Chapter 3 Reading DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt Arewa Novels

DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 33

6K to 9K   out of 97.7K words

yo wayasan lkcn tashi daga wurin partyn



Ban gaya wa mama akan partyn ba don nasan halinta sai tace zata, ranar sunday ƙarfe bakwai sai ga khadija a ƙofar ɗakin mu tana mana knocking,



ni na buɗe mata sai ga baba ya fito daga ɗakin "waye wannan da safen nan" ganin khadija ya sa shi wangale bakinsa


*khadija* lfy kika zo mana da sassafen nan" ya faɗa yana zare ido, jin sunan khadija ya sa mama fitowa daga ɗakin ta da zanin a hannun ta ytana ƙoƙarin ɗaurawa "lfy" itama ta tambaye ta, nima tashi nayi ina zare idin ƙarya kamar bansan komai ba



"ba fa komai baba dama bani da lfy ne, shine hadi yace min inje general hospital na cikin lagos in ga likita sosai shine na biyo yaya ta rakani ko ta riƙe min khalil inna ta tashi shiga" ta faɗa kamar gaske




Tsaki mama taja tayi wucewarta ɗaki shi kuma baba sai ya hau mita "da ba sai ki kirata taje can ta same ki ku tafi ba,amma kin tashi kin doko mana sammako sai kace wani abinne ya faru"


Kallon inda nake yayi "sai ki tashi tunda kin zama sai in ƙannen ki ba su da lfy su dinga futowa daga gidan mazajensu kina raka asibiti, Allah ya bada lfy" ya faɗa wa khadija



Tashi nayi jiki ba ƙwari banji daɗin abinda baba ya faɗa min amma ya zanyi, "bari inyi wanka"
" a a yaya ba sai kinyi wanka ba wanke fuskar ki kawai, ai daga asibitin kasuwar ikko zaki rakani" ta faɗa da ƙarfi don baba yaji ilai kuwa
"kuce yau kawai yawo zakuyi,to ki tabbatar na dawo na same ki a gida" ya faɗa yana shigewa ɗakin



fuskata kawai na ɗauraye na saka hijabi na ja musu ƙofar falon muka kama hanna, ni na karɓi khalil na goya don naga khadija ƙarfin hali kawai take yi




Gidan maryam a A p yake don haka sai muka hau keke napep don da yar tafiya, bakwai da kwata muka isa inda muka tarar madam ɗin an tashi ana ta hidima, mmmmm wayaga su maryam




"sai yanzu kuka zo" ta faɗa tana zunɓurar baki
"au sai yanzu nema, da asuba kike son mu zo ko me"
"ni dai ku zo mu fara don tun bakwai na aiki bbn farhana kasuwa yayo mana siyayyan abinda zamuyi amfani da su" binta mukayi inda ta lissafa mana abinda da zamuyi, springrolls, meat pie, doughnut, sai cup cakes kowanne 300 pieces ,


Zaro ido nayi "maryam jakai ne mu"
"akwai masu taya mu ai" ohhho
"yauwa sai kuma kunun gyaɗar nan da kike yi me farar shinkafa, kinga har na jiƙa gƴadar da shinkafar, ya siyo robobi na yoghurt in mun gama sai mu ɗura a ciki ko ya kikace"
" eeeeeeh hakan ma ya bada ma'ana, muga gyaɗar" nuna min gyaɗar tayi dayawan ta, sannan muka je ta nuna min farar shinkafar da ta jiƙa wuuuuuuu nace ina zare




"maryam me za ai da dawannan uban shinkafar ke da ake sa ƴar kaɗan don ta ɗaure kunun, amma ba komai ayi waina da ragowar"
" waina kuma yaya partyn ƴen gayu kin taɓa ganin waina"
"ko ma partyn uban waye bazan bari ai asarar uban shinkafar nan, ina masu taimaka nan su zo suje suyo mana cefanan waina"



Maryam bata soo yin waknar nan ba amma ba yadda ta iya ni kuma gani nake yi in aka bar shinkafar lalace wa zatai don cikin botikin penti ne ta cika shi dam da jiƙaƙƙiyar shinkafa, masu taya mu aikin suka zo muka basu sautjn sannan muka fara hidimar aikin




ƙarfe 2:00 dai dai mun gama komai hatta da wanka jira kawai muke yi sadiq yazo mu tafi, shima ko da yazo yaga wainar nan sai da yayi ta mitar abin ƴen gayu me ya kai waina, sai da nace musu in ba za aje da waina ba ni ma bazan je ba sannan ya Haƙura aka zuba kaya a boot ɗin mita muka shiga



sabuwar doguwar rigar da khadija ta bani ita na saka ajikina, irin rigunan ƴen india ne me buɗewa sosai daga ƙasan, rigar tai kyau sosai samanta a tsuke yake inda ƙasan ya buɗe sosai don sai inayi ina tattaro ta indai zan hauwuri me tudu ko zan sauka, sai yaba min kwalƙiyar suke yi ni ko kunya ce ma ta kama ni don duk kyan nan nawa na rasa me taya ni ohhhh ni abu





lekki beach muka wuce direct tunda anan ake partyn ko da muka je ƙin ɗauko min waina ta suka yi sai ni na koma da kaina na ɗauko abata da miyar ta da ta sha bogo (ƙashi me taunuwa 😋😋) da kuma pkomo sai nama, na je inada ake jere abincin na ajiye, har anfara shagali kowa yana ta son ya nuna bajintarsa awajen celebrants ɗin ta fannin ko abinda aka kawo na ci ko na sha kona kyauta wato gift, sun yi kyau suma celebrants ɗin wato alh musa sosai inda suka ci kayan su iri ɗaya su da ƴaƴnsu guda huɗu




ganin lkcn sallah yayi yasa na ɗan yi nisa daga wurin partyn don in samu in gabatar da farilla, na ɗau lkc me tsawo ina addua sannan na naɗe sallayata na koma gurin partyn tun daga nesa nake jiyo hayaniyar ƴen partyn, nace lallai duniyar tayi wasu daɗi




Y
ƙaraswa nayi don inga menene yake sa mutane wannan hayaniyar ashe akan waina ta da maryam da mijinta suka ce kauyancine ake ta wannan wasoson, ana so can na hangon babba abokin alh musan da kuƙar wainae a hannun sa ya ɗora ta a sama nkansa mutane suna ta binshi ta basu, dariya nm abin ya bani sosai




sai ga kuma sadiq shima yana ta wani washe baki suna magana shi da alh musan daga gani zuba santi yake yi, matar aƙh musan ce ta matso kusa da mijin nata ta masa magana, sai naga ya juyar da plate ɗin da wainar take ciki a lkcn da ita ta kai hannun ta, ban san lkcn da tintsire da dariya wato yau wainar ta ma tasa masoya faɗa




bayan an gama wasoson wainar sai kuma aka ci gaba da hidimar partyn, abin nasu ya ƙawatar sosai da sosai, sai da la'asar tayi sannan na kuma fita na gabatar da tawa ni ko me akeyi bana barin sallah ta wuce ni haka nake, bayan na dawo naga salon partyn ya canza wai couples dance toooo





couples za a zaɓa su zo su danceee a filin wurin bayan sun gama sai su ma su zaɓo wasu an ɗan jima ana haka sai kuma akea ce ance dance dance dance, sai naga kowane ɗan miji yana jan matar sa suyi rawa saurayi yaja budurwar sa ƴar iska khadija itace har da kawo min khalilkarɓar shi kawai nayi na bar wurin don inna tsaya sai zuciyata ta buga
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By mmn walid nd walida (mrs aliyu)


🎁 *NASIBI WRITERS ASSOCIATION*🎁 we shine with the smile ☺ 😊😊☺ of our readers, so keep smiling while we keep shining ND entertaining u with amazing story love y'all mua Mua 😘😘😘😘




Page :6🌹




can daga nesa daga wurin partyn na samu wuri a yashi na zaina ina kallon yadda ruwa yake yo anbaliya ya na koma wa tekun ba tare da wani wani matsala ba ko wani takura khalil na zaunar akusa da ni don in samu inyi tunanin rayuwata sosai, dama nima zan zama kamar ruwan nan in ta sha'anina batare da damuwa ba ohhh Alƙah ka kawo min ba don halina ba na ɗaga kai sama ina roƙon Allah a ziciyata




kamar an jeho mutum haka naji an zauna kusa da ni haki, a ɗan tsorace na juyo inda mukai huɗu da wani balarabe, balarabe ne sosai ba wai kamar labarawa yake ba kana ganin shi kaga jinin larabawa a tattare da shi, ƙura mai ido nayi ina ƙarewa ƴar kyakkyawa fuskar shi kallo wanda kallo ɗaya zaka gane tsabar kyan da yake ɗauke a fuskar tasan



"Baby kallon ya isa haka, zan ɗan dade a kusa da ke" ƙara sakin bakin nayi ga hausa kuma raɗau abakin ɗan balaraben mintsinin kaina nayi kodai mafarkin nayi yana magana,ƙara katsemin tunanina yayi da cewar "baby am talking to u" baby kuma sai a lkcn na dawo hayyacin na inda na zunburar masa baki nace "baby kuma, wace babyn ka, ko ka zo da babyn kane ka ɗauka nice"



Murmushi yayi wanda ya ƙara fidda masa da tsantsar kyan sa, "am talking to u" ya ƙara faɗa juyawa nayi ko zanga wata a kusa dani ganin babu kowa yasa na tabbatar dani yake



"excuse mr man am not ur baby........... Bai barni na ƙarasa zancen nawa zancen nawa ba ya ɗora da cewar "wasu ƴammata tun ɗazu suke ta bina shine ni kuma nace musu da matata nake suka ƙi yadda shine kawai ganin ki a zaune ke kaɗai ya sani garzayowa don in ɗan lape kafin su gaji su tafi,"




Harara na banka masa ina ƙoƙarin miƙewa ya ma rainani, "noo babay karki ƙoƙarin tashi ya kamata ki juya ki kalli yadda suke binki da kallo" ni har yanzu ina mamaki hausar da take fita daga bakins, zama nayi sannan na kalle shi "a ina suke"
"kalli hannun daman ki zaki gansu su huɗu"



juyawa nayi a wayance wasu ɗima ɗima matan lagos na gani kowacce sai zare min ido take kamar zasu cinye ni, bansan lkcn da juyo na daina kallon su ba, dariya naji yana min "kinga in kika tashi Allah ya haɗa ki da waɗancan ko ƙashin ki baza a gani ba"harara na banka masa tare da murguɗa masa baki




"baby ba a harara ta don dai ni nakawo kaina amma ni mutum ne da bana ɗaukar raini" wata hararar na kuma doka masa na juyar da kaina



wayar sa ya ɗauko yana ta ƴen wayoyin sa inda khalil da ke tsakiyar mu ya fara yi masa gwarancin sa ni shap ma na manta da yaron kawai sai ji nayi ya ɗauke shi yana mai wasa ban kula su don san duk abinsa ina zaune de baze sace yaron ba





wayar sa ce ta fara ringing ya ajiye khalil sannan ya ɗau wayar
"ɗan uwan ya kwana biyu ya garin da jikin hjy kuwa" shiru yayi daga dukkan alamu ɗan uwan nasa yana ansa tambayoyin da yayi masa ne, sun ɗan taɓa jira irin tasu wadda su suka san ko akan menene sannan naji yana cewa "haka tace hjyr, to kace ta kwanta da hankalin ta Allah ya amshi addu'ar ta don gani ma yanzu ga yayar taka"



jin haka yasani tunani waye daga cikin ƙannena,
" a a ai ka bari kawai sai kazo lagos ɗin sai ku gaisa" aka kuma magana daga can ɓagaren
"a haba wannan karon ba ƙarya nake yi ba ɗan uwa, gata akusa da ni" muhawarace kamar yadda na fahimta ta kaure tsakaninsa da ɗan uwan nasa akan sai yayi magana da wadda yace yayarsa ce daga ƙarshe dai aka kada ɗan balarabe, juyo wa yayi ya kalle ni inda ni kuma na haɗe rai



"baby don Allah ga ɗan uwana zaku gaisa"
"a wane dalilin na faɗa ba tare da na kalle shi"
"a dalilin in baki karɓi wayar ba zan tashi in barki da zakunan cen da suke ta kallon ki da tsana har yanzu" ya faɗa yana kare zancen nasa da dariyar mugunta



fusge wayar nayi daga hannun sa na kara akunne na tare da sallama
" wa'alaikis salam yayata ya garin lagos ɗin, ya mutanen gidan" lfy na ansa atakaice



"yayata kece ta farko da ɗan uwa ya fara gabatar mana amatsayin wacce yake so dan Allah ki riƙe mana shi amana, har Allah ya kaimu lkcn da zaki zama tashi kinji" tooo kawai na iya cewa





hira sosai ya dinga min akan mahimman cin ɗan uwan nasa wanda ni kuma wasu in gane wasu in bishi da too kawai,
"ya sunan yayata tawa ne" ya jeho min tambaya kallon inda balarabe yake nayi inda hankalinsa yake kan khalil suna wasa kamar baya sauraren mu
"ka tambayi ɗan uwaan naka mana sai ya faɗa maka"
"to shikenan ga hjyr mu kinga yanzu ta tashi daga bacci bazan bari wannan ɗaɗɗadan zancen ya huce ba ungo ku gaisa"




sai da ɗan ji ɗan jim sannan naji sallama cikin wata kamilalliyar murya, na ansa sannan na gaishe ta addua tai ta doka min akan in kular mata da ɗanta amana, wayyo Allah ni ban san mutum ba amma ƴen uwansa suna ta bani amanarsa to kawai nake binta da shi da kuma in shaa Allah ɗuk ilahirin jikina yai sanyi







"ya sunan ƴar tawa naji tace, bazan iya yi mata musu ba yasa ni nace zainab, Maa shaa Allah babban suna Allah yayi wa tarayyarku albarka ya baku zuri'a ɗayyiba amin nace yo dan Allah me zance
"ina ɗan nawa" ta tamabaya miƙa masa wayar naiy ya karɓa jin wacce ke maganar ne yaga ya ɗan nutsu sai wani shagwaɓa yake kamar wani yaro har da wani cewa baya iya bacci saboda basa kusa da shi




ya ƙaraci dai shagwabaraa sannan ya miƙo min hjy tace zakuyi sallama, karɓar wayar nayi sal da ta ɗan ƙara yi min nasiha mai shiga jiki sannan mukai sallama bashi wayar suka ƙarasa sallamar sannan ya ajiye



shiru ne ya biyo bayan haka ba wanda ya kuma tanka wani daga cikin mu ni ina tunani n hrar mu da baiwar Allah nan shi kuma yana danne danne a wayar sa




hayaniya na jiyo a bayan mu kamar ana kokawa wanne ne yasa muka juya atare da shi don ganin ko me ke faru, hasken camera camera ne kawai yake ana walƙiya afuskokin mu kasancewar duhu ya farayi *shit* kawai nahj yace ya sunkuci khalil ya riƙe mun ya fara jana muka fara gudu inda masu cemerar suke binnu suna.ci gaba da ɗaukar hoton su





kasancewar yashine a ƙasa don haka bashi da daɗin yi gudun a kai wannan ya bawa masu ɗaukar hoton daman samun hotunana namu sosai duk da naga akwai masu karesu da hana su ƙarasowa wajen mu, haniniyar doki kawai naji a bayan mu wanda wannan ne ya bamu damar tsayawa ya wuce sai naga nakan dokin ya sauko ya miƙawa balarabe linzamin ya kama ya hau hannu ya miƙo min na noke


"ya zakiyi da waɗannan vultures ɗin da suke binki" juyowa nayi na ci karo da mutane sunfi biƙa adadin da suke bin mu a guje da camera sasu kuma da abin magana a hannu dats mic daga gani ƴen jarida ne bansan lckn da na miƙa masa hannun ba yai sana dani sai kan doki ya karɓi khalil daga hannu mutumin nan, ya zaburi dokin tuni mukai gaba ba abinda kake gani sai haken camerar tana ɗaukar hotuna too shi wannan ɗin waye shi haka da ƴen jarida suke ta binshi 🤔🤔🤔
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀




By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)


🎁nasibi writers association🎁


Page :7🌹


Wani keɓantaccen waje muka nufi inda muka shiga ni dai har yanzu jikina bai daina rawa ba
"ke da kuka zo, don in san inda suke in kaiki"
"da ƙanwata da mijinta"
"kawo wayar ki sai in kira su" ɗauko wayata nayi wadda ta sha jiki, kallon wayar yayi sannan naga yana ƙoƙarin buɗe ta ciro sim ɗin yayi sannan yai wurgi da wayar tasa wayar ya cire sin ɗin ya samun nawa,




"wane suna zan kira" ya tambaya bayan ya gama daidaita wayar
"maryam" na amsa atakaice, sanin cewar ba kuɗi awayar ne ya sani kau da kai aikuwa yana dannawa yaji ba kuɗi sai ya ja tsaki


"jira ni anan bari in siyo credit naga wayar taki ba ko asi"

Ficewa yayi na bi bayan shi da kallo a tsaye yake me ƙirar ƙarfi irin waɗanda ake cewa giant ga tsayi ga faɗi oohh wannan matar shi zata more irin waɗanda idan sun rungume mace ne zata ji kamar babu wata damuwa a rayuwa lif zata lafe a faffaɗan ƙirjinsa




Bai daɗe ba sai gashi kiran maryam yayi tayi mai kwatance sannan ya ɗauki khalil muka

3 / 33