Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
ya kamu da ciwo kana da kuɗi me zai dame ka na faɗa arai na nai ta wasuwasi na har nima baccin ya kwashe ni ban daina tunanin me yake damun aliyu ba
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :20🌹
Kwanan mu 15 a asibitin sannan a ka sallame mu ya samu sauƙi sosai kuma zuciyar tasa ta daina masa ciwon, amma duk da haka likita yai masa tunin na cewar ya koma ya kuma ganin likitan sa, inda sai daga baya ya faɗa mana cewar shekarun baya ne yayi fama da ciwon inda yake ganin likita a china,
a irin jinyar da nake yi na fahinci cewar tsabar sha'awr da tayi wa aliyu yawa ce ta haddasa masa ciwon cikin wanda shine ummul aba'isin tada ciwon zuciyar tashi, rasa abinda zance nayi da dr ɗin yayi min bayani lkcn da naje office dinshi karɓo takardar sallama, na kuma kuɗiri niyya a raina in shaa Allah in dan tanine Mijina bazai kuma ciwon zuciya ba, babu yadda banyi ba mu saba da shi tun a asibitin amma ƙiri ƙiri yaƙi sai ko ya tsiri baccin ƙarya har na gasken ya tadda shi ko kuma dai ya ɗauki qur'ani ya tsiri karatu
Ko da muka koma gida direct ɓangarensa muka nufa sai da naga ya kimtsa yai wanka ya sha magani ya kwanta sannan nima na wuce part ɗina don inɗan kimtsa
a gare na tadda da shi kamar da mutun nasan ta wannan ɓangaren bani da matsala ɗan watsa ruwa nayi ajikina sannan na shiga yau so nakeyi inyi wa mijina abinci da kaina
Tuwon semo na tuƙa masa da miyar egusi wacce na soya egusi ɗin da ƙwai yadda egusi ɗin zai duddunƙuƙe sannan ya kakkama ragowar kayan da ke cikin miyar, sai farfaesun catfish, sai zoɓo naji ance zoɓo ma magani ne
tun da nazo gidan ban taɓa ganin anyi mana abincin mu na gargajiya ba sai na bature, don haka yau na canza salon da kaina, ko dana gama wanka nafaɗa inda sai da na shafe kusan minti talatin dani da yi masu yimin kwalliya don in fito fes da ni
wata yellow strapless riga na ɗauko wacce iyakacin ta rabin cinya na saka, bata hannu, sai zip a bayan ta, ta kamani sosai tai min ɗam kamar dama jikina aka gwada aka yi rigar, suma sai yaba min suke yi yadda nayi, a zuciyata nace balle kuma shi wanda akayi domin sa
a back yard garden ɗin mu nasa suka jera min abincin sannan na shiga don inga ko ya tashi, yana zaune akan sallaya daga gani ya idar da sallah ne, samun wuri nayi na zauna kusa da shi har ya idar muka shafa tare
"ka zo muje kaci abincin ka" na faɗa ayangance
"ok ganin nan zuwa bari in ninke sallayar na" karɓar sallayar nayi na fara ninkewa
ko dana juyo zan masa magana sai na tsince shi yana kallona, kau da kansa yayi tare da yin gyaran murya
"muje ko" ya faɗa, noƙe kafaɗa ta nayi tare da zunɓuro baki
"ni dai sai ka ɗauke ni" na faɗa ashagwaɓe, murmushi yayi tare da kauda fuskar sa gefe
"in banda abinki kina ganin banni da lfy kice in ɗauke ki"
"to zaka ɗauke ni knka warke" na faɗa tare da matsawa kusa da shi har ƙirjina na shafen sa, murmushin ya kuma yi
"muje muci abinci yunwa nake ji"
hannun shi naja muka ƙarasa garden yai mamakin yadda nasa aka tsara wajen yai kyau sosai har kasa shiru yayi sai daya tanka
"welcome back party na haɗa maka" na faɗa masa a cikin kunnen sa wanda sai danayi ɗage sannan na faɗa, ɗan janye jikinsa ya ɗanyi daga nawa sannan ya samu wuri ya zauna, ko dana zuba mai abinci nan ma naga mamaki tab fuskar sa amma baice komai ba
malmala biyu yaci sannan ya sha zoɓo sosai, kana ya gode wa Allah
"daga ji yau ba abincin cook na ci ba" ya faɗa da fara'a a fuskar sa
"girkin matar ka" na maida masa da martani
"gaskiya yai daɗi kin cancanci kyauta, yaushe rabon da cin abincin gargajiya mai daɗin wannan tun hjy na da rai" jikina ne yayi sanyi
"hjyr ka da muka yi waya da ita a beach itace ta rasu"kallon mamaki ya binki da shi
"baki sani ba" girgiza masa kai nayi da alamar tausayi a fuskata, nan ya shiga bani labarin mutuwar ta da ɗaurin auren mu da guduwar da yayi, ta tausaya masa sosai wai ace mijina ne ya shiga wannan halin amma ban sani ba, koda yake ba laifi na bane duk rashin sani ne ya kawo haka, amma in sha Allah na sha alwashin sai na zama mace me shayar da mijin ta daɗina faɗa araina
ƙara tausar shi nayi tare da bashi haƙuri akan rashin hjyrsa
"haba ba komai ai yanzu ya zama tsohon zance" ya faɗa, shiru ne ya biyo baya, ganin shirun na naiman yin yawa ya sani na ce
"kace zaka ban tukwicin girkin" na faɗa ina karyar da kaina
"nawa kike so faɗi" rufe ido na nayi na ɗora hannuna akan lips ɗina tare da cewa
"guda goma" shiru naji kmar ba mutum a kusa da ni hakan ne ya sani buɗe ido na, yana zaune bai motsa yana kallona,
"baka ce komai ba ko bazaka bada tukwicin ba" murmushi yayi ya jamin hancin na taer da miƙe wa ya kama tafiya, binshi nayi ina shagwaɓar kaifa kace zaka bani tukwici har muka shige ɗakinsa ina yi masa mita shi kuwa ko ƙala baice ba sai ma ban ɗaki da ya shiga wanda ni kuma na samu wuri a gadonsa na kwanta
da daddare bayan na gama komai na koma ɗakin nasa don in kwanta, a kwance na same shi inda nima naje na kwanta kusa da shi, ban daɗe da kwanciya ba ya tashi ya shiga banɗaki, da alwalar sa ya fito ya tada sallah, tun yana yi ina ƙirga raka'a nawa yayi har bacci ya kwashe ni be idar ba, sai ji nayi ana cemin ki tashi an kira assalatu
tashi nayi ina yin magagi don zuwa toilet nan naci tuntuɓe da shinfiɗar sa wato kenan ma a ƙasa ya kwana kenan ko na faɗa araina, raina bai min daɗi ba me yasa yake min haka na faɗa araina, toilet na faɗa nayo alwala ta na fito na tada sallah, har na idar nayi lazimi na tare da azkar bai dawo ba don haka kawai sai na ɗan gyara gadon tare da kwashe shinfiɗar tasa nai part ɗina don haɗa mana breakfast
*************
wasan saurayi da budurwa muka koma yi nida aliyu inda sam baya wani sakan min fuska sosai ba kasa fai ba ma ya fiya magana sai dai in nayi abu yayi murmushin nan nasa, babu wani irin technich da ban bi ba don ganin na jawo hankalinsa kaina a banza wai an shuka dusa, kai da ƙarshe ma daya ga abin nawa ba na ƙare bane sai ya tsiri azimi da sallah dare, ina shigowa ɗakin in ya tsiri sallah har sai na yi bacci yake dainawa ga idon nawa da shegen son bacci kamar na kasa, azimi kwa kullum kusan yana cikisa wai irin azimin annabi dauda yake son yi
Yau ta kama monday an tashi da sanyi sosai kasancewan ruwan saman saman da aka kwana ana tafkawa, kuma har yanzu anayi don aliyu ko masallaci baije ba don ruwa a ɗakin sa mukayi tare, ko da muka idar na yi lazimina tare da azkar na idar sai nazo gaban sa yana jan carbi
"yallaɓai me zaka karya da shine yau inje in haɗa maka da wuri"
"jekiyi kwanciyar ki yau azimi nake yi"ƙwalalo ido nayi yau monday fa"
"to menene ba a ai ranar monday, azimi me falala ma da ma'aiki (saw) da kansa yace muyi, ai banga me zai sani ƙinyin azimin yau ba" girgiza kaina nayi lallai ma mutumin nan na faɗa araina, jiya fa yayi lahadi amma shine yau ma ya tsiri shi
tashi nayi naje na ɗibo ruwa afrigde na zo zan wuce kenan nayi tintiɓe ruwa ya ɓare tas a kan shinfiɗar malam aliyu sarkin azimi da ƙiyamul layli, baice min komai ba ganin haka ne ya sani kwasar shinfiɗar nayi tafi don in shan ya masa
haushin daya bani yasani shanya masa kayan shinfiɗar tasa aruwa, nima garin mugunta ƴar nightie ɗin da ke jika na ta jiƙe, cire ta nayi na ɗaura zani na kwanta, ko daya tashi kwanciya yaje yaga a inda na shanya masa kayan sai ya dawo
"matsa can ƙarshen gadon zan kwanta" naji yace, bance komai ba na matsa sosai har ina ɗan takure kaina da jikin bangon don kar jikin mu ya haɗu, lallai ma wannan mutumin in kasan wata ai baka san wata ba na faɗa rai na
kwanciya yai tare da jan bargo ya rufe kanshi, bai daɗe da kwanciya ba aka doka wata irin tsawa wacce tasani wurgi da zanin da ke jikina na shige cikin bargon nasa tare da maƙalƙale shi
"lfy" naji yace
"tsoro nake ji" na bashi ansa
"tsawa ce ba komai koma wuri ki" ƙara maƙalƙale shi nayi tare da sa masa kuka
"ni tsoro nake ji" kuma wallahi ba qani tsoron tsawa da nake ji
"shhhhhhh its ok" ya faɗa yana ɗan shafamin bayana alamar lallashi
"wait tsaya ba kaya a jikin ki" ya faɗa, ƙara rushe mai nayi da kuka tare da kara shige masa jiki
"sshhhhh nace ya isa haka ko ai gani akusa da ke ba inda zanje" ya faɗa tare da cigaba da shafe min jikina wannan karan bada sigar lallashi bane
nidai bansan hawa ba ban san sauka ba sai dai kawai jinayk minkna ya maida ni cikakkiyar mace thank u thank u thank u shukran shukran kawai yake faɗi duk kunyar shi sai ta kama ni, ko da muka ɗan nitsa sai naji ya jaa min hancina
"auch, da zafi fa"
"naughty girl kin karya min azimina" kunya ce ta kamani na ƙara shige wa jikin sa, shi kuma ya ƙara rungumeni tare da zuba min ruwan kisses😘😘😘😘😘
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*ya muka ji da alamar shigowar sanyi Allah ya sa mu wuce lfy, mata sai a tanadi kayan harka😜😜 don kuwa maza in akace sanyi yayi abin sai a slow da fatan zamu dinga kula da tsaftar jiki Allah yasa mu wanye ƙalau*
Page:21🌹
Rayuwa ta sauya mana dani da ɗan mijina, nida tun ran da ya mayar dani matar sa ban kuma ganin shi yayi ƙiyamul layli ko azimin na shi ba a zuciyata nakan ce daman ba don Allah ake yi ba, sosai na matsa wa aliyu akan muje china ya ƙara ganin dr. ɗin nasa, daga ƙarshe ya yarda in da yai mana visa tare muka luluƙa birnin sin,
Mun sauka Beijing daka birnin china inda muka sauka ana suburda sanyi, don haka kullum muma manne da aliyu na😘 love one tin tin, yaje ya ga dr. ɗin nasa inda ya shaida masa ba wani matsala amma ya dinga gujewa da abinda zai dinga ɓata mata rai, kasancewar da turanciyayi bayanin nasa ya sa na ɗan fahimci wani abin, amma ba duka kasancewar accent ɗin chinese ya fita daga cikin maganar sa don haka ganewa sai ka nutsu sosai
sai yanzu na fahimci dalilin da zakuga sanyi na wucewa sai kiga mata suna laulayi, ashe su maza kasuwar su ce take buɗewa in ana sanyi, ko ya ka ɗan taba namiji sai kaji ka a ƙasan sa, ba damar kana cikin murna kace zaka rungume mijinka abi na gaba da zaka fuskanta shine fuskar ka tana kallon ceiling 😂😂 wayyo gani sabon shiga amma hakan bai sa aliyu tausaya min ba
watan mu biyu a china kasancewar nan ma wani wurin aiki wa mijina kuma ayadda naji anan ya fara samun arziƙin sa, nakan bishi deport ɗin in har jirgin shi daya ɗauko kaya ya iso, ina mamakin ganin irin maka makan jiragen ruwan da mijina ya mallaka at his age, aiki ne sosai ba ƙarami baya faɗa
sai da muka shafe wata biyu sannan muka kama hanya inda muka sauka ƙasa mai tsarki, nai murna nai kuka wai yau nice a ƙasa mai tsarki, mun yi ziyarar mu sosai a madina, ba inda bamu je na tahiri, inda da muka je dutsen uhud na siya dabinon ajwa don gashi nan baja baja kamar basa so, akwai ɗanye akwai busash she ni dai busashen na siya don tsaraba zanyi
satin mu biyu a madina mukai makka sai da muka tsaya a zul hulayfa inda ake ɗaukar niyyar ummara in ka taho daga madina masallaci ne babba sosai da banɗaku na saboda wankan ɗaukar niyya umma,
mu ka ɗau niyyar umara, mukai wanka muka sa haramin tare da yin sallah raka'a biyu kamar yadda yake a sunnan sannan muka shiga mota muka kama hanyar makka
tafiyace miƙaƙƙiya daga madina zuwa makka inda nai ta mamakin wai wannan doguwar tafiyar ma'aiki (saw) da sayyidina abubakar suka yi daga makka zuwa madina don tabbatar da addinin islama, wanda mu muka zo muka same shi a cikin ruwan sanyi gaskiya dole ne ajinjina musu
sai ƙarfe biyun dare sannan muka ƙarasa makka , wai nice yau a garin makka abin kamar a mafarki, direct hotel muka nufa wanda yake a unguwar bin laden, bashi da nisa sosai da haramin,
sai gab da asuba sannan muka je haramin don yin umara, tafkeken masallaci na ci karo da shi, nai godiya ga ubangijin talikai, nayi addu'ar shiga masallaci na shiga, muka shiga har can ciki inda haramin yake, ɗawafi muka kama yi sannan bayan mun gama aliyu ya jani har jikin ka'aba don in sunbace ta tare da yi adda'a nayi kuwa sosai da sosai har mahaifiyata da bata duniyar nan sai da tasan na zo ɗaki mai tsarki yau sannan daga ƙarshe na haɗa da dukkan ƴen uwa musulmai duk na addu'e mu da fatan mai duka zai karɓa.
V
Mm
ko da muka gama ummara, mu ka koma masaukin mu don hutawa, kwanan mu takwas a makka sannan muka wuce jidda inda daga nan muka wuce dubai don aliyu yana da aikin da zai yi anan, kwanan mu huɗu a dubai ya gama abinda ya kawo shi daga nan sai ya tsiri cewar muyi yawo don ganin gari, ni kuma a lkcn ba abinda nake so da wuce bacci, da na ɗan zauna sai gyangyaɗi sai bacci, na ɗauka ko na gajiya ne har aliyu yana tsokana ta wai bazan iya yaƙi ba tunda daga yin ummara na tsiri bacci ba ji ba gani
ganin baccin nawa kamar harda rashin lfy yasa aliyu matsa min muka je asibiti, ko da muka je asibiti bayan dogon bincike ya nuna cewar ina da shigar ciki har na sati takwas da kwana biyar, inda alamu suka nuna a china na samu wannan cikin
farin ciki waken aliyu kamar ya zuba a ƙasa ya sha yai farin ciki sosai har kyauta yayi wa dr ɗin daya dubani mai tsoka, a hanyar mu ta zuwa gida ne ya dameni
"wai nine nayi cikin nan, da gaske, don Allah ya akayi nayi cikin nan, kamar mafarki fa haka nake gani wai nima daga ƙarshe dai zan ga wanda zan ki ra nawa na kaina" ya dinga sunbatun sa shi kaɗai ni daya ishe ni ma kwanciyata nayi nayi kamar ina bacci har na gasken ya zo yayi awon gaba dani
sama kawai naji anyi dani ashe har mun zo hotel ɗin namu bansani ba, da muka shiga ya dire ni akan gado
"wannan cikin naki calls 4 celebration, dole ne muyi celebrating samun ciki ya faɗa cire rigar sa dana ga yana yi yasani na fahimci irin celebration ɗin da zamuyi kai namiji dai sai dai abarshi na faɗa araina
haka aliyu yai ta nan nan da ni akan cikin nan dana samu har tambaya yake yi wai ina ji motsi don Allah kunji wani zance, ko da muka koma nigeria ma haka kulawar tashi bata ragi ba nan ina samun kulawa sosai daga gare shi ko yana office ne yai ta doka min kira mu wuni muna abu ɗaya yana tambayata ya nake ji ko ya fara