Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
ana jamasa numfashin kafin yace zai ɗauki intercom ɗin dakin ya kira reception ya sume
[7:45PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*oppps hello danginsa fans nayi mistake last page 35 ne na manta nasa 36, so da fatan ba,za ku nemi 35 ba*
*masoya dangin sa wannan shafin naku ne kacokam ɗin sa na gode da soyayya ku*
*mun yi baƙi a grp ɗin danginsa duk ina yi muku barka da zuwa da fatan duk zamu ƙaru da juna, don Allah a dinga haƙuri da juna Allah yasa mu dace*
Farkawa nayi na ganni a asibiti hannuna da ƙarin ruwa sai ƙirji na da yake ta faman min azaba, duka zuciyata take ta faman yi kamar zata fasa ƙirjina
riƙe ƙirjin nawa nayi tare da anbaton sunan Allah, pA ɗina ne ya matso kusa dani "yallaɓai ka tashi bari in kira dr. ɗin" ya faɗa ban kula shi ba ya fita
Can zuwa anjima sai gasu shi da dr. ɗin
"sannu ya jikin, ina ne yake maka ciwo" inji likitan
Ban iya magana ba iya kacin ƙirji na dana nuna masa
"sanna" ya faɗa ataƙaice sannan ya ci gaba da rubutu a file ɗin da ke hannun sa
"aliyu kana fama da ciwon zuciya ne wanda ya kai stage ɗin da dole sai anyi mak aiki a zuciyar taka, don haka ya kamata ka fara shirye shirye zuwa aikin da gaggawa"
Ban iya magana ba sai pA ɗina ne ya masa magana inda likitan ya bada shawarar muje china, babu musu pA ɗina ya yadda ya fara yi mana shirye shiryen tafiya
PA ɗina ya so in faɗa wa dangi na akan operation ɗin da zai min tun wannan ana magana ne tsakani life and death amma ƙiri ƙiri na hana shi ba yadda ya iya haka ya haɗa mana visa muka kama hanyar china
mun sauka lfy directly muka kama hanyar asibitin kasancewar an san da zuwan mu yasa bamu wani sha wahala ba, sai kawai aka karɓe ni aka fara bani treatment kafin operation ɗin
Alhamdulillah anyi operation lfy kuma ma shaa Allah ina samun sauƙi ba laifi, ko da jikin nawa ya ɗan fara warwarewa sai na turo pA ɗin nawa ya dawo nigeria don ya ci gaba da kular min da harkokina ni kuma ina jinya ta
******************
hjy ta tare a sabon gidan ta cike da sa a, a da tana jakara takan taimakawa iya idan aliyu ya aiko amma tunda ta tashi shi kenan iya rayuwa ta juya mata, ya kasance wata ran ma abincin da zata ci sai ya nemi gagararta,
Nadama ce sosai ta saukar wa da iya tai nadamar abinda tayi wa salma mmn aliyu tai nadamara abinda tayi wa shi kan shi aliyun gashi yanzu ba ta san inda zata ganshi ba balle ta nemi shawarar sa, haka ta koma abar tausayi don duk ragowar ƴaƴan natan babu me tausaya mata in ma zata samu ta basu su so zasu yi haka rayuwa ta juya wa iya, ga hjy bata kusa balle ta faɗa mata halin da take ciki
nayi jinyata na watstsake dr. ɗina dr juan ya kafa min sharuɗa akan in kula da zuciyata sosai in dena sa abinda zai dame don in samu in zauna ƙalau wannan dalilin ne yasani haɗa dangina da mahaifiyata na sa su kwandon shara na fitar da su daga cikin lissafina saboda duk lkcn dana tuna su sai naji zuciyata tana min ciwo, wannan dalilin ne yasa ni mantawa da lamarin su, wannan shine dalilin daya sa na shafe zancen dangina a zuciyata don ta zauna lfy
*back to labarin*
rungume mijina nayi ina jin tsantssar tausayinsa a raina, lallai ka ga rayuwa sosai
"amma abu haidar baka ganin yafe musun shine dalilin da zai sa zuciyar ka ta zauna lfy" Ƙara jawoni jikin sa tare da kissing ɗina
"habibti bana son ki shiga wannan maganar na riga na kulle zuciyata pls kar ki samin wani sabon ciwon" ya faɗa
"to ina mahaifiyar ka take, baka ganin ya kamata ka neme ta"
"in neme ta ince mata me, ni da ta wurgar da ni tun ina tsumma kina ganin akwai abinda zata min yanzu"
"amma abu haidar baka ganin ...................."
"shhhhhhh habibti bamu haɗu anan ba saboda musu ban baki labari na saboda kiyi min musu, na faɗa miki ne kawai don ki guje wa mutanen na so pls kar ki min haka kar ki ƙara kawo min zancen dangina bani da ban taɓa samun su haka navtashi ni kaɗai kuma ina son rayuwata daga ni sai ƴaƴa na don haka inkina son zaman lfy da ni karki ƙara kawo min zancen su"
"amma baka ganin......." bai ma bari na gama zancen nawa bawa ba ya tashi ya miƙe tare da ɗauko doguwar rigar sa
" naga alamar bakya san in kwana aɗakin nan don haka sai da safe idan kinyi tunanin abinda na faɗa miki da safe ma haɗu" ya fita tare da ja min ƙofa
zama na tashi nayi gaskiya dole ne in gyara tsakanin mijina da *dangin sa* abinda ya fi bani mamaki ma shine wai mahaifiyarsa akwai chances na cewa ƙila tana a raye, amma tunda yake be taɓa tunanin neman ta ba
wace irin zuciya gare mijin dana aura innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai nake faɗa gaskiya dole ne in san yadda zan yi in kawo ƙarshen matsalar nan dangi ai sune mutum, duk da dai yanzu zamani ya zo da mutane suke ɗaukar ƴen uwan su ba abakin komai ba musammam idan ƴen uwa basu da shi amma a ko da yaushe ai mutum rahama ne,
haka na kwanta ina tunanin yadda zan ɓullo da lamarin gyara tsakanin mijina da *dangin sa* haka na kwnta tare da yin bacci na me daɗi kasancewar shawara ta zo min na san ta yadda zan fara mission ɗina
kashegari da wuri na tashi bba tayi wa yaran wanka ni kuma na haɗawa me gidan breakfast tare da kai masa, fuskar sa a sake ba alamar fushi ko wani abun don haka nima sai na saki raina, jikin shi na je na zauna, shi kuma sai ya ƙara jawoni jikin sa tare da sinsina ni
"me jego kina ɗaukar ƙamshi" ya faɗa tare ƙara cusa kan sa cikin jikina
ƙyale shi nayi yadda yake so da jikina ko ba komai ya yi missinga ɗina
"hubbi ka sauko kayi break fast"
"ur wish mi lady" ya faɗa
sai da na tabbatar da ya ci ya ƙoshi sannan na raka shi ya ga yaran wɗanda suka sha kwalliya sannan ya kama hanyar office ni kuma na koma gida don fara misaion ɗina
waya na ɗauko na kira aunty bilki ƙanwar bbn abu haidar na faɗa mata haihuwar tai murna sosai tare da min addua inda nai mata tayin ko zasu zo sai tayi ɗan jim kana daga bisani tace too shike nan in shaa Allah zasu zo
aika mata nayi da kuɗin mota ta account ɗin maƙociyata sannan na kira ta na faɗa mata ga kuɗin mota nan na turo masu kuma don Allah su zo da iya, tai murna sosai tare da cewar zasu zo, komawa nayi na kwanta ina fatan Allah yasa abinda nayi ya kawo ƙarshen wannan matsalar su
Ku yi haƙuri da wannan muna biki ne 😁
[7:45PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*Na kuma kwafsawa last page ba number don haka bari mu barshi a page 35 ɗin*😁😁
Page :37🌹
Kwanana huɗu da haihuwa mutan lagos suka ƙaraso har da maryam ita da take fama da tsohon ciki, sun aunty bilkisai ana gobe suna suka zo har da iyar kuwa
nayi murnar ganin su sosai matar tj salma ma tazo da ɗan babyn ta da ta haifa, wanda ban samu damar zuwa suna ba, nai mamakin da banga ƴen uwan tj ba ko dna tambayi salma si tace tj ne ya ƙi faɗa musu, na san dalilin daya sa ya ƙi faɗa musu sai nayi shiru kawai
Gida ya cika daƙam ya tubatsa yai albarka ko ina baka gani komai sai mutane,
ranar suna nasa akai mana decorating bayan gidan filine babba guda ba komai a gurin nan na sa aka sama kujeru tare da yi masa decoration me ƙayatar wa
anan aka zauna akayi shaglin suna lfy lau inda ɗa ci sunan kakan sa na wjen uba wato sani wanda zamu kira da muhammad, da yamma ana cikin hidimar sunan nan aliyu ya kira ni
rannan na shi a ɓace ba alamar fara'a
"lfy me ya faru ne" na tambaye shi, ranshi a ɓace, ya riƙe min kafaɗa ta tare da haɗa ni da bango
"me na ce miki akan waɗannan mutanen, ba nace miki ba ruwan ki da su ba, me yasa ba kya jin magana"
sai yanzu na fahimci da waɗanda yake magana
"amma abu haidar baka ganin..........."
"shut d hell up, ki kore su yanzu su barmin gidana in ba haka ba ki fuskanci fushi" ya faɗa yana saki na tare da juya wa da barin wurin
sai da na nutsu sannan na koma wajen taro na, ina iya hango su yadda kowacce a cikin su ta saki jiki tana ta hidima tare da dariya ya za ayi ince musu su tafiya ai ban isa ba na faɗa araina sai dai kayi duk abinda zakayi na faɗa araina
aliyu be zo ɗakina ba a daren ranar suna ba kamar yadda yake yi kullum nasan har yanzu fushi yake yi, don haka nima sai na ƙyale shi,
kashegarin suna aka fara haramar tafiya amma banda su iya koma sunce zasu tafi bazan barsu ba don kuwa ni burina shine in gyara tsakanin su kafin su koma, haka muka wuni ana shan hira tsakanin juna na gagga text ɗin aliyu nace war in kore su kafin ya dawo ni kuma sai na yi kamar ban gani ba
Ko da ya dawo da daddare har ɗakina ya shigo tare da min kashedin cewar idan na kuma bari suka kuma kwana a gidan sa to har dani zai kora, hankali na ya ɗan tashi don banga alamar wasa atattare da shi ba
suma anasu ɓangaren wai burin su in haɗa su da shi su gaisa tare da yi masa barka basu san wainar da muke toyawa ba akan su, don hka sai kawai na bisu da cewar baya gari don haka sai suka ƙara sakin jikin zama a gidan
kashegari ma haka gari ya waye rana ta take amma banga alamar su iya suna da niyyar tafiya ba har su khadija da ƴen uwana na lagos suka kama hanya amma su iya ba labari kuma ni fisabillahi bazan iya cewa su tafi ba
sai bayan la'asar sannan naga call ɗin aliyu na ɗauka amma hankalina gabaɗaya ba a jikina yake ba ko me zai ce min
"na ce ki kori waɗannan mutanen ki ƙi ko to ki tabbatar ban dawo na tarar da ke ba" yana gama faɗin haka ya kashe wayar
to faa yau ake yin ta in tafi inje ina na faɗa arai na, har dare jikina a sanyayae yake duk sai naji babu wani kuzari a tattare da ni ni da nayi haka da niyyar gyara amma sai gyara yake shirin taɓa min lfyr aure, wai aliyu wane iri ne na tambayi kaina, kasa bacci nayi don haka sai na zauna don kiran ya dawo in bashi haƙuri amma har kusan ƙarfe sha biyu ba shi ba labarin sa bansan nidai lkcn da bacci ya kwashe ni ba
kashegari da safe sai na aiki me aikina nace mata taje taga idan aliyu ya fito in zai fita ta faɗa min don ina son ganinsa
bata wani daɗe ba sai gata wai ya fito yana waje gurin parking motoci, iya tana ɗakin ta faɗi haka don haka sai ta miƙe
"bari inzo muje mu gaisa" na so in hana ta amma kafin in ce wani abun har tayi waje don haka sai nayi shiru na bita kawai
yana tsaye ya ci kwalliya cikin shadda milk colour ya ɗauko hular sa zanna bukar ya sa kansa yai mutuƙar kyau da kwajini, na ƙarasa kusa da shi tare rage sautin muryata sosai
"ka tashi ƙalau" na faɗa, bai juyo ba balle ya ansa kawai ya cigaba da abinda yake yi
iya ce ta ƙaraso kusa da mu da ƴar fara'ar ta
"ali ina kwana, an samu ƙaruwa Allah ya raya, ai mun ɗan jima a garin nan me ɗakin ka tace baka nan , ashe ka dawo"
kallon iskar da ta kwaso ta ma baiyi ba sai yayi gaba, ni kuma ina tsaye a wurin raina yai mugun ɓaci akan abinda yayi mata ko ba komai ai ta girme shi ita ce fa haifi ubansa duk abinda tayi masa ba kanta tayi wa ba
ashe bai gama rashin mutuncin nasa ba, ƙarasawa yayi kusa da me gadi sannan yace masa da ƙarfi yadda zamu ji
"idan na dawo na tarar da waɗancan a gidana ba a kore su ba abakin aikin ka" ya faɗa yana sa kai ya fice
wannan abun da yayi ya mutuƙar ƙona min rai sai naji kamar ƙasa ta tsage in shiga ji yadda ya disga baiwar Allahn nan a gaban ma'aikatan sa bayan ita ta kasance uwa ce ga mahaifin sa, haƙuri na fara bata inda ita kuma tace
"babu komai abu bari muje mu haɗa kayan mu munma gode da irin karrama mun da kikayi"
jikina a sanyaye na bi bayanta muka koma cikin gida inda naji tana faɗawa ƴaƴanta su haɗa kayan su su kama hanyar kano
"iya har zamu ko sati bamuyi ba" naji ɗaya daga cikin ƴaƴanta na faɗin haka
"to me muka zo yi ba suna ba, naga anyi sunan kowa ya watse to muma zaman me zamuyi, shi me gidan ma baya gari da yana gari ne da sai muce zamu zauna domin sa" ta faɗa
jikina ne duk yayi sanyi nasan tabfaɗi haka ne don ta rufa masa asirin abinda yayi mata amma gaskiya aliyu be kyauta ba,ai ance baƙon ka annabin ka
haka suka haɗa kayan su ina ji ina gani suka kama hanyar gida na bisu da kuɗin motar da nasan zai kaisu kano har da chanji
raina ne yayi mutuƙar baci lallai ma aliyun nan yau in ya dawo yau sai yasan cewar ni ya taba na faɗa araina har yamma haka na wuni ina tunanin irin rashin mutunci da zanyi wa aliyu idan ya dawo don gaskiya ya kaini bango
don yana kuɗi shine zai dinga ganin kamar ya fi kowa zai iya taka kowa ya kwana lafya ba abinda na tsana da ya wuce wulaƙanci ɗan adam yana da daraja, duk lalacewar ɗan adam ne kuma ubangiji yana ƙaunar kayan sa to akan me zamu wulaƙanta su don kawai kai Allah ya fifita akan su
kuma daɗin daɗawa wai mijina ne yake wannan wulaƙan ci gaskiya da sake wai an bawa me kaza kai bazan ɗauki wannan abin ba
[7:45PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:38🌹
Aliyu be dawo gida ba aranar, don da safe dana tambaya sai aka ce min dawo, inda daga ƙarshe na samu lbrn ya tafi china, raina ne ya ɓaci wato ban ma kai matsayin da zai gaya min ba kenan ko, mmm zai dawo ne dani yake zancen
wasa wasa sai da aliyu ya kwashe wata har uku ba shi babu labarin sa shi be kirani ni ma kuma ban kira shi duk da dai ya aiko da wani yaro ya kawo min numbers sa ta can wai ko idan ina neman shi, wato ban isa ya kira ni ba sai dai ya turo min da number ko