Chapter 14 Reading DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt Arewa Novels

DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 33

39K to 42K   out of 97.7K words

itama iyar takan ɗan tanka musu ni dai ina zaune idan anyi abin dariya in dara, mun ɗan jima ni dai buri na in fita daga gidan don haƙurin zama kawai nakeyi, tare muka miƙe da bilkin muka fito har soro mutan gidan suka rako mu inda bilkin ta karɓi number wayata wai don mu dinga gaisawa da kuma wai inta haihu zata kira ni ta faɗa min kasancewar ciki ne da ita ya fito sosai, tj yai ta musu rabon kuɗi hatta yara ƴen ƙanana sai da suka samu suna ta shi masa albarka muka fito har muka ƙule daga lokon gidan suna kallon mu wata ajiyar zuciya na saki dana ga mun bar layin nan kai Allah mun gode ma amma talauci baiyi ba ko kaɗan
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: L🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Paga :25🌹



Har muka ƙaraso inda mukai parking ina tananin bayin Allah nan Allah ya gani ina tausaya musu, kamar suna rayuwa a ƙauye kamar ba civilization, jikina duk yai sanyi na rasa yadda zan kwatanta bayin Allah nan, muryar tj ce ta katse
"madam daga nan sai ina"
"tj nace ma gurin kakar aliyu zanje in gaishe ta" na faɗa jiki na duk yai sanyi har yanzu ina tunanin bayin Allah nan, na ɗauka wani abin yake yi amma ga mamakina in ɗagowa sai naga ya kallona,
"kima nufin baki san gurin wacce kika je ba yanzu" girgiza masa kai nayi
"itace kakar aliyu, iyar da muka ke ɗakinta muka zauna ta ɗauki haidar itace ta haifi mahaifin aliyu" rasa bakin magana nayi


"kana nufin iyar da muka fito daga gidan nan yanzu ita ta haifi baban mijina"
"ƙwarai kuwa, duk waɗannan da kike gani daga matan ƙanin baban sa sai ƙannan baban sa a gidan babu bare, itama wannan bilkin da kika ga ta shigo daga ƙarshe itacw autar iyar, uwarsu ɗaya uban su ɗaya d bbn ɗan uwa"

shiru nayi jikina duk yayi sanyi mekenan yake shirin faruwa aliyu ne *dangin sa* suke rayuwa kamar almajirai, kamar akansu aka yanke wa talauci cibiya abin ma wallahi da ɗaure kai
"tj kana nufin waɗan nan sune dangin aliyu, waɗanda zai kalla yace sune *dangin sa*


gyaɗa kamsa kawai yayi tare da ƙoƙarin buɗe ƙofar don in shiga, shiga nayi amma gabaɗaya hankalima yana tashe, ya za ayi ace wai waɗannan su ne *dangin sa* mutumin da ya mallaki dukiyoyi bila adadin ko jirgin ruwa ɗaya gare aliyu zai iya ciyar da kusan rabin kano amma mutumin daya mallaki jiragen ruwa wai shine *dangin sa* suke cikin wannan baƙin talaucin



"tj kana ganin abu haidar ya san halin da ƴen uwan sa suke ciki" na tambaye shi a ƙage
"gwanda dai ki tambaye shi kinsan ance waƙa a bakin me ita tafi daɗi" ba yadda ban yiba don inji wani abin a bakin tj amma ƙiri ƙiri duk abinda na tambaye shi sai yace in dai tambayi mijina, haka na haƙura nai shiru
"akwai inda kike son zuwa ne kuma"ya kuma jeho min tambaya, bazan iya zuwa ko ina ba don gabaɗaya jikina yayi sanyi ganin irin yanayin da na samu ƴen uwan mijina
"tj kai ni gida kawai gobe nayi yawon amma gaskiya yau ina buƙatar inyi nazari sosai akan halin da bayin Allah nan suke ciki" shiru yayi bai tanka min ba



ko da ya ajiye ni bai shiga gidan ba wai yana sauri, na shiga ni kaɗai salma tai mamakin gani na, na dawo da wuri, nan na rattabo mata abinda na gani a gidan dana je ko zanji wani bayani daga gare ta amma ga mamakina sai ta nuna min bata san komai ba, ba irin tambayar da ban mata ba amma ƙiri ƙiri tace min wallahi bata san komai ba amma dai tasan akwai wata mai tsami sosai tsakanin miji na da *dangin sa*
"to waɗanda suka zo suna fa ba *dangin sa* bane"
"ƙannan baban islam ne"
"meye dangatakar mijinki da nawa" na tambayeta a ƙagare, dafa ni tayi
"in kina son ansar da zata gamsar da ke ki tambayi mijiki" tana faɗar haka ta juya tayi shigewar ta ɗaki ta barni da baki a buɗe


kasancewar hausa ba wani isa ta tayi ba sosai ya sa na tsaya ina nazarin abinda salmar tace amma har na gama bincika dictionary ɗin ƙwaƙwalwata ban ga ne me take nufi ba, haka na shige ɗaki na kwanta don ina buƙatar kaɗaicewa ko nayi ɗan nazari





me ya haɗa mijina da *dangin sa*haka da har yayi tsami har ya iya kallon su cikin halin da suke ya ƙyale su ba tare da ko ɗan kula su ba, me yayi zafi, ko dai sun wahalar da shine lkcn da iyayen sa suka rasu, haka naita saƙa ina warwarewa babu me kama min ni kaɗai nake ta saƙe saƙe na babu me gyara min ko kuma me faɗa min abinda ya faru sai dai injira dawowar shi wanda abin ya faru da shi, ƙila shi ya faɗa min abinda ya faru kai doe ne ma ya faɗa min tunda yanzu ai mun zama ɗaya na faɗa ina mai juyi akan gado don inji daɗin kwanciyata






sai bayan sallah magariba sannan abu haidar ya kira ni, muka gaisa da wasa da dariya,
"mutan kano ya kanon an fara yawon, Allah yasa dai ba a wahalar min da ɗana" ya faɗa a zolaye
"ni ko ka tambayeni ta ɗan ka kake ko" na faɗa tare da zunɓuro baki kamar yana wajen
"yi haƙuri habibti ya kike"
"lfy" na ansa a taƙaice
"an fara yawon ne" ya tambaya
"eewh yau munje jakarah" shiruuuuuu naji yayi har na ɗauka ko wayar ce ta katse sai da nace hello sannan naji yace min




"wa ya saki kije"
"ai naga ƴen uwankane"
"shut up, dont provoke me now young lady, da izinin wa kika je,na ce miki ki je can ne" ina iya jiyo nunfashin da yake fitar wa saboda tsabar fushi da yake ciki

"ki shirya kayan ki yanzu ki bar kano kin gama yawon"
"ban je ko ina baa" ɗitttttttttttt naji ya kashe wayar, me kenan hakan yake nufi na faɗa, raina ya baci sosai da sosai komawa nayi na kwanta abin abu haidar ya fara sha min kai yanzu



*************

sun fito kenan daga meeting zasu cin abinci a wani sea food da ke kusa da deport ɗin da suke yace bari ya kira wannan me yawon yaji ta fara yawon nata amma abin mamaki yana kiran ta sai yaji wani zance da ya fi muni gareshi wai taje wurin waɗan da a aduniyar nan bashida maƙiya kamar su me zai kaita jakarah, ya maimaita tj ka cuceni don me zaka ɗauki mamata da ɗana ka kai wa mutanen da tun ina cikin uwata suke kirana da shege, don me zaka kai min iyalaina wurin mutanen da tunda nake basu taɓa so na ba don me zaka kaimin iyalaina wurin mutanen da basa so na ko kaɗan




lallai yau dole ne ta bar garin nan, don naga almar tj baya son ta zauna agidan sa ne, ɗaukar wayar sa yayi ya kira tj ɗin, ringing biyu tj ɗin ya ɗauka
"ɗan uwa ya birnin sin ɗin" tj ya tambaya ba tare da kawo komai a ransa ba
"tj na gode da abinda kayi min kuma na gano ka baka son matata ta zauna a gidan ka ne shiyasa har ka kaita gidan da kasan na fi tsana, don haka ka tattara min ita ka kai min ita airport ta kama hanyar gidan ta"


shiru tj ɗin yayi yasan cewar aliyun ya faɗi abinda ya faɗa ne cikin ɓacin rai,
"ko baka jine ka mayar min da matata" ya daka masa tsawa
"sai da safe don yanzu dare yayi"
"ban damu ba ni dai kawai matata ta bar min gidan ka yanzu"
"kamar yadda nace sai da safe kawai ka haƙura sai da safe"
"idan bazaka sa ta a jirgin ba zan aiko a ɗauke ta da kaina"
"ince dai tana cikin gidana zanga wanda zai shigo min gida wai da nufin ɗaukar ta ayau, in kuma ka isa ka baro inda kake ka zo ka ɗauke ta" yana gama faɗin haka ya kashe wayar don yasan idan ya ci gaba da biye masa sai suyi ɓatacciya don ya san halin aliyu sarai in dai ta kan *dangin sa* ne sai ya rufe idonsa ya ci maka mutunci



to inba aliyu ba waya faɗa wa zainab maganar jakara, salma salma ce zata faɗa mata ya faɗa aransa amma zata gane kurenta duk jan kunnen da yayi mata akan duk abinda zainab ɗin zata tambaya tace mata bata sani ba amma sai da ta saki baki tayi magana, gaskiya salma baki kyauta min ba ya faɗa tare da shiga motar sa domin zuwa gida dole ne ya nuna wa salmar kuren ta
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Page :26🌹


Tunda muka gama waya da aliyu na kashe wayar gaba ki ɗaya don kar ya dame ni don me bangama yawona ba zaice wai in koma don kawai na je gidan su mtsss na ja dogon tsaki wasu mazan ma sai su, kwanciya nayi ina shirin bacci na ji tj yana ƙwalawa matar sa kira tun daga ƙofar falo, tooo Allah dai yasa ƙalau na faɗa tare da jan bargo na ina mai yin addua ta yin bacci



Tun daga bakin ƙogar falo yake ƙwala mata kira
"salma salma salma" gaskiya yau salma ta ƙular da ni don me zata faɗa wa zainab cewar dangin mijinta suna jakara, har cikin ɗakin nata ya shiga ya tarar tana salla dole ya samu wuri ya zauna don gaskiya baiji daɗi ba




ko da ta idar sai da ya jira ta shafa sannan ya fara mata magana
"yanzu salma don Allah ba nace miki babu ruwanki da sha'anin zainab da aliyu ba ba nace miki duk abinda ta tambaya kice mata baki sani amma shine sai da kika guntsa mata cewar kakarsa tana jakara, me yasa baki bata labarin abinda ya haɗa su da *dangin sa* gabaɗaya ba,"



bata tanka masa ba sai da tabari ya gama ban bamin sa sannan tace
"baban islam ita zainab ɗin ce ta cemaka ni na faɗa mata akan kakar tasa" ta faɗa da fsukar tausayi, kasanceqar tj yana da sanyi sosai ya shi ganin yanayin ta ya ɗan sauko
"to in ba ke kika gaya mata ba waya faɗa mata"
"wallahi ban sani baamma kaje ka tambayeta mana" tashi yayi ya fice dole ya kamata ya san ta ina zainab taji labarin nan





ina kwance bacci ya fara kwasa ta naji knocking,
"yayata nine pls ɗan buɗe muyi wata magana" Tashi nayi na ɗauko hijabi na na saka snnan na buɗe, yana tsaye a bakin ƙofar yana gani na ya koma falo, nima sai na bi bayan sa, wuri na samu na zauna kamar yadda na ganshi a zaune




"yayata don Allah salma ce ta gaya miki akan dangin mijin ki suna jakara ko" Salma? Girgiza kaina nayi
"to inba ita ta faɗa miki ba wa zai faɗa miki ni naga babu wani wanda zaku zauna kuyi hira da shi sai ita" Allah sarki baiwar Allah shiyas yazo yana ƙwala mata kira ɗazu ya ɗauka ita ta faɗa min
"wallahi ba ita bace ta faɗamin ba hasalima ni ba muyi hirar wasu da ita ba" Murmushi yayi na takaici don bai yadda, da naga dai ba zai bar zargin baiwar Allah ba sai na kwashe duk yadda naji ƴen uwansa sun hira na faɗa masa to ya zanyi da ya zargi wacce ba ruwanta ba gwanda ya ji gaskiya ba



mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskar sa, don be taɓa tsammanin abinda zan faɗa nas ba kenan, shiru yayi na wasu ƴen sakanni sannan daga baya yace
"shikenan Allah ya kyauta, mijinki yace in saki a jirgi gobe ki koma don haka ki kwanta da wuri da safe si in kaiki airport" to kawai na iya cewa sannan na juya na wuce ɗaki na kwanta




Da safe da wurwuri na shirya takwas muna airport ina jin lkcn da aliyun ya kira shi shi kuma tj ya faɗa masa gamu a airport ba yadda na iya haka na hau jirgi na koma abj ba tare da nayi yawon ba tunda ya matsa kai namiji sai dai a barshi na faɗa a raina, ina sauka na tarar har ya turo driver na hau na kama hanyar gida



Aliyu bai dawo ba si da na yi sati biyu da komawa sannan ya dawo, babu sanarwa kawai sai ganin shi nayi kamar wanda aka jeho daga sama, duk da dai bai faɗa min ba hakan bai hanani yi mai sauka ta musaman ba, sai da na tabbatar da ya nutsu sannan na gabatar masa da abincin lafiyayye wanda na shiga kitchen da kaina na dafa saboda shiya zauna ya ci sosai tare da godewa Allah sannan na kwashe kayan



Ko da na gama kwashe kayan sai shi kuma ya ɗauki haidar suka tafi garden,ni ma ina gama kwashe kayan na bisu na samu wuri kusa da shi na zauna tare da jingina da jikin sa sannan nace
"abu haidar me ya haɗa ka da dangin ka ne" shiru naji yayi sai na ɗauka ko be ji bane don haka sai na juyo don inga ko me yakeni



ni yake kallo fuskar nan tashi kamar anyi masa da albishir da mutuwa,
"kina son mu zauna lfy da ke, kina son mu zauna ba tare da kowa ya ji kan mu ba, too ina son ki ɗauke kanki daga abinda babu ruwanki a ciki"
"to amma gani nayi dangin ka ne ƴen uwan ka ne" hankaɗe ni yayi daga jikinsa ya tashi tare da ɗaukar haidar
"sai kiyi abinda kike ganin shi ne dai dai agareki" ya faɗa yana kama hanyar ɗakin sa ko da na bishi ya rufe ɗakin da mukulli haka na gama bugawa ta na kama hanyar part ɗina in ɗan yayi kuka ya kawo shi da shi na faɗa a raina



wasa wasa sai gashi mun fara faɗa da mijina a kan *dangin sa* da naga cewar abinda nake so bazan taba samu ba indai har na bari muka ci gaba da faɗan nan ba wani riba da zan samu don haka sai na kwantar da hankalina in dai zan shawo mijina akan *dangin sa* sai dai in canza tsari amma wannan ba zai yiwu ba na faɗa araina, da yamma na tashi nayi masa ɗan wake da farfesun catfish, sai lemun jinja sannan bayan na gama na kwashi kayan abincin na kai masa part ɗin sa na jera a dining table ɗinsa




komawa nayi part ɗina nayi wanka na shirya cikin body hug top ɗita blue colour wacce a gaban ta aka rubuta *YOU AND I* da golden colour, sai leg jeans ɗina wanda iyakacin sa gwiwa ta, nayi parking ɗin kaina a tsakiya sannan na ɗau ki ɗana nayi part ɗinsa don in jira dawowarsa



ko da na koma part ɗin nasa sai da na sake gyarawa duk da yake a gyare yake ban wani daɗe ba sai gashi ya shigo, da gudu na naje wajen sa na rungume shi sai naga yana ƙoƙarin ƙwace kansa ƙara ruƙunƙume shi nayi tare da manna masa kiss a lips ɗin sa hakan ya sa shi yin ɗan sanyi, sai da na tabbatar da ya ɗan sakko sannan na sake shi na ja shi zuwa toiƙet din ya ɗan watsa ruwa, na taimaka masa yayi wanka sannan bayan ya shirya nayi masa jagora zuwa dining table ɗin



sosai ya ji daɗin ganin abincin dana dafa masa amma sai ya dake, na fara zuba masa farfesun tas ya shanye, ya kuma ci ɗan waken sosai sannan ya sha drink ɗin kas ɓoye murnar sa yayi sai ya ce
"kin iya ɓata wa mutum rai amma idan kin so kin iya daɗaɗa wa mutum" ya faɗa yana goge bakin sa da tabƙe napkin ɗin da ke gaban sa
"ai na dena, ba za a ƙara ba"
"gwanda dai" ya ansa a taƙaice


mun koma mun ɗinke sosai nida mijina kamar ba abinda ya faru tsakanin mu, sosai yake ji da ni da ɗana sosai, bilki ƙanwar baban aliyu ta kira ni kuma naji daɗi mun gaisa sosai da ita har na kuma tuna mata idan ta haihu ta kira ni duk da dai ba zuwa zanyi ba amma zan aika mata da ɗan abin hannu na na faɗa araina
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

14 / 33