DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 33

78K to 81K   out of 97.7K words

ne ya kama ni, wannan rashin mutun ci ƙiri ƙiri amma abinda zai ce shine suyi shiru


Yarinyar da ake kira da yusra ne tace
"salma pass me d salt" tsayawa nayi ina kallon su


gabaki ɗaya babu tarbiyya a tattare da yaran salma ma suke ce mata kansu tsaye, itama mimmar sai ta share yusrar bata miƙa mata ba


"salma am taking to u"
"kinsan abinda ya kama ta kice kafin in baki salt ɗin"
"kina nufin in ce miki pls" Gyaɗa mata kai mimmar tayi




"da ince miki pls gwanda kar inci abinci" ta faɗa tana miƙe wa

"yusra habibti zauna lemme pass u d salt" inji yayar tatan, ƙin zama tayi ta shi ta miƙe ta hayewar ta sama


wani kallone uban ya bi mimma da shi wanda ƙiri ƙiri ya nuna itace me lefi
" ki daina yin abu kamar wata uwa a wajen mu, in tarbiyya kike son yi kije kiyi wa mataccen ɗan ki ba mu ba" hisham ya faɗa yana mike wa shima



yau naga ta kaina na kuma faɗa, ita ma yayar yusrar sai ta tashi har da cewa wai mimma ta sa loosing appetite ɗin itama ta bar wurin, kamar inyi mimma kuka haka neji, kanta yana ƙasa baza ka iya ganin fuskar ta don haka ba za iya faɗin mood ɗin da take ciki ba amma daga gani bata ji daɗin abinda ƴaƴan mijin ta suka yi mata ba



sai ya rage mu kaɗai tun marasa kunyar yaran sun fita
"so aliyu kace maman ka ƴar saudiyya ce, a wane garin" inji mijin mimma


"oh ban sani ba don ban ma santa ba, bamu taɓa haɗuwa da ita"

"me ya same ta"
"she died the day i was born" ɗago kaina nayi ima kallon aliyi shi da yace mmn shi tana da rai amma yanzu yace ta mutu


"oh am so sorry may her soul rest in peace" in mijin mimma ita ma mimma sai tayi wa mmn aliyun addua


"amma baka tambayi bbn ka lbrn ta ba"
"ya mutu kafin a haife" sosai suka nuna tausayin sa

"amma gaskiya kaga rayuwa, ka rasa iyayen ka lkc ɗaya, lkcn da kake mutuƙar buƙatar su"


"haka Allah ya ƙaddara"
"do u miss dem"
"no babana kawai nake missing, ita kuma mmna lefin ta na gani da ta iya barina a wannan cruel world ɗin ta tafi without looking back how selfish of her"


"bata da zaɓi ne shi yasa alkcn mutuwa mutum bashi da zaɓi" Inji mijin mimma

"ba wai zaɓi ne bata da shi ba son kai ne kawai, ƙiri ƙiri tasan banni da wani bayan ita, amma duk da haka saboda selfishness irin ta da rashin imani da rashin tausayi ta iya barina a lkcn"


Daga maganganun aliyu kana ji kasan akwai baƙin ciki a tattare da su, riƙe masa hannu nayi alamar lallashi, juyowa yayi ya kalle ni yayi murmushi
"but who cares yanzu Allah ya haɗa ni da wacce ta fita a rayuwa so bana ji komai" Ya faɗa yana kallona


Murmushi nayi masa tare da shafa gefen fuskar sa wanda hakan yasa shi lumshe idon sa


"am soo sorry to hear dat, a wurin grans dinka ka tashi"


" no its a pity da babu wanda yake son ɗauka a lkcn da aka haife ni don ƙiri ƙiri tun kafin a haifeni babu jituwa tsakanin mum ɗina da inlaw ɗinta, amma yet bayan ta haife ni ta iya barina bata yi tunanin wa zai kula da ni ba, dats y i said she is selfish"


shiru duk muka yi maganar sa akwai tausayi sosai, kukan mimma kawai muka ji, ajiye table napkin ɗin da ke hannu ta tayi ta tashi da gudu ta bar table ɗin, binta muka yi da kallo sai da ta ɓace sannan mijinta yace
"kar ku samu damuwa ita ma ɗan ta ne ya mutu yana baby a hannun kakar sa shi yasa in taji lbrn baby ya rasa ɗaya daga cikin parents ɗin sa sai ta tuna ɗan"

"hypocrite" na kuma jin aliyu ya kira da shi, juyowa nayi na daka masa harara ,yaushe mijina ya ɓaci da zai dinga kiran mijina da hypocrite

tausayi ta bani sosai don haka sai nace
"bari inje in lallashe ta" aliyu ne ya riƙe min hannu na tare da zaunar dani,
"ba hurumin ki bane, kinga shima mijin daya ajiye ta be damu da ita ba sai ke uwar shishigi" ya faɗa da hausa yadda mutumin ba zai fahimci me muka ce



komawa nayi na zauna suka ci gaba da tattaunawa akan harkokin su, ganin na gaji da zama gashi ina son sanin halin da mimma take ya sani cewa don Allah a nuna min rest room


me aikin su ya kira yace ta kaini guest room, barin su nayi suka ci gaba da maganganun su na business ni kuma na bi me aikin nasu, sai da muka bar gurinsu sannan nace mata ta nuna min ɗakin mimma wurin ta zanje, tayi min kwatancen ɗakin na haura sama
[11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: A hankali na tura ƙofar ɗakin tana zaune a gaban mudubin ta tana kuka, kus da ita naje na dafa ta


Sai da ta goge fuskar ta sannan ta juyo da murmushin
"y r u crying" na tambaye ta
"lbrn mijiki ya sani tunowa da nawa ɗan"
"am sorry kin ce ya mutu ko" gyaɗa kanta tayi


"Haƙuri zaki yi ki tayi masa addu'a, shi kawai yake buƙata"

" ya za ayi ɗana ya yafe min" ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka
"ni na jawo ya mutu very innocent of him amma ya haɗu da uwa dat is full of childish, i just cant forgive my self for d death of my innocent baby"


Kuka ta kuma ci gaba da yi ina ta bata haƙuri, sai da ta ɗauki lkc sosai sannan ta haƙura bayan na tabbatar mata da cewar a kodayaushe ƴaƴa sukan yafe wa iyayen su balle nasan ɗan ta yana aljanna don haka bazai wani holding grudges against her ba


A hankali ta ɗan sakko har muka fara hira dai, irin na yadda ta zam successful likitan yara tace saboda son da take yi wa ɗan ta ne da dana sanin mutuwar sa da tayi ne yasa ta zama likitan yara


Na jin jina mata daga gani tana kewar ɗan nata sai dai muce Alƙah ya jiƙan sa, wani hoto ne ya ɗauke min hankali a kan mudubinta na ɗauko shi,da graduation gown a jikin me hoton tana dariya, tsaya wa nayi ina ƙarewa pic ɗin kallo, wannan kamar pic ɗin mmn aliyu


Juyowa nayi nace mata
"mimma wacece wannan" zuwa tayi kusa da ni ta karɓi pic ɗin
"nice lkcn graduation ɗina" ta faɗa da alamar alfahari


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un mimma ce mmn aliyu, kuma ya sani amma, ya subhanallah, ko shi yasa akan dining yake ta faɗa maman shi tana son kai don ya cusguna mata,


Hawaye ne ya cika idon na goge shi a don bana son ta gani, me yasa mijina baya son ya sanar da mmn shi ya nanan a raye, wayyo wannan wace irin ƙaddara ce ɗa yana son rama abinda mahaifiyar shi tayi masa da ƙuruciyar sa


Futowa nayi daga ɗakin inda naga aliyu yana nema na zamu tafi mimma har ƙofar gida ta rako ni mukayi sallama gaba ɗaya jikina a yayi sanyi ganin wannan irin relation ship ɗin nasu muka kama hanyar man city ni da miji kowanne mu zuciya ba daɗi, ni ina tunanin me yasa mijina zai yi wa mmn sa haka shi kuma Allah ne kaɗai ya san abinda ke ransa
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Page :49🌹


*na Sadauƙar da wannan page ɗin ga dukkan masoya na gidan aure da waɗanda suke shirin yi Allah ka barmu da mazajen mu ka ƙara musu son mu ka rufe musu idon su daga ganin aibin mu ka buɗe musu idanuwan su don su dinga ganin alkhairan da ke tattare da mu, masu matsala a gidan aure Allah ya kawo musu sauƙi, masu zaman lfy Allah ya kuma zaunar su lfy waɗanda suke shirin aure Allah ya sada su da nagari waɗanda har yanzu basu samu ba Allah ya haɗa da nagari, Allah ya barmu da masu son mu yau ina cikin murna*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼





Sai 12 :40am na dare sannan muka shiga gida, kowannen mu zuciya cike da tunani, ɗakin yara wuce direct don in duba su, baccin su suke hankali a kwance ga amina ma a kan kujera


Tashin ta nayi nace ta koma ɗakin ta sannan na kuma yi musu addua tare da kashe musu fitila na fice, ko da na shiga ɗaki aliyu yana toilet, kaya kawai na cire na zauna ina jiran ya fito


Wanka yayi don ya fito gashin kansa yana ɗigar ruwa, tashi nayi nima naje na yi wankan sannan na fito na shirya na kwanta kusa da shi


"habibi yau me kayi a gidan su mimma kace mmn ka mutu"
"she is as good as dead to me" ya ansa

"ba nace ka daina wannan abun ba, wai sai yaushe zamu zauna ne ba tare da ka kawo mana wani problem bane, wat u did to dat innocent woman is unfair"


"unfair me na mata da ya zama unfair don kawai na faɗi tahirin rayuwata"

"labarin naka kamar kasan zai ƙona mata rai ne shi yasa ka dinga faɗin shi haka, did u intend ta hurt her"

"why will i hurt her wen i dont even know her"
"ranar da ka fara ganin ta ka kira ta da hypocrite wannan ya nuna ka santa"


"less stop dis conversation here bacci nake ji kinsan gobe akwai partyn da zamuyi attending kuma kin san ba nigeria ba ne don haka babu african time, we have to be there on time" shiru nima nayi aliyu baya son ya faɗi wani abu, amma ina da tabbacin mimma ce maman sa na so mu ci gaba da conversation ɗin amma ba hali



Bacci ne ya kwashe ni don na gaji, cikin dare na ji nishi a kusa da ni, farkawa nayi naga aliyi yana murƙususi riƙe da qirjin sa


Ohh my goodness zuciyarsa again na faɗa tashi nayi na dafa shi sai naji ya ce
"magani na pls" tashi nayi na ɗauko maganin nasa na ɓallo su dai dai yadda dosage ɗin yace miƙa masa nayi tare da bashi ruwa


Da ƙyar ya iya karɓa ya sha, cikin minti biyu bacci ya kwashe shi amma kafin yai bacci ya bani tausayi sosai daga gani yana fama da zuciyar nan tasa don har kuka sai da yayi


Gyara masa kwanciya nayi don ya ji daɗin baccin sai na ci karo da pics ɗin mimma na wajen sa, ohhh my goodness mijina ya gano mmn sa amma ƙiri ƙiri ya ƙi nuna mata cewar har yanzu yana a raye


Cuzguna mata yake son yi amma on d other hand shima he is suffering, gwanda ma ita bata fama da matsalar zuciya amma shi fa, zuciyar sa bata da lfy yet duk da haka ya hana ta ta samu sassauci kullum ƙara danƙara mata ƙiyayyar mutane yake


Sai yanzu na fahimci dalilin daya sa mijina ya samu ciwon zuciyar nan sabida gabaki ɗaya rayuwar sa ya taso cikin ƙunci da cuzgunawa daga mutane don haka zuciyar mijina babu komai a cikin ta sai ƙiyayya


Zuciyar da ke cike da soyayya na ba kowacce take lafiya ba balle ta mijina tun yana yaro ya cika zuciyar sa da tsanar *dangin sa* ya za ayi a samu lfy a tare da zuciyar da tun tana ƙarama babu abinda ke cikin ta sai ƙiyayya


Shi aliyu be fahimta bane shine maganin zuciyar sa inda zai dena ƙiyayyar da yake da ya zauna ƙalau amma burin shi yanzu naga alamar ya ƙuntatawa mahaifiyar sa, bayan kuma na san koda zai ji daɗi ya ganta a halin ƙunci yet shima a ƙasan zuciyar sa sai yaji ciwon nan kasancewar mahaifiyarsa don an ce blood is thicker than water, no matter stage ɗin da ɗa ya kai wajen resenting iyayen sa dole deep down in him dole a samu ɗan tausayi ko da ƙalilan ne na iyayen


In haka ne kuwa aliyu kenan be san cewar ɓacin mimma ba shima ɓacin ransa ne, kallon shi nayi baccin sa yake yi peacefully nace araina, bazan barka da wannan halin ba dole i have to tell mimma u r her lost son ko a kawo ƙarshen wannan abin don faɗa mata kamar jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne



Ita a ɓangaren ta zata daina blaming kanta na mutuwar ɗan ta kaima ka samu sauƙin zuciyar nan taka, haɗa pics ɗin nayi na ɗora akan bedside so nakeyi idan ya tashi da safe ya gane cewar nasan abinda ya sashi ciwon zuciyar, na koma na kwanta



***************


Kashegari ras ya tashi ba dole ya tashi ras ba tunda ya bar zuciyarsa ta huta, da wuri ya fita tare da faɗa min sai dare zai dawo in tabbatar da na shirya kafin ya dawo,


Yana fita nima na shirya tare da amina muka tafi shopping don banni da kayan da zani partyn,


Mun samu wani boutique a ƙasan hotel ɗin, muka shiga daga gani boutique ɗin na masu hannu da shuni ne ganin yadda ake nan da mu


Na faɗa musu "dinner gown"
"wane irin dinner ne" inji attendant ɗin
"well kamar businee dinner ne"
"mostly cocktail aka fiyi in dai business dinner pls come with me" binta nayi muka je inda cocktail gowns suke, amma to my surprise kusan duk babu wanda musulmai zasu saka



Don haka sai na faɗa mata ni musulma ce, sai tace min in zaɓi wanda nake so za a iya gyara min yadda zaiyi covering ɗin na



Wata armani gown na ɗauka gabaki ɗaya bayanta sa kwashe yake, sai wasu zare da akayi kwalliya da su abayan ta, gaban ta kuma stones ne akayi kwalli da su, sai satin da aka belt da shi tai kyau sosai



Bayan na ɗauka sai muka wuce, ware house ɗin su inda anan tailor ɗin su suke, wai lallab bature ya ci gaba, gida gudane ware house ɗin nasu baka gani komai sai kekuna, baka jin komai tsit kawai kamar ba kekuna ne suke aiki ba


Gurin wata muka je ta gwada ni tare da nuna min yadda rigar zata koma, babu abinda za a taɓa a wajen rigar, cikin ta ne kawai za a saka material da zai rufe jikin mutum, rigar baƙa ce amma sai suka ce zasuyi amfani da silver material a ciki, wanda zasu sa masa kƴalli yadda zai dinga ɗaukar ido ta ciki



Nidai kawai binsu nayi da to sai nace musu suyi min ɗan himar wanda zan yane kaina da shi, nan ma suka amince na biya su kuɗin su inda suka ce min in zo da daddare du shirya ni



Wato bature yana da wayo irin waɗannan designers ɗin idan ka sai kaya a wajen su da wuya su barka ka shirya da kanka instead sai suce kazo su shirya ka ba don komai ba sai don indan suka shirya ka zasu ma yadda duk inda kabi sai an yaba saboda kiran costomers, don in an yaba za a tambayeka a ina ka siya kunga sun kuma samun costomers ke nan



Nai musu complain ɗin rolling ɗin himar ɗin duk suka ce suna da expert kawai inzo har da kwalliya duk zasu yi



Mukai total har da kuɗin shirya ni na biya su na kama hanyar hotel ɗin da muka sauka inda na bar su amina boutique ɗin suna siyayya ko da naje sun gama don haka na biya muka koma sama


_you are light, the guide of our life, you are the essence of beau...........ty, the best mankind,for ever you'll be, the source of truth, peace be upon u ohhh muhammad(saw) even though i cant see ur face, ur presence is always all around me, ur names on my mind, every single day peace be upon u oh muhammad (saw)_ *kar ku damu ina rubutu ina jin waƙar nan ne yasa nace bari in rubuto ta tayi min daɗi sosai by mahir zain*



Sai da nayi sallah magriba sannan na na shiga wanka ina fitowa kawai na saka kaya sannan na sauka boutique ɗin don nasan yanzu sai inga aliyu



Kwalliya sukai min sosai don ma ina hana a saka min wani abun ne ɗan ciki na daya fara turowa sai akai wa wurin ciki wani design a jikin rigar baza ka ɗauka ciki bane


Aliyu ya kira ni Nace masa ya same ni a boutique ɗin ko da yazo na fito be gane ni, har na

27 / 33