Chapter 16 Reading DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt Arewa Novels

DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 33

45K to 48K   out of 97.7K words

bisimillah suka iya ba


itace ta wanke min ɗana tas ta shirya shi nima ta samin ruwan wanka na yi naji daɗi sai bacci daga ni har ɗan jaririn

abu haidar ne ya faffaɗi haihiwar tawa don ni ko ta kan waya ma ban bi ba ina ta kaina, da daddare daya dawo directly ɗakina ya shigo ya ganmu kwance reras ni da ƴaƴa na sai ga hawaye again a idon sa


tooo wannan kukan sa na biyu kenan a yau lfy na faɗa ina jawo shi zuwa jikina tareda shafa masa baya alamar lallashi
" idan na ganki da ƴaƴan nan nawa sai in godewa Allah wai yau ni aliyun dana rayu cikin ƙyama da kyara daga dangi na wai yau nine da ƴaƴa har biyu sai inji zuciyata ta karye"


kara shafa masa baya nayi tare da cewa
"duk abinda ka gani ya samu bawa muqaddari ne daga Allah haka Allah ya ƙaddaro masa don haka duk abinda ya same mu bama cewar ba zamu yafe ba sai dai mu yafe hakan zai kara kusan tamu da ubangiji" gyaɗa kai yayi

"zainab kenan wasu abubuwan sun wuce mutum ya yafe sai dai kawai ya ɗauke kansa daga wurin gaba ɗaya"
"kamar me fa"
"kar ki damu bari inje in watsa ruwa a jikina yau duk zan feɗe miki daga biri har wutsiyar sa na abinda ya haɗa ni da dangi na har na watsar da su"

to kawai nace ya manna min kiss tare da faɗin i love u with all my heart sannan ya wuce toilet don wanka, komawa nayi na kwanta ina tunanin yau me zanji ya haɗa aliyu da *dangin sa* Allah dai yasa matsalar da zan iya warware wace da sauki na faɗa a raina
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Page :29🌹

*Asalin labarin*

jakara ta kasance unguwace tsohowa zaka gane hakan ne idan kayi la'akkari da irin gine gine da ke cikin unguwar wanda yawancin su ginin ƙasa ne, inda a ɗaya daga cikin gine ginen ƙasa ya kasance na mlm musa me icce ne,


sana'ar icce yake ko an san shi sosai kasancewar iccen shi akwai sauƙi sosai, yana da mata ɗaya tare da yara 10 maza 5 mata ma 5,


acikin ƴaƴan sa sani shine na biyar, yaro ne zuciya tun yana ƙarami, yake neman nasa na kansa, mlm musa yana da mata ɗaya wadda ƴaƴan ta suke kiran ta iya,

markaɗe shine sana'ar, inda in ta kunna injinmarkaɗen ta tun safe sai ya kai 1:00 na rana a kashe ba saboda tsabar markaɗe



mlm musa beyi ilimin boko ba don haka be sa ƴaƴan sa, ya kan de jasu zuwa wajen sana'ar sai da itacen sa su taimaka mishi, sani shi kaɗai ne yake makarantar boko a gidan shima da kanshi ya sa kanshi kuma yake ɗaukar nauyin kansa don daga malam ɗin har iyar babu wanda ya damu da boko


abokin sani wanda gidan su yake jikin su sanin shine kaɗai yake ƙarfafa wa sanin akan karatun boko wanda tare da shi suke yi, kuma da taimakon Allah Allah bai hana sani wani abin na biya wa kai buƙatar mkrt


sai ya wuni yana taimakawa iya markaɗe inda in ta bashi ladan aikin sa sai ya adana yayi hidimar mkrt da shi a haka yake karatun nashi, ana ta gurgurawa da daɗi ba daɗi haka suka dinga karatun su inda duk lkcn da abu ya kakare wa sani abokin nan nasa me suna buhari shine dai me taimaka masa don bai isa ya tinkari iyayen sa ba sai suce ai ba su suka aike shi ba


ko da suka gama secondary school, sai suka fara fafutukar neman jami'a, inda Allah ya taimake su suka samu abu zaria, inda suke karantar ɓangaren lab science duk da dai sani likota ya so zama amma hakan bai samu ba


suna cikin shekarar su ta biyu a jami'a gwammatin kano ta raba scholarship, da taimakon malamin secondary ɗin su wanda ya shige musu gaba suka samu scholarship ɗin inda zasu india karatu


murna a wajen waɗannan bayin Allahn ba a cewa komai ba, ba su ba har iyayen su, gwanda mahaifiyar buhari wadda ake cewa hjy da gumin ta ɗan ta yake karatu,


amma mlm musa da iya waɗanda basu san ta yadda ɗan nasun ya samu ilimin ba ma suna ba a barsu a bayan wajen murnar ɗan su zashi india karatu, duk wani wanda yake mu'amala da iya ko mlm musa ya san da wannan zancen


a kazo aka fara shirye shiryen tafiya duk wannan ɗokin da iyayen da sani suke ko da aka zo batun kuɗi duk sai suka noƙe, sani shi yayi fafutukar shi shi kaɗai ba tareda taimakon kowa ba har Allah yasa suka ɗaga zuwa kasar india lfy don karatu


sun sauka india lfy sun fara karatun su lfy lau ba kama hannun yaro duk inda kaga ɗaya sai kaga ɗayan haka suke, sun maida hankalin su sosai akan abinda ya kawo, a haka har suka ƙare shekarar su ta farko lfy ba matsala, ba su dawo gida ba acan suka zauna sukayi hutun to in sun dawo ma wa zai basu kuɗin jigin komawa



a shekarar su ta biyu a mkrt ne Allah ya haɗa sani da matashiya ƴar saudiyya, me suna salma, da farko ƙawance ne ya ɗa su, amma daga baya sai ƙawance su ya koma soyayya


Tun suna yi a rufe har suka fito da shi kowa ya sani, salma riga sani shiga mkrt don ita a 3rd year ɗin ta take, ina take karantar medicine,


Soyayya su ce ta kaisu ga ɗaura aure don gudun gujewa ruɗun shaiɗan, buhari ya so ya hana sani yin auren nan, amma sani ƙiri ƙiri ya ƙi ya biyewa salma suka ɗaura aure, inda suke tare a sabon gidan su


soyayya suka dinga zubawa sannan ga karatun suna yi hankalin su kwance duk wanda ya gansu saisun bashi sha'awa ganin yadda suke son juna tare da tattalin junan su




Suna cikin shekara ta biyu da aure Allah ya sa salma ta samu ciki, murna sosai sani da matar sa salma suka dinga yi, suka shiga tattalin cikin,



tun buhari na kau da kai daga lamarin su har ya koma shima yayi tsamo tsamo cikin hidimar cikin siyayya sukayi sosai har Allah ya kaisu lkcn haihuwa


lami lafiya ta haihu amma ƴar ta zo ba lfy, inda bayan kwana biyu tace ga garinku nan baƙin ciki a wajen salma da sani kamar ba gobe har kuka sai da suka yi, sannan daga baya suka dangana


pls kuyi haƙuri da wannan yau uziri yai min yawa salam 🙏🏻
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺


Page :30🌹



Sai da ta ɗan huta na shekara ɗaya sannan suka kuma trying, kuma Allah ya basu sa a ta sami cikin, wannan karon ba karamin kula sosai suka ba wa salmar ba, sannan suna karatun su lfy, inda ahalin yanzu salmar tayi graduating shi kawai take jira ya gama su koma gida



Sun gama yanke shawarar cewa baza su zauna a nigeria ba sannan bazasu zauna a saudiyya ba zasu samu wani garin su zauna ne, ganin haka yasa suka yanke hukuncin zuwa nigeria salmar ta haihu daga nan sai su wuce saudiyya don dangin salmar suga babyn kafin nan sun gama shawarar inda zasu zauna



Duk wani siyayya na haihuwa sun gama, lkcn da sani ya gama course ɗin sa a lkcn cikin salma yana wata tara haihuwa ko yau ko gobe don haka sai suka shirya tafiya nigeria inda suka bar buhari zai yi musu lodin kayan su ta cargo kafin ya biyo bayan su



Sun sauka lfy a nigeria inda suka wuce jakara directly sani yaga yadda unguwar ta ƙara lalacewa, wato a nigeria in ba unguwannin masu kuɗi ba to vaza ka taɓa ganin cigaba ko, ya faɗa a ransa



A farkon layin su taxi ɗin da suka ɗauko ta faka, suka tako a ƙafa, salma tana ta mamakin irin wannan rayuwar amma bata kushe masa ba ganin shi take so kuma ba anan zasu yi rayuwa ba,



har suka cikin gidan yana mata bayanin yadda halin rayuwa yake a nan nigeria mu ita kuma tana gyaɗa kai cike da tausayawa, a tsakar gida suka ci karo da iya inda da sairi sani ya je ya rungume ta



waigowa iya tayi cike da tsoro waye wannan, ganin ɗan ta da ta daɗe bata gani ba yasa yin saurin ƙara ruƙunƙume shi, tare da sakin kuka, sai daya rarrashe tayi shiru, sannan ya nuna mata salma wacce tun shigowar su tana tsaye tana kallon su
"iya ga matata dana aura a india, amma ƴar saudiyyace" ya faɗa yama miƙa salma hannu wanda ita kuma ta ƙaraso tare da riƙe hannun nasa



wani shegen kallo iyar ta bita da shi daga sama har ƙasa, ganin salmar da tsohon ciki ya sa iyar ƙara murtuke fuskar ta
"abinda kaje ka koyo kenan a indiar, kazo da mace da tsohon ciki kace matar kace, uban waye ya ɗaura maka aure da ita, ko an gaya maka saboda bamu da ilimi yasa kake tunani cewar bamusan sai da aure ake kiran ɗa ɗan halak ba" ta faɗa tana miƙa wa salmar harara, wanda hakan ne yasa salmar sunkuyar da kanta tare da ƙara shigewa jikin mijin nata


wannan abun da salmar tayi ƙara tunzurawa iyar rai yayi"au karuwancin da kuke yi zaku zo ku ƙara nuna min a gaba na, ai ba sai kun kwatan ta ba cikin da ke jikin ki ya isa ya nuna sheƙe ayar da kike yi da wasu mazan"
"iya ba fa haka bane wallahi matata ce, sai da na aure ta fa sannan, wannan ma ba shine na farko ba ta farkon ta rasu"
"kawai cewa zakayi ta gama zuzzubar da cikin mutane shine wannan ta ƙi zubar da shi ta maƙala maka, ta wai ma waye shaidar cewa ka aure tan"


"iya buhari mana shima yana nan tahowa cikin satin nan"
"ni zaka rufe a bai bai, to wallahi ban yadda cikkn nan ba naka bane shege ne, kuma bazan yadda ka zauna da karuwa ba sai dai ka ƙyale ta ta koma can gari su taje taci gaba da watsewar ta, haka kurum bazan haɗa zuri'a da kuruwai ba"


"iya don Allah kidaina faɗin hakan wallahi matata ce"
"wai baka ji me nace bane ban yadda ba, me kake in cewa mutane sani ya je turai ya dawomin da karuwa a matsayin matar sa harda cikin shege, wallahi ƙarya kake ban tonawa kaina asiri ba babu ɗan da ya isa ya tona min" ta faɗa tana gyara kallabin wanda sauran ƙiris ya faɗi saboda tsabar masifa



babu yadda sani baiyi ba don ya fahimtar da iya amma ta rufe idon ta tai ta tafka bala'in tun suna yi su kaɗai har ƴaƴanta suka fara shigowa suna taruwa


duk wanda ya shigo yaga sani ya dawo sai ya fara murna amma da yaji faɗan da iya take yi sai su koma bayan ta suna goyan bayan ta na bai isa ya haɗa su da shege ba, a cikin faɗan nasu ne ma yaji rasuwar mahaifinsu shekara uku da suka wuce abu goma da ashirin suka haɗu suka haɗar masa ya rasa acikin ƴen uwan nasa wanda zai ɗan fahimce ahi koda so ɗaya ne su dai burin su kawai ya kori salma da cikin da ke jikin ta, su tsaya ma suji abinda zai ce su ƙi kawai haniya suke yi tsakanin su tare da rantsuwar baza su zauna da karuwa ba



kasancewar gidan su buhari katangar su ɗaya da su sani yasa hjyr su buharin jin hayaniyar tasu, tasan tsakanin iya ne da ƴaƴanta kamar karta shiga sai kuma wata zuciyar tace ki shiga haƙƙin maƙotaka ce tasa, hijabin ta dake jikin ƙyaure ta ɗauko ta saka tayi gidan iya


ko da shiga taga sani tayi mamaki amma sai ta danne don sulhu ta zo yi daga baya taji lbrn ɗan natan, tambayar abinda ya faru tayi inda wata matar wan sanin tayi wa hjy bayanin abinda ya faru, to ita hjy bata ga abin tada jijiyoyin wuya ba menene don yaro ya auro farar mace ta faɗa



har wajen iyar tajee tayi mata nasiha akan tabi abin a sannu don a samu a shawo kan maganar amma iyar ko sauraran ta batayi ba inda daga ƙarshe ta ƙare wa hjyr tanadi tas har da cewa ita taga ɗan ta ita ma ta jira taga da wace tsararbar ɗan natan zai zo mata dashi



ba haka hjy ta so ba ta so iyar ta kwantar da hankalin ta har a samu bakin zaren amma daga dukkan alamu iyar ta riga tayi nisa kuma harda laifin ƴaƴanta don kuwa su suke ƙara zugata, can ta hango sanin idon shi ya kaɗa yayi jajir sai lallaɓa matar da yazo da ita yake yi wacce ita kuma take a tsugunne tana kuka, su kuma ƴen uwan nasa suna gurin iyar suna ta zigata




har kusa da shi hjyr ta ƙarasa tayi masa nasiha sosai akan darajar uwa sannan ta kama hanyar gida don bata ga alamar iyar tana da niyyar sauraren wani a wannan lkcn ba


haka aka wuni ana abu ɗaya babu sassau a cikin lamarin ta tubure sosai sai salmar ta bar gida, inda maƙarraban ta ke zigata


sani hankalin shi ya kasu biyu ga faɗan da iya take tayi ta ƙi shiru duk tabi ta tara mutanen unguwa ta sheganta masa ɗa tun kafin ya zo duniya, ga ita kuma salmar ta tada hankalinta baza iya zama ba tafiya zata yi, ga wani azababben ciwon kai da yake damun sa wanda ya sashi yaka ganin dishi dishi, matsawa yayi kusa da salmar wadda har yanzu take kuka domin ya lallashe ta amma ga mamakin sa jikin ta zafi rau da shi


"subhanallahi salma zazzaɓi kike yi ne" ya faɗa yana ƙara taɓa jikin ta tabbaa zazzaɓi ne, tausayin ta ne ƙara rufe
"isbiri la tabki habibti" ya faɗa tare da share mata hawayen da suke gangariwa daga idon ta
"saufa ashtari lakkid dawa" gyaɗa kanta kawai tayi, tare da gyara zaman ta


tashi yayi ya miƙe don ya je ya samo mata magani, dole ne ya bar salma ta tafi saudiyya, dole ne ya haƙura salma har sai Allah ya daidaita su da mahaifiyar sa dole ne salma ta tafi in ya so idan ya fahimtar da iyar cewar salmar halak malak ɗin sa ce in yaso daga baya sai su kuma tsara yadda zasu ci gaba da rayuwar su, amma bazai iya rayuwa ba salma ba taya ma zai iya rayuwa babu salma a cikin ta dole yasan yadda zai yi salma ta riga ta zama komai na shi na rayuwar zai san yadda yayi ya shawo hankalin iyar bayan ya mayar da salmar yasa ganin salmar anan ne yasa iyar tayar da hankalin ta amma da zarar salmar bata anan idan hankalin iyar ya kwanta in shaa Allah zai san yadda zai shawo kanta ta yadda da auren nasu da salma hakan zaiyi ya faɗa yana gyaɗa kansa




gabaki ɗaya tafiya yake yi amma sam bai san inda yake jefa ƙafarsa ba don yayi zurfi a cikin tunani, baya iya ganin komai kawai tafiya yake yi ƙugin mota kawai yaji tare da sunkuce shi da motar tayi ta maka shi da ƙasa wani azababben zafine yaji ya ziyarci kansa wanda bai taɓa ji ba, ƙoƙari yayi don ya motsa amma sai ya kasa, idon shi a buɗe suke amma baya gani komai sai duhu haniyar mutane yaji suna ƙarasowa inda yake
"kar ku taɓa shi kanshi ne ya fashe yake zubar da jini" tun yana iya fahintar abinda suke cewa har ya koma ya daina


inna lillahi wa inna ilaihir raji'un ai ya mutu inji wani daga gefe
[7:45PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the

16 / 33