Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
wata takarda ta bani wai idan aliyu ya warke in bashi
Hannuna yana rawa na karɓa idona taf da hawaye na faɗa mata abinda tj yace murmushi tayi "ba komai duk abinda ya kamata ayi za ayi" ta faɗa tana shigewa office ɗin ɗr. ɗin
Jimawa kaɗan sai gata ta fito idon ta cike da ƙwalla binta nayi na riƙe ta mimma lfy
"wai dr.yace my heart is weak ba za a iya bawa aliyu ba he need a strong heart" kuka ta fashe da shi babu abinda nake yi sai hamdala don nasan mijina ba zai so ya rayu da zuciyar mmn shi ba
Tj be ƙaraso ba sai dare asibitin ya wuto direct, nan ya samu halin da ɗan uwansa yake ciki shima keɓewa yayi da dr. yace wai a cire tasa a sawa aliyun tooooo😳😳😳
Shima dr. ɗin yace ba za a cire tasa ba don he is very healthy kuma basa cire zuciyar lafiyayyen mutum su sawa mara lfy don ba shi da 100% na surviving bayan opperation ɗin, sukan fison zuciyar mutumin da yayi accident kuma aka fidda ran shi amma mutumin da yake da rai basa wannan gangancin
Sai alkcn na fahinci kenan hakan ne amma yayi wa mimma ƙarya, cakumar wuyar rigar shi mimma tayi tace
"ka cire min zuciyar da ke jikina ka sawa ɗana gwanda in mutu shi ya rayu, bazan iya rayuwa babu shiba pls pls pls" sai ta sa kuka
dr ɗin ya basu haƙuri tare da cewar ai samun zuciya ba wani abun bane kullum sai an mutu don haka kawai suje donation office su cike form the earlier the better
Tj ya faɗa masa cewar "mu musulmai ne zamu fi buƙatar zuciyar musulmi"
"dont worry if u r lucky u can find a muslin dying" ya faɗa yana fita
Donation dept ɗin muka je muka cike form, sannan suka ce mana muje idan an samu za a yi mana magana, da daddare bayan mun fito daga asibitin muka wuce manchester muka ɗauko yaran anan nake faɗawa junior abinda ya samu aliyun ya tausaya mana sosai sannan yace akwai abokin sa a nan asibitin manchestan zai yi masa magana ko za a samu zuciyar"
Godiya mukai masa sosai sannan muka fito da yaran, mama na kira na faɗa mata halin da aliyun yake ciki har da kukan mama, na ce mata zan turo su amina can har da su haidar su zauna a wajen ta har sai abinda hali yayi
A ranar su haidar su kar england kuka kawai nakeyi ina tausayin ƴaƴa na yanzu idan aka ce ba uban su ya zasu yi duk da de dukiyar da aliyu ya tara tafi ƙarfin ace ta ƙare nan kusa ko da juyata akeyi amma kuma uba kuma faaa Allah ka tashi mijina kasa a samu zuciyar nan
a daren muka koma liverpool ɗin, muka koma da sassafe muka je asibitin muna zuwa akai mana albishirin an samu zuciya murna kamar me amma kuma ba ta musulmi bace, nan fa murna ta koma ciki
*****************
yau kusan watan mu biyu a asibitin aliyu yana dai kwance a gaskiya innace a kwanciyar mu ba a samu zuciya ba nayi ƙarya don har wani aka kawo shima da irin matsalar aliyu amma ana samun zuciya aka biya aka yi masa dashen tunda shi kafiri ne, zuciyar musulmi tayi wuya sosai kasancewar ba garin musulmai bane
Kuma da in bari a sawa mijina zuciyar wanda ba musulmi ba gwanda in barshi a haka ƙia yanzu idan ya mutu ya wuce aljanna wacce haka muke fata amma idan aka saka masa ta kafiri fa ya zo yana kafirci bayan shekaru ɗari ya mutu ya shiga wuta fa ai ba ƙaunar sa nake yi ba
Tj da mimma sun so a saka masa kowacce ce amma ni na dage akan bazan yadda ba, bawai ba sa ƙaunar sa ba amma suna tuananin yadda zasu ne idan baya nan, mimma tana ganin Allah ya haɗa ta da ɗanta don haka bazabta bar shi ya mutu ba shi kuma tj yana ganin ba zai iya ba in babu ɗan uwan sa, inda na biye musu da tuni anyi aliyu aikin nan amma naƙi, naga gabaki ɗayan su hankalin su ba a jikin su ba don haka ni kuma sai na zama jaruma dole a cikin mu a samu jarumin in ba haka ba sai yadda hali yayi
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:53🌹
Bayan zaman asibitin ya ishi dr. ɗin aliyu ya ga babu wani cigaba ganin munƙi yadda da kowane zuciya indai ba ta musulmi ba, dr. yai mamaki sosai wai ne yasa bama son kowace zuciya, nai masa bayani zuciya ita ce mutum hadisi ne guda da ma'aiki saw yake cewa "akwai wata tsoka a jikin ɗan adan idan ta gyaru komai na jikin sa ya gyaru idan kuma ta ɓaci komai na jikin sa ya ɓaci" idan kuwa haka ne don me zan bari a sawa mijina zuciyar kafiri, bayan wnnan tsokar da ma'aiki (saw) yake magana ba kowacce bace face zuciyar ɗan adam
Don me zan bari a sawa mijina zuciyar da take ba a gyare ba, ko kaɗan dr. be fahimta ba, a zuciyata nace tayaya zaka fahimta tunda ba imani gare ka ba
"to yanzu zaku so kuga ɗan wanku ya mutu bayan ga zuciya," murmushi nayi tare da gyaɗa kaina
"in dai har haka ƙaddarar sa tace zan barshi ya mutu a matsayin sa na musulmi zan fi son haka akan in bari a saka masa zuciyar kafiri"
Sam dr. kasa fahimtar mu yayi don haka sai ya kawo mana shawarar mu canzawa aliyu asibiti wai akwai wani dr. Shima cardiologist ne tare sukai karatu kuma musulmi ne a ƙasar musulmai yake mu koma can ko Allah zai sa mudace amma zaman da mukr yi anan kamar zaman jiran mutuwar sa muke tun da babu wani hope
Nayi murna sosai ko ba komai akwai chances ƙila aliyu ya samu zuciya, a saudiyya cardialogist ɗin yake dr. ɗin namu yai masa magana tare da tura masa duk wani halin da aliyu yake ciki, ƙasancewar aikin sa ne nan da nan yace mu taho
Ƴ
Muka fara shirye shiryen komawa saudiyya, garin ta'if da ke ƙasar saudiyya anan asibitin yake, akan babban titin shiga garin yake kafin ma ka shiga cikin gari, ƙaton asibiti ne, wanda kamar branch ne na asibitin amri hospitals wani asibitin aikin zuciyane a india
Kana ƙarasowa zaka ga sunan asibitin wato *amri hospitals (annex)* muka shiga da shi wanda tun daga airport ɗin jidda ambulance taje ta ɗauko kasancewar aliyu bazai iya ci gaba da numfashi ba in dai babu oxygen don haka dole ne sai da medical practitioner kusa, duk da dai mimma pediatric ce amma ba za ayi bata kulawa da shi ba kasancewar mahaifiyar sa ce
Muna shiga da shi aka shiga da shi theater again don sai sun sake duba shi, sun daɗe don kusan awan su takwas da shi a theater inda daga ƙarshe suka fito
Binsu mukai gabaɗayan mu inda muka damu dr. Hisham shi kaɗai a office ɗin sa, wurin zama ya nuna mana muka zauna sannan shima ya zauna tare da ɗauko file ɗin aliyu
"a binciken da muka yi ya nuna aliyu is in a critical condition, ya buƙatar urgent heart transplant, don haka dole muyi yadda zamuyi don samun zuciyar don kuwa nan da 2weeks in bai samu zuciyar ba komai ze iya faruwa"
Ya faɗa da confidence a tattare da shi, shiru kawai mukai dukan mu, mun rasa ma me yin magana a cikin mu wai sati biyu, nice ma nayi ƙoƙarin yin magana
"yanzu kana ganin nan da sati biyun zamu iya samun zuciyar"
"ya dangan ta, amma akwai chances na za a asamu tunda kullum mutuwa ake yi a duniya, in shaa Allah yau na daka team akan su ne mo mana zuciya a kowane asibitin in shaa Allah za a samu"
Anan ma sai da mimma tace a saka masa zuciyar ta dr. Hisaham dariya yayi, yace mata mu musulmai ne wannan abinda ya samu ɗan uwan naku ƙaddara ce, ba abinda ya kamata da ya wuce muyi masa adduar Allah ya bashi lfy,
Amma ina kuka taɓa ganin an cire zuciyar lafiyayye don a sawa mara lafiyar da chances na survival ɗin sa is not stable, ku bari kawai mu duba yadda muka saba ba yau na fara wannan aikin ba, kuma in shaa Allah zai warke, ɗan uwanku bashi da wata matsala da ta wuce ta zuciyar sa mun duba duka organs ɗin jikin sa they are ok and fit don haka daga anyi transplant ɗin in shaa Allah shike nan"
Allah ya sa muka ansa baki ɗaya sannan dr. Hisham ya sallame mu,aka fara neman zuciya
Kullum sa rai muke yi ko zamuji an damu zuciya abin takaici yawancin mutanen da ake kawo wa zuciyoyin na da matsala, ko ace hayaƙin taba yayi wa zuciyar illa ko kuma dai wani matsala na daban ga kuma lkc kullum ƙara wucewa yake yi
Kuma jikin aliyu a kullum ƙara tsanan ta yake, inda dr. Hisham yake shaida mana cewar da lkc ya cika zai cire wa aliyu abinda yake taimaka maka bugun zuciyar, don shima yana da lkcn expiring
Ko kaɗan kasa fahimta nayi sai na tanbayeshi to idan ka cire masa kuma yaya zai yi, shiru likitan yayi sannan yace
"shi wannan abun da kike gani akwai lkcn da yake aiki, idan zuciyata ta kai certain point na weakness to barin abun a jikin mutum ya fi cire shi haɗari, don me makon ta taimaka masa sai ta kashe shi so gwanda a cire in dai har lkcn ya yi"
"to in aka cire kana ganin zai daɗe har mu damu zuciyar"
"a yadda zuciyar mijinki take yanzu in aka cire masa zai iya yin awa sha shida, amma daga nan sai yadda hali yayi bazan muku guarantine zai ci gaba daga nan ba" shiri kawai nayi ni yanzu ma bana kuka idan naji halin da ake tunanin mijina nan gaba don kullum sai ka ƙara jin wani matsalar
Yau ana saura kwana biyu appointment date ɗin cirewa aliyu abinda yake sa shi bugun zuciya yayi, ya tashi tun da muka zo saudiyya sai yanzu ya farka, yayi fari ya wani ɗashe kamar ba shi ba
Zuwa nayi kusa da shi na tashe shi a daidai lkcn tj da mimma suka shigo don sunje neman zuciya amma daga ganin fuskokin su an san ba a dace ba
"ɗan uwa ka farka"
"gyaɗa masa kansa yayi amma be ce komai ba" kira likita mukai yi ko za a iya bashi wani abun yaci, amma likitan yace kar a bashi komai nurses ɗin su zasu masa preparing abinda zai ci
Aliyu ya gyara zaman sa sosai inda mimma ta zauna kusa da shi tare da dafa shi ya kalle ta yayi murmushi nayi mamakin da ya canza na ɗauka idan ya farka ya ganta zai haukace amma sai na ga saɓanin hakan
"pls ki yafe min da duk abinda nayi miki..................." bata bari ya ƙarasa ba ta rufe masa bakinsa, ta fara kuka tana bashi haƙurin itace ya kamata ta roƙi gafarar sa
Nima sai suka bani tausayi, aliyu sai ya fara barin wai wasiyya................ Hmmmm babbar magana
"tj don Allah idan na mutu ka auri zainab ka riƙe min ƴaƴa na" ya juyo gare ni
"naso ace na zama uba da miji da jigo gare ku ke da ƴaƴa na amma ban ga hakan na shirin faruwa ba don Allah ki kular min da ƴaƴa na kuma ga ɗan uwanan ki aure shi shi kaɗai ne zai iya kular min da ku" kuka ne ya kwace min inda tj ya matso har kusa da aliyun sannan yace
"ni ban karɓi wannan amanar taka ba idan zaka tashi ka kula da iyalinka ka tashi idan kuma baza ka tashi ba shike nan ni dai ban karɓi wannan amanar ba" yana gama faɗin hakan ya fice sosai na ga alamar kuka a tattarebda shi daga gani baya son yi ne a gaban mu
Mimma da bata san abinda yake faruwa ba ta tambayeni na faɗa mata ita ma kukan take yi
"haba ya za ka faɗi haka na rayu akan rashin sanin kana raye yanzu na ganka kace kuma zaka kuma barina, tayaya kake shirin inyi iya rayuwa babu kai, ada ina da ƙuruciya shi yasa na iya jurewa amma yanzu i cant do wihtout u"
Kuka duk muka sa inda aliyun yake ƙara jaddawa mimma ta kular masa da mu ita kuma tana girgiza kai, muna cikin wannan halin ne zuciyar aliyun ta kuma motsawa wayyo Allah dai kun tausaya masa yadda yake yi gaba ki ɗaya lkc ɗaya ya fita hayyaci sa switch ɗin da ke kusa da gadon sa na danna nan da nan sai ga likitoci sun danno suna zuwa kora mu waje sannan suka fara aikin sun babu kama hannun yaro
Fitar mu ke da wuya sai ga wata mata ta shigo tana rusa ihu wai a taimaka mata ihu take yi iya ƙarfin ta, nurses ɗin asibitin ne suka fito da gudu sai ga shi an shigo da wani akan wheelchair duk jikin sa jini barin ma kansa an ɗaure kan da wani ƙaton bandage amma duk da haka jinin zuba yake, theater aka wuce da shi directly
Basu jima ba sai ga dr.hisham ya fito daga theater room ya doso wajen matar, da larabci naji yana mata magana don haka ban ganr me yake cewa sai kukan ta kawai na kuma ji sai ta bani tausayi
Lallashin ta ya dinga yi sannan ya ce wata nurse ta kawo masa file matar ta sa hannu ko da aka kawo file ɗin mema kon matar ta sa hannu sai kawai ta fara ihu tare da tsalle kamar ana dukan ta
Abin ya bani mamaki ban gama mamaki ba sai ga dr.hisham ya zo wajen mu
"mr aliyu kinga waccr matar da take kuka" gyaɗa masa kai nayi,
"ɗanta mutuwa zai yi nan da yen mintina don haka naso ta sa hannu a cire zuciyar sa idan ya mutu kafin zuciyar ta daina bugawa amma kamar bata fahinta ba amatsayinki na mace ko za ki iya yi mata magana aka...............
Be gama bayanin nasa ba na warce file ɗin nayi wajen matar me ihu, sai da na fara lallashin ta da turanci kasancewar tana ji dai da naga zuciyarta ta nutsa sannan nayi mata maganar signing
Aikuwa kamar na kuma tursasata sai ta kuma zunduma uwar ƙara wai za a kashe mata ɗa ne, babu yadda ban yi ba, tun ina yi ni kaɗai sai ga mimma ma ta shigo taji halin da ake ciki
Mimma har durƙusawa matar nan tayi akan ta sa hannu amma matar nan ƙiri ƙiri ta shafe wa idon ta rashin M, da anyi mata maganar sai ihu
Tun likitocin suna tausaya mata har suka gane bata son bayar wa ne, wani dr. ne ya fito daga theater room ya zo yayi wa dr.hisham magana a kunne nan da nan naga hankalin dr. Hisham ɗin ya tashi
Karɓar file ɗin yayi yaje kanshi tsaye yace mata ɗan ta ya mutu ɗin hakabta sa hannu a cire zuciyar tasa, wallahi matar nan sai ta fara abu kamar me bori, tana ihu tana tumuwa a ƙasa tana abu kamar na mahaukaciya
Ɗaga ta nayi ina kuka ina cemata don Allah ta dubi girman Allah ta bamu zuciyar nan ko bata bamu don komai ba ta dubi cikin da ke jikina ta ba mijina zuciyar ɗan ta ko na haihu abinda zan haifa ya ga uban sa amma matar nan ƙiri ƙiri ta ƙi
Can zuwa anjima sai ga wannan dr. ɗin ya kuma fitowa ya kuma faɗawa ɗr.hisham magana again a kunnen sa, kawai sai naji dr.hisham ya ce mata
"zuciyar ɗanki ta daina harbawa i hope u are happy 4 not helping those in need" wulla mata takardar yayi a fuskarta yayi gaba
Zama nayi a gaban matar nan ina kallon ta ina kuka ita ma mimma haka dai naji kamar wannan itace damar mu ta ƙarshe amma matar nan ta nuna rashin imani a tattare da ita
Tashi nayi da naji dr.hisham da wasu likitocin suna guje gujen shiga ɗakin aliyu don na'urar dake ɗakin sa ce take alarming ```ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit``` alamar danger muna zuwa kusa da ɗakin aka dakatar da mu
Kuka kawai nake yi sun jima sosai sai ga su sun fito inda dr.hisham ya buƙaci ganin mu, muka bishi office ɗinsa, sai daya zauna sannan ya fara magana
"a bisa binciken da mukayi mun gano cewar gaskiya aliyu inbai samu theater nan a yau ba in shaa Allah