DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 33

63K to 66K   out of 97.7K words

da ce masa akai shi wajen mahaifiyar sa


shidai be tanka mata ba don shi a ganin shi babu abinda zai sa ya nemi zainab bayan ita bata ne me shi ba, kai inta neme shi ma sai ya wana ta sosai ya ja mata aji don tasan cewar shi ba kanwar lasa bane (``` ni dai mmn walid nace zamu ga me jan ajin kai da kake fama da ƴaƴa da ita da take ita kaɗai```)




be koma gida ba sai daya biya ta wani pediatric hospital ya sa suka yo masa hayar nanny wacce tasan kan yara sosai, sannan ya haɗa da ita da yaran ya kai gida shi a tunanin sa ya gama da wannan
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺




Page :40🌹



Bamu muka iso kano ba sai ƙarfe takwas na safe kasancewar sai yamma muka taso, ina sauka na kama hanyar jakara gidan su aliyu, ko da naje na ga sauka kyakkyawa kuma yanzu iyar ba laifi don gaskiya ina turo mata ɗan abin inna samu


Tea ta haɗa min da egg ɗina har da bread, sai da naci na ƙoshi har na manta rabon da inci abinci, sannan nai mata bayanin zuwa na, tai mamaki sosai sai tace min ina ƴaƴan na faɗa mata duk yadda mukai da shi,


Ita kanta sai da naga jikinta yayi sanyi ƙila ta tuno da rayuwar aliyun ne
"haƙuri zakiyi abuu ki koma ɗakin ki ki riƙe ƴaƴan ki"
"iya ƙyale shi jikan nan naki be san darajar ɗan adam ba ya ɗauka kuɗi sune komai, idan yaji a jikin sa ya fahinci daraja ta na koma, amma yanzu nan nika zama" na faɗa tare da gyara zama na



"to shi sanin fa kin yaye shi ne"
"ina fa ya kwace shi, amma ai ina matse nonon idan ya ciko don haka zan cigaba da matse wa kar yayi tsamin har Allah yasa ya dawo da shi"
"ohhh ni saude wannan hali naku na yaran zamani"
"iya wallahi ba laifina bane" Iya de bata yadda ba babu yadda bata yi da ni ba akna in koma naƙi, haka ta haƙura ta zubawa sarautar Allah ido don ba yadda zatayi dani



da daddre da ƴaƴan ta suka dawo sai ta gabatar musu dani amatsayin na zo zan ɗan zauna ne amma bata faɗa musu daliin zuwan nawa ba, nima kuma sai naji daɗin hakan


kashegai iya ta kaini na zazzaga cikin gidan daga waje gidan yake ƙarami amma idan ka shiga ashe da girma sa waje waje ne kamar gidan ƙauye sai dai kowa ya ɗan gyara nasa dai dai ƙarfin sa



daga can ƙarshen gidan ne wani part shi kuma amma ya rushe ina jin ko rashin samun gyara, har gurin rusashen ginin muka je
"kinga nan nan ne gadon mijin ki"
"iya da gaske na faɗa fuskata da fara'a"
"sosai ai marigayi sani yana da gadon baban su, don haka kinga ai doe a ba mijinki gadon uban sa kuwa ko"


tsayawa nayi ina kallon gurin a taƙaice zai iya yin ɗaki biyu da ɗan banɗaki da kitchen harda ɗan tsakar gida, sai na juyo ga iya
"za a samu masu gini a unguwar nan"
" me ze hana ai ɗana lawan ma magini ne me zakiyi"
"ginawa zanyi in zauna a cikin sa"



mamaki ne taf fuskar iya
"kinsan kuwa gini da cin kuɗi" ta faɗa
"ba komai ai nima na zo da su"
"shi ke nan zanyi wa lawan ɗin magana sai a fara"
"yauwa iya" na faɗa



ko da ɗan iyar ya dawo oyar ta faɗa masa ra'ayin zainab ɗin na son gina part ɗin ijina sai yaji daɗi ko ba komai ɗan ɗan uwan su zai dawo gare su, tayi masa baya non ɗakin biyu take so da ɗan banɗaki inda hali da kitchen da tsakar gida



dariya yayi yace "kina rena wurin nan idan nace miki zeyi ɗaki uku da banɗakin babba da tsakar gidan kuma fa, ai shi fili kina ganin shi haka idan an gina shi kuma abinda za afitar a ginin yana da yawa"


nai masa godiya tare da cewa yayi min ɗaki biyu kowanne da banɗakin sa da kitchen da tsakar gida


muka rabu da shi akan zai je ya ga nawa ginin zai ci kuma nawa zan fara bayar wadon a samu a fara a sa, nai masa godiya sosai, bayan kwana biyu kuwa sai gashi ya kawo min list,



aunty bilki na kwasa muka je banki nayi using atm card ɗin da aliyu ya bani tun ina gidan nayi withdrawing kuɗin da zasu ishe ni sannan daga nan nayo iya cefa ne, ko da na kawo masa kuɗin a ranar yasa yaran sa suka fara ƙarasa ruguza ragowar ginin da bai zube ba tare fara haƙa



**************

aliyu dai rayuwa ta juya masa abaibai, don kuwa yaran gabaɗaya basa jin daɗin canjin da suka samu, ya rasa abinda yake masa



mohd baya cikakken kwana biyu da lfy bini bini ya kama gudawa ko amai, kuma indai ya kama yin su baya denawa har sai in an sa masa ruwa don gudawar tsululu haka yake yin ta



shima kanshi haidar zazzaɓin dare yake ta fama da shi ga yawan kiran ```ammi naa```kullum dare haka ake fama da shi, anke asibitin amma ina har nanny ya sha canza musu ko nannies ɗin ne amma ina



shi kanshi ba daɗin yake ji ba yana fama da zuciyarsa wanda ayanzu takan tayar masa akai akai ya sha zuwa asibiti sai likita yace masa ya daina damun zuciyarsa da bakin ciki ya dinga barinta tana huta wa saboda he has a weak heart very weak one,zata iya bugawa at any moment idan ya cika damun ta kuma zai iya rasa rayuwar sa saboda hakan, tayaya zai iya wai controling ɗin ta bayan zainab ta tafi kuma wai ƴen gidan su sun ƙi neman sa don sulhu



abubuwa ne suka haɗu suka chakuɗe masa, rasa yadda zaiyi yayi ga yaran kusan kullum basu da lfy barina mohd har yanzu ya kasa sabawa da madarar da yake sha, ba irin madarar da ba ai masa trying ba amma duk a banza be dena gudawar nan ba duk ya lalace da shi


shi kanshi haidar kusan kullum da zazzaɓi yake kwana tare da kiran sunan zainab ɗin, wayar sa ya ɗauko ya kira tj yai masa bayanin duk halin da yake ciki, don bashi da wanda zai gaya wa da ya wuce shi



faɗa sosai tj ɗin yayi masa kamar wani ɗan yaro sannan yace zai zo abujar suje lagos don dawo da ita, ba abinda aliyu yake yi sai godiya sai kace qanda tj ɗin yayi masa kyauta



tj ma be ji daɗi ba ko kaɗan ɗauko wayar sa yayi ya kira zainab ɗin amma wayar ta a kashe take don haka sai ya ajiye, ya fara haɗa kayan sa domin zuwa abujan, aliyu yana da matsala menene na korar da mace har da kwace mata ƴaƴa, daga gani zanab ɗin ba ƙaramin haƙuri take yi da ɗan uwan nasa ba


sarai ya san halin aliyu ba haƙuri gare shi sosai, ko ma dai menene idan Allah ya kaimu muka je maa jo ko menene, su ma iyayen zainab ɗin basu hankali ba ya fɗa a ransa, ai da sai su kira shi suji me ya haɗa su ko basuyi don komai ba sayi hakan dan ƴaƴan zainab ɗin


kashegari da safe tj ya bi jirgin safe daga kano zuwa abuja daga nan suka bi private plane ɗin aliyu zuwa lagos ƙarfe 11:00 dai dai na safe sun sauka agarin lagos daga nan suka kama hanyar gidan su, fisabillahi aliyu farin ciki ne taf zuciyar sa ganin yau zai ganta amma a fiskar sa sai ya wani haɗe rai kar ace ya kasa





amma abin mamaki da takaici sai mutan gidan su zainab suka ce ai bata zo ba, aliyu yai musu bayanin cewar shi da kanshi yasa ta amota drivern sa ya kawo ta lagos amma inaa suka dage bata zo ba



a bayanin da yake musu ne mama ta gano ai ranar da zainab ɗin ta gano cewar ranar da zainab ɗin tazo suna shagamu, don hka sai ta kira me aikin ta tare da tambayar ta ko tayi bakuwa ranar da ta tafi shagamu,




me aikin ta tabbatar mata da ƙanwar ta tazo a kwatancen da me aikin tayi na baƙuwar anan suka gano cewar zainab ɗin ce, to amma ina ta tafi daga nan shine babu wanda ya sani, nan aka shiga neman ta amma inaa duk inda ake tunanin za ta je amma abin mamaki bata nan


ko da su aliyu suka ga babu wani nasara sai suka kama hanyar abuja tare da yaran don yace ba zai iya barin yaran nan lagos ɗin ba duk da dai mama ta o ya barsu, amma ƙiri ƙiri ya ƙi haka suka koma jiki duk babu ƙwari
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Page:41🌹



Zainab tana zaune duk abin duniya ya ishe ta bata taɓa ɗaukar cewar zata daɗe haka ba ba tare da ƴaƴan ta ba amma gashi yanzu kusan watan ta ɗaya har da sati, kullum ta tashi matse nonon ta takanyi kukan yaushe Allah zai haɗa ta da ɗan ta,



Ita shap tama manta cewar ita ce ta ɓoye kan ta duk laifin ɗorashi take yi akan aliyu, kuka ne ya kwace mata tana me tausaya wa kanta, Allah ya taimake ta ma iya bata nan ta tafi biki ita kaɗai ce aɗakin



ganin shirun yayi yawa yasa ta ɗauko wayar ta da tun ran da ta bar gidan aliyu ta kashe ta bata kuma kunna ba ta kunna don ta shiga watsapp ko zata ga abinda zai ɗebe mata kewa ta daina tunanin don kar ta haifar wa kanta wani ciwon



Saƙon ni ne sosai suka dinga shigo min waya kamar zasu tsaga wayar yawanci na grps ne sai kuma na ƴen uwa da suke ta tambayata ina na shiga, ashe aliyu ya je gidan mu ke tunda gashi ance mijina na nemana



banda lkcn sa na faɗa, saƙin mimma ne ya ɗauke min hankali sosai tambataya take ƙfy ta kuwa kwana biyu saƙon sun fi ɗari duk na tambayar ina na shiga ne



ɗaukar wayar nayi na danna number ta don inkira ta, don gaskiya ina neman wanda zanyi magana da shi in ji daɗi, ni ƴar adam ce don haka dole at stage ɗin da nake i really a shoulder to lean on an cried ma heart out,



kun san wani lkcn baka san mutum ba amma zaka ga u can talk to him musamman ma yanzu social media freinds some will love u honestly kuma zasu iya baka shawarar da zata fidda ka cikin tashin hankali don haka mimma na ɗauke ta kamar irin mutanen da ban sani ba amma zata iya bani shawarar da zata kwantar min da hankali


ringing biyu ta ɗauka tare da cewa
"ma za hadatha laki, ma hadatha li jawwala tiki, ai na dakalti,"

kuka kawai na sakar mata don gaskiya i really need to cry ina bala'in son yi kuka sannan in samu me rarrashina, bata hanani kukan ba sai da nayi me isa ta sannan na yi tare da cewa
"good day mimma"
"how dy, habibti"
"fine" Na ansa shiru ne ya biyo baya daga ni har ita
"habibti will u like to talk about wats rong wit u" ta tambaya



na shiga rattabo mata yadda mijina yake da matsala da da *dangin sa* da yadda matsala ta juye kaina, na faɗa mata komai bata katse ni ba har sai da taji na yi shiru alamar na gama sannan ta fara


Mimma ji tayi kamar zainab ɗin ta fama mata wani mugun ciwo da har yanzu yaƙi warkewa acikin rayuwarta, har gobe idan ta tuno da ɗanta daya rasu, sai tayi kuka duk rashin hankali da ƙuruciya da yasa ta tafiya ta bar ɗanta a hannu wanda bata sani har yayi sanadiyyar rashin ɗan, har gobe gani take yi da bata bar ɗan ta ba da ƙila yana nan yana rayuwar shi kamar kowa, hawaye ne taf idon ta zuciyarta tai mata ɗaci kamar zainab ɗin tana tariyo mata tarihinta ne da labarin da take bata sai da ta ɗan nutsa sannan ta fara magana don gaskiya bazata bari yarinyar nan ta tafka kuskuren da ita ta tafka ba wanda hanyanzu yake bibiyarta, ya ƙi kyale ta har gobe tana mafarkin ɗan ta


"habibti da farko dai baki kyauta, tayaya ɗan ki zai shiga tsakanin faɗan ki da mijinki" faɗa sosai mimma tayi min kamar ta ari baki tana yi kuma muryata na rawa kamar wacce zata yi kuka




mimma tayi faɗan ta dosai wanda ba abinda nake yi sai shesheƙar kuka inda itama kaga jin yadda take maganr kamar kuka take yi
"kuma abu na ƙarshe da zan faɗa miki shine ko ki koma gidan mijinki ko kuma ki sa aɗauko miki ƴaƴanki ki riƙe kayan ki, don banga zaman me kike yi ba babu ƴaƴan ki a kusa da kesalam" ta faɗa tare da kashe wayar



jikina ne duk yayi sanyi duk kalmar da mimma ta faɗa gaskiya ne uwa da tausayi aka santa, to yanzu ya zata yi, zata koma ne ko kuma zata sa aɗauko mata ƴaƴan ne


kai komawa gidan aliyu ba option bane bani da niyyar komawa zaman gidan sa har sai ya sauko daga fushin da yake yi da *dangin sa* sannan zan saurare shi ta faɗa a ranta



To yanzu wa zansa ya ɗaukƙ min ƴaƴan nawa, na tambayi kaina, su linda da rebecca ba zasu taɓa kwaso min ƴaƴan nan ba don kuwa tsoron aliyu suke ji, na fi son in samu wanda baya shakkar aliyu ko kaɗan



tj ne ya faɗo min a raina ina rawar hannu na ɗauko wayata na danna number sa lallai tj ne kawai zai iya taimaka min a wannan harkar don shine kawai baya tsoron aliyun kuma aliyun be isa yace zeyi masa barazanar sa ba na faɗa



tj yana zaune a falon gidan aliyu tun da suka dawo daga lagos ya kasa tfy don ya fahimci aliyun yana cikin tashin hankalin rashinganin zainab ya san daurewa kawai yake yi yana nuna bai damu ba, ko kuma yace don ƴaƴan sa amma daga ganin sa ba acikin kwanciyar hankali yake ba


Kusan kullum yaran basu da lfy barin ma haidar kusan kullum da zazzabi yake kwana mohd de nashi da ɗan sauki sosai tunda yanzu gudawar da sauƙi sai dai amai da yake akai akai wanda kuma ba laifi be wani ji jiki ba kasancewar yana shan ruwan gishiri da sugar, ya tausaya wa yaran sosai faɗan iyayen yaran ya shafe sun bashi tausayi sosai



wannan ne dalilin daya sa shi kasa komawa kanoya ɗan zauna ko dan yaran, wayar shi ta fara ringing, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya kai hannu ya ɗauko ta



ganin harafin *yayata* akan screen ɗin ya sa sji daga wayar jikin shi na rawa
"ina kika shiga" shine kawai abinda tj ya iya faɗa
kuka na saka masa tare da yi masa bayanin halin da nake cikinsa na son ganin ƴaƴa na


lallashina yayi tare da neman sanin inda nake, sai da na sashi yai min alƙawarin ba zai faɗawa aliyu ba kumabtare da min alƙawarin zai kawo min ƴaƴana sai na faɗa masa ina gidan iya




tj yayi mamaki sosai sannan yace mata yana abujan ya faɗa mata irin halin da yaran suke ciki ya kuma roƙe ta tadawo, kuka sosai na sakawa tj tare da roƙar sa ni dai kawai ya kawo min ƴaƴana, babu irin rarrashin da tk be yi min ba amma naƙi daga ƙarshe dole ya haƙura akan zai kawo su mukai sallama da niyyar zai taho kano yau da su



daɗi naji sosai tare da godewa Allah da kuma tj ɗin da zai kawo min ƴaƴana bayan na ɗauke tsammanin ganin su kusa



22 / 33