Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
ba duk ya wani rikitani
"ai nace kaci ko ba inda zan kuma tafiya"na faɗa kaina a ƙasa
"ban yadda sai dai a bani a baki" wata sabuwa inji ƴan caca
rasa yadda zanyi na yi ƙatse min tunanin yayi
"to kinga alamar da naci da na ciwo wa kaina kenan tunda gashi kinƙi ki bani da kanki"
gutsuro tsokar naman nayi na kai masa bakin sa, riƙe hannuna yayi wanda hakan ya sa na kalle shi cikin idon sa
"pls habibti kar ki ƙara guduna kinji, u r my everything u nd d kids r all i have"
gyaɗa masa kaina kawai nayi hawaye taf idona
"i really miss u dat it really aches here" ya faɗa yana kai hannuna me naman zuwa wajen zuciyar sa, sakin naman nayi don sai in ɓata masa rigar sa
"pls stay by my side am not perfect buh i will try my possible best nd be a good husband to u"
"i miss u too" na iya furtawa daga ƙarshe, kalmar ta dake shi sosai don ya nuna jin daɗin sa da na faɗa haka
"really den show me how much.............."
Ban barshi ya ƙarasa ba na kai lips ɗin bakinsa inda na barshi ya ƙarasa ragowar aiki
Cak ya ɗauke ni sai bedroom, yahuza da bamu ci kenan, ni kuma mmn waleed da kwaɗayi sai na zauna cin kayana abinda da za suyi a ɗakin matsalar su ne ni dai inyi kwaɗayi na ko da yake bani kaɗai bace can na hango *FAIZA BABA* leƙowa ta taga wulla mata tsoka nayi na cafe da baki oohhh su fa'iza da kwaɗayi
Mun sasanta sosai da ni da mijina inda duk wani bashi da ke kaina ban yi wani yunƙura kasa biya ba tas na biya sai dai sam barka, soyayya muka shiga zubawa ni da ɗan mijina yanzu babu laifi yana kula *dangin nasa* sosai matsalata ɗaya itace shin mahaifiyar sa tana da rai ko kuma bata da rai
Ina son tambayr shi amma sai na ɗan ja ɗan lkc ganin bamu daɗe da shiryawa ba komai a hankali za ayi shi, aliyu be nemi in bishi abuja sai dai yakan je in ya samu lkc kuma ya zo, har da tsaraba yake zuwa da shi ai ta rabo a cikin gidan
Yaran gidan har sun san bbn haidar don in aka ce yana kano, to haka zaka ga gidan cike da kayan ciye ciye ina jin daɗin yadda yake kula da *dangin sa* duk da dai daga gani har yanzu be gama sakin jikin sa da su ba, don baya zama yayi hira da su
Daya dawo ya shiga ɗakin iya suka ɗan gaisa idan ya fito ya dawo part ɗin na baya kuma fita sai masllaci ko kuma in tj ya zo zasu fita shine yake fita, duk ƴen samarin gidan da basu da sana'a ya kwashe su ya basu abin yi, wannan ne yasa mijina ya zama zakaran gwajin dafi,
Yau na tashi gabaɗaya ba na jin daɗi jikina, sai na ɗauka ko yau da gobe ne kun san ance tafi ƙarfin wasa, amma ga mamakina tafi tafi sai abin ya zame min jiki bana jin da daɗin komai sai kwakwa ga miyau da yake yawan tarar min wannan ne ya tabbatar min na kuma samun passenger a tare da ni
Shiru nayi ban faɗawa aliyu ba ko da yazo yai ta dai mitar nayi kyau nayi ƙiba nayi freash ni daɗi na nake ji a kano shi kuma yana abj yana cin kwakwa(wahala)
Duk da nasan ba wani kwakwa da yake ci kawai dai mita ce irin ta ɗan adam yai mamakin ganin yadda nake cin kwakwa ta, sai yace
"ashe bani nake cin kwakwa ba ke kike cinta"
Ko kaɗan ban so y fahici ina ɗauke da ciki don haka sai na bishi da cewar lkcn ta ne shiyasa nake sha'awar ta, ganin yadda nake cin kwakwar nan ba dare ba rana ga miyau ya sa shi ɗauka ta ya kaini asibiti wai ko banda lfy ne, har da cewa
"dauɗar ciki yake damun ki, ke da kika taso cikin yarbawa ya kamata ki din ga shan magani jedi jedi don shan zaƙin ki yayi yawa"
Har muka je asibiti yana lissafo min magungunan dauɗar ciki daya sani, ni dariya kawai yake bani yadda ya daddage da dauɗar cikin nan ko ya zai yi idan yaji dauɗar cikin nawa babyn sa ne
har cikin consultation room ɗin muka shiga tare, dr. ya rubuta sunana da shekaruna sannan ya ɗago ya kalle ni
"hjy me yake damunki" kallon aliyu nayi don ni ba bu abinda yake damu kawai tattago ni yayi ya kawo ni asibiti
"ni dr. babu abinda yake damuna kaga wanda ya kawo ni nan"
Dr. ɗin ya kalle ni da mamaki sannan ya kalli aliyu, sai aliyun yace
"dr. Ƙyale ta dauɗar ciki take fama da shi tai ta tara miyau ga kuma cin kwakwa ba adadi, ni ina tsoron kar tuƙar kwakwarbtai mata illa ne"
Murmushi dr. yayi tare da tambayata last dana ga period ɗin, wannan ya nuna min dr. ɗin ma ya harbo jirgin nawa
Na faɗa masa ya fara ƴen rubuce rubuce sa sannan ya bamu test da scanning, muka je nayi a wajen scanning ɗin ne nace wa aliyu ya biyo ni muje scanning room ɗin
Macece tayi mana scanning ɗin don haka a sake nake ko da ta zo daidai wajen da babyn yake wanda be fi sati 12 ba sai tayi pause din monitor ɗin tare da nuna shi
"alh ga babyn naka" ta faɗa wa aliyu
Shi aliyun da ke gefe har yanzu be san me ake ciki wai shi duk a tunanin sa abinda yake sani zubda miyan ake nema
"baby faa kika ce" ya faɗa da mamaki
"yes kusan 12weeks babyn yake" ta kuma faɗa
Ƙara matsowa yayi kusa da monitor ne amma ba'a iya gani komai sai wani hatsa hatsa don haka sai dabya kai fuskar sa har gaban monitor sannan yace
"ni fa babu abinda nake gani sai wani hatsa hatsa" ya faɗa kuma kalƙon monitor
"alh ai ba a gani sosai kaga har yanzu babyn ba wani fara halittasar akayi ba"
"ok kin dai tabbatar da ba dauɗar ciki bace baby ne" murmushi tayi tare da gyaɗa kai
Ya juyo ya kalle ni h
"habibti kinga ashe ba dauɗar ciki yake damun ki ba baby na ne", shafa min ciki yayi tare da kissing lips ɗina tare da ce mi "thank u 4 everything"
Har muka koma gida yana cewa
"dama nace ba lallai bane dauɗar ciki bane amma ban taɓa kawo cewa ciki gare ki ba" kallon shi kawai nayi kamar ba shi kaɗai yai ta mitar dauɗar ciki gare ni amma wai yanzu kuma ya canza zancen
A hanyar gida ya tsaya ya siya min kwakwa ta wannan karon harvda dabino ɗan agadas don kwakwa da dabino ba dai daɗi ba ga daɗi a baki ga aiki a jiki 😉
Mun koma normal life ɗin mu amma yanzu gabaɗaya zaman garin kanobya fita raina don haka ko wannan zuwan da aliyu yayi sai na tuntuɓi ko yana sha'awar mai da mu abuja
Rungume ni yayi sosai wanda har sai da naji ɗan zafi a rungumar tasa daga gani in ya tafi yana kewar mu ba kaɗan ba
Ana gobe zamu tafi muna zaune a falo duk na gama haɗa duk wani kayana yara ma sun yi bacci muna ɗan kallo aliyu yana zaune ni kuma ina kwance akan cinyar sa sai nace
"habibi ina da wata alfarma ɗaya"
"anything 4 u habibti"
Kamar bazan yi magana ba sai kuma na buɗe baki na
" ina mahaifiyar ka" shiru yayi kamar yana nazari
"wallahi ban san inda take ba"
" baka ganin ya kamata mu neme ta"
"kina son ganin ta ne" gyaɗa masa kai nayi
"in shaa Alƙah zan nemo ta ko don ke, amma ganin ta zai yi wuya tunda bansan komai nata ba sai sunan"
"ba komai in shaa Allah zan taya ka"
"no sweetheart just concentrate on dis" ya faɗa yana dafa min ciki na
"Ok buh promise me to look 4 her soon"
"in shaa Allah habibti"
Muka ci gaba da hirar mu har lkcn bacci muka koma ɗaki muka kwanta sai da safe
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:46🌹
Kashegari da wuri muka fara shirye shiryen tfy ƙarfe 8:00am muna airport, domin hawa jirgen da zai kai mu birnin tarayya abuja, aliyu ne ɗauke da mohd inda ni kuma na riƙe hannun haidar, tj ne ya rako mu airport, sai tsokanar aliyu yake yi
"ɗan uwa nan gaba in aka kuma daka maka yajin nan gidana zan kawo yayata in ɓoye ta" shiru mayi banɓtanka musu ba don maganar ba tawa bace
Shima aliyu be tanka masa sai ma cigaba da yayi da anfani da wayar sa wacce take hannun sa tun da muka shiga motar ko me yake yi da ita oho
mun hau jirgi lfy mun kuma sauka birnin tarayya ƙalau muka kama hanyar gida, Alhamdulillahi na je na samu gida kamar yadda na barshi tsab da shi, sai ma ƙarin gyara daya samu
Hankali na a kwance na ci gaba da tafiyar da hidimar gidana ba tare da wani matsala ba muna waya da su iya sosai ina jin halin da suke
idan akwai wani taimako ko wani sabga ta tashi suna faɗa min zan faɗawa aliyu shi kuma sai ya aika musu da abinda ya samu
gaskiya aliyu ya canza ba laifi don ya fi da, matsalata ɗaya dashi yanzu na rashin ƙara yi magana akan neman mahaifiyar sa
ko da irin nayi masa magana akai sai yace shi ya ki kyautata zaton ta mutu, amma ina ƙara ƙarfafa masa gwiwar akan ya neme ta
rannan muna zaune aka kira shi a waya cewar an samu me irin sunan mmn nashi, sai yasa aƙara bincike sosai akanta
amma abin mamaki sai aka gano ba ita bace, na ɗauka zanga hankalin shi ya tashi ko be ji daɗin abin sai na gan shi je ia very calm kamar ba abinda ya faru wannan abun ya bani mamaki don haka sai na tunkare shi in dalilin shi na nuna ko in kula
"habibi kamar bakayi baƙin ciki daya kasance ba ita ce mmn ka ba ko" murmushi yayai ya juyo ya kalle ni
"na rantse miki da Allah ko kaɗan bana son haɗuwa da ita"
"me yasa"
"saboda ita ma ɓa ƙauna take yi ba"
"ya akayi kasan hakan"
juyowa yayi sosai ya kalle tare da riƙe min hannuna
"habibti matar da ta yarda ni ta gudu ranar da ta haife ni kina ganin zata kuma biɗa ta, kin san me yasa ta yadda ni"
girgiza kaina nayi don ni a labarin daya bani kamar ƙuruciyace take ɗawainiya da ita a lkcn
"ta yarda ni ne don ta manta da ni da kuma mahaifina, inda ta yarda ni ko don wani abun ba wannan ba ya kamata ko so ɗaya ne ta neme ni amma ko da wasa bata taɓa tunanin in ɗan jaririn dana ajiye ba" maganar shi akwai ƙamshin gaskia
Fisabilillahi abinda mijina ya faɗa gaskiya ne amma tunda sulhu nake neman yi da shi da mahaifiyar sa sai na kaɗe baki nace
"Akodayaushe ka kasance me yiwa ɗan adam uzuri, ina lefin mu neme ta in ta nuna da gaske so take yi ta manta ka ɗin is fine by us in kuma wani uzurin sai muyi mata ko"
Kina ganin akwai uzurin da zai sa mace taƙi neman abin da haifa har zuwa shekara 30+ kina ganin akwai irin wannan"
Rasa bakin magana nayi don gabaɗaya maganar shi tafi tawa gaskiya haka na haƙura na sakko tare da cewar ni dai don Allah kawai ya neme ta don ni, yai min alƙawarin zai neme tan don amma idan ta nuna bata son mu'amala da mu bazan ƙara tada zancen ta
Na amince sannan yace min zai sake sa waɗan su su kuma bincika masa ita, godiya nayi masa sosai inda ya katse min tare da cewar
"kede kiyi fatan kada Allah yasa ta watsa miki ƙasa aido in kun haɗu"
"amin kawai nace tare da rungume ni
*****************
Tafiyace ta kama aliyu china inda ya nemi mu tafi tare ni kuma na nemi alfarmar in ɗauko ƴar autar mu mu tafi tare saboda da yara zamu ni kuma in fama da kaina
Aliyu be musa min ba yace mu tafi da hannatu ma ta dinga taimakawa aminar kula da yaran
Mama na kira na shaida mata tafiyar da zamuyi da amina, murna a wajen mama kamar me, ta haɗa amina ta hankaɗo min abuja, passport akayi masu ita da hannatun muka shiga neman visa barin ƙasa
Tun da amina tazo sai ta shaƙu da yaran sosai komai itace take musu tare da taimakon hannatu, kullum zaka tsince su ita da hannatun a tare ko a kitchen ko a ɗakin yaran wannan ne ya sani sakin jikina
Visar tamu bata fito ba ko ince tasu amina don tamu ta fito tun yaushe, aka aiko wa da aliyu gayyatar bikin ƙarasa sanin juna na masu manyan jiragen ruwa na duniya, tare da haɗin gwiwar masu manyan kamfononi na duniya, kasancewar ɗaya baya iya ci gaba da sai taimakon ɗaya
Taro akan sanin juna tare da sanin kan abinda ya dace ayi tare da gina kyakkyawar mu'amalat tsakanin masu company da masu yi musu dakon kaya zuwa garuruwa wanda sai kana da babban matsayi sannan za a gyace ke
A england za ayi, a garin man city, yaron aliyu na can ya kira shi don an bada iv ɗin har da aliyu kasancewar an san shima yana da manyan jiragen da suke shige da fice da kayayyaki
Ko da aliyu yaji saƙon sai yace wa da yarin nasa shi ya wakilce shi don shi bazai iya zuwa ba zai je china
"sir wannan harkar fa ta manya ce, manya manya ne na ƙasashe zasu taru, wannan zai bada damar ka haɗu da manya kaima ka ƙara bunƙasa taka harkar"
"shiyasa nace kaje"
"sir ai wannan dole sai kai, kasan manyan nan sun fison su haɗu da mutum in person"
"in son zanje china ne ni da iyalina faa"
"haba sir tun yaushe kake wannan harkar, wannan ai kamar dama ce muka samu, tun yaushe muke wannan harkar amma bamu taɓa samun daman irin wannan ba, kaga wannan damar zata sa ka ƙara bunƙasa sunan ka da kuma harkar tamu, muma adinga dama wa da mu" shiru aliyu yayi amma shi san zuwa england ɗin nan beyi masa be
Duk da duk abinda peter yake faɗi gaskiya ce ze kasance dama ce gare shi ya ƙara faɗaɗa harkar sa, barin ma ya haɗu da masu manyan kampononi kala kala, tunda yanzu iyakacinsa, ya kai ɗanyan mai china da america, ya ɗebo kaya daga china, america, thailand, saudiyya sai dubai
Amma hanyan zu be samu chance ɗin da jiragen sa zasu dinga duniya da kaya ba duk da dai cewar yana da jirage masu girma da ingancin da zasu dinga iya zaga duniyar tare da kwasar kaya ko a ina da kaisu duk wani loko da saƙo da duniyar
"ok peter make the preperation i will be there in shaa Allah"
"inn jaaa Allah" inji peter
"i will be coming with my family and my wife's sister so look 4 a comfortably hotel 4 us"
"yes sir"
Ko da aliyu ya kashe wayar sai ya gayawa zainab cewar sai sun fara biyawa ta england domin ya halacci meeting ɗin kafin su wuce china
Da farko bata so hakan ba don ita bata da wani buri daya wuce ta gansu a china don aliyu ya je ya kuma ganin dr. sa don tana lure da shi yana fama da zuciyar sa kawai ɓoye mata yake yi, amma tasha farkawa da daddare ta ganshi a zaune riƙe da ƙirjin sa yana salati
Sam ita bata san wannanɓhali irin na mijinta ba, ace mutum yana ciwo amma ba zai je asibiti ba shine ma dalilin da yasa ta ce zata bishi chinar amma in ba haka ba me ze kaita birnin sin da wannan cikin duk da dai har yanzu be fi wata uku ba