Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
a matsayin matar sa
Sun sha koke koke sun kana gada ƙarshe aka kaimu masauƙin mu, dangin mimma babban dangin ne sosai a cikin garin makka, mun zazzaga su kana daga bisani muka koma ainihin gidan mimma wanda ta gada a wajen mahaifin ta
Sai da na kusan arba'in sannan tj ya zo duk ya rame kamar ba shi ba sai a lkcn ya sanar da aliyun mutuwar salma, kuka ne kawai aliyun be yi na tausayawa ɗan uwansa da yayi tare da kuma ƴar ta da ta bari
Sai da tj ya nutsu ne sannan aliyu yace masa yana son ya raka shi gidan ummu yahya zai mata godiya, tj ma ya yadda da hakan don haka sai muka fara shirin zuwa madina gurin ummu yahya,
Da sassafe muka shirya muka kama hanyar madina, bamu isa ba sai azahar don haka directly masallaci muka wuce inda tj ya tafi kama mana hotel
Sai da muka sallaci isha'i sannan muka koma hotel ɗin da aka ka mana wanda bashi da nisa da haram ɗin, wanka nayi kawai na hau gado sai bacci, ina jin aliyi ya shigo yana min mitar
"matar nan tun da akai min aikin nan na fahimci gudu na kike yi yanzu ma dana gama budgeting in mun zo madina muyi honey moon shine kafin ma in shigo har kin yi bacci ko"
Ban kula shi ba bacci na kawai na cigaba da yi don bacci ne sosai a kai na, kyakkyawar runguma naji yayi sannan shima baccin ya kwashe shi
Kashegari sai da azahar sannan muka koma harami sai da mukai la'asar sannan muka fito don zuwa gidan ummu yahya, wani kanti muka fara tsayawa tj yai musu siyayya sannan muka kama hanyar gidan, ɗan tafiya ne babu laifi sannan muka zo, inda mukai parking mota muka fito, gangarwa za a yi a shiga wani lungu don haka sai tafiyar ƙafa
Su aliyu suka samu wasu yaran suka ɗau musu kayan sannan muka kama hanya, gida na uku a layin muka tsaya inda tj ya ce mu shiga ni da mimma muyi musu magana
Ƙwanƙwasa ɗan ƙyauren gida mukai, wata ƴar dattijuwa ta zo ta buɗe da fara'ar ta, muka gaisa sannan tace bata gane mu ba, tj ne ya matso ko da ta ganshi sai ta ɗan tsorata don ta san bata nuna masa gidan ba
Hanya ta buɗe mana muka shiga gidan, ɗan ƙaramin gida da ɗan tsakar gida sai ɗakuna guda uku da banɗaki ɗaya da kitchen a cikin gida sai kuma uban shirgi daga wani lungu can ƙarshen gidan
Ɗakin farko tai mana izinin mu shiga, muka shiga da sallama, babu komai a ciki sai dadduma sai tv akan tv stand ɗinta da wani yaro yana zaune yana kallon cartoon
Ko da muka shiga yaron kawai bin mu yayi da kallo tj ne yace
"al amin ta'al" da ɗan gudun sa ya taho ya faɗa jikin tj yana dariya tare da ce masa abbu,
"ɗan yahya ne wannan" inji tj, wayyo Allah na sai naji tausayin yaron har ƙwalla ta cika min ido, aliyu ne ya miƙa hannu ya ɗauke be ƙiba shi ma aliyun sai al amin ya kira shi da abbu
A daidai lkcn ummu yahya ta shigo da tray da lemu da ruwa akai inda naji tana yi al amin larabci, mimma ce ta tanka mata, inda daga baya mimma take faɗa mana wai ummu yahya tace al amin kar ya ƙara kiran mutane da abbun sa ba ta faɗa masa abbun sa yayi tafiya ba
Aliyu ne ya gyara zama sannan ya kalli ummu yahya ya tambayeta tana jin turanci, da murmushin ta ta gyɗa kai
"daga yanzu nine abbun yaron nan, don zuciyar abbun sa a jikina don haka babu abinda ya baban tani da abbun sa, baƙi idan kin ce masa kar ya kira wasu da abbun sa ba amma ni abbun sa ne"
Hawaye taf ya cika a idon ummu yahya inda take faɗa mana tunda mahaifin yaron nan ya rasu duk wanda ya gani sai ya kira da abbun sa
"to kar ka samu damuwa ga abbun ka ya dawo kaji al amin" aliyu ya faɗa yana shafa kan yaron kamar al amin ɗin yana ji
Tj ne ya ɗan tambayi matar yahya inda ummu yahya tace tana wajen aiki,
"aiki kuma, ai bata fita takaba ba"
"addini ya halatta mace ta nemi abinda zata rufa wa kan ta asiri koda tana takaba" ummu yahya ta faɗa
Haka ne amma ummu yahya ina dangin ku" inji mimma, sai da ummu yahya ta ɗan nutsa sosai sannan ta fara magana
" mu mutanen syria ne yau shekarar mu uku kenan a nan yaƙi ne ya koro mu daga syria, inda muka rasa duk wani dangi namu a cikin yaƙin yayana wanda ya kasance mahaifin nadia matar yahya kenan da matar sa da ƴaƴan sa, a gabana aka harbe su ina laɓe ya hana ni fito wa
Mijina uban yahya shima aka kashe shi a kan idon na don haka sai mukai ƙaura da ni da yahya da nadia muka taho da taimakon wani ɗan uwan mahaifiyar nadia wanda yakan sance yana taimakawa mutane suna tsira daga tashin hankalin nan
Tunda muka zo nan na ɗaura wa yahya da nadia aure don bana son in tafi in barsu su kaɗai ba tare da aure ba amma kunga inda aure a tsakanin su bazan ji komai don Allah ya ɗauki raina ba nasan na bar su a matsayin ma'aurata" ta daka ta
"daga yanzu ni zan ci gaba da kula da ku ni zan maye gurbin yahya in shaa Allah" inji aliyu
ummu yahya ƙi tayi sai da su mimma suka ba ki sannan ta yadda har da kukan ta,mimma ce ta ɗauki baby yahya wanda muke kila da mu'allim ta bawa ummu yahya
"ga yahya mun kuma samu, matar aliyu ta haifa" da hawaye a idon ta ta karɓe shi tayi kissing ɗin shi sannan ta rungume shi,
mun jima acan inda aliyu da tj suka fita suka barmu
ni nayi wa ummu yahya girki, sai kusan shida sannan nadia ta dawo, mun gaisa sosai da inda inda ummu yahya tayi mata bayanin mu muƙa ɗan taɓa yar hira sannan su aliyu suka zo muka tafi
Satin mu biyu muka koma nigeria mimma ma nigeria ta bimu, ashe ta kashe auren ta bamu sani ba wai dama rashin aliyu ne yasa ta zaman auren amma yanzu taga ɗan ta baza kuma rayuwa babu shi kusa da ita ba
Bamu daɗe da komawa ba su mama suka zo da su maryam suka zo duba aliyu, inda aka dawo da su haidar
Ko da suka tashi tafiya sai aliyu yace amina ta zauna, mama taji daɗi sosai da aliyi yace zai riƙe amina, ko da suka tashi tafiya aliyi yayi musu kyauta sannan ya kuma tuna musu da tafiyar su hajjin su
Aliyu ya ɗora tj akan kula da su ummu yahya, komai suke so da komai na al amin tj ɗin yayi musu
Nima naje kano nayi wa ƴen uwan salma gaisuwa tare da ɗauko islam ta dawo hannun na don naga sai pasin pasin akeyi da ita tj yaji daɗi sosai aliyu ma ya dawo da tj aiki nan kusa da mu a abuja inda ya gina musu gida kusa da juna shi da mimma wanda yake ƙasan jikin namu
Kowannen gida part biyu akai masa mimma tayi ta mita wai ita gidan da aka gina mata yai mata girma sosai don haka sai aliyu ya bata haidar da mohd su koma wajen ta duk da haka gidan part ɗaya kawai take anfani da shi
lkcn tafiyar hajji yayi su mama suka tafi mu kuma muka bi ta international muka je hajji ban ma san dani za ayi ba mun yi aikin hajji lfy mun gama sannan muka dawo, muka je madina domin gaisawa da ummu yahya
[7:47PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: [12/7, 7:20 PM] Mmn Waleed💖: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:56🌹
*last page in shaa Allah tank u sooo much 4 ur support babu abinda zance sai shukran gare ku masoyan dangin sa yau Allah ya kawo ƙarshen littafin da fatan kun ji daɗin sa*
*ina fatan zaku saurare ni a sabon littafina me sunan*
💐💐 *RABO NACE*💐💐💐
*ana mugun tare*🤝
[12/7, 7:20 PM] Mmn Waleed💖: Mun je gidan ummu yahya inda muka same babu lfy sosai amma kuma tace an sallame ta ne ma daga asibiti, aliyu yai ta faɗan tj be faɗa masa amma sai ummu yahya tace ai shima be sani ba itace ta faɗawa nadia kar ta faɗa don kar hankalin wani ya tashi
Karɓar mu'allim yahya tayi a hannuna tana shinshinashi tare da sunbatar sa ina iya hango wasu hawaye a idon ta amma si tayi koƙarin mai da su nima sai nayi kamar ban gani ba
Aliyi ne ya matsa kusa da ita
"ummu yanzu kema fa uwa ce gare ni don me zakice kar a faɗa mana ciwon ko gaskiya ban ji daɗi ba"
Haƙuri ta dinga bashi, muka tambayi nadia da al amin ummu yahya tace sun je kasuwa don kuwa nadia ta fita takaba, mun ɗan jima sai ga nadia ita ma aliyu yai mata faɗan cewar kar ummu ta ƙara ciwo bata kira shi ko tj ta faɗa ba
Kanta a ƙasa ta ansa, sai magariba sannan muka tashi tafiya sai ummu yahya tace
"Aliyu zamu koma syria ni da nadia da al amin mun gode sosai da ɗawainiyar da kake yi da mu"
Daga ni har shi ɗin bamu san lkcn da muka dawo ba daɓar haka na zauna a ƙasa
"ummu yahya syria me zakiyi a syria yanzu"
Murmushi tayi sannan tace
"bana son in mutu in bar nadia ita kaɗai sai wannan ɗan yaron shiyasa nake son maida ita cikin dangi, ko da de babu na kusa amma ai bazamu rasa dangi ba"
Kuka na saka mata
"don Allah ummu yahya karki koma syria ya za ai al amin ya tashi a syria a wannan tashin hankalin da ake fama da shi a syriar zaki kai yaron da bai son tashin hankali ba can, don Allah ummu yahya ku zauna anan"
Aliyu ne ya katse min maganata
"nima gaskiya hankalina be kwanta da zaman da kuke yi ku kaɗai anan ba, amma kuma syria ba gurin zuwa bane, me zai hana ku bimu nigeria sai ku zauna da mu tunda mun ruga mun zama ɗaya" aliyu ya faɗa
Kallon kallo muka tsaya muna yi inda daga ƙarshe ummu yahya tace ita bata yadda ba tunda take bata taɓa zama liability ba kuma in shaa Allah da tsufanta baza ta zama ba
Babu yadda bamu yi ba amma ummu yahya ta riga ta kafe sai sun koma syria haka muka tashi muka koma masauƙin mu ni dai zuciyata gabaɗaya bata kwanta min da tafiyar nan syria ba garin da kwata kwata basu da zaman lfy
Ko da muka zo kwanciya na so imu ƙara maganar amma sai aliyu ya hana ni yace da safe zai ƙara komawa wajen ta in shaa Allah
Da gari ya waye aliyu be samu damar zuwa gidan ummu yahya ba sai ni naje na same su suna ta haɗa kayan su wai ƙarshen watan nan zasu koma
Ɗaki na shiga kusa da ummu yahya na zauna akan tafiyar na cigaba da yi mata magiya amma sai tayi murmushi tace
" zainab na riga na gama yanke shawara, kuma in banda abinki in muka biku a wane matsayi muke a wajen ku"
"aliyu yace zai auri nadia" kawai naji baki ya furta
Ɗagowa tayi ta kalle ni sosai taga a magana ta babu ƙarya duk da dai ƙaryar nake yi, don Allah ya za ayi in bar ɗan yaron da zuciyar uban sa take ƙirjin mijina shiga cikin tashin hankalin bayan nasan cewar ƙaddarar uban sa ta haɗu da ta mijina in ban taimaka masa ba ai na zama butulu ban gode wa Allah ba ƙenan
Ajiya zuciya ummu yahya tayi sannan tace
"Zainab kin gani auren nadia da yahya ni na haɗa su ba wai son take yi ba amma saboda ni nawa tunanin ya bani cewar wannan shine mafita bata so haka na haɗa, yanzu kuma kice in kuma tursasata ta auri mijinki saboda wai mu je mu raɓu kusa da mu wallah bazan iya ba, amma kuma bazan hanaki tambayar ta kije kiji inta yarda ni banni da ta cewa"
Fita nayi na samu nadia tana haɗa kayan su al amin yana wasa kusa da ita zama nayi na zayyano mata ban ɓoye mata komai ba amma sai na ɓoye mata cewar ni na nemi auren
Shiru tayi kamar bata yadda ba sai dana ƙara nuna mata illar komawar su syria ko ta yadda zai shafi rayuwar ɗan ta sanna da ƙyar ta aamince tana kuka ban san ko kukan me take yi ba amma daga dukkan alamu tana tuna tsohon mijin ta ne
Ɗakin na koma na faɗawa ummu yahya murmushi tayi sanna tace maa shaa Allah
Sai da aliyu ya dawo gida da ddare sannan na faɗa masa ɓaran ɓaramar da naje nayi kamar ya rufe ni da duka haka yai ta min faɗa ni dai shiru nayi ina kallon ikon Allah be haƙura ba har sai da na kira mimma na faɗa mata itama tace hakan shine dai dai sai da tayi masa magana sannan ya sauko ya yadda
Oh Allah ni abu naga ta kaina wai macen da za ayi wa kishiya zaka ganta ana lallaɓa ta amma banda ni wai ni nake lallaɓa mijin na nayi abu kaɗan sai yace
"wallahi kika ɓata min sai ma ince na fasa auren" sai in bishi da ban haƙuri
Dole na danne kishi na na ci gaba da lallaɓa mijin nawa wanda aka saka ranar ɗaurin sa sati biyu masu zuwa, na kira tj na faɗa nayi mamakin da naji kamar be yi murna ba amma kuma sai na share don tunda salma ta rasu tj ya koma wani salihi
Aliyu ya tubure shi ƙwandalar shi ba za tai ciwon kai ba a auren ni dana ɗauko auren sai in yi masa, haka na zage dantse don ma su nadiar sunce basa son komai na bidia kawai a bada sadaki amma kuma dole ayi wa amarya sutura, don haka kullum sai na fita kasuwa don siyowa amarya lefe
In na dawo gogan ko ta kaina baya bi sai dai kawai yai ta cewa aikin sa kai nake yi don haka bana buƙatar sannu sai kace in na aura masa ita ni zan more ta, don Allah ƴen uwa ba daga ya shiga wannan babban ɗakin ya kwashi roman damokaraɗiyyar da ke tattare da ɗakin ba ba kuma sai a hankali ba, namiji fa duk inda yake namiji ne daga an buɗe masa wannan ƙofar ya shiga ya ji abinda ke ciki shike nan an gama zance, amma dubi yadda yake min
Ana gobe ɗaurin aure ne muna zaune da shi yana kallon news ni kuma ina ƙara haɗa kayan mu don ana gama ɗaurin auren zamu koma nigeria
"habibi na ɗauka tj zai zo"
"me ze zo yayi miki" ya tambaya ba tare da ya kalli inda nake ba
"auren ka mana ya kamata ace yana nan"
"auren dolen de da kike son yi wa mijin ki, ni wallahi ban taɓa ganin mace irin ki ba wai da yiwa miji aure" ya faɗa yana yatsine fuskar sa, taɓe bakina nayi don banni da ta cewa
Wayata ce ta fara ringing dubawa nayi naga number nadia, ɗauka nayi da fara a ta
"our bride to be in shaa Allah" na faɗa a zolaye murmushi tayi sannan ta gaishe ni
"dama number abu haidar nake"
"zakiyi masa magana ne" na tambaye ta
"eeeh ina son magana da shi ne"
"ok gashi ma kusa da ni" miƙa masa waya nai sannan na tsokane shi
"amaryar ka tana son jin muryar ka" ƙin karɓa yayi da farko sai da na tashi daga inda nake na zauna akan ƙafar sa sannan na kara masa wayar a kunne sa, sai da naji ya ansa sallama sannan na sakar masa wayar na bar wurin don kar zuciya ta kwashe ni
Sai da ya gama sannan ya shigo ɗakin da fara'ar sa daga gani ta faranta masa ne, kusa dani ya zauna
"habibti ga wayar ki, ashe yarinyar nan haka take kai gaskiya na gode da kike son haɗa ni da ita hmmmm *rangaɗi* gaskiya ta haɗu"
Wani ƙululun bakin ciki ne ya tokare min wuya sai nayi kamar banji shi ba, surutun shi ya dinga yi dana gaji kawai sai nahaɗe bakin da nashi don bana son in furta komai don