Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :23🌹
Ko da na koma ɗakina kasa shiryawa nayi duk zancen su sai nake jin sa kamar yanzu akayi shi sai dawo min yake yi yana min yawo a ƙwaƙwalwata, ga shi bana son faɗawa kowa saboda wannan kamar sirri ne day kamata in ɓoye tunda ya shafi mijina kuma ba abin alkhairi bane, khadija ce ta shigo ta ganni zaune ba tare da nasa kaya ba
"tooo me jego a zaune yai ba kaya a jikin ta" ta faɗa tana kama bakin ta
"kodai jikin ne" girgiza mata kai nayi
"ai kuwa ya kamata ki sa kaya a jikin ki don kar sanyi ya kama ki, muje in taya ki zaɓar kayan don yau naga gaba ɗayan ki bakya jin daɗi" closet ɗin muka tashi muka nufa, nidai tafiya kawai nake yi amma jikina gabaɗaya a mace yake na rasa abinda yake min daɗi
Wata jar shadda ta ɗauko min ɗinkin bubu sabuwa dal
"karɓi saka wannan" ta faɗa tana miƙo min,
"khadija ina mama" na tambaye ta
"tana can wajen rabon kayan suna kinsan duk yau za a watse, itama wannan ƴar iskar tana can, sun tasa kaya a gaba suna ta rabo, sukan duk waɗanda take mutunci da su da basu samu daman zuwa ba ta ɗiban musu, har da maƙotan ta, kinji ƴar iska" murmushi nayi maryam ai yadda kasan mama ce ta haifa ta wajen shishshigi da rawar kai haka take
"wani abu naji daga bakon ƴen uwan aliyu da suka zo ya tsaya min a rai" dawowa tayi kusa dani ta zauna tare da zare min ido menene
tas na kwashe abin da naji na faɗa mata ba tare da na ɓoye komai ba,
"haba biri yayi kama da mutum, nan mama take cewa ita fa bata ga wani abinda ya nuna alamar cewa waɗannan da suka zo suna sun haɗa wani abun da mijinki ba, shi fari tas kana ganin shi ka ga balarabe su kuwa ko ni nan na fi su haske" ta faɗa tana kallon hannun ta
"mahaifin shi baƙi ne kamar ki, na ɗauka dangin mahaifinsa ne tunda yace mmn shi basaudiyace"
"to ina iyayensa suke" shiru nayi don tunda nake ban taɓa tanbayar sa ba hasalima daga gani baya son a dinga yi masa zancen *dangin sa*
"ina tunanin sun rasu koo don tunda nake da shi bai taɓa cewa ga inda suke ba, to kinga ƙila sun rasun" na faɗa ina kallon ta
"ba shakka ƙila sun, sannan shi kuma ya tashi a wurin *dangin sa* inda suka yi masa ƙila ruƙon sakaynar kashi ina jin shi yasa shima daya girma ya watsar da su" khadija ta faɗa tana mai jinjina kanta alamar gaskata abinda ta faɗa
haka muka zauna muna ta tattaunawa akan abinda yasa aliyu ya daina kula da *dangin sa* amma har muka ƙare zancen namu bamu samu wani ƙwaƙƙwaran dalili ba
"kinga ance waƙa a bakin me ita tafi daɗi, ki bari idan aka watse si tambaye shi hankali akwance ƙila yai miki bayani ya fi wannan shaci faɗin da muke tayi" khadija ta faɗa tana me ƙoƙarin kauda mana da zargin da muke, don kar muje mu zargi bayin Allah waɗanda basuji ba basu gani ba,
"hakan zanyi ya na iya, amma ya zama dole in san me yasaijina ya ke wulaƙanta *dangin sa* baya taimaka musu ya barsu suke rayuwa kamar almajirai"
"hmmm Allah dai ya kyauta kar kiyi saurin yanke hukunci baki san me ya faru ba"
"haka ne Allah dai ya kyauta" na faɗa ina miƙe wa
ko da muka je sallama da su kawai kallon su nakeyi gashi ina son tambayar su dalilin daya sa suke wannan maganar amma ba dama tambayar su don sai suce nayi musu laɓe ina kallon su haka suka kama hanya suka tafi ciki na cike da tambaya amma ba daman yi
su khadija sai da suka ƙara kwana biyar sannan suma sukayi haramar tafiya, bayan na cika su da goma ta arziki kai ɗan uwa da daɗi yake, haka suka tafi ina kewar su ya rage daga ni sai mama, don ita tace sai anyi arba'in haka sukayi da baban mu wato ita mama babu ruwanta da yiwa kanta baƙin ciki inda wata ce cewa zatayi bazata zauna ba saboda ƴar kishiya ce amma mama ko a jikin ta zaman ta tayi
na so mu keɓe da mijina watoa abu haidar don in samu in amayar masa da tambayoyin da ke ciki na amma hakan ya gagara don kuwa aiki yake yi tuƙuru ba kama hannun yaro, idan ya shigo wurin mu kusan a tsats tsaye yake ganin mu ya ƙara gaba, ga kuma mama bana son inyi masa tambayar tana nan
sai da mukayi arba'in da kwana biyu sannan mama ta fara haɗa ya nata ya nata don tafiya ita ma, abu haidar ya kaita siyayya hmmm naga hidima wurin mama ta kwaso kaya kamar ba gobe haka ta dawo dasu niƙi niƙi, sai shi wa mijina albarka take yi, ni dai kawai riƙe baki nayi ina kallon iyayen kayan da mama ta kwaso Allah ya kyauta na ce a raina
ranar da mama ta kama hanyar lagos ranar shima abu haidar ya kama hanyar china wurin wani project da suke yi shi da wani ɗan china, bayan ya yarde min inje kano yawon arba'in, har airport na raka shi sannan na dawo da zummar kashegari zan tafi kano wayyo daɗi yaushe rabona da birnin dabo Allah ne kaɗai ya sani na faɗa a raina
kashegari da wuri na kama hanyar kano a mota kasancewar ina son ganin gari sosai, tafiyace miƙaƙƙiya daga abuja zuwa kano, a gajiye liƙis na sauka don na manta rabona da irin wannan tafiyar, directly gidan tj na nufa don nan zan sauka, ɗakine guda aka haɗamin da ban ɗaki a cikin sa, watsa ruwa nayi kawai na kwanta don na gaji sosai, bacci kawai nake so don jiya kawana nayi ido na biyu
[7:44PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :24🌹
Bani na fito daga ɗakin ba sai da safe sannan na fito saboda gajiyar da nayi ko abincin dare banci ba, ina jin salma ta shigo ɗakin ko motsawa kasa yi nayi
Sai da nayi wanka nayi wa haidar na shirya sannan na fito falon gidan sanye cikin shadda ta brown ɗinkin bubu kasancewar ni akwai son buba sannan na ɗauko hijabi na ɗora tunda gida ba naka bane
Tj na tarar a falon da salmar suna karya wa, ina fitowa salma ta karɓi haidar inda tj ya karɓe shi daga hannun ta"yaron nan kullum kamar shi baban sa ƙara fitowa takeyi" ya faɗa yana kallon haidar
"da baban sa ko dai mamansa, ai wannan kamar su ɗaya da zainab kudai kun fiya son kai ne, haka da haifi Islam kace kamar ku ɗaya"
"ai ku bakusan kama bane shi yasa, me ya haɗa wannan da mamansa ai wannan kamar ɗan uwa yayi kaki haka yake bari kiga ya ƙara girma.............."
"a lkcn ma zaka ga kamar tasa da uwarsa ta ƙara fitowa" salma ta ƙarashe masa zancen nasa, sakin baki yayi yana kallan ta
"to ai shike nan zamu gani" ina dai ban tanka musu ina dai zaune ina jiran su gama musun su mu gaisa
"sannu wannan baƙuwa Allah ya zuba miki bacci, tun da kika zo gidan nan kike bacci sai kace wata kasa" tj ya faɗa yana dariya, murmushi nayi tare da cewa
"ina kwanan mu" duk nayi musu jam'i
"lfy kin iso ƙalau tun jiya nake sa idon ganin ki salma tace kina bacci, bayan kafin kizo ba irin jan kunnen da ba ayi min ba akan in kula da ke da haidar sosai" ya faɗa a zolaye, murmushi nayi kaɗan daga aikin abu haidar ne zai aikata na faɗa araina
"bari a kawo miki abinci" inji salma
"no bazan sha shayi ba indai da cheery noodles ita nake son ci, bari ma kiga in shiga kitchen ɗin in dafa" tashi nayi tsam na shige kitchen ɗin don gabaɗaya ban sake ba
Biyo ni tayi
"ya baƙuwa da girki, ko kina son aliyu yace bamu riƙe masa amanar da aka bamu bane"
"ko kaɗan akwai yadda nake son dafa noodles ɗina ne, karki damu" na mayar mata da martani tare da murmushi
"to bari in taya ki"
"ba komai kije ki sallami mijinki tukunna"
"yace ya ɗau hutu daga wajen aiki har sai kin tafi don zai dinga kaiki unguwa" shiru nayi ina sauraren ta sai banji daɗi ba
"laaa dama kince ya ci gaba da aiki ai da driver na zo saboda yawon"
"wannan kuma ki gaya mai da kanki ƴar amanar mu" ta faɗa tare da dafa min bayana, murmushi na cigaba da yi ita kuma ta fice
ko da nagama dafa abata na juyo ta plate da niyyar in wuce ɗaki amma salma sai ta hanani tace sai dai in zauna a falo inci tj ya fita, ba yadda na iya haka na zauna a falon nan ba dan na so ba, sai dana kammala sannan ya shigo ɗauke da haidar ga islam a hannusa, tana gani na ta taho a guje ashe bata manta dani ba
"lallai islam ashe bakya manta mutane" na faɗa
"ai wannan kusan kullum sai tayi hirar abj" salma ta ansa min, tj ne ya zauna sannan ya ce
"yayat yaushe za a fara zaga dangin ne, kuma ina zaki fara zuwa" shiru nayi don ni ban san kowa ba acikin *dangin sa* ba tunda muka yi aure ba wanda na sani, gashi waɗanda nake tunanin sune *dangin sa* ɗin sunce ya kasa kulawa da *dangin sa*
"jakara, jakara zan fara zuwa" na faɗa tabbas jakara naji sunce a nan kakarsa take,
nayi mamaki sosai dana ga alamar tsoro ko ince mamaki a fuskar tj
"jakara zaki je"
"eeeh nan nake son in fara zuwa ko akwai wani abinne"
"no no no no ba komai" ya faɗa yana girgiza kansa kamar ba a cikin hayyacin sa yake magana ba
"sai muje anji ma in kin shirya"
"ba abinda zanyi ni a shirye nake" na faɗ ina gya hijabin da ke jikina
"ok bari in watsa ruwa sai in fito, tashi yayi ya shige ni kuma na koma ɗaki ɗauke da haidar a hannuna, ban kawo komai a raina ba illa murnar da nakeyi yau ɗana zai ga *dangin sa* na ɓangaren uban sa, nasan ƴen gayu ne ƙila ma farare ne kamar abu haidar ɗin
ƙara duba kaina nayi a mudubi na tabbatar ko shugaban ƙasa zan iya gani a haka sannan hankalina ya kwanta bana son inje gidan ƴen gayu a raina ni, na zauna ina tunani na na yadda ƴen uwan abu haidar zasu karɓe ni ko da fara'a ko a wulaƙance ni dai sai saƙe saƙe na nake tayi, salma ce ta shigo ta ce min yana jirana, ɗan ƙara kimtsawa nayi tare da sa mayafin da zai shiga da kayan, sannan na ɗauko haidar na fito
A mota na same shi ya buɗe min sit ɗin baya na shiga ni da ɗana, na zauna sannan muka fara tafiya, kasancewar bansan garin kano ba yasa bansan ina muke daso ba, bayan mu ɗan yi ƴar doguwar tafiya muka zo wata unguwa wacce layikanta suke a tsuke sai da dabara ma sannan muke iya wucewa,
ƴar tafiya muka yi kaɗan sannan tj yayi parking, muka fito ya karɓi haidar ya fara tafiya, mun yi tafiya da ɗan dama kafin mu zo wani ɗan durƙusash shen gida wanda yake ginin ƙasa ne, duk gefen soron wajen gidan ɗan pilastar da akayi masa ya zazzage ana gani jar ƙasa muraran,
Soro biyu muka shige waɗanda duk sun dafe kamar ana girki a cikin su, sannan muka shiga, tsakar gidan na ƙasa ne ko arziƙin siminti bai samu ba, yara ne a baje a tsakar gidan suna ta wasansu a cikin ƙasa ba tare da iyayen sun damu ba, sallamr mu ce ta katsewa iyayen hirar su da suka yi dandazo sunayi ba tare da sun kula da halin da ƴaƴan su suke ciki ba, gabaɗayan su suka juyo tare da ansa mana
"wa 'alaikumus salam, a a awata sabon gani tijjani ne yau agidan namu, lallai yau za ayi ruwa da ƙanƙara" inji wata wacce daga ganin ta zata haifi tj ɗin,
"mmn habu wallahi uzuri ne yayi min yawa kiyi haƙuri"
"kayya ba komai ku ƙaraso ai iyar tana ciki"
ƙarasa shiga ciki muka yi inda kwata tayi wa gidan kwalliya, sai da muka tsallaka wata yar ƙaramar kwata sannan muka shiga wani ɗaki wanda saka durƙusa sannan zaka shiga,
babu abinda ke ɗakin sai wata ƴar tsuhuwar kujera guda ɗaya a gefen ɗakin wanda cushion ɗin kujerar duk sun patattake kana ganin soson cikin kujerar wanda shima yayibaƙi ya yayyage, ƙasan ɗakin an simince shi amma duk ya fargashe ramuka ne aoaai a ɗakin kamar ba mutun ne a ciki ba, bangon ɗakon yai baƙiƙƙirin da shi kamar ana girki da murhu a ɗakin, sai iayayen calandu na mutane duk an zagaye ɗakin da shi
Wata ƴar tsohuwace ta fito daga cikin uwar ɗakan ɗakin,
" wa nake ji kamar ahmadu, lallai yau nayi gamo da alheri" ta faɗa tana fitowa tare da ƙoƙarin gyaran ɗan kwalinta tsohuwa ce amma daga gani harda rashi ya sa ta ƙara lalacewar tata
tabarma ta ɗauko ta shinfiɗa mana muka zauna, bayan mu gaisa ne take cewa
"wannan dai ba sirikar tawa bace ba koo, ko kuma idon nawa ne"
" iya idonki ras yake ba ita bace matar ali ce, ta haihu shine tazo gaishe ku" tsayawa tayi tana kallo na
"ali dai ali alin hjyr" ta faɗa, murmushi yaya tare da gyaɗa kansa
"shi kuwa" hannun ta na rawa ta matso ta ɗauki haidar da ke hannun tj, sai ga hawaye a idon ta, ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah don har yanzu bansan inda muka zo ba, amma koma ina ne daga gani talauci ya zuba ƴaƴa har da jikokin sa a gidan nan, don babu wacce zaka gani kace bata fama da babu har ita tsohuwar da ke gaban mu tana fama da babu, zanin jikin ta kawai zaka kalla kasan cewar talauci yai mata damƙar kuku
tashi tayi ta fita sai gata da mutanen gidan sai shigowa suke yi ana gaisawa da ni suna ɗaukar haidar, da yake ɗakin ba wani girma gare shi don haka sai wasu sun fita sannan wasu suke shigowa ko da aka gama gaisuwar sai gashi an kawo mana ruwa a wani kwanon silba, ni bin kwanon nayi kawai da kallo amma gaskiya bazan iya shan ruwa cikin sa ba, ganin cewar kamar bazamu sha ruwan bane yasa iyan tace wa wata yarinya da bazata wuce shekara shida ba
"humaira zo kije gidan ummi kice nace ta bani pure water guda huɗu nayi baƙi" a guje yarinyar ta tafi can zuwa jimawa sai gata ta dawo duk tayi duƙun duƙun da ita
"iya kinga ina cikin gudu na faɗa kwata"
"ina aiken da na miki" iyar ta tambaye ta
"au tace wai shekaran jiya da kikayi baƙi kika karɓi na 15 baki aiko mata da kuɗin ba" yarinyar ta faɗa batare da damuwa ba
fuskar iyar ta nuna damuwa sosai tj ne ya ce
"iya karki samu damuwa bama jin ƙishi ma" ya zaro 1000 ya ba yarinyar gashi nan jeki ce ta ɗauki kuɗin ta, yarinyar ce ta kuma kallon iya inusa me shago ɗazu yayi min maganar bashin sabulun wankan da kika karɓa"
"kije shima ya ɗauka aciki" inji tj wallahi matar duk sai ta bani tausayi don ƙiri ƙiri kana gani kasan cewar tana buƙatar taimako, tj ne ya katse shirun da mukayi tare da tambayar iyar ragowar ƴaƴan nata inda ita kuma take bashi ansa dai dai sanin ta
Wata mata ce ta shigo ɗaki kamar an jeho ta
"lfy bilki sai tace wacce aka koro"
"wallahi iya yara ne suka je gidana suka ce matar ali tazo shine wanki ma nakeyi na ajiye na fito don inganta"
"ina kwana sirika ta" ta juyo gare ni muka gaisa
Suka gaisa da tj har tana mai ƙorafin ya yada daita shi kuma ya dinga kawo mata uzirin sa na baya zama ne
hannun ta da ke jike ta goge tare da miƙowa iyar hannu kawo jikan nawa inganshi, ta karɓi haidar tare yi masa addua, sannan ta juyo gareni
"ashe a abuja kika tare" gyaɗa mata kai nayi
nan ta zauna suka dinga hira da tj