Chapter 24 Reading DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt Arewa Novels

DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   24 / 33

69K to 72K   out of 97.7K words

ya shiga da sallamar sa aliyun ansa shi kawai yayi tare da kau da kan sa don tj ɗin ba ƙaramin bashi haushi yake ba, ya ƙi dawo masa da matar sa


kusa da ɗan uwan nasa ya samu wuri ya zauna
"ɗan uwa ashe baka ji daɗi ba" be kula tj ɗin ba ya ci gaba da cin fruit ɗin nasa, ya rame sosai daga gani yana jin jiki

"ɗan uwa me nayi haka da zafi da kake jin haushina har baka da lafiya amma ka kasa faɗamin"ya kuma tambayar sa


"me kake so ince maka tunda kaƙi ka dawo min da iyalina gashi har ciwo ya kamani saboda rashin su"
"ɗan uwa tace bazata biyo ni bavya zan yi"
"ba sai ka kore ta daga gidan ka ba in taga bata da inda zata ai dole ta dawo gidan ta koo"


"ɗan uwa ai zainab bata gidana, haba da tana gidana da tuni na kaɗo maka ita"


juyowa aliyu yayi yana kallon tj
"ban gane bata gidan ka ba tana ina kake nufi" sai da tj ya ɗan ƙara gyara zaman sa sannan yace
"tana jakara gidan iya"


hankalin aliyu ne ya kuma tashi me zainab take nufi da zata tafi gidan mutanen da baya ƙaunar ko jin sunan su ta zauna ita da ƴaƴan sajuyowa yayi wajen tj yace
"tun yaushe take gidan ko kana nufin dama tun can tana can gidan shine baka faɗa min ba ka bar min ƴaƴa na gidan da nafi tsana a rayuwata" shidai tj shiru yayi kawai don daman yasan idan aliyu yasan cewar zainab tana jakara yasan sai anyi ɗan ƙaramin yaki da shi saukowa yayi daga kan gadon yana neman hanyar fita tj ne yayi magana "ɗan uwan ina zaka je ne"

"zan je in dawo da iyalina ne don bazan bar su su zauna awannan gidan ba" ya faɗa yana buɗe ƙofar ɗakin tare da bugo ta da ƙarfi tj ya bishi a baya yana kiran ɗan uwa ɗan uwa amma aliyu ko juyowa be yi ba babu yadda ya iya haka ya bi bayan sa shima gwan da ya bishi don daga dukkan alamar aliyun ranshi ya baci sosai da jin zainab ɗin tana jakara
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Page:44🌹


Duk irin kiran da tj yake yi wa aliyu be kula shi tafiyar shi kawai yakeyi yana hanyar fita daga asibitin, wata nurse ce ta zo da zunmar dakatar da aliyun amma irin kallon da yayi mata yasa ta kaucewa
"malam dr. be sallame ka ba" ta faɗa da ƙarfi



ko kula ta be yi ba sai nine na ƙarasa kusa da ita nace mata
"ki ce dr. ɗin patient ɗin sa ya sallami kansa ya tura bill ɗin office ɗin aliyun za ayi settling, gyaɗa kanta kawai take yi don tana mamakin wannan patient ɗin wai ya sallami kansa shida dr. ɗin yace case ɗin sa is serious it can even call for theater amma shine ya fice



Aliyu kasa jiran suje airport ma yayi yace wa tj kawai su tafi a mota, sai da suka biya ta gidan shi aliyun inda tj ɗin ya ɗan haɗa masa kaya, wand aliyun yai ta mita shi ba zama zaije yayi a kano ba ya na zuwa ya tattaro kan iyalin sa abuja zasu dawo



Suka kama hanyar kano wanda aliyun yake bayan motar sa crv, inda tj yake driving tare da rufe duk gilasen motar da sakin Ac dai dai yadda mutum ze sake, babu abin dabyake tashi face sautin ƙira'a na shaikh mahir al mu'aiqely aliyu yana son ƙira'ar bawan Allahn nan don haka sai yaji nutsuwa tana saukar masa ahankali duk wani baƙin ciki da yake ciki yaji yana yayewa a hankali tuni wani bacci me nauyk yayk awon gaba da shi



har suka iso garin kano karfe 11:15 na dare aliyu yana bacci ba magariba balle isha, tj directly gidan sa ya nufa da shi, don duk son dawo da iyalin sa be isa ya shiga gidan mutane da wannan daren ba,


ko dabya tsayar da motar yai mamakin da har a lkcn aliyun baccin sa yake yi hankalin sa akwance daga ganin ba ya samun bacci, tausayin ɗan uwan nasan ya kama shi sosai, ɗan tattaɓa shi sannan aliyun ya farka, ganin shi a gidan tj ya fara faɗa
"ce maka nayi ka kawo ni gidanɓka ka kaini can inda zainab ɗin take ayau zan kwaso su kuma mu koma abuja a yau ɗin"


"to duk dai abinka ka haƙura ka duba lkc ko inkaga ya dace ka ke gidan a wannan lkcn ga mukullin motar nan ni dai bazan kaika"



Tj ya faɗa masa tare da miƙa masa keys ɗin amma aliyun be karɓa ba sai ma duba agogon sa da yayi, yai mamakin ganin yadda lkc ya wuce haka, ko da yake da yamma suka baro abujar, fitowa yayi daga motar tare da bin bayan tj ɗin inda shikuma tj ɗin yayi masa jagora zuwa inda zai kwana


Wanka kawai ya shiga yayi yaji daɗin jikin sa sosaia kasancewar ya daɗe rabon sa da yayi wani baccin kirki, ko da ya idar da sllah a kan sallayar wani baccin ya kuma kwashe shi, in da tj ya kawo masa shayi don yasan atsarin aliyu baya cin abinci bayan 10:00, ko daya kawo masa sai ya tarar da ɗan uwan nasa ya bacci don haka sai ya ɗan ƙaro masa sanyin ac ɗin tare da lilliɓe shi ya ja masa ƙofa



kashegari da safe tun daya yai sallah asuba ya koma bashi ya tashi ba sai karfe 11:25 na safe gaskiya yayi bacci rabon shi da wannan baccin har ya manta duk sai yaji wani nauyi da yake ji a jikin sa ya ragu, wanka yayi inda yana fitowa ya tarar da tj ya shigo da break fast, be iya cin komai ba sai ɗan tea da slice bread guda ɗaya, sannan suka kama hanyar jakara da niyyar yana zuwa zai kwaso su su koma abj



a daidai inda ake parking a nan tj ya parker don mota bata shiga lungun su iyan da ƙafa suka ci gaba da tafiyar tasu, aliyu yai mamakin har yanzu unguwar ta nan yadda yasanta shekara 20 tun lkcn da ƴaƴan hjy sukai masa wulaƙancin nan, sai kuma in ya zo ganin hjyr sa aɓoye


yana ratsa cikin unguwar amma duk wasu memories na ƙuruciyarsa yana dawo masa kamar a lkcn abin ya faru, sai ya ji ya kuma tsanar unguwar da mutanrn cikin ta don babu wani memory na ƙuruciyar sa da yake tunawa ya ji daɗi duk na ɓacin rai, dake zuciyar sa kawai yake yi amma can ƙasan ran shi gabaɗayan sa aƙunci yake




suna karyo kwanar gidan iyar duk a tunanin shi zai ganshi a rakyakkyaɓe amma ga mamakin sa sai ya ga gidan ya fi kowane gida haskewa, tj kamar yasan tunanin da aliyu yake yi sai yace masa
"kaga gyaran da zainab tayi musu" harara kawai aliyu ya bishi da shi wato da kuɗin shi tazo tana yi musu burga ko to ko ma dai menene daga yau ya ƙare, ya faɗa a dai dai lkcn da suke zuwa ƙofar gidan



Iya ce a tsaye a soron gidan wandabyanzu ya sha fenti suna ciniki da me man ƙuli haidar a goye a bayan ta, tun da aka kawo su kullum in dai ze yi bacci sai iya ta goya shi haka ta saba masa don haka ko bacci yaji sai kawai ya ɗauko zani ya taho wajen iya, ita kuma bata gajiya sai ta saɓa abinta abaya tai ta hidimar ta,


Aliyu yai mamakin ganin haidar a bayn iyar ba haka yayi tunanin zai samu iyalin nasa ba, tj ne ya fara sallama, iya ta juyo zata ansa amma sai taci karo da fukar aliyu, mamaki ne cike taf a fuskar ta amma sai ta dake kasancewar ta kasa karanta halin da yake ciki


"ahmadu kune tafe da ranar nan" iya ta tambaya
" mune iya mun biyo matar mu ne" tj ya faɗa da niyyar ya ƙona wa aliyu rai ai kuwa ya ci karo da wata muguwar harara

"ai kun kyauta" inji iya

Aliyu ne ya ƙarasa bayan iya don ya karɓi ɗan sa, amma abin mamaki sai haidar ɗin ya noƙe kafaɗarsa tare da ƙara shigewa cikin iyar, tj ne yace
"ai wannan in iya ta ɗauke shi babu wanda ya isa ya raba su sai don ganin kansa"


Janye hannun sa aliyu tare da ɗan basarwa,
"amadu ka raka shi mana wurin abun ko kuma tsaye anan ga zafi ga rana"
"to iya ai da wai mufara gaisawa da ke ko, ina wuni" inji tj
"lfy lau kun zo ƙalau" tj ya ansa Allah Allah yake aliyun ya gaida iyar amma sai yaji shiru, can kuma sai yaji aliyun yace
"ina yuni ya muka same ku" kamar baya so haka yayi gaisuwar


Iyar ta ansa da fara'ar ta tare da tambayar shi hanya, ya ansa ba yabo ba fallasa, sannan tj yayi masa jagoran cikin gidan


Tas tsakar gidan yake shima ya sha gyara da siminti wanda akayi masa gyara bayan an gama min, kowacce mace tana ɗakin ta kasancewar zafin da ake tafkawa ga babu wuta, sai solar da aka kunna inda kowacce ta gudu ɗaki ko tana kallo da iyalan ta tana shan fanka ko kuma dai sina shan fankar kaɗai



Ko da su aliyu suka shigo gidan a share yake tas ba kowa don haka directly bangaren zainab ɗin suka wuce wanda aliyun yai mamakin ganin ita ma wai bangaren ta daban



Zainab tana zaune a falo ta gama girki kenan ta ci tana jiran kiran sallah tayi ta ɗan kwanta, gaskiya yau ana ƙwalla rana sosai


Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin naji wanda hakan ya dawo dani daga tunanin zafin da ake dokawa
"waye"
"yayata nine"
"lallai tj yau an kawo mana ziyara ne gaskiya baka gajiya Allah ya saka da alkhairi, da ɗan uwan nan naka zai ga yadda kake kula da iyalinsa da ya wulaƙanta da ..................."


Maƙwat na haɗiye ragowar maganar da zanyi ganin aliyu a bayan tj lkcn dana buɗe kofar, duk sai naji kunya, matsa musu nayi suka shigo, tj dariya ce take son suɓuce masa ina kallon shi yana toshe baki tare da kallon aliyu wanda shi kuma ya haɗe rai daga gani be ji daɗin maganganu ba


Suka shigo kowa ya nemi wuri ya zauna
"tj ina wuni ya salmar ta daɗe bata leƙo ni ba" na faɗa da ɗan borin kunya ta

"Tana nan tace ma in gaishe ki"
"ina wuni" na juya na gaida gogan wanda gabaɗayan hankalinsa yake kan mohd wanda yake dabo yanzu


Tashi yayi yaje ya ɗauko ɗan ɗan nasa tare da rungume shi daga gani yai missing ɗin shi sai ya bani tausayi, shin shina shi kawai yake da sunbatar sa duk sai na tsargu na raba wannan soyayya, tashi nayi tare da shiga kitchen na haɗo musu abinci


Ko da na kawo sai da tj yayi wa aliyu magana sannan ya sauko ya fara ci don gabaɗaya hankalin sa yan kan mohd


Saukowa yayi ya zauna tare da taƙwashe ƙafar sa ya fara cin abinci tuwon shinkafa ne da miyar kuka wadda ta sha wake sai tantaƙwashi ga kuma man shanu wannan ne yasa aliyu babu abinda yake yi da ya wuce loma



Sai da suka ci suka ƙoshi sannan na kwashe kayan, aliyu ya so bayan sun gama cin abinci tj ya tafi, Amma tj sai ya gyara zama ya fara hira da zainab


Tun be lura ba har ya lura da kallon da aliyun yake masa kan ya fita don har nuni yake masa da kai inda yake nuna masa hanyar ƙofa amma sai tj ya yi kamar be san me aliyun yake nufi ba




Ai har yanzu ban gama wana ka ba, tj ya faɗa a ransa, sam ban san wainar da suke toyawa ba don hankalina gabaɗaya yana kan tv, na kan dai ji dariyar tj akai akai, ashe kunna mutumin yake yi


Kiran sallahr azahar ce ta katse mana hirar tamu
"sai ka tashi mu tafi masallaci" inji aliyu


Miƙewa sukai yi,
"yayata bari muje muyi sallah sai mu dawo don yau agidan nan zan ci na dare" tj ya faɗa a zolaye ban gane zolayar aliyu yake ba amma naga dai bayan ya gama maganar tasa ya sa dariya, ban kawo komai ba suka fice



Ko da suka fi sai da aliyu ya kai wa tj harbi da ƙafar sa,
"haba ɗan uwa me kuma nayi"
"dan uban ka baka ganin lkcn da nake maka signa ka tashi ka tafi, ka zo ka tsare mutane da surutun ka na banza, har da cewa wai anan zaka ci na daree wallahi muka idar da sallah baka kama gabanka ba sai nayi mugun saɓa maka" ya faɗa yana yin gaba, dariya ce sosai take cin tj amma sai ya dake tare da nuna shi be ma san me yayi




Ko da suka idar da sallah sai suka shiga sabgogin su, basu koma gidan ba, sai bayan sallah isha sannan aliyu ya samu kansa don duk wata kadara tasa ta kano sai da tj ya nuna masa ita, kuma duk da haka basu gama,


Karɓar motar yayi a hannun tj inda ya wurgar da tj ɗin a hanya wai ya nemi hanyar gidan sa don shi be iya cin ƙwan makauniya ba, yj sai ɗan adai dai ta sahu ya ɗauka ya kama hanyar gida tare da murnar shiryawar ɗan uwan sa da matar sa




Har ya kama hanyar gida sai ya ga bazai shiga haka salin alin ba don haka sai ya karkata akalar motar yayi wajen yahuza suya, ya siyo musu tsire da kuma gasashshiyar kaza sai youghurt me sanyi, har ya kama hanya sai kuma ya dawo yace a sake masa irin haɗin da ya siya





Sai ƙarfe tara na dare ya shiga gidan yana nan dai tsakar gidan shiru, ɗakinɓiya ya shiga direct inda yaci karo da ƴen uwan baban sa



Sun gaisa amutunce sannan ya zauna kowanne sai ya rasa abinda zai ce don ba sabawa suka yiba, da aliyun yaga shirun yayi yawa sai kawai ya ɗauko ledar yahuzar guda ɗaya ya miƙa wa iyar
"ga wannan kici" ya faɗa atakaice
"an gode Allah yayi albarka, ya ƙara buɗi"


A ciki ciki ya ansa amin ɗin, ya miƙe yai musu sallama tare da fita daga ɗakin ya nufi ɓangaren zainab ɗin
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



*wannan page na wata me ƙwadayi ne da tace zata ciii yahuza suya kin san kanki ko sai na kama suna*


🍗🍗🍗🍖🍖🍗🍗 *ba a samu yahuza ba amma ga wannan*


*F. B* da ke nake 👈🏻😉


Page :45🌹



Tun bayan azahar nake sa ran dawowar su amma sai naji shiru, bayan la'asar na tashi na ɗarao na dare, ko dana gama na kintsa komai Wanka nayi na shirya sosai, don nasan yau ba sauƙi iya ta kawo min haidar bayan yayi bacci na haɗa shi da mohd na kwantar da su, don bana son su ɓata mana hirar mu ta yau



ba su suka dawo ba sai ƙarfe 9:10 na dare nayi mamakin dana aliyu shi ka ɗai, ko daya shigo sai nayi masa tayin abinci, sai yace sai ya fara wanka



ruwan wankan na haɗa masa tare da gayyatar sa toilet ɗin, ya shiga ya watsa ya fito, sannan ya canza zuwa ɗan gajeran wando sai ƴar vest kasancewar zafin da ake yi, don ma da wuta



gabatar masa da abinci nayi tare da tsarabar da ya kawo yaci ba yaba sai ya ce
"naman ai na siyan baki ne kin ga ban isa in ci ba sai da yardar ki" kunya ce ta ɗan kama ni wai siyan baki



tura masa plate ɗin nayi gaban sa
"muci tare"
"ni na isa yanzu inna ci wayasan ina za akuma guduwa" Ya faɗa a zolaye ɗan murmushi nayi, duk na kasa sakewa sai kace ba aliyun da sani

24 / 33