tayi don duk ta tsorata da irin iyayen kayan da umar ya jibge mata tare da bata kuɗi har dubu ɗari
"umar ni kuwa yaron nan yanzu sana'ar me yake yi"ta tambaya, umar yai mata bayani irin aikin da aliyun yake yi da kuma wahalar da ke tattare da aikin
dukda dai hjy ta tausaya wa aliyun amma hakan bai hana ta tambayar umar ɗin ba
"yanzu kana tunani zai iya samun wannan dukiyar"
"kai hjy abinda yafi haka a sai ya samu"
ya bata ansa sai da umar ya kwantar w da hjy hankali akan aliyu sannan shima ya kama hanyar gidan shi cike da siyayyar da aliyun yayi masa wanda zai ishe shi da iyalen sa har a gama azimi
hjy kamar yadda ta saba wannan karon si ta raba shi kashi uku don gaskiya kayan abincin ka kaɗan bane shi kanshi buhun shinkafa sai da ya aiko mata da buhu takwas banda kwalayen taliya, buhu biyu ta aikawa da iya tare da ragowar kayan abincin da aliyu ya aiko mata
sannan ta aika wa da ƴaƴanta kashi ɗayar ita kuma ta ajiye kashi ɗaya, da daddare iya da kanta ta shigo don yin godiya inda hjyr tace mata ai nima arziƙinki nake ci, ta faɗa tun da dai duk abuna jikan ki, iya sai washe baki tare da faɗin haka ne
iya takanas ta gayyato ƴaƴanta wai suzo su ga abinda jikanta ya aiko mata, kowa ya tamayi wane jikan idan iyar tace aliyu sai kaji anacewa iya dama kina da jika aliyu ne, sai kaga iya tana zazzare ido ba damar ansawa
ita kanta hjyr sai da ta gorantawa ƴaƴan ta da suka zo mata godiyar kayan da ta aika musu, tace to me mummunar ƙaddara ce ya aiko min sai jikin kowacce yayi sanyi, sai yanzu suke danasanin abinda sukai yi wa bawan Allahn nan da sun san haka Allah zai buɗa masa cikin ɗan kanƙanin, duk sai kunya ta kama su lallai basu kyauta ba
**************
haka aliyu ya cigaba da neman sa , ba dare ba rana kusan duk dwport ɗinnan an san shi saboda kwazon sa da kuma aiki tsakani da Allah don haka kafin kace me, har ya taka matsayin da bai taɓa tunani zuwa nan kusa ba
***************
*bayan shekara biyar*
yanzu aliyu ya zama babba kuma me faɗa aji a deport ɗinnan ya tara kuɗi ba kaɗan duk wannan abinda ya keyi bai sa shi mantawa da hjyr sa ba yanzu shi ba yaro bane, yara gare shi kusan duk wani jirgi da zai shigo nigeria aliyu ya san da zuwan sa sannan yaran sa ne masƴ aikin sauke kaya, duk da ƙanƙantar shekarun sa hakan baisa waɗanda ke ƙasan sun raina shi ba, don duk girman ba zai ɗauki raini daga gare ka don kawai ka girme shi, sannan shi mutum ne da baya son son jiki aiki kawai, ko kayi ko kuma ka nemi wani ubangidan hakan ne yasa yaran sa sukai fice, aikin sa yake da biyan buƙata ba tare da ɓata lkc ba
wannan dalilin ne ya sa aliyun yai fice kuma ya zaman yana ɗaya daga cikin abokanan harkar tasu ya kasance shine babba, duk da ƙanƙantar shekarun sa
akwai wani alh tahir bala ɗan siyasa ne kuma ya kasance yana da jiragen ruwan kuma companyn aliyu ne suke kwashe masa kaya indai jiragen sa sun ƙaraso
ko da lkcn zaɓe ya zo sai ya nemi aliyun da ya bashi aron kuɗi domin yin canfen amma sai aliyun yai using wannan oppurtunity ɗin sai yace wa alh tahir bala ɗin ya sai da masa da jirgin sa guda ɗaya,
alh tahir ɗin yai ta faɗa tare da banbami sannan yai gaba, ko da yaje ta ƙure masa haka ya dawo dolen sa ya siyarwa da aliyun jurginsa guda ɗaya don kawaibya rabar da kuɗin ga mutane don ya samu kujera
wannan jirgin da aliyu shine yai asalin silar arziƙin aliyun inda da wannan jirgin ya mallaki jirage masu yawa da girman gaske, don kuwa ahalin yanzu ba inda jiragen sa basa zuwa ba don ɗauko kaya ko kuma kai kaya wannan dalilin ne yasa shi fara fantamawa, ba ma shi kaɗai ba hatta hjy yanzu sai dai tayi kyauta ba ita kaɗai dai dai da ƴaƴanta yanzu sun zama wasu har iya itama ba a barta abaya ba, har bawa mutane labari take yi wai jikan ta ne wanda hjy ta riƙe saboda ɗan saɓanin da suka samu da mahaifiyarsadon Allah kunji faa🤔🤔
aliyu ya kai hjy hajj da umma ba sau ɗaya ba inda yanzu umar ya bar lagos ya koma kano yana kula da dukiyar aliyu da ke kano don yanzu sun zama ƴen uwa duk abinda ya faru a gidan umar hjy tana zuwa har ƴa gare umar me sunan hjy saboda tsabar jin daɗin zaman tare, tj ma yanzu sai fantamar sa yake yi ya zama ɗan gaye karatun sa kawai yake yi babu kama hannun yaro
aliyu ne ya siyawa hjy gida dan karere a unguwar sharada sannan ya sa suka tashi suak tare acan inda aka sha shagali babu kama hannun yaro
sai da hjy ta koma sharaɗa sannan aliyu ya zo ta ganshi da farko bata gane ba amma kuma daga baya sai ta gano shi don yanzu ya zama aliyu ɗan balarabiya fari tas da shi ga kyau ga cikar zati
an sha ƴen koke z kafin daga bisani aka fara hirar yaushe gamo aliyu ya bata lbrn irin gwagwarmayar daya sha da irin wahalar daya sha amma da yake ɗan halak ne sam bai ambato mata irin cin fuskar da ƴaƴanta sukai masa ba hjy har kunyar sa take ji amma ta kasa cewa komai don yanzu babu abinda bai yi ƴaƴanta ba babu wacce be kai hajji ba
hjy ce ta tashi taje ta ɗauko masa wata ƴar jaka ta bashi buɗewa yayi ya ga wasu hotuna ne, nan hajiya ta zayyano masa tarihin rayuwar sa da alaƙar da ta haɗa da iya da yadda mahaifiyar sa ta tafi ranar da
ji yayi duniyar gabaki ɗayan ta tayi masa zafi ya rasa abinda yake masa daɗi ya ji ya tsani iyar da duk wani wanda ya shefeta har da ita mahaifiyar tashin da ta tafi ta barshi acikin tsumma bayan tasan wace irin rayuwa zaiyi ba
zuciyar shi ce tavfara wannan bugawar da take yi na rashin saiti ba abinda take masa sai, ba abinda yake ji sai jiri da ganin dishi dishi yanajin hjy tana bashi bakin wai ya haƙura ya rungumi *dangin sa* ba bu abinda yake yi daya wuce gyaɗa kai kamar yana fahimta
tashi yayi yace hjy bari inje sai anjima, to kawai tace yai hanyar waje tj ne ya bishi hjy ta kira shi tace mai ya ƙyale aliyun har sai ya sauko, mota kawai ya shiga ya sa driver ɗinshi ya kaishi hotel ɗin daya sauka don yana buƙatar zama shi kaɗai ko ya samu yayi tunani
kwanan shi uku a rufe a ɗakin daya sauka babu abinda yakeyi banda kuka me yayi wa mahaifiyar shi da zata wurgar da ɗan data haifa ta gudu in iya ta ƙishi ita sai ta kishi kuma tun randa ta tafi bata kuma waiwayar sa ba, ya za ayi ya iya yafewa mutanen nan daga mahaifiyar tasa har iyar bayan a dalilin su ne yasa shi yin ƙuruciyar sa cikin,ƙunci, tsangwana da gori shi bai taɓa more wani abuwai kuruciya ba a wajen hjy da tj ne kawai yake samun sassauci babu ni babu su, ya faɗa da ƙarfi
bugawar da zuciyar sa ke yi ga wani azababben ciwo da takeyi ne ya fara wuce ka'ida don yanzu numfashin sa ma da ƙyar ya ke iya fitar da shi ga zazzabi ya rufe shi ruf da ƙyar ya lalubi wayar sa ya kira pa ɗinsa akan ya zo ya kai shi asibiti yai masa kwatancen hotel ɗin da yake
yana gama wa yaji kamar an caka masa wani abu a zuciyar sa tuni ya fara neman nunfashinsa wanda yake ji kamar