Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
Si da aliyu ya rarrashe ta tare da faɗa mata kwana goma kacal zasu yi a england ɗin sannanɓta sakko, sai kuma mimma ta faɗo mata,
Ai mimma tace a england take lallai kuwa in haka ne in shaa Allah in taje zata neme ta
Dole aliyu ya canza akalar neman visar su zuwa england, cikin ikon Allah suka samu sai shirye shiryen tafiya,
Ta lagos zamu tafi don haka nayi murna sosai ko ba komai zan ga gida, ana sauran kwana biyar mu wuce england aliyu ya barmu muka tafi lagos
Mun sha yawo sosai a lagos sannan Allah ya kawo mu lkcn tafiya,
Aliyu ya zo har gidan mu sun sha hira da baban mu sosai inda yayi musu alƙawarin kujerar makka da shi da mama da khadija da maryam
Baban mu harda hawayen farin ciki don be taɓa kawo ba, ko da yake naji su maryam suna cewa tunda na auri me kuɗi sunji mama tana cewa mijina zai kai su hajji ita da baba basu san har da su ba
Ni kaina ban san da tafiyar ba sai naji aliyu ya kuma shiga raina na kuma godewa Allah daya bani miji irin sa, mama har da rawa kun san idan aka ce mutum al'adar bayarabe ta shige shi doe sai an masa uzuri, ni ma nayi masa godiya sosai su maryam ma suka kira shi taka nas su kai masa godiya
Ran da zamu tafi har airport su mama suka rako mu mama sai rawar kai take yi ƴar ta zata tafi turai, muka yi sallama muka kama hanyar shiga jirgi sai turai ɗin gaske
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:47🌹
mun sauka lfy garin man city sannan muka kama hanyar hotel ɗin da peter ya kama mana, five star hotel dake kan titin neil lane, babban hotel ne me bene 95, inda peter ya kama mana presidential suite ɗin hotel ɗin
Suite ne me ɗakuna barkatai kitchen dining area, har da ɗan garden ƴar varender da ke kusa da living room, gaskiya ya ansa sunan shi presidential suite don komai me tsada ne
Unparking kayan mu kawai muka yi, ni da aliyu muka ɗauki master bedroom, amina ita da hannatu ko wannan ya ɗau ɗaki ɗai ɗai sai akar bar wa yaran ɗakin ɗaya, wanda yake kusa da na amina
ina cikin gyaran kayan aliyu ne naci karo da wasu pics daga gani na da ne, wata balarabiya ce ɗauke da ciki da wani ɓakin mutum kusa da ita ya rungume ta ta baya, ko wannen su ɗauke da murmushi, matar tana bala'in kama da aliyu kana ganin ta kaga mahaifiyar sa
Tausayi ya bani daga gani yana kewar ta sosai don dai bazai faɗa bane, amma yadda yake yawo da su ko ina har cikin wallet ɗin sa ma na taɓa ganin pic ɗin don de kamar baya son in sani ne ya sa nima nayi shiru
Pics ɗin kusa kala goma kala kala, ɗaukowa nayi tare da dawowa kusa dai
"habibi, su waye waɗan nan" na tambaye shi, sai da ya fara kissing ɗina, yakan yi kissing ɗina ne idan na tambaye shi magana me ɗan wuyar bada ansa
"ƴar ƙauye iyaye na ne"
"kuna kama da mmn ka sosai" hanci na ya ja min har na ɗan yi ɗan ƙara
"ki kalla sosai i resemble my innocent father"
"Allah habibi kunfi kama da mmn ka"
"shhhhh taya ma za ayi inyi kama da ita, am a photo copy of my papa" na san jin haushin abinda mmn tayi masa ne yasa baya son yace yana kama da ita
na kau da maganar don ko ɗan ƙaramin yaro yaga aliyu yaga mmn shi yasan sun yi kama ba kaɗan ba,
"i suppose wannan na cikin kai ne ko" na nuna cikin mmn shi daya fito sosai
"yep ɗat happens to be meee" ya faɗa da murmushi a fuskar sa
"do u miss her"
"no i never miss her, ban san ta ba bansan halin ta ba ban san komai nata ba ta yaya za ayi in missing abinda ban sani ba"
"i mean wataran kana cewa dama tana nan ko"
"no i never wish for 4 dat" ya faɗa yana tashi
"lets end d conversation here its boring" ya faɗa yana haɗa pics ɗin tare da yi musu ɓuya sosai
" na taho da su nedon kince sai na cigiyo miki ita don haka am going to use dis pics in shaa Allah, dont even think other wise"
sarai na san baya son hirar iyayen sa ne ko me yasa oho kai Allah ya kyauta na faɗa a raina
mimma na kira na shaida mata muna england a man city tai mamaki sosai don bamuyi da ita zan zo ba, dama naso ne onyi surprising ɗin ta, tai min alƙawarin zata zo, ni kuma nai mata kwatancen hotel ɗin da muka sauka
kashegari kuwa ta kira ni akan nayi expecting ɗin ta around 2:00 na ji daɗi sosai, da yake turai ya shige ta sosai ƙarfe 2:00 dai dai sai ga call daga reception wai ina da guest,
nace a barta ta shigo, minti biyu ne da ɗan sakons ya kawo ta suite ɗin mu, ina buɗe mata na rungume ta ban taɓa ganin ta ba sai yau
Kissing ɗina tayi a gefen fuskata duka biyun tare da ƙara rungume ni,
"ai nal aulad, where r kids" ta tambaya
Ƙwala wa hannatu kira nayi nace mata ta kawo su haidar,
Kawosu tayi, mimma ta dinga ɗaukar su tana kissing ɗin su sam ta kasa a jiye yaran ta taɓa wannan ta taɓa wancen, har ƴar ƙwalla sai da na gani a idon ta, wanda ya ke ɗauke da glass irin na likitoci,
Kallon mimma na dinga yi kamar na san kamar na san fuskar ta, amma shap na manta a ina na san ta, ko dai ban santa ba gaskiya na san wani me kama da ita, medicated glass ɗin da ke fuskar ta ne ya sani kasa tantance a ina na san fuskar ta, ko kuma a kalle kalle na na film ɗin larabawa ne oho ni dai nasan fuskar nan tata
"Mimma me za a kawo miki" na tambaye ta
"am full habibti"
"no mimma at least ko ba yawa ne ki ɗan ci kaɗan"
Gabaki ɗaya hankalin ta yana kan yaran, na sa akawo mata abinci da ɗan abin sawa a baki daga kitchen ɗin hotel ɗin
Da ƙyar ta iya ajiye haidar taci abinci ɗan kaɗan shima, pics ta dinga ɗaukar yaran, naso muyi hira da ita sosai amma sam hankalinta yana kan yaran,
Ba wani hira mukayi ba sosai sannan tace zata tafi duk da dai sai da ta kai kusan 5:20 sannan ta tashi nayi mata laƙawarin zuwa gidan ta
Ta bani address ɗin ta a liverpool take, na duba address ɗin nasu gidajen su na turai bashi da wuyar gane wa ba kamar namu ba nai mata alƙawarin zuwa gidan nata kafin mu tafi
Roƙo na ta dinga yi na don Allah in zo in kuma taho da su haidar na ansa mata da too
Har reception na rako ta anan ne ma muka ɗan tsaya muna hira kasancewar an tafi kira mata cab,
Aliyu ne ya shigo ya tarar da mu a reception ɗin yai mamakin ganina, sai na gabatar masa da mimma, yakan ji hirara ta a wajena sosai
"habibi ga ka yau ga mimma ta" na faɗa ina nuna masa ita
Da murmushin sa ya ƙaraso kusa da ita, amma abin mamaki suna haɗa ido sai naga fuskar shi ta canza, tsayawa yayi yana mata kallon mamaki kamar ya santa
Sai da nayi masa magana sannan ya dawo hayyacin sa
"habibi kasanta ne" na tambaya
"ta ina zan san ta" ya faɗa rai a ɓace
"ina jiran ki idan kin sallame ta"
Jikina duk yayi sanyi yadda yayi wa mimma sam ban ji daɗi ba ina laifi ta bar abinda take yi tazo kawai don tagan mu amma irin tarbar da zai mata kenan ohhh ni abu zan ga ran da mijina zai shiryu
Jiki a saɓule na raka ta itama bata ji daɗi ba amma kuma bata ce komai ba bayan ta tafi na dawo don yau aliyu yana da bayanin da zai min na wulaƙanta baƙuwata da yayi
"Habibi me kayi wa baƙuwata kenan" na faɗa lkcn da na shigo ɗakin mu wanda na tarar da shi a kwance yayi rigingine yana kallon ceiling
"habibi kasan mimma ne da yasaka yi mata wulaƙanci bayan ta zo daga liverpool kawai don ganina da yaran amma shine kake wulaƙanta ta"
Tashi yayi zaune
"a ina kika santa" ya faɗa ba tare da wasa afuskar ba
"so nawa zanɓfaɗa maka a yadda muka haɗu da ita"
"just tell me for GOD's sake" ya faɗa da tsawa
Na faɗawa aliyu yadda muka haɗu da mimma, shiru kawai ya yana saurare na, ko da na gama sai yace min
"ki rabu da ita Hippocrate ce"
"huuuh 🙊 subhanallah, abu haidar a ina kasan ta da har zaka kira ta wannan sunan"
"just shut up an leave me alone" ya faɗa haushi naji na tashi gaba ɗaya na bar ɗakin, a cikin abinda yake yi kamar ya san mimmar amma me yasa baya son faɗa min ko wacce ce ita
ban kuma kula shi ba da magana mimma ba, gashi nayi mata alƙawarin zuwa ko ya za ayi inje, na faɗa araina
Bayan kwna biyu sai gashi ya zo da rana yana shiryawa, tashi nayi na je wajen sa tare da tambayar sa ko ina zashi don yai mana alƙawarin zai kai mu zaga gari da yamma
"habibi yaushe zamu fita ganin garin"
"sorry habibti ba yau ba kinga peter ya haɗa min dinner da wani mutumin ɗan ƙasar saudiyya, wai yana da kaya sosai da za ai masa shipping, shine yace pls inje gidan sa muyi dinner da iyalen sa"
"ohh cikin garin nan ne"
"noo liverpool ne, akwai train da zai tashi zuwa liverpool nan da 00:30 mins idan nayi sauri zan samu"
Jin an ambaci liverpool ya sani miƙewa,
"don Allah habibi zani"juyowa yayi ya kalle ni
"are u sure" ya tambaya, gyaɗa masa kai nayi
"ok hurry up and get ready we have a train to catch" da sauri na tashi na fara shirya wa in shaa Allah sai naje gidan mimma
"yaran faa" na tambaye shi
"ohh barsu kawai ai dinner ce kawai bana son yaran su kawo wani matsala, kin san official meeting ne"
"ok kawai nace
Cikin shadda ta greenish blue me ɗinkin fitted gown wacce ta sha surfani tun daga sama har ƙasa na sako tare da ɗauko pendants ɗina silver wanda ya shi sosai da kayan
Mayafina na ɗauko wanda yai dai dai da kayan sannan na ɗauko stiletos hill ɗina na saka sai na fito kamar wata tauraruwa
muka fito muka kama hanyar station ɗin mun yi sa ar samun train ɗin on time mukai boarding muka fara tafiya zuwa liverpool tare da burin zuwa gidan mimma in dai muka je liverpool ɗin
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: [11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
[11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: Page: 48🌹
Lfy muka isa liverpool a train muka sauka sannan muka hau cab tare da ba driver ɗin address ɗin gidan da zamu, ƴar purse ɗin da ke hannu na na ɗauko na fito da address ɗin mimma
"Habibi don Allah in mun fito daga dinner sai muje ko" hankalin shi gabaɗaya yana kan wayar don haka be kalli ƴar paper da na bashi ba, sai cewa yayi
"wa kika sani a liverpool da zaki gidan sa"
"gidan mimm ne nayi mata alƙawarin zanje"
"stop dreaming dear babu inda zaki" ya faɗa
"kamar yaya" juyowa yayi sosai har ina iya jiyo nunfashin sa dake sauka akan fuskata
"sweatheart ba nace u should 4 get about her ba, i dont like dis relationship"
"amma ................"
"no amma just do me a favour nd stop talking about her u aint going any where, i hate d sight of her"
Oh my goodness wai sai yaushe mijinta zai bar halin sa ne,
Tafiyar 00:30 mins ne ya kaisu gidan da za suyi dinner, ran zainab a ɓace yake don haka kallon ma batayi ita da take cewa in suka fita zata yi using oppurtunity don ƙarewa garin kallon amma tun bayan ɗan faɗan su da aliyu ta cushe fuskar ta tare da juyawa gefe ta share shi
Ko da suka zo gidan ya biya me cab ɗin sannan suka ƙara ƙofar gidan inda suka dan na door bell ɗin
Wata yarinya ce ta zo ta buɗe daga gani bata fi sa ar zainab ɗin
"u r welcome" ta faɗa
shiga suka yi inda tayi musu jagora zuwa sitting room inda iyayen su suke,
"mr aliyu its a pleasure seeing u in my home u r highly welcome"
"the pleasure is all mine" aliyu ya faɗa suna musabaha da me gidan
"i believe this is ur wife" ya faɗa yana nuna zainab wacce ita kuma take ɗan murmushi
"yes she is zainab"
"oh wat a nice name, nice meeting u mrs aliyu"
"nice meeting u too" na maimaita
"yusra habibti tell ur mum our guest r here" ya faɗawa ƴar sada ta buɗe mana gidan
"yes dad" ta tashi ta fara hawa bene
Me aikin su ya kira ta kawo mana ruwa da lemo, ni dai gabaɗaya raina a ɓace yake abinda aliyu yayi, mmn tasun ta sauko tana maganar ina baƙin, to my surprise mimma
da murna ta na ƙarasa wajen ta tare da rungume ta,
"mimma" na faɗa
"habibti" ta faɗa tare da ƙara rungume ni
Nayi murnar ganin ta, ƙarasowa tayi cikin living room ɗin don su gaisa da aliyu, haka ya ansa gaisuwar tata fuskarsa babu yabo ba fallasa,
jana tayi zuwa kitchen
"zo muje mu haɗo wa boys ɗin mu ɗan snacks" binta nayi ina jin daɗi duk da dai ina feeling guilt na yadda mijina yake mata amma ita sam bata damu ba
A kitchen take tambayar yaran sai nace mata ai ban san nan zamu zo ba, Bata kawo komai ba ta yadda da abinda na faɗa
Muka haɗa ɗan snacks wanda yake a cikin leda ne a fridge kawai reheating muka sake yi a micro wave sannan muka ɗauko muka fito
Ajiyewa mukai agaban su sannan muka zauna muka fara hira, bamu daɗe da zama ba wani ya zo ya hankaɗo kofa ya shigo, gabaki ɗayan mu hankalin mu ya koma kanshi
Mimma ce tayi masa magana
"hisham come and say hi to our guest" ta faɗa masa, kamar ba ze zo ba sai kuma ya zo
miƙawa aliyu hannu yayi suka gaisa ni kuma ya min sallama, daga nan sai yayi sama, mu kuma muka koma hirar mu, sam ban ga tarbiya a tattare da yaron da mimma ta kira da hisham ba kanshi a tsaye yake daga gani kan nashin yana hayaƙi
cook ɗin su ta gayyace mu dinner ta gama muka tashi muka tafi, kowa ya nemi wuri ya zauna, inda mijin mimma yake zaune kan kujerar da take kallon ta mimma sai ni kuma na zauna kusa da aliyu,
Aikawa tayi a kira yaran gidan su zo muyu dinner, matan ne kawai suka sakko amma ban da hisham ɗin, mun ɗan jima kafin mijin yace kawai muci abinci ƙila hisham ɗin ya ƙoshi ne
Muka fara dinner sai ga hisham ya sauko a gadarance ya samu wuri kusa da bbn shi zauna, fara cin abinci yayi babu ko bismillah mun lura gabaɗayan mu, mimma ce tayi masa magana
"hisham baka yi bismillah ba"
"ina ruwanki da ni ko plate ɗin mu ɗaya ne" ya faɗa a wulaƙance
Abun ya bani mamaki ɗaga ido nayi na kalle su naga kowa babu abinda ya dame shi kamar dama sun saba
"ƙyale ta ta fiya sa kanta akan abinda da babu ruwanta, acting lika mother" inji ɗayar
"its ok kids, lets just eat we have guest today, salma behave ur self" shine abinda mijin yace
Mamaki