Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
bacci taji kamar ana ƙwanƙwasa ƙofar gabanta ne yai mugun faɗuwa inda tatashi taga da gasken ƙofar ɗakin ake niyyar buɗewa harda murɗa handle ɗin ƙofar Allah ya taimaketa tana kullewa da Allah ne kaɗai yasan mutumin da yake son shigo musu da kuma wace irin mugunta da ya zo da ita, tashi tayi a hankali ta ɗauki islam ta nufi cikin closet ɗin ta, can ƙarshen closet ɗin taje ta rakuɓe tana mai kiran sunan ubangiji ya kawo mata ɗauki tare da kuka mara sauti
ko da yaga taƙi buɗewa haka ya haƙura don kansa ya koma part ɗin nasa tare da yin abinda ya saba yi wato wanka da ruwan sanyi sannan ya kwanta haushin da ta bashine yasa ko buɗe computer ma bai yi don yasan sarai tana jinsa
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: .🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:16🌹
Ko da ya tashi da safe be bi ta kanta ba don ba ƙaramin haushinta yake ji ba, office kawai ya shirya ya wuce ya mitar wace irin yarinya ce
Shi a yadda ya ɗauki mata wasu ababe ne da basu san darajar da Allah yayi musu ba ashe har yanzu be san karatun mata ba, yana mamaki yadda yammata da suke kawo masa kansa suna rushing ɗin sa yana wulaƙantasu amma wannan ƴar ƙaramar yarinyar tana neman rikita masa lissafi mita ya dinga yi har ya isa office ko ɗan fara'ar da yake yi wa ma'aikatan nasa ma yau basu samu ba
Sai da naga gari ya waye sannan na iya buɗe ƙofa linda na gani ashe ta daɗe tana bugawa kasancewar ina cikin closet ɗin yasa ban ji ba
"madam are u ok" ta tambaya
"ina fa ok jiya wani ya shigo yana neman shigar min ɗaki" na faɗa mata atsorace, kallo na tayi alamar bata yadda
"baki yadda bane"
"no ma'am but am sure na rufe ƙofar falon nan, ƙila ko mafarki ne"
"mafarkin me abinda na gani da idona"
Na faɗa ina zare mata ido
"ok ma'am zan gayawa oga zai san yadda za ayi" ta faɗa tana mai ƙarasowa cikin ɗakin
Ta dudduba ko ina bata ga wani abin da ba dai dai ba don haka sai tace "bari in kira oga inyi masa bayani, ki shirya ki fito 4 breakfast" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin
yana zaune a office yana tunanin yarinyar nan da take rena masa sense ɗin sa wayar sa ta ɗau ƙara, linda ya gani don haka ya tabbatar wani abin ne ya faru
"hello linda"
"hello sir dama madam ce take complain ɗin ana ƙwanƙwasa mata ɗaki sannan" shiru yayi abinda zata yi asa kenan kuma yanzu ta faɗa wa masu aikinta yana zuwa ɗakinta
"sir y r u quite"
"ba komai abin ne nake tunani, tasan wanda yake buga matan"
"no ita dai kawai tace taji knocking, ni a tunanina imagination ɗinta ne kawai" ajiyar zuciya yayi ganin cewar bata faɗa musu shi ne ba
"ok just assure her cewar she is sfe ba komai"
"yes sir"
"emmm linda prepare today's dinner with me i will be dinning with her"
"yes sir"
Ta faɗa daga nan sukayi sallama, ko da taje ta faɗawa zainab ɗin cewar ba komai, zainab ɗin dai bata yadda ba amma ta sha alwashin koma waye sai ta kama shi
ko da lkcn cin abinci yayi linda ta gayyace cin abincin, jeans ne ajikin ta da ƴar ƙaramar body hug wacce ta tsaya mata iya cibiyar ta sai parking ɗin gashin ta da tayi a tsaki kan wanda jelar ya ɗan saukar mata yana lilo
fitowa nayi don zuwa wajen cin abin cin
"linda ina islam take"
"tana dining room ɗin"
"ok bari kawai inje sai in bata abinci acan"
su islam wasan ne kuma har dinning room yarinyar akwai ƙiriniya sosai gata bata zama wuri ɗaya so full of energy,
ko da naƙarasa cikin dinning room ɗin a zaune na ganta a kan kujera tana cin abincin ta
"ohh har kin fara baki jiran ni ba ko" Na tanbayeta ina ɗan dariya
tsoro naji ashe da mutun a ɗakin ban ganshi ba da shigo don yana gurin bar yana tsiyayowa kansa lemo
"bismillah zauna muci abinci tun ɗazu nake jiran ki" ya faɗa tare da ja min kujerar zama
rasa abinda zanyi nayi ga kayan jikina ga kaina ba ɗan kwali duk sai ƙare min kallo yake yi, juyawa nayi da niyyar guduwa ban ankara ba naji ya kamo ni ya haɗa ni da jikin sa yana sauke numfashi da sauri da sauri
ƙoƙarin ƙwace kaina nayi amma ina ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane
"relax relax kawai naji yana furta min a kunne na inda maganar sa tasa jikina yin shiruda kuma daina kokawar kasanceqar tasirin da tayi a jikina da gaɓoɓina
kuka na sa masa shi kuma ya shiga lallashina tare da shafe ilahirin jikina yana wani irin numfashi
"4 God's sake zainab wat do u want" ya tambaye ni
"ni ka kaini gida"
" gida kike so nan ba gida bane me yasa bazaki saki jikin ki da niba" azzalimmi in saki jikina ka cuce ni na faɗa araina
"ni dai don Allah ka dubi girman Allah ka maidani gida gaban iyayena" na kuma faɗa
"to shike nan kije zan yi tunani tukun na" ya faɗa yana sakina
a guje na kama zan bar ɗakin ƙara kamoni yayi yan ƙara mannani aqirjinsa tare da kissing ɗin wuyana sannan ya sake ni
"ki zauna kici abincin ki ni zan fita inci a waje naga alamar nine ba a son gani" ya faɗa yana yin hanyar waje
wanda ni kuma hakan yai dai dai da tsugunna wata ƙasa tare da dasa wani sabon kukan, in da naji islam ta hau kaina itama tana nata kukan, dole na share hawaye na na lallasheta sannan na zauna na ci gaba da bata abincin ta
tun daga lkcn na tsiri yawo da hijabi ko ina in dai zan bar ɗakina to da hijab ɗina a jikina, ban san cewar duk aikin banza nake yi ba shi ta ɗakina ma yake shan kallon sa ya more, mun sha cin karo da shi sai in zura a guje inyi ɗaki in barshi anan
rasa yadda zaiyi da ita yayi ta zauna ma suyi maganar fahimta taƙi da ta ganshi kamar taga wani dodo sai gudu ga wani hijabi da ta tsiri sawa duk yasan don shi takeyin hakan bosho ke nan ya faɗa
yana zaune a ɗakinsa yana tunanin ta yadda zai ɓullo mata ko ta saurare shi
"khadija khadija" shine abinda da iya faɗa, lallai ya ƙura yarinyar tana da saukin kai zata iya shawo masa kanta, wayar sa ya ɗauka ya lalibi number khadijan ya kira sai da ta gama ringing ta tsinke ya kuma kira sannan ta ɗauka da sallamar ta
"khadija ce" ya tambaya bayan ya ansa sllamar
"e ni.....ce......" Ta faɗa tana ɗan jan harufan alamar mamakin jin muryar namji ya kira ta
"ok aliyu ne mijin zainab"
"laaaaa ina wuni" ta faɗa da fara'ar ta wadda yana iya gane wa ne ta yadda tayi magana
"lafiya ƙalau ya gidan da me gida"
"lfy lau, ina yayar tun da ka tafi muke tasa ran ta kira mu amma shiru"
"wallahi khadija yayar nan taki ce ta matsa sai na kawo ta gida ni kuma gaskiya banni da ra'ayin haka"
"kash amma yaya bata kyauta ba"
"shine nake cewar idan kinga ba damuwa ko ku zaku iya zuwa ku ganta kinga ƙila idan taganku wataƙila hankalinta yafi kwanciya ko"
"to shike nan bari in kira maryam sai inji yadda zamuyi in zamuje sai mu sanar da mazajen mu inyaso zuwa magariba zan kira kaji duk yadda mukayi" godiya ya dinga zankaɗa mata har yasa ta jin kunya sannan sukayi sallama
oohh yaya ban sanki da wannan hali ba,wayar ta ta ɗauko ta kira maryam inda suka tsaida shawarar kowacce ta tambayi mijinatan, haka akayi kuma cikin sa a kowacce mijinta ya yarde mata
ko da aliyun ya kira khadijar ta shaida masa yai murna sosai sannan yace mata akwai flight gobe da ƙarfe 11:30 na safe lagos zuwa abj in zasu biyo yasa ayi musu booking
"to shi ke nan Allah ya kai mu" ta faa ta kira maryam ta shaida mata tafiyar tasun gobe da safe ce
ƙarfe goma dai dai na safe aliyu ya turo da driver ɗin sa na lagos ƙofar gidan maryam tare da taimakon ta wajen yi masa kwatance, a shiye suke tsap don har maryam ma tazo suka shiga suka kma hanyar airport tare da rakiyar mijin maryam, sun biya ta gidansu sunyi bbn su sallama inda mama ta dinga faɗan ba a gaya mata ba aida ƙafar ta ƙafar su, shidai baba cewa yayi da sun sauka su kirashi, da haka sukai salama
A airport ɗin duk aka gama duk wani abinda za ayi suka hau jirgi ya ɗaga da su birnin tarayya
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page: 17🌹
Khadija bata ga wautar su ba sai da sukayi kane kane a jirgi sannan wani abu ya faɗo mata, to in banda ma rashin tunani irin nasu tun da yayar nan ta tafi babu wanda ya taɓa ganin ta ko jin labarin ta, sai dai shi mijin, amma daga zuwa yace musu wai taƙi sakin jikin ta kawai sai su kuma suka kamo hanya suka taho ganin ta, oh Allah kasa ba ajalin mu yake kiran mu ba
juyawa tayi ta kalli maryam wacce take ta ƴen kalle kallen ta ga farhana a hannun ta tana ta bacci, ita ta baro khalil a wajen mama kasancewar yanzu cikin ta ya fito sosai don haka bata yawo da shi
suna sauka ta kunna wayar ta sai ga kiran aliyu nan
"na turo driver ya ɗauke ki na bashi number ki don haka zai kira ki, ni na shiga meeting ne sai dare" To kawai ta iya cewa jiki a sanyaye
"Allah yasa ba meeting ɗin siyar da mu ya shiga ba"
ilai kuwa sai gashi driver ɗin ya kira ta, tai masa kwatancen inda suke ya ƙaraso tare da ɗaukar kayan su zuwa wurin motar, wata baƙar continue discussion ce suka dosa glass ɗinta duk tinted ne baka ganin na ciki (ta wata tace *ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba* 🤣🤣🤣🤣
cikin khadija ne ya ƙara ɗurar ruwa shike nan su tasu ta zo ƙarshe ta faɗa tare da yin bismillah tana shiga motar tare da yiwa Allah addu'ar ya tsera tar da su
ko da suka je gidan ma khadija ganin irin girman gidan yasa ta kasa hakuri
"maryam nifa tsoro nake ji"
"tsoron me" inji maryam ɗin wacce hankalinta gabaɗaya yan ga kallan kataferen ginin da suke ƙoƙarin shiga
"yaya khadija don Allah dubi irin gidan da yaya take rayuwa acikin sa"
lallai har yanzu maryam ba nazari a lamarin ta wato ita kyawun gidan ma take hangowa ba irin hatsarin da suke shirin shiga take yi ba yanzu idan aka garƙame ka awannan tafkeken gidan ko tokar ka a ganine
share maryam tayi ta ci gaba da addu'a suna shiga cikin kataferen gidan kamar na shugaban ƙasa, sai da suka ɗanyi tafoya a cikin a cikin farfajiyar gidan, sannan suka samu sukayi parking
Ƙofar motar aka buɗe musu wani mutun ne sanye cikin bakaƙen suit da gilasin sa baƙi ya bude musu tare da cewa "welcome" a cikin muryar nan tasa kamar a shaƙe shi
maryam ce ta ansa da fara'ar ta ita kuwa khadija fitsari ne kawai be zubar mata, kai duba tayi taga farfajiyar cike take da maza tiƙa tiƙa duk sanye cikin bakƙaƙen kaan da glass ɗin abtsaye ƙiƙam kamar an dasa su
wawuro maryam tayi "mun shiga uku maryam gidan yankan kai aka kawo mu" itama maryam ɗin da jikin ta ya fara sanyi ganin waɗannan ƙattin yasa itama yin shiru
"dis way pls" ya faɗa tare da nuna musu hanyar da zasu bi da hannu sa, bin shi sukayi a baya duk jikin su yayi sanyi
sunyi tafiya ta kai ta kusan minti goma kafin su ƙaraso wata ƙofa daga ganin ta ƙofar falo ce, door bell ya danna aka buɗe masa,
"they r here" ya faɗa tare da juyawa, matar da ta karɓe su me ɗan fara'a ce ba kamar mazan ba
"do come in pls" tace musu haka suka shigo jiki yayi sanyi, tsayawa sukayi suna ƙarewa ƙayataccen falon kallo
"pls wait here let me call madan"
"ok" suka ansa a tare
ina kwance ina game ɗina rebecca ta shigo
"madam u have guest"
"guest kuma tell them am sleeping" na faɗa na cigaba da game ɗina, ni wacece a gidan na da zanyi guest, ko kuma waye ma nawa yasan inda nake da za a ne mi, ƙila baƙin aliyu ne yace a kawo su in yi entertaining ɗin su ko a wane matsayin oho, ci gaba nayi da game ɗina hankali kwance
ko da ta fita taje ta sanar musu sai jikin su yayi sanyi, anya yayar da suka sani ce, maryam ce tayi karfin halin cewar
"go and tell her, her sisters from lagos maryam and khadija are here to see her" tsayawa tayi tana ƙare musu kallo tana tunanin taje ko kar taje
riƙe hannunta khadija tayi
"pls pls pls and pls i take God beg u call her 4 us" ganin iɗin roƙon da suke mata ne ya sa ta tausaya musu
"ok lemme go again but if she say she will not come out now u will have to wait oooh" ok suka bata ansa
ina kwance ni nama manta da wata rebecca ta zo
"madam"
"ooooooo..... Wat again"
"they say i should tell u dat ur sisters from lagos morya and kadija are here"
jin an anbaci sunan ƙannena yasani sakkowa daga gadon aguje nayi falon ban dai gaskata abinda tace ba amma ai ance gani ya kori ji
sune kuwa atsaye ƙiƙam, a guje naje na rungume su ina kuka ashe zanga ɗan uwana, suma rungume nin suka yi muks ci gaba da kukan mu, sai da muka yi mai isar mu sannan muka nutsa
"ku zo muje ɗakina" na faɗa ina jan hannayen su
"rebecca Kawo musu kayan su ɗakina, na faɗa ina yin gaba da hannun ƙanne na
"ya akayi kuka san inda nake"na tambaye su
"mijinki mana, shi yace mu zo"
"mijina kuma waye kuma mijina" na tambayesu, tsayawa sukayi suna kallon juna
a lkcn ne rebecca ta shigo musu da kayan nasu,
"ina linda tayi"na tambaye ta
"bata dawo daga kasuwa ba"
"ok haɗo musu ɗan abin sawa abaki"
ko da ta fita ƙara matsowa nayi kusa da khadija
"waye mijin nawa, yaushe aka ɗaura min aure" tsayawa sukai suna kallon juna
"yaya da gaske baki san kina da aure ba" gyaɗa musu kai kawai nayi don wannan lamarin ya girmi tunani na, ina da aure to me yasa miji bai taɓa zuwa inda nake ba
"to me gidan nan yaya aliyu" kamar in gwaɓe wa maryam baki wai wani yya aliyu, harara na bita da shi na kuma fuskantar khadija don ita a lamarin ta ba ta waasa
"Allah yaya me gidan nan ne mijiki, ke da tun zaman da kike yi a gidan baki san zaman aure kike ba" kaina ne ya kuma juyewa
"yaushe aka ɗaura min auren ban sani ba"
"kusan wata bakwai ke nan ko maryam"
neman maryam mukayi muka rasa ashe ita tuni tayi cikin closet ɗina
"yanzu yaya duk wannan kayan naki ne" muka jiyo muryar ta, kamar inje in rufe ta duka hka nake ji don haushi, wai ina da aure da kuma aliyu duk yaushe hakan ta faru na kuma tambayar kaina
ƙara dawo da hankali nayi ga khadijar wadda itama hankalinta yana kan kayan da maryam ta fito da su daga closet ɗin tana nunawa
"yanzu khadija wa ya ɗaura min ba tare da sani na ba"
"baba ne " ta faɗa a taƙaice
hawaye kawai naji yana zubar min ashe baba sai da ni yayi shi yasa bai